Showing 117001 words to 120000 words out of 244445 words

Chapter 40 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16427

samu Daddy ya bari su yi allurar cikin sauk’i ta ji muryar Yash yana cewa
‘’Ok,d’an bani 2 minutes,’’ sai da ta kalle sa tukunna ta fahimci waya yake yi,sai da ya ajjiye wayar tukunna ya kalli Daddy yace‘’Am Daddy family Dr ya zo
Ince ya bari shikenan tun da kace asibiti za’aje ko?’’

‘’No,bar shi ya shigo d’in kawai tun da ya riga ya zo.Ya’isha je ki shigo da shi
Idan ya tafi sai a wuce asibitin,ba dad’i ka kirawo babban mutum ya baro aiki ya zo kuma a ce ya koma.’’

Wata kalar zufar da ta ketowa Mommy sai da Yahanasu ta ganta b’aro b’aro a kan goshinta tsabar yawan ta.

Cikin in ina da rashin sanin tudun dafawa Mommyn tace
‘’Daddy nake ganin gara a ce ya tafi
Namiji ne bai kamata ya tab’a matar aureba….”

“Ya’isha je ki shigo da shi mana!’’
Daddy ya fad’a da d’an k’arfi kamar ma bai san Mommyn tana magana ba dan ya fara k’ulewa da ita
Ya ga alama tana neman zarce gona da iri tun lokacin da ya goya mata baya a kan case d’in Yashjub da su Yasira ya bata goyon baya ita da su Yasira,ya ga alamar kamar so take ya dinga biyeta akan komai….bayan shi ba wai bayan ta ya bi ba ko a wannan lokacin yana da nasa dalilin shiyasa….

Ganin har ya na shirin fita amma su basu da niyyar fita ne ya sa cikin kakkausar murya ya kalle su yace
“A bar Yahanasu Manubiya Yashjub da Yasmeen a d’akin kowa ya fito….jikin Mommy har karkarwa yake yi zuwa yanzu..
ta riga ta san one more move daga gare ta to tsaf Daddy zai b’aro jirginta shiyasa kawai ta hak’ura ta yi kalmar shahada ta fice ta wuce sama d’akin ta direct.

Ita dai Mannubiya ba da ban Daddy ne da kan sa yace ‘a duba ta’ ba to da babu abun da zai sa ta kuma tsayawa a duba ta dan ba ta son ta sake ganin wani disappoint d’in a idananun Yashjub…

Su Daddy suna tsaye a parlourn Ya’isha ta shigo da Doctor,suna gama gaisawa da Daddy ta wuce da Doctor d’in ta kai sa har d’akin ta fito, itama ta nemi guri ta zauna hankalinta chaaa a tashe.


A Chan d’akin kuwa Dr yana shiga suka hau gaisawa da Yashjub sai da ya kuma yi masa Allah ya sanya alkhairi tukunna cikin zolaya yace
‘’Ai ba wani abun tada hankali bane amai is a normal thing a pregnancy but bara dai in duba .”

Shiruu duk suka yi kafin ya fara dubata sai da ya kuma tambayar abubuwan da suke damunta da date na last period d’inta ya ji tukunna ya matsa kusa da ita
Kamar yadda Yasmeen ta ga alamun cikin a tattare da ita hakanan shima amma bai fad’a musu ba
Instead sai ya zaro pt a cikin box d’insa ya basu yace “gashi ta je ta gwada”

Cikin son fahimtar da shi Yashjub yace “Yasmeen fa ta duba ta yanzu ba ciki ba ne”

Da d’an mamaki Dr d’in ya juya ya kalli Yasmeen kafin yace “da me kika duba ta??”

Dibi dibi ta hau yi kafin tace ‘’ban ji a pulse d’inta ba sannan na ga bp d’inta bai yi kamar na masu ciki ba”
ta fad’i hakan tana addu’ar Allah ya sa kar ya haddasa mata case.
Sai da ya k’ura mata ido sosai
kafin cikin d’an b’acin rai yace ‘’Doctor Yasmeen kin san abun da kike yi kuwa??a bp da pulse dama ake ganin ciki???
What else ki ka yi bayan BP d’in da kika gwada??”.
Cikin nemawa kanta mafita tace
‘’Duk na gigice ne na ga tanata amai I wasn’t myself shiyasa..gaba d’aya duk ta bani tausayi…”

Cikin fushi yace
‘’Really??!,yanzu idan aka kawo miki family member d’in ki in a critical condition Ashe ba za ki iya yin abun da ya kamata ba?are u really this weak!!!”

