Showing 123001 words to 126000 words out of 244445 words

Chapter 42 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16479

ya zaiyyane masa hakan a rikice.
‘’Slow down Yashjub” Daddy ya ce kafin ya d’aura da cewa ‘’relax!!ok..”tukunna ya juya ga Mommy yace ‘’Ina Manubiya??”

‘’Tana asibiti”kawai tace da alama ran ta a b’ace yake kafin ta d’aura da cewa
“Duk ya bi ya d’agawa mutane hankali kalle mu gabad’ayan mu a rikice shine tsabar rashin sanin ciwon Kai zai ishemu da Manubiya!Manubiya!!,
Mannubiyan baby ce?goyota yake so mu yi mu taho da ita crime scene irin haka salon shima idan mun yi hakan yace za ‘a cutar da ita??”

Numfashi Daddy ya fesar kafin yace”yanzu fa lokacin murna da farin cikin kasancewarsa safe and unharmed ne godiya ya kamata mu yi wa Allah,ba wai haushi ya kamata ki ji ba‘’sai kuma ya maida hankalin sa ga wayar da yake yi yace ‘’Yashjub Manubiya tana asibiti mu kuma muna estate d’in ka”.
Without thinking twice yace ‘’okay bara in je asibitin’’ daga haka ya kashe wayar kitt!!!.

Shiruuu Daddy ya yi ya kusa minti d’aya da wayar a kunnen sa…kafin da kyar ya zaro ta ya mik’awa Yassir jikinsa a matuk’ar sanyaye….ya rasa dalilin da ya sanya no matter how ya kauce ya goce duk dan a zauna lafiya dole shi kuma Yashjub sai ya fito fili ya nuna masa Manubiya ta fi su matsayi a wajensa itace za ta zo first a sama da kowa da komai na rayuwarsa..he can’t help it but to think anya idan ya yi sake ganin Yashjub d’in ma ba zai gagaresa ba kuwa wata rana?!….
Yahansu ce ta ce
“Daddy mu je asibitin,chan ya nufa ko?”

Saida ya juyo ya kalle ta tukunna ya d’aga mata Kai alamar ‘eh’ da ‘to’ daga haka ya wuce cikin tsananin mutuwar jiki.

Yana wucewa Ummi ta bi bayansa bayan ta bawa Munirat makullin motarta ta ce ta taho a ciki dan tanaso ta d’an fahimtar da shi dalilin da ya sa Yashjub d’in ya yi haka saboda ta fahimci ya ji haushi.
Tana wucewa suma suka fara shigewa motocin su suna bin bayansu.
Wajen ya rage daga Yasira sai Yassir da Mommy da Baba larai
Mommy tsananin mamakin yanayin Yassir da kuma b’acin ran Yashjub ne suka hanata motsi har sai da Baba larai ta tab’o ta tace “mu je ko?”
tukunna ta samu ta d’auke kan ta daga kan Yassir da kyar
suka nufi motar Yasira.
Suna zuwa ta bawa Yassir key amman sai ya zauna a wajen mai zaman banza yace “ta ja su kawai”
dan shi kam ba ya jin hannun sa zai iya d’aukar makullin ma ballantaana aje ga jan motar.



A rikice Yashjub ya k’arasa cikin asibitin ko parkin mai kyau da ma’ana bai yi ba hakanan ya fito ya rufe motar ya afka ciki dan tun d’azu dama ya tsinci kanshi da fara jin tsananin fad’uwar gaba yanzu kuwa da yake ta kiranta bata d’auka kuma ya ji bata tare da su Mommy he can’t help but ya yi tunanin wani abun ne ya sameta
Yana dialing number yana wani irin gudu gudu sauri sauri haka ya afka cikin d’akin.

