Showing 18001 words to 21000 words out of 244445 words
ya sanya gaba d’ayansu su ukun sukayi shiru ba wanda ya kawo zancen rashin da’ar Yassir,kowa kawai ya rik’e abun a cikin ranshi kawai.
Su biyu suka tartare
masallacin suka kunna turare
daganan ya Nafi’u ya d’auki jakar kud’in dama shi su Baba suka cewa ya k’arba tun lokacin da Abokin Daddy ya mik’o.
Da sauri kaka Mallan yace ‘’yanzu menene abun yi?’’bai jira an bashi amsa ba ya d’aura da cewa’’ku kawo kud’in akwai
wani Abokina da d’ansa yake kayan d’aki na gani na fad’a kunga sai a basa ya had’a mata komai mu samu mu fita kunya itama yarinya ta fi k’arfin gori kar ku biyewa Mahifinsa dan ya ce kar a kawo komai ya zama dole mu yi mata ko dan mu fita kunya.’’
Da mamaki Ya Nafi’u yake kallonsa daman tun d’azu ya k’ule da behaviorn da kaka Mallan d’in yake yi a gaban su Daddy gaba d’aya ya basu kunya sai wani zumud’i yake yi,shiyasa yana shirin ci gaba da magana yanzun Ya Nafi’u yace’’dakata Kaka Mallan
da kai da wa za ku fita kunya??’’bai jira jin amsar shi ba ya d’aura da cewa’’besides what are u even doing here?’’
Da sauri Baba Habu ya juya
ya fice gaba d’aya daga cikin masallacin
Cikin takaici ya Nafi’u yace
‘’Ba kai ka ce ba zaka zo ba jiya?ina har hantarar mu ka yi da muka je gaya maka?’’
Cikin fushi kaka Mallan yace
‘’Ka ci ubanka Nafi’u!ashe baka da hankali?banza d’an
karere kawai’’
Da sauri ya Musbah yace
‘’A’a kaka Mallan Nafi’u kam ba d’an karere bane a wannan lamari a ko wanne lamari ma na rayuwarmu Nafi’u ba d’an karere bane dan ya yi mana uwa da uba’’
Salati kaka Mallan ya rafka kafin yace ‘’Musa kana ji abunda suke yi min ba za ka
ce komai ba?’’
Sai kuma ya fashe da kuka daga nan kawai ya juya ya fita
yana cewa ‘’Dama amana nakeso in rik’e ammanm tunda bakwaso shikenan,kai musa ubanka yana chan kabari
amman na san an haska mishi wanna son datse zumuncin da kake k’ok’arin yi’’.
Numfashi Baba ya fesar ya girgiza kai yana msmakin yadda sam kaka mallan
ba shi da lissafi baya jin
shakkar ya ji kunya ko ya zubar da kanshi indai ta b’angaren abun duniya ne.
Kuma ya tabbata inda gari banza ne Nafi’u ya yi masa haka ya san da sai ya tara musu jama’a ya yi musu tijira amma dake yaga da akwai abu a wajen su shine ya kwantar da kai har da kuka,a hankali a fili yace’’Allah ya kyauta’’ yana aiyyanawa a ranshi inshaaAllah zuwa anjima zai je ya yi musu godiya da shi da Baba Habu,Allah ya sa su k’are lafiya.
Suna zuwa suka mik’awa Manubiya kud’in ta…kasa karb’a ta yi dan tashi d’aya fargaba da kunya suka rufe ta daga k’arshe ma sai ta saka musu kuka
Murmushi kawai duk aka yi ana kallonsu ita da Jidda da Siyama da Muhsin da suka shiga taya ta kukan.
Ya’ar tattaunawa aka yi su ya Nafi’u suka ce Daddy yace kar azo da komai amma dukda haka tunda ga kud’i nan ta samu sai a siya mata gado mai kyau da tsada da shi,Shi kuma da Ya Musbah da Baba za su siya mata y’an kayan kitchen dangin su flask sannan za su yi y’ar walima.
Kowa yayi amannah da hakan banda Manubiya sam ta k’i yarda a yi hidima ko wani kayan daki,dan ko da su ya Nafi’u ma suka fita cewa
tayi’’kud’in a barshi kar a siya mata komai,za ta bawa Baba ya Nafi’u da Ya Musbah jari bayan auren da shi.
