Showing 135001 words to 138000 words out of 244445 words
kuma hukunta mai laifin kashe mutanen nan,justice must be served!.
A nan a take suka fara shirye shirye kuma suka yi alk’awarin ba za su bari Yash ya sani ba dan sun san zai yi yunk’urin ya hana su especially ma ita Manu da a yanzu ba shi da wani burin da ya wuce ta yi ta hutawa kawai.
Dama Yahanasu tana da connections kasancewar lawyer dan haka tun a lokacin ta shiga making phone calls aka fara shirye shiryen first step……
Yashjub ma sai chan dare ya samu ya dawo….Yahanasu ta wuce gida shi kuma ya nema waje ya zauna ya ruk’o hannun Manubiya….bai so Manubiya ta sani ba gudun kar ya d’aga mata hankali amma kuma ya yiwa kansa alk’awarin ba zai sake b’oye mata komai ba tun lokacin da su Yasira suka kusan had’a masa bomb da zancen Kausar,dan haka ya shiga zayyane mata yadda duk abunda ya faru da binciken da suka fara tun a yau…successfully cctv ta yi capturing incidence d’in tun shigowar y’an ta’addan har fitarsu kuma mutane biyu ogannnin cikinsu babu mask a fuskokinsu sannan an shaida guda d’aya dama ana neman san dead or alive…dan haka yanzu step d’in da suka d’auka shine na kama wannan mutumin ta wajen sa ne kawai za a gane waye ya turosu a ji komai dan muddin suka kamasa kalar interrogation d’in da za su yi masa dole ma ya fad’i gaskiya…….
Shiruuu Manubiya ta yi jikinta duk babu dad’i,kusan step d’in da ita da Yahanasu suka d’auka shi su Yash d’in suma suka d’auka amma su sun yi nisa dan su ko binciken cctv d’in ma ba su yi ba….kamar yadda ya ce ba ya so ya b’oye mata komai shiyasa itama ta fara k’ok’arin gaya masa shirinsu ita da Yahanasu amma sai ta ji yana cewa”dan Allah dan annabi ki kwantar da hankalinki,ba na son ki yi komai..if not because ba na son b’oye b’oye a tsakanin mu da ba zan gaya miki ba,dan haka dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kular mun da ku..inshaaAllah all will be fine,ok?”
Ajiyar zuciya ta sauk’e,a take ta fasa gaya masa saboda har ga Allah tana son ta taimaka dan haka kawai ta jini jina kai a hankali ta yi huggin d’insa…
Ba dan Yash ne da kansa ba da babu abunda zai sa Doctor ya bar Manubiya ta fita ba tare da ya sallameta ba…sai da ya sake dubata tukunna suka tafi dubo
Baba ita da Yashjub…
Had’add’en private hospital mai kyau da tsada Yash ya kai sa dan har ya ma fi na family Doctor d’insu da Manubiyan take kwance.
A harabar asibitin suka tarar da Jidda a tsaye ta kauda kai gefe da wani,sai da suka k’arasa tukunna suka fahimci ashe Ya Yusuf ne…
Da mutuntawa suka gaisa shi da Yash kafin ya kalli Manu itama ya gaida ita daga haka ya yi musu sallama ya tafi…
Yashjub ne ya iya amsashi dan daga Manubiya har Jiddan babu wanda ya tanka masa, ita Jidda haushi da tsanar sa ne yasa tunda suka fito ba ta ce komai ba Manubiya kuwa tsantsar mamaki ne ya hanata yin magana dan ba ta yi expecting ganin Yusuf da Jidda a tare ba.
Sai da Yashjub ya rakasu bakin k’ofar d’akin tukunna ya juya bayan yace “su shiga zai je ya d’an siyo abu idan ya dawo sai ya ga jikin Baban su wuce..”
Da “to”suka amsa shi daga haka ya wuce…ko gama fita daga corridor d’in bai yi ba Manubiya tace”Jidda me kike yi da Yusuf a waje???”