Sai da numfashinsa ya kusan d’aukewa da ya shiga ya ganta yashe a k’asa wan war kamar matacciya,k’amewa kawai ya yi ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya.
Kafin da kyar da taimakon addu’o’in da yake ta jerowa ya samu k’afafuwansa suka basa had’in kai wajen k’arasawa inda take a rikice ya durk’usa,hannu sa yana wani irin karkarwa haka ya kamo hannunta ya d’aura a ta wajen pulse d’inta
A take ya saki wata k’akk’arfar ajiyar zuciya sai kuma ya rarumo gorar ruwa ya b’intike kan ya shiga shafa mata
yana d’an tapping fuskarta still hankalinsa a mugun tashe.
Wani nannauyan numfashi ta ja ta fesar idanunta a rufe ta shiga magana a rikice a tsorace ‘’Mijina!dan Allah Mommy ku ce ya dawo,mu je mu nemosa,babu abunda zai same shi, Ya Yash d’ina idan ya bar ni wallahi mutuwa zan yi”

Kallon fuskarta kawai yake yi yana jin wani kalar tausayi da tsantsar k’aunar ta tana dad’a ratsa shi, a hankali wata kwalla ta ziraro ta biyo ta sauka a kan fuskarsa..cike da taka tsantsan ya d’agota ya saka ta a jikinsa wanda jin k’amshin turarensa da kuma jinta a jikin Mijinta ya sanya ta dawo haiyyacinta ta yi sauri ta bud’e idanuwanta domin ta tabbatr wa kanta da shi d’in ne?
A hanakali ya d’ago fuskarta yana kallon cikin idanunta yace ‘’babu inda zan tafi in barki, inshaaAllah muna tare har gaban abada.”
A hanakali ta lumshe idanunta tana hawaye tana jin wani sanyi yana ratsa ta..
…Da farko gefen kumatunta ya fara murzawa kafin daga baya ya matso da fuskarta sosai garesa cikin shauk’i k’auna da bege ya had’e bakin su waje d’aya…..
Kamar ance ‘action’haka su Kausar suka antayo cikin d’akin gaba d’ayan su.
Da sauri Daddy ya juya ya fita har yana d’an tuntub’e,ya riga ya gan sa ya ga he’s fine,very fine ma kuwa!
Dan haka ya nufi mota ya wuce gida ya bari akan idan Yash d’in ya koma gida sai ya ji komai daga bakinsa.

Daddy yana wucewa Yashjub ya saki Manubiya ta hanyar yin k’asa da ita ya saka ta a cikin k’irjinsa yana maida numfashi a hankali ba tare da ya juya ba yayin da ita kuma kunya ta sanya ta sake ruk’unk’ume sa ta cusa kanta sosai a cikin k’irjinsa.

Da sauri Kausar ta juya za ta bar wajen tashi d’aya suka yi karo da Yassir…cikin son ganin yanayin ta da idanun ta ya tare hanyar yace’’Ina za ki je ?’’
Ya yi mata tambayar
Fuskarsa babu alamun wasa dan ransa a mugun mugun b’ace ya ke dama.
Ba tare da ta kalle sa ba tace ‘’matsamin hanya in wuce Yasir ba ni da lafiya‘’
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin zagayesa dan ya tare k’ofar.
Wata mahaukaciyar damk’a ya yiwa hannunta wanda har sai da tace”Wayyo!”a hankali tsabar azaba
Bai damu ba!hakanan ya dawo da ita gaban sa yace ‘’I’m not done with you yet,look at me na ce ko!!?”ya fad’i hakan cikin karsashi kamar wani ubanta a lokaci guda yana mai sake damk’e hannunata da take ta k’ok’arin kwace wa.
Ganin yana shirin karya mata hannu ne yasa ta d’ago idanuwanta da suka yi jazir suka cika taff da kwallah tace’’Yassir za ka karya mini hannuna fa’’sai kuma hawaye ya b’alle mata shaar.
Da sauri Baba larai wadda ta lura da su ta matso tace’’ikon Allah,Yassir meye hakan kake yi kamar ka samu hannun k’ato?cika ta mana!”.
Ko gezau bai yi ba ballantana Baba larai ta sa ran zai kula ta ko ya amsa,ya kafe Kausar da manyan idanuwanshi da suka yi jazir yana hango tsantsar kishi da k’aunar wanin sa a cikin idanunta…
Kukan da Kausar take yi ya Isar wa su Mommy dan haka duk suka juyo
Da sauri Mommy ta matso ta ce ‘’me ya faru?Yassir cika ta mana”
Haka ma Yasira ta matso ta fara k’ok’arin kwatar hannun Kausar d’in amman bai kula kowa ba
Sai da Mommy ta daka masa tsawa cikin b’acin rai tace’’ka cika ta mana!”
Tukunna ya juyo ya zubawa Mommyn ido sai kuma kawai ya saki Kausar d’in ya juya ya fita.
Yana fita Kausar ma ta fita duk da tana tsoron su sake had’uwa da shi amma ta gwammaci ya daketa ma idan sun had’un akan dai ace ta ci gaba da zama a cikin d’akin nan!.
Da ikon Allah kuwa da ta fita babu Yassir babu alamar sa dan kamar walkiya haka ta nemi sa ta rasa,
har ta kunna motar ta ta fice daga asibitin babu shi babu kyallin sa.