‘Dama ta shirya za ta gayawa Yashjub ba za ta zo da komai ba to kuma yanzu tunda iyayenshi sun buk’aci hakan to Alhamdulillah’’
Murmushi Mama ta yi kafin ta matso ta dafa kanta tana jin
tsananin k’aunar Manubiyan a ranta,za ta iya cewa bata tab’a had’uwa da yarinyar da ta shiga ranta lokaci d’aya ba
kamar Manubiya tanada hankali da hangen nesa,ahankali Mama ta sauk’e ajiyar zuciya bayan ta dafa kanta tukunna tace’’Ba za ayi
haka ba Manu,ba zai yiu mutanen nan su kawo har naira miliyan biyu sannan ga sadaki a gaba da zasu kawo
amma kice ba za’a kai ki da komai ba,ni sai naga rashin dacewar hakan’’ta fad’i hakan tana mai juyawa ta kalli Inna kafin tace ‘’ko ya ki ka ce??’’
Lumshe ido innar ta yi ta bud’e alamun eh sannan a hankali ta d’an yi murmushi,murmushi suma duk suka yi kafin Aisha tace ‘’Nima na bi bayan su inna
gaskiya Manubiya kamar yadda baban khairat yace ya kamata ko gado wanda za ki saka a d’akinki d’an waje mai kyau a samu a siya miki,ki je da shi,ba dan komai ba ko dan kema ki dinga gani kina jin dad’i sannan atleast muma zamu ji dad’i bamu kai ki haka ba komai ba kuma ke kanki kin wuce gori,dukda dai na san a yadda suke da kud’in nan ba lalle su yi k’arancin tunani irin na k’ananun mutane ba
amman fa y’an uwanshi mata fa su shida yace miki ko?kinga kuwa ai mata ba‘a rabamu da k’ananun maganganu ba,dan haka gara kawai ki bari ayi miki wani abun su Baba Allah zai duba su suma’’.
Dasauri Siyama tace ‘’Nasan ma zai bawa ya Musbah aiki shi mijin naki inshaaAllah’’
Murmushi Aisha tayi kafin tace
‘’Ban d’au wannan akai ba
amman dai in ya bayar Alhamdulillah’’
Ba yadda Manubiya ta iya haka nan ta yarda ba dan ta so ba amma dukda haka sai da aka ware duba d’ari d’ari
akan zata bawa ya Musbah d’ari ya Nafi’u d’ari Baba d’ari
sannan ta ware kud’in saka Muhsin a makaranta,ba dan
Mama da Aisha sunso ba haka suka yarda suka yi respecting decision d’inta.
Still Manubiya ba ta so ba amma sai da su Siyama suka fitar da anko,ba yadda ta iya haka ta yarda ta biye musu ta barsu za su yi ankon atamfa wadda za su saka ranar da za a kaita dan walimar ma
tace’’dan girman Allah su hak’ura tunda za ayi wuni in an d’aura aure kar su d’aurawa kansu hidima da yawa.
Siyama dama tanada d’an kud’in ta dan haka ita da Aisha da Manubiya da Mama suka cikawa Jidda
A take a lokacin Aisha ta fitar musu da atamfar da za su yi aka turawa Siyama a wayarta
akan za ta nunawa anty umma sai kuma sukace zuwa
anjima za su lek’a itada Jidda har side d’in su Uncle duk su nunawa kowa dukda dai an ja layi an musu tsakani amman za su gwada sunsan za su samu lada.