Numfashi Jidda ta fesar kafin tace”Baba ne ya ce in rako sa…”
Kukan da ya taho mata ne ya sa ta yi shiru ta fara kokawar danne wa..cikin rashin jin dad’i da rashin fahimta Manubiya tace “Jidda ai da sai ku tsaya a nan da kika fito ya wuce ke kuna ki juya meye naki na yi masa rakiya har chan waje?? Jidda Yusuf ne fa!!!”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya tace”da ya zo ya gama dubiyar ya tashi tafiya shine ya kalle ni yace wai ‘ba rakiya!’
‘In zo in rakasa’! a gaban Baba da Inna tsabar ba shi da tarbiyya.Sai da ya fad’a sau uku tukunna Baba ya kalle ni yace”mu raka sa da ni da Muhsin amma muna fitowa ya cewa Muhsin d’in ya koma ni kuma ya kamo hannu na ya jani kamar wata kayan wanki saboda ya ga Ina shirin komawar,ko da muka fita da na fara k’ok’arin juyawa gani na yi yana shirin runguma ta shiyasa na tsaya kawai.
Tsabar rashin sanin darajar manya saboda Allah adda Manu ta ya Baba zai ce mu rakosa amma ya kora Muhsin.”
Cikin rashin Jin dad’i Manubiya tace”kuma wai a haka ace Baba ba ya ganin laifin Yusuf??”
Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin tace”yana gani fa! kawai kawar da kai yake yi wasu lokutan saboda gudun magana amma ni na san yana gani…ba ki da lafiya ne shiysa ban gaya miki abunda ya faru ba….kin san tunda ya yi kud’i ba shi da Aboki sama da Kaka mallan to shekaran jiya Kaka mallan d’in ya nemi ganin ya Nafi’u da ya musbah,Ya musbah bai je ba sai ya Nafi’u,shine fa tsabar rainin wayo kaka mallan d’in yake ce masa wai ya fad’i ko nawa yake so su basa ya saka baki a yi aurena da Ya Yusuf,wai duba da abunda yake ta faruwa a tsakanin Baba da su Baba habu ya san Baba maybe ya chanza ra’ayi dan haka Ya Nafi’u ya yi naming price ko nawa su bashi ya yi convincing Baba. Shi kuma kaka mallan zai tsayawa Ya Yusuf ko su Uncle ba su yarda ba a d’aura.”
Cikin takaici Manubiya tace”kutt me ya ce masa shi kuma?”
“Kema kin san ai ya Nafi’u ba zai yarda ba…wane tudu wane gangare suka bi daga haka dai hayaniya ta fara tashi,shine fa akayi fad’a da ya Nafi’u da kaka mallan har da Uncle a case d’in wanda da ga jin hayaniya ya afka parlourn ya yi ruwa ya yi tsaki.To dai daga k’arshe Baba ne ya je ya raba da kyar ta hanyar janye ya Nafi’un …shine fa cikin dare wajajen k’arfe d’aya kamar waenda aljanunsu suka tashi haka kurum Uncle ya zo ya shigo har cikin d’aki wai Baba ya zab’a ko su ko ya Nafi’u,saboda ba zai you Yaro ya yi musu rashin mutunci ba kuma ya ci gaba da huld’a da shi yana shigo musu cikin gidan ba. Haka nan dai suka yi ta hayaniya wallahi kamar mata daga k’arshe Baba ya ja bargo ya kwanta kawai ya rabu da su,shine suka yanke mana wutar d’akin da na d’akin Muhsin kuma suka d’auko wasu takardu wai d’akin Muhsin d’in ma rushesa za su yi filin rabi ne na Baba rabi kuma nasu…a ranar babu wanda ya runtsa.Ya Yusuf dai shi yake ta k’ok’arin hanasu Anty Umma ma har kuka ta yi tana lallab’asu tana so ta ga an rufe case d’in amma sai tujara suke yi kaka mallan yana gefe yana mana gori kala kala..har da cewa ya Musbah ya gudu ya barmu,kema wai an bi kwad’ayi an aura miki mai kud’i gashi ba ya tsinana mana uwar komai ko kwayar shinkafa bamu da ita rabon da ya ga mun yi girki har ya manta,wai dama shiyasa ya ke so a aurar da ni a Ya Yusuf ya rufa mana asiri ya dinga ciyar da mu amma mu kuma mun k’i yarda.”
