Showing 93001 words to 96000 words out of 244445 words
ba zai yiu ba ba zan zauna in zuba ido zumuncin ku ya tarwatse ba saboda rashin tunanin ka da kuma gigin giyar soyayyar da ka kurb’a.”
Yashjub ji yayi kamar ya d’aura hannu aka yayi ta faman zunduma ihu…ta ya Daddy zai biyewa waennan Yaran ya hau kan maganganunsu ya zauna daram sannan ji fa tone d’insa sai kace na mace yana magana kamar ta mata
yanzu wannan d’an k’ank’anin abun har ya kai a titsiyesa a gaban su haka…….
Muryar Daddy ce ta katsesa jin yana cewa”ina sauraron ka,
ka fad’amin exactly abunda ya faru.
Ku kuma”
yayi maganar referring to su Yassira yace”kar in ji bakin ku
har ya gama magana.”
Wato dai a gaban Yaran nan za a yi masa haka!alk’alanci kenan Daddy zai yi musu shi da k’annen sa….
“Ina jin ka mana!”
Ya ji muryar Daddyn a d’an zafafe.
A hankali ya d’ago ya kalli Daddyn yace”Ba su kula ta ba.
Kaff cikin su saida na yi magana tukunna Yadira ta gaida ita‘’
Da takaici Mommy tace
“Saboda ba su gaida matar ka ba shine ka koro su daga gidan ka??’’
Cikin son fahimtar da ita yace
‘’Mommy saboda sun rainani kuma sun ki su yi abunda nace a gabanta sun nuna min ban Isa ba shiyasa na koro su
Baya ga haka Mommy taya za su je har gidan ta su k’i su kulata sannan kuma ni da kaina in ce su yi su k’i yi
Maatata ce fa!’’
Ai ko da ace ba za su gaida ita ba da ko ‘Hi’ ya kamata su ce mata…..”
Cikin tarar numfashin sa Ya’isha tace
‘’Daddy cewa ya yi duk sai mun gaida ita har Yasira da Kausar,kuma fa ita ma bata kula mu ba how yake expecting mu mu gaida ita?.”
Throw pillow Daddy ya jefawa Ya’isha cikin fad’a yace
“Ba na ce bana son jin bakin kowa ba?”
Da b’acin rai sosai ya juya ga Yashjub ya ce
“Yashjub’’
Ahankali Yash ya kalle sa ya ce
‘’Na’am Daddy’’
Cikin bada umarni da fahimtar wa Daddy ya fara magana
‘’kamar yadda na fad’a d’azu
ba zan bari giyar soyayyar da ka sha ta lalatamin zumuncin dake a tsakanin ku ba!ba zan bari wata mace ta shiga tsakanin ku ba dan bakasan yadda muka sha fama ni da mahaifiyar ka wajen ganin mun daidaita kanku ba!”
Ahankali Yash ya lumshe ido yana mamakin yadda su Daddy suka d’auki laifi gaba d’aya suka d’aura wa Manubiya…ta yaya Manubiya za ta shiga tsakanin sa da su Yasira shi kuma ya yarda..
Dan mai ya sa tun farko idan irin haka ta faru a tsakanin su ba’a d’abbak’a abun sai yanzu da yayi aure?
Kuma shi rainin da suka yi masa a gabanta ne ma ya sake harzuk’a sa ya koro su a
tunanin sa ya Isa da su.
Inda ace ci musu fuska ya so yi ai da a gaban Manubiyan zai fatattake su…Ita Manubiyan ma da suke ta cewa ‘za ta shiga tsakanin su’ bama ta san da case d’in korar sun da yayi ba.
Ahankali tunanin sa ya dawo cikin parlourn jin Daddy yana cewa “Inaso ka sanar da Manubiya idan kuma ba za ka iya ba ni zan sanar mata cewa
‘Ya’isha da Yusra za su gaida ita wannan dole ne!amma
tun daga kan Ya’isha har zuwa kan Yassir har Kausar ita ce zata gaida su tunda duk sun girme ta.’”
Da mugun sauri Yashjub ya d’ago sosai ya zubawa Daddy idanuwan sa.
“Kwarai kuwa”Daddy yace shima yana kallonsa kafin ya d’aura da cewa
“Ba wai nace dole in sun had’u sai ta gaida su ba,ruwanta ne idan taga dama ta kula su in bata ga dama ba karta kula su
amman kasancewarsu yayyu a gareta yasanya bazai yiu ace su su fara gaida ita ba.