Bayan kamar awa biyu
su Aisha suka tafi kasuwa itada Siyama da Jidda,suna fita Mama ma ta yi musu sallama ta tafi dan tanaso ta
karb’i number wata mata
a wajen Ammi mai sayar da magungunan gyara na mata
InshaaAllah ita za ta yiwa Manubiya uwa,tana tsananin k’aunar yarinyar sannan ba ta samu chance da damar aurar da tata y’ar ba wadda a yanzu tana kyautata zaton ta riga ta yi aure ta ma hayayyafa,dan
haka inshaaAllah za ta zamewa Manubiya uwa ta yi mata duk wani gata,ta
aurar da ita.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 08
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
In da rabo idan Allah ya k’addara za ta ga y’ar tata ta ga jikokin ta Alhamdulillah
In kuma Allah ya riga ya k’addara sun rabu kenan to
Allah yasa hakan ne mafi alkhairi,fatan ta shine Allah ya sa itama y’ar ta ta samu
wadda za ta tsaya mata kamar yadda itama za ta tsayawa Manu da zuciya d’aya tunda itakam ba ta da ikon zuwa
ko da kusa da ita ne ballantana ta kula da ita.
Ba za ta yi counting akan kishiyar ta da ta bari a wanchan gidan ba dukda ba ta tab’a kamata da wani mugun hali ba amma kishiya a duk inda take kishiya ce.Ta san ba za ta cutar da y’arta ba tunda idan ta tuna yadda mijinsu yake tsananin son y’ayansa ta san ba zai bari ba,amma kuma ta san ba za ta tsaya mata ta kula da ita ba kamar yadda ko waccce uwa take yiwa y’arta tsakaninta da Allah dan duk girman y’a mace to tana buk’atar uwa ko wadda za ta zame mata kamar uwa a rayuwarta.
Da yamma lik’is likitar
Inna ta dawo…kamar ko yaushe yanzun ma ba kyama ba komai haka take kula da duba inna da wasu ingina
sannan ta d’an yi mata exercise.Sai da duhu yayi tukunna ta tafi…
Wani abun mamakin kafin dare kusan kaff mak’oftansu Manubiya sai da suka shigo,har k’awayenta da sukayi islamiyya tare ita tama manta da wasu dan ba harka suke yi tare ba tun rabuwar makarantar amma haka suka dinga shigowa suna yi mata Allah sanya alkairi suna
tambayar ta anko da event nawa ne.
Itakam sai dai tace musu’’ba komai ba event’’kawai.
Haka dai suke tafiya suna masu cewa’’idan an fitar ko an chanza ra’ayi za’ayi event d’in kar ta manta da su ta sanar musu da wuri dan Allah’’
Gaba d’aya ita kam ta shiga damuwa idan ka ganta ta yi jigum ta zama so silent.
Sai da hayaniyar ta ragu tukunna ta samu ta aika Muhsin ya je ya karb’o mata wayarta daga charji dan kwana biyu Nepa suna nuna musu hali.
Dama ta san sai ta ga misscalls d’insa dan haka ko tsayawa k’irga wa ma ba ta yi ba ta shiga kiransa dan itama ta yi missing d’insa iya wunin yau da ba ta ji muryar sa ba duk wani iri ta ke jinta,tana tsananin son Yashjub amma kuma ba ta so ta yi aure a d’auke ta a rabata da ahalinta….
‘’Assalam alaiki Matar Yashjub!!’’
Muryar sa ta katse mata tunani,ba ta san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba,dan wani sanyi ta ji yana ratsata daga jin sunan da ya kira ta da shi,
Cikin sanyin muryar a hankali tace’ameen wa alaikassalam’’
Murmushi ya yi kafin yace’’ba ki ce mijin Manubiya ba’’
Shiruu ta yi tana murmushi k’asa k’asa dan haka yace’’ashe wata za ta ganni na zo yanzunnan tunda na san hanya kuma wallahi idan nazo sai k….’’ameen wa alaikassalam mijin Manubiya’’
Ta fad’i hakan cikin tarar numfashinsa dan tana tuna abunda taurin kanta ya janyo mata ranar a asibiti.
Aikuwa murmushi da dariyar da ya shiga yi sai da ya mamaki da dariya itama,kafin chan ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace‘’bana jin akwai sunan da aka tab’a kirana da shi na ji dad’i kamar wannan,da farko da na kira ki fushi nakeyi dake akan cillar da wayarki da kika yi tun d’azu na kasa samunki amman yanzu kam na daina kin yi bribing d’ina da wannan daddad’an sunan,dan sake fad’a mu ji….’’
