Showing 189001 words to 192000 words out of 244445 words

Chapter 64 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16492

ya yi bai jira an basa izini ba ya tura k’ofar d’akin nata ya shige…a nan ya tarar da Yasssir.Yana shiga Yassir d’in ya fara murmushi ya taso ya nufi bakin k’ofar inda Junior ya ja ya tsaya,kamar zai yi
hugging d’inshi haka Yassir d’in ya matso shi yana cewa”My best Man!Our savior…”

Daddagewa Junior ya yi ya zuba masa naushi yana huci.
D’agowa Yassir ya yi yana dariya ga jini yana zuba daga hancinsa dan ya fasa mishi hanci,yana murmushin yace”My pleasure!”

Tsaki Junior yayi bai
damu da ya sake bi ta kan Yassir ba ya k’arasa ya kamo hannun Kausar ya d’auko sirinji

Cikin rashin fahimta tace “me kuma za ka yi??”
“Test zan kuma yi”
Kawai yace mata
dan ya tsaneta.

Matsowa Yassir ya yi yace
“Ki barshi ya d’auka,ba komai ai.Kawai dai ka tabbatar ka sake kawo result d’in 12 days
besides y do you even need it?tunda ka riga ka san k’arya za ka sake rubutowa??”
Ya fad’i hakan yana mai dafa kafad’arshi.

Juyowa Junior yayi ya zuba mishi ido fuskar nan tamau!!
kafin ya tunkud’e hannun Yassir d’in.
Already ya gama d’aukar jinin dan haka ya tartara komai ya fara k’ok’arin juyawa.


“Oh no!
Haba Junior
U and I are best friends fa
Ba zan iya tolerating wannan attitude d’in daga bestiena ba
Haba mana! you of all people ya kamata ace ka san ba zan tab’a exposing
Nak***ss d’inka ba kawai dai na san za ka yi mini abunda nakeso idan ka ji na fad’i hakan,na san hakan shine kad’ai abun da zan yi in iya controlling d’inka which is the reason da ya saka na ajjiye video d’in dama in the first place saboda ban san me gobe ta k’unsa ba,but daga yau ba zan k’ara ba tunda na ga ranka ya b’aci sosai!!na ma
goge video d’in!!Forgive me
Pretty please!!”
Ya fad’i hakan cikin had’e hannuwansa biyu waje d’aya sannan ya yi kalar tausayi da fuskarsa.

K’ura masa ido Junior yayi
shima Yassir d’in shi yake kallo da serious face kafin dariyar da ta taso masa ta samu nasarar kufcewa bayan ya fara fesar da ita a hankali
a hankali da farko.

Kauda kai kawai Junior ya yi cikin fushi ya juya ya nufi k’ofa zai fita.Da sauri Yassir ya bisa ya rik’o hannunsa
yace”Pls mana!!
I’m serious I’m sorry..so sorry
truce???
Ya fad’i hakan yana mik’o masa hannunsa alamun su yi musabaha.
Juyowa Junior ya yi kafin ya kalleshi yace
“Na san ba ka goge ba!.
U want truce?”
Ya yi mishi tambayar yana kallonshi.

Da sauri Yassir yace
“Yes,Wallahi.”

“I need u to delete it,
ba ma na buk’atar dole sai na ganka ka yi deleting dan na san za ka iya sake yin kmr ka goge bayan baka goge d’in ba,kawai inaso ka goge tsakanin ka da Allah da kuma darajar friendship d’in da yake a tsakani na da kai!
Dats all I’m asking for Yassir
This might be a joke to you
but to me! it’s not a joke.”

Numfashi Yassir ya fesar ya saka hannuwanshi duka biyu a cikin aljihu cikin yin serious sosai da fuska shima yace
“Actually this is no joke to me either,I’m morethan serious.
Sannan video d’inka is safe Junior safe with me
Me alone
Untill u try to tell the truth…..”

Yadda Junior yake ji kmr ya rufe Yassir da duka ya b’ata komai ne ya sanya shi juyawa kawai da sauri ya fice daga d’akin ya banko musu k’ofar ransa a mugun b’ace.