Idan ta kula su ta gaida su su amsa
In kuma bata kula su ba
wannan alhakin yana a kanka
na ganin ka daidaita alak’ar dake a tsakaninta da su
kaine za ka nuna mata cewa yayun ta ne kuma ta dinga gaida su saboda a samu a zauna lafiya a raya zumunci.
Sai kuma magana ta biyu
‘Daga yau har gaban abada idan su Yasira za su je gidan ka a rana sau goma to baka da iko sannan baka Isa ka kore su ba!na san gidan ka ne nasan kai ka siya ka zuba furnitures ka yi komai da kanka amman ni kuma nine uban ka!
dan haka in dai ni na haife ka,to Yassira,Yahanasu,Ya’isha,Yadira,Yasmeen,Yusra,Yassir kai har ma da Kausar za su je gidan ka a duk lokacin da suke so
In ma hutu suke so su yi za su je su yi har sai sun gaji dan kansu tukunna su dawo amma kai dai baka da ikon koro su…in har kuma kace za ka yi taurin kai to zan sa ka had’omin spare key na kaff gidan naka in rabawa ko wanne a cikinsu….
Ban d’aura auren da zai tarwatsamin kan ya’ya na ba wallahi.!”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce
‘’a kiyaye” daga nan ya wuce sama.”
Shiruu Yashjub yayi ya ma kasa cewa komai
Har sai da Mommy tace
“Sai magana ta uku!Yadira ta had’a kayan ta tun d’azu
In kun zo tafiya ku wuce da ita
za ta zauna a gidan naka for sometimes.”
Saida ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce
“To Mommy ba damuwa,amma jiya na gaya miki za mu tafi Cyprus..y not a bari sai mun dawo t….”
Cikin tarar numfashinsa tace
“Ka wuce da ita,idan kun zo tafiya sai ka dawo da ita in kuka dawo sai ku koma tare da ita”
Ahankali yace”Mommy, jibi ne ai…”
Cikin fushi tace
“Ka san Allah Yashjub in ka gwada min taurin kai idan bance ku tafi honeymoon d’in tare da ita ba ka chanja min suna..”
Shiruu ya yi kafin ahankali ya ce “Shikenan Mommy..ki yi hak’uri”kafin ya kalli Yadira ya ce “Ki d’auko jakar ta ki yanzu zamu wuce.Bari in yi wa Daddy sallama”
Ya fad’i hakan yana mai hayewa sama.
Murna a wajen Yadira ba a magana…tashi d’aya itama ta yi wuff ta haye ta je d’auko kayanta.
Ko da Yashjub ya je wajen Daddy basa hak’uri yayi sosai
tukunna dakyar ya samu ya d’an sauk’k’o bayan zazzafan warning d’in da Daddyn ya zuba masa akan “indai har yanaso su zauna lafiya da shi tou ya ja k’annen sa a jiki…duk ranar da aka ce ya mutu shi ne Uba!…kar ya biyewa mace ta rabasu tun yanzu.”
“InshaaAllah”kawai Yashjub d’in ya ce daganan yayi masa sallama suka rabu lafiya
A ranshi yana mamakin yadda Daddyn yayi masa sannan yadda suka d’auki laifi kachokam suka d’aura akan Manubiya wadda bata ji ba bata gani ba
It’s like kamar ma Daddyn har ya fara jin haushinta ne tun kafin a je koina kawai dai bai nuna masa bane but ya fahimta dan tunda har Daddy yace “har Kausar sai Manubiya ta gaida ita ai abun babu sauk’i dan duk mutumin da Daddy zai yi favoring Kausar akan sa to yakamata ayi gaggawar gyara tsakanin su
Shiyasa kawai ya hak’ura yake ta basu hak’uri…ya san su iyaye ne fushin su garesa masifa ne sannan kuma yasan yanzu yana yin taurin kai ko ya yi wata maganar to Manubiya zai sake janyowa bak’in jini a wajensu.
A d’akin Yahanasu Yadira ta samesu dan haka suka fara shirin tafiya.
Manubiya ce tace “tana so ta je ta yiwa su Mommy da Ummi sallama”dan haka Yadira da Munirat suka tafi rakata.
Suna fita Yahanasu tace
‘Ayi hak’uri Yash
ayita hak’uri…d’azu Ina kitchen naji mommy tana waya da su
Yassira suna ajjiyewa na ji ta kiraka dama tun daga nan na san akwai matsala aikuwa da suka tashi shigowa kusan dukkansu da kuka suka shigo
wai ka kore su k’annenta kuma suna gidan yanzu haka.
Dama yadda na ji Mommy da su suna yiwa Daddy bayani shi kuma yana fad’a na san kawai ya riga ya hau shiyasa ban saka Baki ba.