Sai da ya sake cewa’’plsss mana’’kamar zai yi kuka tukunna tace’’mijin Manbiya’’
Cikin tsananin nishad’i ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin yace’’Allah ya barmu tare Allah ya tabbatar mana da alkhairi’’
Ahankali tace’’Ameen’’
Daganan suka shiga hira Manubiya in banda mamaki ba abunda take yi dan murna da zumud’in da Yash yake yi har tsoro ya fara bata kamar a kanshi za’a fara aure a duniyar nan,wani abun ya bata dariya wani abun ya sata jin kunya,har sunan y’ar su ta farko sai da ya tsayar dan shi yace ‘’ya fi son ta haifa masa baby girl a farko mai kama da ita sak! sak!!InshaaAllah amman in Namiji Allah ya fara basu shima zai yi tsananin murna as long as daga gareta ne babu abunda zai gani next bayan auren su da zai sanya shi matuk’ar farincikin da sai ya kusan suma kamar ya ga jninsa shi da ita,ranar bai san wani kalar farin ciki zai yi ba,yana masifar son yara yana kuma masifar son ta dan haka ta yi imagining kalar dad’in da zai ji idan ya samu babies daga wajenta…..’’
Ita kam Manubiya gaba d’aya hirar ta sa ta fara zama mata uncomfortable dan yadda yake batun soyayyar da zai nuna mata!ciki!da haihuwa!kanshi tsaye ba kara abun ya girme mata tunani gaba d’aya ji take yi kamar ta nutse,shiyasa ta samu ta yi masa wayo tace’’bacci take ji sosai’’dan ta samu ya barta,da kyar kuwa ya barta bayan ya ce mata’’ta shirya gobe inshaaAllah zai zo su d’an fita su sayi abubuwan buk’ata da za ta yi amfani da su a biki’’.Kafin ya d’aura mata da zazzfan ‘i love you’d’in da sai da ta ji sa har tafin k’afafunta da tsakiyar kanta,tukunna suka kashe wayar.
Tana ajjiye wayar ta shak’i numfashi sannan ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi gasar rik’e numfashi.
……
Sai dare bayan sun kammala dinner tukunna Abokin Daddy ya yi musu sallama ya tafi,ko cikin gida Abhi bai bari sun shiga ba,anan garden d’in inda suka zauna da Abokin Daddyn yace wa Daddy’’ya tsaya za su yi magana’’.
Murmushi kawai Daddy ya yi dan dama ya lura da yanayin Abhi tun d’azu shiyasa ahankali tun kafin Abhi ya ce wani abun ya dafa kafad’arsa yace ‘’Abhi
da mai kud’i da talaka duk Ubangiji ne ya haliccesu,
Yashjub yarinyar ya nuna yana so itace zab’insa,namu kawai mu yi supporting d’in shi mu aura masa ita ko da kuwa a bukka take’’
Cikin katse shi Abhi yace‘’seriously???talaucin
nasu is too much,Yashjub is way too rich ya je wajen ta’’
Numfashi Daddy ya fesar kafin yace‘’and yet he did,so dan Allah Abhi kawai mu yi supporting d’insa.’’ya fad’i hakan a gajiye.
Shiruu Abhi ya yi yana tunani a cikin ransa’’wallahi in da ace ya san irin wannan Yash zai kwaso da ya gwammaci ya yi masa auren dole da y’arsa Naeema yarinyar tana son shi shiyasa ma ta ce ita zata zauna a gida har a yi bikin a k’are dan ba zata iya ganin auren sa ba,baya so ya yi masa dole shiyasa bai tada maganar ba,amma yanzu yana dana sani dan gwara auren dole akan wannan auren da yake shirin yi…..’’
Cikin son fahimtar da shi Daddy yace’’na san kaine a matsayin uba tunda a wajen ka yake karka ga kamar na yi maka shishshigi dan Allah ka fahimceni brother sannan kar ka nuna kamar ba ka so kaje ka bawa Hajiya Mama k’ofa itama ta fara,na san ita ba zata k’i auren saboda talaucin yarinyar ba amma indai taga kana kakkaucewa tashi d’aya zata saka questionmark sannan ta fara cewa itama bata so,ka san kuma na riga na yi musu alk’awari tun ba yau ba kuma nima hankalina sai ya fi kwanciya in ya auri wadda yakeso
sannan
Yash is very obidient baya biye biyen mata s ganina tunda ya nuna wannan yace yana so the best thing da za mu yi shine mu aura masa ita.