Ahankali Manubiya ta d’an dafe kanta sakamokon sarawar da yake yi mata tace “wash!!!”
Sai da ya gama watsawa Yasmeen kallo tukunna ya juya ga su Yashjub ya shiga yi musu bayanin yadda za su yi amfani da pt d’in.
Suna wucewa cikin toilet d’in ya juya ga Yasmeen ya shiga yi mata fad’a had’e da yi mata nuni da abubuwan da ya kamata ta fara yi next time idan an kawo mata patient a irin wannan condition d’in Sannan yace ta cire fargaba ta daina saurin giigicewe dan za ta jawa kanta problem dan ko shi tbh yau kam he is very disappointed in her!”

Su Yashjub suna shiga toilet d’in Manubiya ta kalle sa tace
‘’Ko dai za mu ce masa mun yi kawai?
Ba na son gwadawa ni kam har ga Allah.’’
Ta fad’i hakan tana hard’e hannuwanta a k’irji.

A hankali Yashjub wanda ya samu hope da kwarin guiwa daga jin yadda Doctor d’in yace “Yasmeen ba ta gwada yadda ya kamata ba”ya matso kusa da ita yace
“Ki taimaka ki gwada! pls…for me?’’

Shiruu ta yi ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “to ka fita”

Wata dariya yayi yace “Yarinya ba ki da wayo ashe….”

…Daki daki yadda aka nuna musu haka suka yi.
Dayake doctor d’in ya ce “idan sun gwada su ajjiye for five minutes saboda result d’in ya fito sosai”
Ya sa Yashjub ya karb’a ya ce bari ya kai kan window su jira time…..
Daga ita har shi gabansu fad’uwa yake yi
Haka ya nufi window da tsinken da niyyar ajjiyewa idanunsa a kai
Kawai ya ga layi na biyu ya fara kamawa
Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin sa yayi
Da wani irin sauri ya juyo ya koma gareta ya tsaya a gabanta ya ma kasa magana kawai ya kafe abun yana ganin yadda layi na biyun yake kuma fitowa yana turuwa yana dad’a baiyyana.
Ganin yadda ya kad’u sannan ya mayar da kafatarin hankalinsa ga tsinken ne ya sa Manubiya matsowa tace ‘’mai kake kallo?’’k’irjinta yana d’an bugawa.
Ahankali ya d’ago lumsassun idanuwansa da suka cika taf da kwallah ya kafe ta da su kafin ya juyar da fuskar tsinken gareta wanda a yanzu jajayen layuka biyu suka fito rad’au!Hannun ya na rawa ya saita mata shi a dai dai saitin fuskarta a lokaci guda kuma hawayen da suka tarar masa a idanu suka samu damar b’alle masa,a take yayi mata wata mahaukaciyar runguma ya fashe da wani irin kuka…..
Ita kanta Manubiya hawaye ne suka b’alle mata.
A take wani sanyin farin ciki da annashuwa mara misaltuwa ya mamaye masoyan…lamoo ta yi a jikin sa tana hawaye tana jin yadda yake kuka bilhakki da gaskiya jikinsa har karkarwa yake yi sannan zuciyarsa tana wani irin bugu..

Sun jima a haka kafin Manubiya ta d’an fara k’ok’arin zamewa a hankali tace
‘’Godiya za mu yi wa Ubangiji….’’

Ahankali ya sake matseta a jikinsa yace
“Tun d’azu nake godiya,Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ya rabbi…bayan fatar baki da zuciya ina so in yi godiya ga Ubangijina…..’’
Murmushi ta yi a hankali tace ‘ka yi ta sadaka’’
Sai da ya sauk’e wata k’ak’k’arfar ajiyar zuciya ya tsaida kuka da hawayensa da kyar tukunna ya cika ta ya d’ago fuskarta ya yi cupping a cikin tafukan hannuwansa sannan yace
‘’Thankyou Manu,I become complete and happy because of you,sannan gashi yanzu za ki bani gift d’in da na dad’e Ina kwad’ayi,na gode Baby I love you more than life itself….”
Ahankali ya sake sakata a jikinsa ya rungume.
Sun jima a haka yana ji kamar kar ya cikata su tsaya a haka har abada,kafin da kyar suka saki juna ya wanke fuskar sa suka fita.