Kausar tana fita Yashjub ya mik’e bayan ya gama sauk’e Manubiya daga jikinsa ya kalli Yassira yace “Yasira ya za a yi ku fice ku bar patient haka? sannan da kuka zo fitar ba ku kira nurse ko wani ba kawai kuka fice ku ka bar ta ita kad’ai ga shi har ta suma babu wanda ya sani bayan kin san ba ita kad’ai bace ba!”.

Sai da Mommy ta yi da gaske tukunna ta danni zuciyarta tace
“Am,Yashjub ba ta wannan ake ba! yanzu ka fara fad’a mana Ina ka je ka k’i amsa waya tukunna”.

Cikin d’an b’acin rai yace ‘’Mommy a sume fa na shigo na tarar da matata sannan ku ce ba ta wannan ake ba??”

Ai kuwa cikin fushi kamar jira takeyi dama,tace
‘’wai wanne kalar Iskanci da rashin sanin ya kamata ne yake d’awainiya da Kai ne Yashjub??!
Ashe baka da hankali kaima ban sani ba? fad’a za ka yi mini yanzun a gaban Yara ko yaya?
Tsabar iskanci ina tambayar ka abu kaima kana ce mini wani ‘ya na yi abun da bai kamata ba?’.”

Ahankali Manubiya ta mik’e da kyar tace ‘’Mommy ki yi hak’uri nice ban yi masa bayani ba”
Sai kuma ta kalli Yashjub tace’’Ya Yash nice na ce su je zan iya…..”
Cikin katseta Mommy ta daka mata wata uwar tsawa,ta hanyar cewa’’Ke dallah malama rufewa mutane Baki!”
Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya d’an firgita ya d’aga kai yana kallon Mommy cike da mamaki al’ajabi da rashin jin dad’i.

Cikin b’acin rai da takaici Mommy ta d’aura da cewa’’bana son munafurci da iyayi da kankamba!,a tunanin ki idan kika ce masa ke ce kika ce mu tafi mu barki zai fasa dukan mu ne?ko kina tunanin ke ce za ki gyara tsakaninmu ko kuma ki sanya ya k’i jin haushin mu?.Har yaushe kika zo balle ki yi tunanin yin wannan shishshigin???”

Cikin rashin jin dad’i Ummi ta matso tace ‘’haba Mommy,ki yi tunani mai kyau mana,Manubiya fa surukar ki ce kuma matar d’anki na farko a ganin ki hakan da kike yi ya dace?ai ba wai tana tunanin ita zata saka Yashjub ya yi muku wani abun bane kawai ta so ta rufe maganar ne ta hanyar cewa ita ta ce ku tafi ku barta.’’
Cikin fushi Mommy ta juya ga Ummi sannan tace ’’Tabbas Ummi kwakwalwarki ba ta da rik’e abu!
Yara sun gaya miki nima na gaya miki amma har kin manta ko? to bari in sake tuna miki yanzu!daga yau har abada banaso ki sake yi mini shishshigi,kamar yadda na cewa Manubiya bana son ta yi mini shishshigi to kazalika kema dan baku da bambanci da ke da ita.’’
Shiruu Ummi ta yi kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma kawai ta juya ta kalli Manubiya tace ‘’ki yi hak’uri kiyi ta hak’uri haka rayuwar auren yake duk hak’uri ne a ciki,Allah ya baki lafiya’’daganan ta juya ta kalli Munirat tace ‘’wuce mu tafi.”
Suna zuwa daff da k’ofa za su fita Ya’isha tace “gara dai duk wanda ya san shi bare ne ya fita dama hakan ne ya dace a yi tun farko ai.”
Ko kallon ta ba su yi ba haka suka saka kai suka fita.