Yana fita Kausar tace”ka san dai Abotar ku ta lalace forever ko?”

Sai a lokacin Yassir ya juyo,inda take ya nufa ya zauna a gefenta ya ruk’o hannunta a hankali yace”I don’t give a f**k!!ki manta da shi kawai mu duba kanmu first a ko da yaushe
In ba haka ba akwai matsala.”

Numfashi ta fesar tace”yeah nima ba wai damuwa na yi da shi ba kawai dai gaya maka na yi sannan ko komai ya yi settling ya wuce don’t trust him ever saboda zai iya cewa shima bari ya rama.”
Cikin kawar a zancen Junior d’in ta d’aura d’ayan hannunta a kan nasu ta damk’e da kyau tace
“Thankyou Yassir”
Murmushi ya yi kafin yace
U re welcome
Sweetheart…ai I’m doing it for us…”

Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin ta kusa kwafsawa ya sa ta d’an yi murmushi ta kawar da zancen tace “ya akayi da masu evidence?”
Sai da ya fesar da iska tukunna yace “da farko 5m suka buk’ata, da kyar muka tsaya a three, na tura musu 2 gaba d’aya kud’in accnt d’ina kenan yanzu saura 1.Sun ce dai sun ma riga sun goge but kin san halin Irinsu 2 hours suka bani in tura musu cikon ko su sake yi mini b’arna.
Gyara zama ta yi tace “a drawer chan akwai sark’ata,ka d’auka ka saida sai ka cika musu a samu a wuce wajen.….”

Jin jina kai ya yi yana jin babu dad’i kafin ya ce”inshaaAllah zan siya miki dozen d’in ta.”
A hankali ta yi wani d’an guntun murmushi ta zuba mishi ido ba tare da ta ce komai ba.
Shima itan yake kallo kafin ya fesar da numfashi yace”bara in tafi… kafin ma wani ya shigo
d’akin nan a ganmu tare a san ba haushin ki nake ji ba!”

Murmushi duk sukayi shi yana jin tsananin k’aunarta tana ratsashi ita kuma tana jin tausayinshi kad’an dan ba ta san ya zai ji ba idan ta auri Yashjub…..

Sark’ar ya d’auka har da receipt ta bashi suka rabu bayan yace mata duk abunda take buk’ata ta kira shi …..

Yassir yana fita Yadira ta kira ta tace”Junior yana jiranta a k’asa Daddy yace scanning mai kyau yake so a yi dan haka ta fito su tafi…

Hakanan ta shirya ta fito bayan sun yi waya da Yassir ya ce”ta je,ba komai..shi har ya kama hanya yana so ya gama da masu evidence da wuri.”

Har suka k’arasa office d’insa babu wanda ya cewa wani uffan…Yassir kam ya tura masa messages sun fi biyar duk threats…
Lucky for them colleague d’insa ba ya nan dama office d’in nasa na cikin asibitin su biyu ne kawai shi da wani d’an India.

Rai a b’ace haka ya yi scanning d’in…yana fara scanning d’in kuwa ya ga cikin ya fi 2 months kamar yadda ya yi lissafin d’azu a gida.
Gashi dai ciki k’ato amma ya na ji yana gani ya dank’ara 2 weeks a jikin report da conclusion amma ya san tabbas ko Yasmeen in ta gani wata rana sai ta gane…shi
kuma da gangan ya bar shi a haka ya bar komai b’aro b’aro
Atleast ya bar hint kuma ko ta kwab’e by then ya san ba shi da case da Yassir,hopefully.

Suna gama scanning d’in ya mayar da ita gida shi kuma ya koma domin ya kammala had’a result d’in jinin da ko tab’a jinin bai yi ba saboda kamar yadda Yassir ya fad’a no need na jinin tunda k’arya zai rubuta.