Fuskar Yash kawai Yahanasu ta kalla ta fahimci kuka ya yi kuma tana da tabbacin kukan farin ciki ne dan haka ta k’arasa garesu da sauri ta had’asu ta rungume cikin tsananin murna tace ‘’congratulations’’a hankali
yayi murmushi ya ce ‘’Thankyou Yaha,‘’wanda hakan ya sake tabbatar mata ai kuwa Baki har kunne haka ta hau murmushi mai had’e da dariya tana jin tsananin farin ciki.
Ita ta k’arba abun gwajin ta kaiwa Dr.

Cike da murna ya matsa kusa da su ya yi congratulating d’insu sannan ya d’aura da cewa “a halin yanzu ba zai ce ga exact weeks na cikin ba amma anytime from now suna iya zuwa clinic d’insa a yi gwaje gwaje a tabbatar da lafiyar Baby.”
A take Yashjub ya ce “su tafi yanzu tare da shi kawai”
Murmushi Dr d’in ya yi yana yaba tsananin kulawar Yashjub ga Babyn da matar sa..sai a lokacin tukunna Yasmeen ta matso tana murmushi ta yi congratulating d’insu
Dariya Yashjub ya yi yace “young Dr! sai na bawa Baby labarin yadda kika kusa d’ura masa allura ai saboda rashin kwarewa…”
Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana murmushi a ranta tana jin kamar ta fashe da kuka tsabar regret da kunya da takaicin Mommy…a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma tana jin wata nutsuwa dan tabbas ta ji dad’in zuwan Doctor if not because of him da tuni ta aikata abunda ita kanta ba za ta tab’a yafewa kanta ba.

Waje suka nufa gaba d’ayansu ban da Mannubiya…

Ba iyaka Manubiya wadda ke daga d’aki tana jiyo su ba hatta Yahanasu wadda dama ba ta so ma maganar ta fito ba,sai da ta ji kunyar yadda Yashjub ya zage yana mai sanar wa y’an parlourn ai Manubiya ciki gareta!.
Har gaban Daddy ya je ya tsaya ya gaya masa cike da tsananin murna da farin ciki..
Sai da ya gama fad’a ya ga kowa ya yi shiruu yana kallonsa a take kuma sai wata kalar kunya ta lullub’esa.
Murmushi Daddy ya yi yana jin wani farin cikin da ya dad’e bai ji ba kafin ya dafa kafad’ar Yashjub d’in yace
‘’Allah ya inganta Allah ya raya ya kawo mana sanyin idaniyar mu duniya lafiya.
Tun da nake da kai zan iya cewa ban tab’a ganin farin ciki irin wannan akan fuskar ka ba.”
Sai da ya d’an k’ura masa ido kafin yace “har kukan murna ka yi ne??”
Ya yi masa tambayar da alamun sigar zolaya wanda
hakan ya sa Yash d’in sake sunkuyar da kan sa k’asa sai kuma ya juya da sauri yace
‘’Bari mu je asibiti’’
Ya fad’i hakan yana mai ficewa waje.
Sai da Yahanasu ta koma d’aki tukunna suka kimtsa suka fito.
Manubiya ta ji dad’in rashin ganin kowa a parlourn dan dama ba ta san ta Ina za ta fara had’a ido da su ba…..



Had’ad’d’en checkup ya sa aka yi mata.
Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya sa akayi masa scanning da taimakon bayanin likitan ya ga location d’in jininsa d’an sati biyu tukunna..
Dr kan sa ya sha kyauta…sai bayan sallar magrib bayan an gama yi mata allurai da k’arin ruwa leda d’aya suka karb’i magunguna tukunna suka nufi gida cike da murna da farin ciki…
Shi yake driving sai Manubiya a gefen sa da Yahanasu a baya.
Sun zage da shi da Yahanasu suna ta lissafin kayayyakin Baby da abubuwan da ya kamata a fara siya…

Murmushi kawai Manubiya ta yi tana sauraron su tana jin wani sanyi a ranta tana kuma sake godewa Allah wanda ya bata Yashjub a matsayin Miji.
Sam murna da zumud’in da ya ke yi a kan cikin ya gagara b’oyuwa,dan ko baka tab’a ganin sa ba tashi d’aya za ka fahimci yana cikin tsananin farin ciki a yau.