Suna fita Mommy ta d’aura daga inda ta tsaya ta balbale Manubiya kamar ba surukar ta ba wanda hakan ya sa hatta su Yasira sai da suka yi mamakin ta,sun san cewa Mommy ba ta son Manubiya,amma ba su yi tunanin za ta iya balbale ta a gaban Yashjub ta ci mata kamar haka ba,dama tun d’azu kafin su baro estate d’in Yashjub suka fahimci kamar akwai abun da ya fusatata sosai a tashi d’aya yanzu kuwa sun tabbatar dan in da ace ranta ba a b’ace yake over ba to da bazata yi wannan b’aranb’atamar haka ba.

Zuwa yanzu Yashjub ya gama fahimtar tabbas Mommy fa ba ta son Manubiya kawai dama pretending take yi tun farko dan ko shi Yaro ne abubuwan da suke gudana a gaban idanunsa sun Isa su fahimtar da shi hakan,but meyasa zata dinga pretending a gabansa sannan me ya fusatata haka?dan tabbas ba iyaka maganar Manubiya bace ta harzuk’ata ta kaita ga rufe ta da fad’a babu ji babu gani irin haka.
Gabansa ne ya yanke ya fad’i da ya tuna incidence d’in jiya yadda Yasmeen tace Mommy ce ta turo ta da kuma yadda tace Manubiya ba ta da ciki gashi ta dage sai ta yi mata allura!dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi anya ba Mommy ce ta turo ta ta zo ta yiwa Manubiya allurar da za ta zubar da cikin ba kuwa?..dan shi kansa da farko ya yi tunanin rashin kwarewa ne ya sa Yasmeen d’in tace Manubiya ba ta da ciki amma da ya zauna ya yi tunani tun a jiyan sai ya fara wani tunanin na daban!
But a bayanin Doctor ya fahimci ita kanta Yasmeen d’in ba lalle ace ta fahimci akwai cikin ba ballanta har su yi yunk’urin zubarwa!sannan tayaya?how? Mommy za ta bayar da goyon baya a kashe masa d’a?noo it can’t be babu mahaifiyar da za ta aikata haka ga d’anta babu ita a duniya!……


A b’angaren Manubiya kuwa shiruu kawai ta yi ta k’i cewa komai ta sunkuyar da kanta…da farko hawaye take yi kafin daga baya ta daina,tabbas zuwa yanzu ta tabbatar da Mommy ma a bayan y’ay’anta take duk ba sonta suke yi ba,dama sai da ta yi tunanin’ta ya Mommy za ta so ta bayan Kausar niece d’inta ce,amman kuma yadda ta nuna sai kawai ta kawar da tunanin but yanzu kam ta fahimci ashe shigo shigo ba zurfi ta yi mata…dan gashi yanzu idan banda tsana k’iyayyar ta babu abunda take hangowa k’arara a tattare da Mommy.
A ko da yaushe k’ok’ari take yi ta ga ta gyara tsakanin su amman ta lura sam waennan sun yi nisa ba sa jin kira… tunda har da mahaifiyarsu a gang d’in tabbas abun ba k’arami bane sai dai ta d’ukufa gayawa Ubangiji.
Ba za ta tab’a yi wa Mommy rashin kunya ba kuma bazata k’i ta ba tunda uwar mijin ta ce amman fa one thing is for sure ba za ta yarda da cin fuska ba shiyasa ta yi shiru ta k’i ba ta hak’urin da ta yi niyya kawai ta sunkuyar da kanta k’asa…...

Sai da Mommy ta yi mai Isar ta tukunna ta kalli Yashjub tace ‘’d’azun Ina ka je da ake ta kiran ka ba ka d’auka???”