Mun d’auka maganar d’akin Muhsin fad’i kawai suke yi ashe su sun d’auki abun serious dan da muka zo duba ki bricklayers suka nemo wajen mutun shidda suka nuna musu d’akin aka fara rushewa…Baba yana d’aki sai jin rushe rushe ya yi da hayaniya,baya so ya kula su yace tun last two weeks ya lura kawai neman masifa suke yi da shi shiyasa ya k’i fitowa ya tsaya a d’aki ya yi ta kiran Ya Musbah shi kuma ya k’i d’auka to inaga bak’in cikin hakan ne ya sa muka shigo muka tarar da shi a sume……
“Innalillahi wa Ina ilaihirrajiun”
Manu ta ke ta maimaitawa kafin ta share hawayenta ita ta ma rasa bakin magana,chan tace”kuma har yau bai zo ba?”
Jinjina kai Jidda ta yi alamun “eh”kafin tace “inna tace mini d’azu da na fita siyo mana abinci ya kira Baba ya yi masa ya jiki inaga message d’in da na yi masa ya gani sannnan ya ce gobe zai zo….”
A hankali Manu tace”da ke da Muhsin mu je gidana mana kafin mu ga yadda hali zai yi su Inna kuma tunda suna nan they are safe dan gaskiya Jidda ba za ku koma gidan nan ba abun ya yi yawa an kai peak!”
Murmushi Jidda ta yi cikin jin tsananin tausayin kansu tace”Adda Manu kin manta su waye dangin mijin na ki ne?ai kema kin san zamn mu a cikin gidan ki ba abu mai yiwuwa bane ba….”
Shiruu duk suka yi kafin Jidda ta sake cewa”Ya Yusuf dai tunda ya zo ya ke ta bada hak’uri kuma ya kawo takardu wai ya siye mana gaba d’aya filin daga wajensu har ya kira an fara gyarawa…..
To dai wannan karon gaskiya Baba ya zuciya dan tunda Ya Yusuf ya zo bai sake da shi ba daga amsa gaisuwa ya ja bakinsa ya yi gum!Inna ce ma ta d’an saurare sa kad’an,har da cewa wai ya sayi sabon fili zai yi maaana gini waye waye Baba ya yi hak’uri kar ya damu dan ya Musbah ya daina kula mu inshaaAllah indai yana raye da shi da Inna ba za su yi kukan rashin d’a ba.”
“Wai shi Yusuf yana nufin aikin bankin ne duk ya azurtashi haka??”
“Hmm”Jidda tace kafin ta d’aura da cewa”Siyama ta ce mini idan fa kika shiga side d’in Baba Habu za ki d’auka a hotel kike tsabar yadda ya gyara sa,ya yi interlock a gaba d’aya compound d’in gidan ya sakawa iyayensa solar shi kuwa gidan da ya gama ya koma akace har abun tsoro hawa biyu fa,motocin sa fa uku,wayar sa wadda ta fito last month ita yake rik’ewa…y’an unguwa sai magana ake yi amma iyayensa da kaka mallan sunce hassada ce ya ci gaba da business d’insa ya dage da addu’a kawai ya yi harkar gabansa kar ya kula kowa….”
“Ha’a Manu yaushe kika zo??”
cewar Inna wadda ta fito da niyyar bin bayan Jidda dan ta ji shirun ya yi yawa…a hankali Manu ta tafi jikinta ta rungume ta…cikin rashin jin dad’i inna tace “yanzu Yarinyar nan sai da kika fito?duba fa hannunki har da cannula!to Allah ya kyauta..””Bismillah”daga haka ta juya ta nufi ciki suka mara mata baya.
A zaune suka tadda Muhsin yana assignment Baba kuma yana zaune a kan gadon jinyarsa yana kallon k’ofar da alamun shigowar tasu yake jira dan ya ji Inna ta ambaci sunan ‘Manu!’.
A hankali ta k’arasa ta d’an durk’usa ta gaida sa tukunna ta zauna a kujerar mai jinya ta shiga tambayarsa ya jikinsa..