Na yanzu ya faru sai a kiyaye gaba dan Allah Yash karka basu k’ofar da zaka janyowa baiwar Allah n nan bak’in jini a wajen Daddy…”
Ajiyar zuciya ya sauk’e daganan yace
“InshaaAllah’’
Ba a wani dad’e ba su Manubiya suka dawo
Sark’ar gold Ummi ta bata y’ar k’arama wadda ba za ta wuce 4OOK ba a cewarta ta ajjiye a tunanin ta za’ayi bud’ar kai ne sai ta bata tou kuma ashe su basa bud’ar kai…daga nan ta d’an yi mata nasiha.
Mommy kuwa sallama kawai sukayi daganna suka fito Manubiya tana mamakin yadda yanayin fuskarta ya chanja dan d’azu sam ba haka ta yi mata ba a gaban Yash.
Yash yaji dad’in gift d’in Ummi matuk’a kuma bai ji dad’in rashin ganin gift daga wajen Mommy ba yana sane ko a lefe ma ba ta basa komai ba Mom da Hajiya mama sai Yahanasu ne kawai suka bada…dukda ya san yau d’in ranta a b’ace yake
amman ai dama Uwa tana tanadan gift d’in amarya a irin wannan ranar ko da ace ta bayar da na lefe,ya san maybe za suce ai ya yi komai ya saka komai amman ai Ana bada gift ne saboda karramawa ba wai dan babu ba.
Har mota Yahansu da Munirat da Yassir suka rakasu da Yadira da akwatunan ta biyu.
Sai da suka ga ficewarsu tukunna suka nufi main door,
signal kawai Yassir ya yi wa Munirat daga nan Yahanasu bata san inda sukayi ba ita dai ta ganta ta shiga parlourn ita kad’ai.
Kausar tana ganin ficewarsu ta windown d’akinta ta koma ta kwanta ta fashe da wani irin kuka babu abunda yafi b’ata mata rai irin yadda yake wani rik’e mata jaka yake bud’e mata murfin mota.
Tana kwance tana ta faman kuka a haka ta ji an bud’e k’ofar d’akin an shigo.
Ta san Mommy ce dan haka tace ‘’I’m fine”
Murmushi Mommy tayi ta nemi guri ta zauna a kusa da ita kafin tace”Ki yi hak’uri Kausar
saura d’an k’an’kanin lokaci
nasan da ciwo amman ki k’ara hak’uri…
Ki duba kiga yanzu da ikon Allah Daddy ya fara karkatowa side d’inmu duk abunda muke so shi yakeyi.
Shima Yashjub d’in ki duba kiga ni ko b’acin raina ba ya son gani ai da ba haka yake ba.
Ki kwantar da hankalinki na yi miki alkawri indai kina da ni bazakiyi kuka ba…”
Ahankali ta tashi ta zauna tana kallon ta tace”thanks for everything Mommy,but na ga suntafi da Yadira kenan ba ranar dawowarta nan gidan kwana kusa kenan?idan fa ba ta dawo ba babu ta yadda za ayi mu…”
Cikin katse mata magana
Mommy tace
“Kar ki damu zata dawo
komai a hankali a keyi
ki kwantar da hankalin ki kinji”
Ahankali Kausar ta jin jina Kai daganan ta matsa ta kwanta a jikin Mommy tana mai sauk’e wata nannnauyar ajiyar zuciya.
Mommy tana so ta fad’a mata zancen tafiyar su Yash honeymoon amma kuma bata san ta Ina za ta fara rarrashinta ba dan ita kanta tun jiya da ya gaya mata ta rasa Ina za ta sa kanta…she just hope Yadira ta yi abunda ta tura yi a gidan…inshaaAllah in dai har ta yi to ita Manubiyan ce da kanta za ta tarwatsa batun tafiyar tasu.
Suna fita Daddy ya sauk’e ajiyar zuciya dan shima yana tsaye ta window yana kallonsu har suka fice….ya san he s a little bit hard akan Yashjub b
amman kuma idan bai yiwa tufkar hanci da wuri ba tou tabbas akwai matsala.. duba da yadda ya Yash ya kori k’annensa ranar da aka je d’auko amarya dukda ya san laifin su Yasira ne but a yadda shi da kansa ya rok’esa sannan ya ce su had’a kawunansu sam bai yi tunanin Yash zai sake korar su daga gidan sa ba,baya ga haka kalli yadda yake nan nan da Manubiya ya san zafin soyayya ya san ya mutum yake ji shiysa ya fahimci indai har bai tashi ya tsaya a kan Yash ya yi masa wuta wuta ba to a yadda ya rikice a kan Yarinyar tsaf zai yi fatali da zumunci ya zab’i soyayya……MANNUBIYA
(Book 2)
Page 24
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Tunda su Manubiya suka kamo hanya babu wanda yace ‘k’ala’ a cikin motar…Abu d’aya ta lura da shi shine yanayin Yash gaba d’aya ya chanja kamar yana fushi.