Wayar ta ce ta d’auki k’ara, wanda hakan ne ya katse musu hirar ta su
shi da Yahanasu.
Kamar ba za ta d’auka ba
sai kuma ta sa hannu ta d’auka.
Tana nan kishingid’e a yadda take haka ta saka wayar a kunnenta ba tare da ta bud’e idanunta ba tace ‘’Assalam alaikom’’
Ahankali Abbakar ya lumshe ido daga d’ayan b’angaren yace ‘’Wslm Manu,ykk kwana dayawa’’
Shiruuu ta yi ta k’i yin magana ta k’i cewa komai
Cikin yanayin sanyin muryarsa yace ‘’Abbakar ne’’
Yanzun ma shiruu ta yi dan dama tun farko ita ta fahimci shi d’in ne..
Wato sai yanzu zai waiwayeta sai yanzu zai nemeta haka kurum ya d’auke kafa ya yi shutting nata out
sai yanzu zai wani kira ta!.

Muryar sa take ji yana magana amma ba ta fahimtar sa sakamokon aman da ya taho mata tashi d’aya…dan haka kawai ta kashe wayar ta ajjiye a gefe ta d’ago ta kalli Yashjub. Wanda yake mamakin waye ne ya kira ta haka ta gagara cewa komai
Kuma kamar muryar Namiji ya ji yana magana.

Da sauri ta toshe bakinta ta na yi masa nuni da ‘za ta yi amai’
dan haka ya ja ya faka a gefen titin da sauri ya bud’e motar ai kuwa ta shiga shek’awa…
Aman da ta yi sai da ya ba su tsoro tsabar yawan sa.
Ba yadda ba ta yi da shi kar ya koma ba amma haka ya juya akalar motar aka maida ita asibitin.
Suna zuwa kuwa Doctor ya yi admitting d’inta,sai a sannan Yahanasu ta kira su inna ta sanar da su haka ta kira Ummi itama dan ta ji ta shiru bata neme su ko ta ce za ta zo ba kuma d’azu bata ganta a k’asa a parlourn ba dama.
Ba ta yi mamakin jin Ummin bama ta san ciki ne da Manubiyan ba
Tace mata “d’azu ta je side d’in Daddy ta tarar ya fita da ta sauk’o ta tambayi Yadira kuma tace mata wai sun je gidan su Manubiya ne za ta gaida iyayenta”

“Hmm”kawai Yahanasu tace
Daganan ta mik’awa Manubiya wayar suka gaisa da Ummi har ma da Yashjub ta yi musu murna daga nan tace musu gata nan zuwa inshaaAllah.A daren kuwa ta zo.
Su inna ne dai Yashjub ya kira ya lallab’a su yace “jikin nata da sauki su bari gobe su zo yanzu dare ya yi”.

Aikuwa washegari da sassafe d’akin ya cika taff su Inna da Ummi duk suka baiyyana,
Manubiya har da kukan shagwab’a da ta ga su Innaa.

Gata kam ranar ta ganshi har da d’an hawayen farin cikin ta.
Abinci kala kala daga wajen Ummi Inna har da Mama wadda shigar ta gidan kenan ta tarar ana shiri dan haka ta ce “su jira”
Haka taje ta had’o mata d’an Malale mai d’an karen dad’i tace a kawo mata bayan ta kira ta ji ya jikin nata….




Yassir gaba d’aya ya fice daga haiyyacinsa
A tsarin sa sai bayan kamar kwana d’aya zai aiwatar da shirin sa amma kuma farin cikin da ya ga Daddy yanata yi ne ya sake hassala shi dan d’azu ma da Daddyn zai fita ji yayi yana waya a kan Yashjub d’in ya san kuma gift ko wani abun zai k’ara masa in ba da kyar ba.
Ga Kausar kuma da ya lura da yadda ta burkice itama tashi d’aya…abun ba k’aramin sake hassala shi ya yi ba.
Shiyasa kawai ya shiga d’aki ya rufe ya shiga aiwatar da shirin nasa.