Har dare gidan shiruu kowa ko
dinner yau kam babu wanda ya tab’a kowa da abunda ya damesa su Mommy kuwa kamar an yi musu bushara da gidan aljannah dan haka suka sake k’aimi wajen aikin da suka saka a gaba kwana biyu inshaaAllah yau za ta tunkari su Daddy da maganar auren Yash da Kausar tunda gashi komai ya zo musu da sauk’i sun samu hujja….a da tace ba za ta bari Kausar ta auri Yashjub ba amma Manubiya ce ta farkon da ta fara fusatata dole ta yi using Kausar ta taimaka musu su kawo k’arshen Manubiya. Another reason d’inta shine da ta zauna ta yi tunani duba da yadda Daddy ya chanza mata abubuwa suka fara rinchab’ewa ya sa ta ga dole fa ta tsaya a kan Kausar d’in ta auri Yashjub,atleast susamu su samu abunda suke so in yaso daganan ba sai Kausar d’in ta san me suka shirya ba cikin sauk’i za su zagayeta su yi abunda ya dace ba tare da ta san su d’in ne ba,kuma ta san a yanzu idan ta taimaki Kausar to za su shirya komai zai gyaru tsakaninsu za ta daina ganin kamar ba ta so ta taimake ta ne.Daganan sai ta taimaka mata itama dan akwai aikin da take so Kausar d’in ta yi mata bayan ta auri Yashjub a kan Daddy,ta hakan ne kawai take ganin abubuwa za su gyaru a yadda ya birkice kwana biyun nan…………


Yashjub kuwa waya ya yiwa Manubiya yace mata”wani abu ya rik’esa…ta yi hak’uri idan ya dawo zai yi mata bayanin komai.”
Sam bai ji alamun ta ji haushi ba instead addu’ar fatan alkhairi da samun nasara ta yi ta yi masa daga haka suka yi sallama dan ta ji yanayin sa kamar yana gaban su Daddy…shi kuwa tunda ya shiga side d’in nasa wani Irin zazzab’i ne ya lullub’esa.
Suna gama wayar ya lumshe idanunsa daganan wani Abu kamar bacci kamar suma ya dannesa ba shi ya samu kanshi ba sai da gari ya yi duhu sosai….yana duba time ya ga har an idar da sallar isha…dan haka ya mik’e da sauri ya nufi bathroom yana istighfari…zazzab’in da ciwon kan sun sauk’a dan gashi har yana iya tafiya sakamokon d’azu da ya kasa tashi ma amma fa sharkaff yake jinsa cikin gumi shiyasa yana shiga bathroom d’in ya sakar wa kansa shower yana jin yadda zuciyarsa ta shiga dagulewa dan tashi d’aya komai ya dawo masa sabo…….

Sai da ya idar da sallolin yana cikin karatun Al’Qurani,kiran Daddy ya shigo wayarsa ya ce “ya zo yana son ganinsa kafin ya wuce gida.”



Sama sama hayaniya ta fara tashi a cikin gidan kafin ta karad’e ko’ina.
Ko ba a fad’a ba ansan Kausar ce dan ga muryarta ana ji
dan haka duk suka firfito parlourn saman….

Akwatuna wajen ashirin suka gani a jejjere…

Dafe Kai Hajiya mama ta yi
kafin ta k’arasa inda suke tsaye Yassira ta rik’e mata jakar hannunta ta hanata tafiya ita kuma Kausar d’in tana k’ok’arin kwacewa tana kuka tana cewa”ki bar ni in tafi
kowa ya samu salama.”


Hajiya Mama tana zuwa ta fincike jakar daga hannun duk su biyun ta yar kafin tace “Yanzu ke ashe rashin tsoron Allah n naki har ya kai haka?
Apart from tashin hankalin da kika saka mu a ciki throughout
shine kika sake cin wani burin hana kowa bacci??.
Ki wuce ki shige ciki kafin gobe da safe a san yadda za a yi da ke!”.
Ta fad’i hakan tana mai juyawa za ta koma inda ta fito.


Cikin kuka Kausar tace
“Eh ai dole ku ce in zauna…in zauna a ci gaba da aibanta ni sannan kowa yana jin haushina ana bi na da mugayen tunani da sharri!.
Haba Hajiya mama
Ni ce ma na saka ku a cikin tashin hankali
Ba ku ba??
Ni na yiwa kaina cikin??”.