Murmushi ya yi duk da bai so ta fito ba duba da yanayin jikinta amma kuma ya yi matuk’ar jin dad’in yadda ta damu ta taho dukda itanma a kwance take…
Cikin fesar da numfashi ya yi ta’auzi ya kawar da shed’an d’in da ya fara comparing masa himmar Manubiya da Ya musbah a kansa,tukunna yace”ya jiikin naki?”
A hankali tace”Alhamdulillah”
“MashaaAllah Allah ya inganta”ya ce kafin ya d’aura da cewa”ki kira mijinki ku koma Manu dare fa ya yi,ai na warke ma Alhamdulillah”
Murmushi ta yi tace”ya tafi siyo abu sai ya dawo za mu tafi..”
Jin jina kai kawai Baba ya yi daga haka suka d’an tattauna Akan batun su Uncle,Manubiya ba ta so ace Yashjub ne ya bawa iyayenta gidan da za su zauna a ciki ba,amma ba ta da choice tashinsu a kusa da su Uncle shine mafita dan abun nasu ya yi yawa..shiyasa har wani sanyi ta ji da ta ji Baba yana gaya mata ai Ya Nafi’u ya yi masa batun maganar da suka yi shi da Yashjub shi kuma
ya amince,inshaaAllah yana fita daga asibiti za su tare,dan d’azu ma Yash d’in ya zo ya d’auki ya Nafi’u suka je ya basa gidan tare da makullai da takardun.Da Nafi’un ma har yana cewa zai zo ya kawo yanzu to sai nace ya barshi kawai dare ya yi..ma had’u gobe.A gidan ma har da b’angaren Musbahu Allah ya sa dai Baraka ta yarda ya dawo gidan su zauna….”
Ahankali Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace zai dawo inshaaAllah Baba,ku dinga yi masa addu’a kar ku bar b’acin ransa a cikin zuciyoyinku fushinku a garesa masifa ne.”
Jin jina kai Baba ya yi kafin yace”ki na da gaskiya kam,Allah ya sa mu dace.”
Knocking suka ji dan haka Muhsin ya mik’e ya je ya bud’e k’ofar….cikin girmamawa ya gaida Yash ya amsa masa da kulawa tukunna suka k’araso cikin d’akin a tare bayan Muhsin ya maida k’ofar ya rufe.
Sai da Yashjub ya d’an russuna tukunna ya gaida Inna da Baba suka amsa ya tambaya ya k’arfin jikin yace”Alhamdulillah”
Wallahi dama shiyasa d’azu bai shigo ba yanzu ma kawai ya ga dare sosai ne shiyasa ya shigo tafiya da Manubiya kar ya barta tana yawo ita d’aya da dare…Sam ba ya so su Baba su yi masa godiya amma suna gama gaisawa suka hau yi masa godiya har da su Jidda wadda itama sai yanzun ne ta ji batun daga bakin Baba.
Kamar zai nutse k’asa haka ya ji,hakanan ya sunnar da kai yana ta faman cewa”Ameen Ameen.”
Ba su wane dad’e ba,suka yi azamar tafiya,Saida duk ta yi musu sallama tukunna ta yi hugging Jidda ta ba ta atm card d’inta da ta d’auko
daga jaka tace gashi,karb’a Jidda ta yi tukunna ta fara shirin rakasu,murmushi Yashjub ya yi ya ce “ta barshi ai su biyu ne.”
Daga haka suka tafi Yashjub yana tunanin
“Ba dan suma a asibiti suke ba da sun tafi da su Jidda”.
A mota Manubiya ma ta so yi masa tata godiyar amma ya yi kicin kicin”wai idan ta yi sai sun yi fad’a”
Har wani turo baki wanda hakan ya sa ta fara dariya….
“Shine amma baka gaya mini ba?”
“Na san zugawa za ki yi ai ki hana,shiyasa na zagaye ki!”
Ya bata amsar yana mai d’an juyowa ya kalleta.
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace”da Ya Nafi’u kuka yi magana kenan?”
Sai da ya d’an yi shiru tukunna yace”ni ne na tambayesa na nace shi ne ya gaya mini komai”
Cikin mutuwar jiki tace”ba lalle ai ya Musbahn ya yarda ya tashi daga gidan da yake d’in ba.”
Kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace”na sa a nemo mini number landlord d’in nasu,kar ki damu zai tashi.”
Shiruuu ta yi haka shima Yash d’in daga nan har suka k’arasa asibiti.Kowa da tunanin da ya ke yi,Yashjub gaba d’aya hankalinsa yana a kan wayar Manubiya ne ya lura wayar a silent take kuma sai faman kiranta ake yi tana rejecting shiyasa ya tafi tunanin ko dai wannan wanda ya kira ta ta k’i cewa komai jiya ne?
To kenan ta san waye tunda har take k’in d’auka…bai yi expecting za ta b’oye masa wani abun ba shiyasa shima ya yanke a kan ba zai tambayeta ba,zai danne kansa ya ga iyakar gudun ruwanta.Amma fa yadda zuciyarsa take yi sakamokon kishin da ya ke tunzurosa hatta jijiyoyin gaban goshinsa sai da suka fito rad’au!.
A b’angaren Manubiya kuwa Abbakar ne yake ta nacin kiranta da messages na ban hak’uri wai yana son magana da ita yana neman taimakon ta,ta ji zafin yadda ya banzatar da ita amma kuma babban dalilin ta na ignoring d’insa Yashjub ne! Ba ta so su samu matsala ita da shi saboda wani Abbakar kuma he made it pretty clear to her cewa ba ya son relationship d’inta da Abbakar d’in kwata kwata ko gaisawa ba ya so su yi!…ta san ba ya son shi saboda yana tunanin kamar son ta yake yi kuma ta tuna b’acin ran da ta ji a muryar sa ta kuma gani a fuskarsa duk a ta dalilin Abbakar d’in,shiyasa yanzun ta ke jin tsoron gaya masa ‘Abbakar d’in ya na ta kiranta,ya turo mata message yana buk’atar taimakonta.’Ta zab’i kawai ta rabu da shi da zarar ta nutsu za ta nemo yadda ake block ta yi blocking d’insa gaba d’aya,ta san Abbakar ya taimaka mata ba adadi ya kamata ace ta taimakesa yanzun itama amma Yashjub comes first a komai na rayuwarta kuma tunda ya nuna ba ya son ko gaisawa ne su yi da shi inashaAllah za ta yi masa biyayyaMANNUBIYA
(Book 2)
Page 30
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Duk yadda Yassir ya so ya jira ya d’an saisaita kansa kafin ya fuskanci Kausar kasawa ya yi…ba ya so ya tunkare ta yanzu dan tabbas zai iya illatata amma kuma zuciya da bak’in cikin rashin samun nasarar kashe Yashjub da kuma kishi ne suka k’i su barshi ya jira d’in dan haka kawai ya nufi gida gadan gadan.
A b’angaren Kausar kuwa
A rikice ta shiga gidan itama
sakamokon wani amai mai k’arfi da ya hanata sukuni yake ta faman yunk’uro mata…ta na shiga d’akin ta kuwa ya taho da mugun k’arfi..
Da gudu ta nufi toilet amman tun kafin ta k’arasa ta fara sakinshi.
Ta jima tana yi kafin ta samu ya d’an sarara mata ta shiga mayarda numfashi…Yanayin k’arnin aman ne ya firgitata ya tsoratata,haki ta shiga yi tana addu’a a lokaci guda ta shiga hargitsa toilet d’in tana neman pts.
Da ikon Allah kuwa ta samu
dan haka ba ta yi wata wata ba ta auna kanta.Bata iya ajjiyewa lokaci ya cika ba hakanan ta shiga safa da marwa a cikin band’akin da abun a hannunta idanunta kyam a kai,gaba d’aya ta hargitse ta ma rasa tunanin me za ta yi…tun da take ba ta tab’a
jin tsoron shigar ciki da fargaba da tashin hankali kamar na yau ba!.
Aikuwa tashi d’aya ta fara ganin alamun positive…kafin ma ya gama tabbatar mata da hakan ta fashe da wani irin kuka ta durk’ushe a wajen tana kallon yadda abun yake yi mata nuni da tana d’auke da ciki ne.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
ta shiga maimaitawa a