Suna zaune ana ta hira da Ummi da Innaa kawai sukaga an turo k’ofa an shigo.
Ita kanta Manubiya ba ta yi tsammanin ganin Mommy ba
duba da yadda kaff cikin su babu wanda ya d’au waya ya kirata har ta kwana ta ke shirin wuni….

Cike da sallama faram faram Mommy ta shigo suka hau gaisawa Yasira da Ya’isha suna a bayan ta.

Yahanasu ce ta bawa Mommy kujera ta zauna bayan sun gaisa.
Cike da girmamawa su Jidda da Muhsin ma suka gaida ita sab’anin su Ya’isha da suka koma gefe suka k’ame kamar ba su ga su Innaa ba.

Suna zaune d’akin ya yi jugum tun shigowar su Mommy
Yashjub suka shigo shi da Najeeb wanda ya d’an rame kana ganin sa ka san yana cikin damuwa…

Karairaiyar da Ya’isha ta dinga yi da shishshige masa har zuwa lokacin da ya fita saida ya bawa Jidda kunya,shi kuma yanata basar da ita kamar bai ma san ta na yi ba.
Hakanan ya yi wa Manubiya ya jiki bayan ya ajjiye uban tulin laidojin hannusa ya juya ya yiwa su Innaa da Mommy Allah ya k’ara sauk’i ya fita.
Murmushi kawai Jidda ta yi a ranta tace”kina nan kina iyayi”
“Yana chan yana ziryar zuwa gadon k’aya ba a kula sa.”



A d’akin su Inna suka zo suka tarar da Ummi shiyasa Ummin ta mik’e ta fara haramar tafiya dan ta na so ta d’an ba su guri kuma ta lura kamar akwai maganar da Innar ta ke so su yi saboda taga matar sai yawan yin shiru ta ke yi kamar tana ta tunani.
Ummi tana mik’ewa Yahanasu ma ta mik’e tace “Bara itama ta je ta d’an shirya tanada client da za su had’u in the next 2 hours”
Ta riga ta san Yashjub yananan ba inda zai je 24/7 shiyasa hankalin ta kwance sukayi musu sallama ta bar su Mommy a d’akin suka tafi tare da Ummi wadda take ta addu’ar Allah ya sa su Mommy ma su yi kan gado su bar Manubiya da y’an uwanta su d’an keb’e dan ta san rabon da su yi eyes to eyes tun kafin ta tafi honeymoon..

Ita kanta Manubiya so take ta keb’e da ahalin nata dan ta lura ba iyaka Inna ba hatta Jidda kamar tanada damuwa
bayan ta Al’ameen wadda ta riga ta san ta da ita..
Sannan kwana biyu ba ta ji Ya Musbah ba kuma ta kirasa a waya ko jiya ma bai d’auka ba! “anya kuwa lafiya??”
Ta yi wa kanta tambayar a cikin ranta.
Illai kuwa! wannan itace damuwar su Innar saboda tun bayan sati 6 da suka wuce
da Baraka ta tare Abu bai yi dad’i ba…zuwa yanzu Inna ta fahimci ashe ladabin kura Baraka ta yi musu,
tunda gashi yanzu ta rabasu da Ya Musbah…
Tana tarewa ko sati ba ta yi ba tace “ita ta tsani unguwar”
Haka nan jikin sa yana rawa ya d’auki d’an kud’in da ya tara zai biya kud’in registration d’insa dan lokaci ya kusa cika
Suka tashi a unguwar suka kama wani gidan a Na’ibawa chan nesa da su Inna tsabar rashin adalci irin na Baraka.
Kuma ta hanasa fad’a musu sai a ranar da za a tashi d’in.

Da dafarko da suka tashi yana zuwa duk bayan kwana biyu a d’an mashin d’in sa,sai ya dawo zuwa bayan sati d’aya tou tun daga nan basu sake saka shi a idanunsu ba gashi kayan abincin su ya k’are. Jiya babu kalar kiran da Jidda ba ta yi masa a waya ba amma ya k’i d’auka….
Tabbas sai yanzu Innaa ta yi data sanin barin shi ya dawo da Baraka
Dama baba yace mata “Indai Baraka ce tou kuwa za ta sha mamaki…”
Gashi kuwa k’iri k’iri ta rabata da d’anta kuma tun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login