Cikin tsananin fushi Hajiya mama ta juyo tace”idan ba ki
rufe Baki kin daina zancen
ciki da ni ba sai na fasa miki Bakin wallahi!
Shegiyar Yarinya mara kunya
kawai!.”

Fashewa Kausar ta kuma yi da wani sabon kuka
kafin tace”Eh tabbas kam!!na ji na kuma yarda ni shegiya ce
amman kuma yanzu ai ga shege zan haifa muku!jikanki!.”

Duk yadda Hajiya mama ta so daurewa kasawa ta yi sai da ta juyo a fusace ta kifawa Kausar mari!

Da kyar Yassir wanda suka yi da ita akan za su yi pretending kmr yana fushi da ita na y’an kwanaki,ya iya danne kansa.

Cikin fushi Hajiya mama tace
“Like I said ki koma ciki
kafin zuwa gobe in gama tunani”.

Cikin kuka Kausar tace
“Ni kuma na k’i yarda in k’ara kwana d’aya a cikin gidan nan!.
Haba mana! wai shin maraici da rashin uba hauka ne??
shikenan sai a dakeni a hanani kuka?
ce muku akayi Inada burin in haifi shege??.

Bari ki ji in gaya muku
last miscarriage d’ina
Likita ya tabbatar mini in har na sake samun wani fitar cikin to mahaifata ba za ta sake rik’e ciki na tsawon wata hud’u ba!meaning ba zan sake haihuwa ba!.
Tun daga ranar na riga na yanke na gama tsara rayuwata
yadda zan kula da kaina da yadda zan yi aurena in haihu sai dai kash!!!tashi d’aya bagatatan Yashjub ya tarwatsa mini tsari da duk wani abun dana shirya.

Amma dukda haka kaff cikinku babu wanda ya duba yadda akayi raping d’ina haushina ma ake ji da hantarata da kyarata saboda bani da kowa ba ni da gata ko??.

Kowa in banda cin fuska ba abunda yake mini a cikin gidan nan safe da dare dan haka na gama tsarawa zan tafi kuma
rest assure idan na fita kowa sai ya san abunda ya faru dan babu wanda zan b’oyewa kowa sai ya san wannan d’an Yashne
Daganan kuma ba za ku sake ganina ba
Ni ko d’ana.
Tunda dama abunda kikeso kenan na yarda zanyi rayuwata ni kad’ai tunda dama bani da kowa”.

Da sauri Mommy ta matsa inda take ta yi hugging d’inta cikin
kuka tace
“Kausar u have me
Kinada ni ga y’an uwan ki
Kinada gata mana Kausar.”

“Kar ki yi mini haka Mommy
kar ki kashe mini guiwa
Ki ci gaba da fushi da ni kmr yadda kika d’auka da
farko hakan zai fiye miki.”

Zuwa yanzu kowa ya hallara har Yashjub wanda Daddy ya kira yace ya zo yana son ganin sa kafin Kausar ta fara dramar tata.

Tabbas Mommy tana son Kausar da gaske shiyasa ta sake fashewa da kuka cikin
kukan tace
“Ke nake gani na ke jin sauk’in rashin y’ar uwata Kausar idan kika tafi kika barmu ni da Larai
kin san ba kiyi mana adalci ba.
Haba Kausar ya zaki yiwa uwar da ba ta san komai ba sai k’aunarki haka??”

Hawaye ita ma Kausar d’in ta share tace
“Mommy na san kina sona
amman anzo gab’ar da a cikin gidan nan nan da y’an kwanaki dole ki zab’a Ni ko d’aya a cikin y’ay’anki kuma na san dole Yashjub da farin cikin sa da rufar asirinsa za ki zab’a tunda ba zai tab’a yarda a haifi cikin nan ba saboda abubuwa dayawa ni kuma saboda mahaifata da aka ce za ta lalace in na kuma zubar da ciki
Wallahi ko sama da k’asa za ta had’e ba zan zubar ba!.
Besides in banda gori da masifa da bak’ak’en maganganu babu abunda nake janyo miki a cikin gidan nan fa
Na gode da yadda kika tsaya tsayin daka akaina kika bani gata but lokaci yayi da ya kamata nima in tsayawa kaina
shekaru na sun ja
Uwa ce ni so I can take care of myself and move on…..”