A yadda yake son Manubiya hana sa aurenta is the last thing da za mu yi a wannan situation d’in da yake ciki,idan ka lura ba ya shiri da kowa he’s always moody ga kuma Khadijah wadda har gobe ta k’i ta gyara halinta ballantana a samu ya sake da ita…..Abhi farin cikin ya’yannan nakeso
Ingani,idan ni bana cikin farin ciki bai kamata ace suma ba za su yi ba’’
Shiruu kawai Abhi yayi a take tausayin d’an uwan nashi ya lullub’e shi,ya lura tabbas idan suka zubawa Khadijah da Kausar harma da Baba Larai ido tsaf za su kashe mishi d’an uwa da bak’in ciki
tunda ya san ba zai iya yin magana ba kuma ba zai iya aikata komai ba…haka kurum mata ta tattaro gaba d’aya danginta ta tare a gidan tak’i gaba tak’i baya,suna sane da yadda ta hanashi k’ara aure bayan kowa ya san yanaso
sai yanzu da Allah yayi.
D’an tapping shoulder d’in shi Daddy ya yi kafin yace’’yanzu mu je ciki,tunda ka zo ba ka shiga ba ba ka ga amarya ba ma’’.
Girgiza kai kawai Abhi yayi kafin yace‘’idan Hajiya Mama ta zo ma gaisa da ita a tare’’
Yana shirin shigewa Yashjub ya k’araso wajen,tun d’azu da safe da suka fita shi da Najeeb sai yanzu ya dawo…har k’asa ya durk’usa yayi
musu godiya bayan sun gaisa daga nan suka wuce tare shi da Abhi dan a side d’insa dama Abhi ya sauk’a,hakanan da Abhi da Daddy suka yi ta mamakin tsananin murna da walwalar Yashjub d’in ta yau abunda ba su saba gani ba.
Ajiyar zuciya daddy ya sauk’e bayan sun shige kafin ya furzsr da iska a hankali ya lumshe idanuwansa.
…..
Washegari da Asubah around 4:00am Daddy da Abhi suka nufi airport domin d’auko su Hajiya Mama.
5:00am dai dai jirginsu ya yi landing a garin Kano…
Suna tsaye suna jiransu
Daddy ya hango Junior ya karyo kwana
Murmushi Daddyn yayi
kafin yace’’Wai!!ai ban ga
chanjin a hotuna da video call ba kamar yanzu a fili’’.
Da sauri Abhi ya d’ago shima ya kalli direction d’in da ya ga Daddy ya na kallo yana tsananin murmushi…..dogon saurayine wanda a k’alla zai kai shekaru 27 a duniya,kalar
fatar sa bak’i ne irin mai shek’i da kyau d’in nan,ba shi da muni kuma ba za a kirashi da kyakkyawa ba yana da fad’in k’ashi sannan jikinshi a murd’e yake dan kallo d’aya za ka yi masa ta fahimci ya saba da ziyartar gym.
Sanye yake da dogon wando pencil bak’i irin na maza sai bak’in takalmi da farar riga mai gajeran hannu me kama jiki an rubuta ‘lucky trip’a jiki
yayinda kanshi yake cikin hula irin ta sanyi bak’a itama ya d’an tura ta baya kad’an,sai jakarsa bag pack da ya goya da trolly…
Daddy yana cikin k’are mishi kallo ya k’araso daff dashi
yana zuwa ya sa hannu ya yi huggin Daddyn yace
’’I miss u Daddy’’
Murmushi Daddy ya yi ya d’agosa yana mai sake k’are masa kallo kafin yace’’Imam ya gida ya uk ya aiki??’’
Murmushi yayi yace’’Alhamdulillah
Ina wuni’’
Cikin katsesu Abhi yace ‘‘Ina Hajiya Mama?’’
Dariya Junior ya yi kafin yace
‘’Suna chan tana karb’ar number wata mata,wai matar tace mata tana Maganin mayu da asiri shine ta tsaya karb’ar numberta wai