Kamar ba zai ce komai ba
sai kuma kawai ya lumshe idanuwa ya bud’e yace‘’d’azun Ina fita sai na tsaya waya,a gani na gwara in tafi da ambulance da sojoji da k’arin y’an kwana kwana…Ina tsaye Ina waya na ga driver d’ina ya zo ya yi parking dama na aike sa ne akwai takardun da zai karb’o mini,yana zuwa ya yi mini knocking glass ni kuma na bud’e masa d’ayan k’ofan nace ya ajjiye takardun a wajen….a nan ne ya ji wayar da nake yi ya fahimci abunda ya ke faruwa an haka ya tsayar na gama wayar ya jajantamin yace mu je tare…motar da ya zo da ita ta fi gudu kuma duk na b’ata lokaci wajen yin waya shiyasa na karb’i makullin nace masa ya maida wannan cikin asibiti ya yi parking sai ya zo
mu tafi…
Ina ga magana sai na ga su Innaa sun fito gashi arean nan ba a samun abun hawa shiysa na cewa drivern nawa ya fara yin gaba ni kuma na tafi kaisu gida.”
Sai da ya d’an yi shiruu ya d’an kalli Manubiya kafin ya d’aura da cewa “muna zuwa muka tarar Baba ba shi da lafiya shine na mik’a su asibiti…”
Cikin tarar numfashinsa Mommy tace ‘’saboda uban ta bashi da lafiya shine ka gagara d’aukar wayar uwarka da ubanka??”
Da sauri yace “a’a Mommy ba haka bane,garin kiraye kirayen wayar da na dinga yi ne saboda yadda na rikice inaga na saka wayar tawa a silent
sam ban ji kiran ku ko d’aya ba wallahi.”

Wani irin kallo Mommy take yi masa kafin chan kawai ta juya ta fice kamar wadda za ta tashi sama ba tare da ta sake cewa komai ba.
Hakama Yassira ta matso da da’n guntun hawayen ta wai “she almost died d’azu da ta yi tunanin wani abun ne ya same sa ashe shi yana chan yana hidimar gabansa ya barsu hankalinsu duk a tashe kuma ya zo amman ko ya nuna damuwar sa akan d’aya daga cikin su gaskiya abunda yake yi bai kamata ba sam! it’s either ya gyara ko kuma su d’au mataki dan wallahi tsaf sai su fice a harkarsa shima saboda gaskiya abun nasa ya yi yawa ta san shine babba akanta amma dole ta gaya masa ‘he is wrong!’.”
Tana gama fad’in haka ta juya itama a fusace ta fice ..
haka suka juya one by one suka fita zuciya a kumbure.
Su ne suka yi rashin mutunci amma tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wadda ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi ji suke yi kamar su mutu dan tsabar bak’in ciki
Takaici da tsanar Manubiya ta rufe musu ido ta hanasu walwala Yasira da Ya’isha har ma da Mommy ji suka yi inama ace bata farfad’o daga sumar da ta yi d’azu ba kawai da ta wuce lahira…..

…Yarinya sai ka ce y’ar gwal?ace estate d’in ka ya kama da wuta amma ka tafi hidimar iyayenta ba ka je ba sannan da ka gama still ba ka je estate din naka ba ka dawo wajenta saboda ka ji bata d’aukar waya!tabbas ba lalle ma ya san da mutuwar driver d’insa da batun y’an fashin ba tunda har yanzu bai tsaya ya nutsu ya saurari kowa ba ballantana ya ji bayani……




Su Ya’isha suna fita Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya ta juyo ta kamo hannunsa.
Tun kafin tace wani abun yace
‘’Ki yi hak’uri,dan Allah Baby ki yi hak’uri,komai zai yi daidai inshaaAllah kar ki sa damuwa a ranki”
Ahankali ta d’an yi k’asa da kanta kafin tace’’ kar ka sa komai a ranka dan Allah,k’addara dama tana zuwan ma bawa ta ko wacce irin hanya
InshaaAllah Ubangiji zai mayar maka da abunda ya fi estate d’in ka.”
Sai kuma ta kallesa tace”InshaaAllah ma duka ne ya k’one ba,sannan Allah ya sa ba a rasa rai ba,I’m fine now..ka je ka ga halin da bayin Allah suke ciki….”


Jinjina kai yayi ya jata suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace‘’ba gobara bane,Najeeb ya ce mini,y’an fashi ne but yanzun zan je inshaaAllah sai in ji komai…”
A hankali tace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun…”
Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata ido ya san idan ya zurfafa zancen itama za ta fara zargin abunda yake zargi sannan hankalinta ya tashi kamar yadda nasa yake a tashe maybe ma fiye da nasa d’in,shiyasa ya sauk’e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login