Gaba d’aya har Yadira kan Kausar suka rufa suka shiga lallab’ata amma ta birkice furr ta dage akan “itafa sai ta bar gidan”,su kansu sun tsorata da Lamarin nata ballantana su Daddy

Ba abunda yafi daga musu hankali Irin yadda ta rantse ta sake rantsewa akan idan
ta sa k’afa ta fice ba wanda zai
sake ganinta ko ita ko d’an da za ta haifa tunda babu wanda yake buk’atar su.

Tsaki Hajiya mama ta yi tace”ai sai ku yi”
Daganan ta juya ta wuce ta nufi d’akinta ta shige ta banko k’ofar da k’arfi.

Sai a lokacin Abhi ya matsa
kusa da ita yace”Kausar ki je d’akinki ki zauna..zuwa nan da
2 hours zan neme ki,in decision d’in da na yanke still bai yi miki ba sai ki tafi babu wanda zai tsayar da ke.”

“Kausar plss..Listen to us
b’acin rai da zuciya ba abunda yake janyowa sai da na sani!.

Fushi ne mukayi dake na y’an lokuta amma yanzu komai ya wuce..kar ki yi punishing d’inmu ta hanyar rabuwa da mu har abada
Muna k’aunarki ke d’in y’ar uwarmu ce jininmu ce!.”
Cewar Yasira


Shiruuu kowa ya yi
kafin Kausar ta juya kawai
ta wuce ta koma ciki ba tare da ta kalli kowa ba,ranta fess!!
Ba abunda ya fi yi mata dad’i irin zuwan Yashjub kuma ta tabbata maganganunta sun yi tasiri a kansa duba da yadda ta ga ya tsaya yayi shiruuu
a stairs d’in ya ma kasa k’arasowa saman.
Tana shiga ta rufo k’ofar ta da sauri ganin su Yasira sun biyota suna shirin shigowa suma.

Dama Mommy bataso ayi abunda ta shirya ta kuma gama tsarawa a gaban Hjiya mama dan ta san idan sama da k’asa za su had’e ba za ta tab’a yarda ba
Shiysa ta yi godiya ga Allah da ta ga tunda ta shiga ciki bata sake ko lek’owa ba.

Daddy Abhi sai Yashjub wanda Abhi ya k’arasa ya ja hannnunsa ne suka nufi saman,dan haka da sauri jikinta har yana rawa ta bi bayansu.

Suna shiga parlourn Daddy itama ta kutso
Kai bakinta d’auke da sallama.

A fusace Daddy ya juyo yace”the last time da kika hawo mini side d’ina me na ce miki???”

Cikin in Ina tace”Haba Daddy meeting fa za a yi wanda ya shafi rayuwar d’aana dole ka ganni a nan mana sabo…”
Cikin katseta da b’acin rai sosai yace”za ki b’ace mini daga gani ko sai na yi ball da ke??”
Hawaye ne suka b’alle mata kamar an kunna famfo..
Cikin son tura mata wani bak’in cikin ya matso kusa da ita yace”da ke da frame ba ku da maraba a cikin gidan nan bi ma’ana sai dai a kalle ki ki kalli mutum shi kenan amfanin ki!.

Daga yau! ko da wasa na ganki a wajen da ake serious maganar da ta shafi ni ko y’ay’ana Wallahi ranki sai ya yi masifar b’aci bana buk’atar ki a cikin komai nawa! ko yunk’uri kika yi na son shiga cikin maganata ko ta yarana wallahi bak’anta mini rai kike yi.!
Tsabar tsaurin ido ko Ummi wadda na damu da ita ba ki ganta a nan ba amma ke k’ok’ari kike yi ki shigo!….”

Da mugun sauri Mommy ta juya tana hawaye kamar ruwan fanfo,bibbiyu haka ta sauk’a daga stairs d’in ta nufi side d’inta inda ta bar Baba Larai tana mai had’a hanya….

Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 38
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.

Ba ta b’oye musu ba dan zuwa yanzu tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login