Sam ba ta yi mamaki ko ta ji haushi akan tahowa da Yadira da suka yi ba,kawai dai ta saka a ranta maybe hutu za ta yi musu ko kuma zaman d’aki ko kuma ma maybe za ta zauna a wajen su ne har abada tunda as far as she knows Yash shine Babba a gidansu kuma dole dama yadda yake da rufin asiri ya kamata ace yana ragewa Daddy waensu abubuwan.
Addu’arta d’aya itace’Allah Ubangiji ya sa Yadira kar ta zame mata matsala’…dukda ta lura ko d’azu da suka zo ita da Yusra ne suka gaida ita sannan yanzu ma bataga alamun rashin kunya ko rashin mutunci a tartare da Yarinyar ba,sai dai kuma ta fahimci ba sa yi mata rashin mutuncinsu idan a gaban Yash ne but yanayin Yarinyar na yanzu ta ga kamar ba irinsu bace ita dan haka ta saka kyakkyawan zato a ranta ta yi ta addu’ar Allah Ubangiji
ya sa su zauna lafiya ita da Yadira…dan tabbas ta san tafiyar Yadira ba kwana kusa bane idan ma za ta tafin d’in kenan!duba da yadda ta ganta da akwatunanta d’urma d’urma har guda biyu da jaka.Ta san ko tafiyar ma da za su yi honeymoon definitely sai dai su barta a gidan a turo wata babba ko mai aiki ta zauna da ita kafin su dawo….tanata wannan tunanin ta ga Yash ya d’auki hanyar gidansu,ba ta san lokacin da ta fara zuba murmushi ba wanda har sai da Yashjub d’in ya ji ya d’an juyo ya kalleta suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya kafin yayi wani d’an guntun murmushi ya maida hankalinsa ga tuk’in da ya ke yi.
Tun lokacin da su su Ya Musbah suka bar gidan Manubiya yake k’unci!.
Gaba d’ayan su sun ji haushi kuma sun ji babu dad’i game da halin da suka je suka tarar da y’ar uwar tasu a ciki amman kuma
dama Ya Nafi’u ya san akwai abunda yake damun Ya Musbahn kwana biyun nan dan tun kafin su je gidan Manubiyan ya ke la’akari da shi ya lura damuwar tasa ta yau ma ta fi ta kullum….shiru kawai ya yi masa ya na mamakin yadda k’iri k’iri wai yau shine Ya Musbah yake b’oye wa damuwarsa dan ya lura sam baya so ma ya fahimci yana da matsala.
Shiyasa yau kam ya na yin parking a k’ofar gidan ya cewa su Aisha “su shiga wajen inna, za su taho nan ba da jimawa ba da shi ya Musbah.
Sai da Ya Musbah ya bud’ewa Muhsin wanda suke zaune a gaban tare da shi ya fita
tukunna ya juya ya kalli ya Nafi’u ba tare da ya rufo murfin motar ba yace
‘’Jiya ma ka tambayeni kuma amsa d’aya zan baka,’ba abunda yake damuna’saboda dagaske babu abunda yake damuna d’in‘’.
Cikin tarar numfashin sa ya Nafi’u yace
‘’Ko kuma dai ba za ka gaya min ba saboda ka san ba zan tab’a goya maka baya ba ko?,
Haba Musbahu na fa san a kan Baraka ka shiga wannan damuwar.”kafin ya gyara zama ya fuskance sa tukunna ya d’aura da cewa”har wanne dad’i ku ka yi da Baraka da har zai sanya kake missing d’inta har haka?.
Baraka fa Musbahu!”
Ya k’arashe maganar tasa cikin rashin jin dad’i.
Shiruuu Ya Musbah ya yi kafin yace”ba fa a kan Baraka na shiga damuwa ba!shin ba ka ga halin da muka tadda Manubiya sannan muka baro ta a ciki ba ne?”
Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace“Jiya waye ya je wajen Baraka bayan sallar Magrib???”
Da sauri Ya Musbah ya d’ago ya kalle sa sai kuma cikin fushi yace “Bibiyata kake yi?”.
“Babu zancen bibiya a nan!
amsa kawai nakeso ka bani”.
Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya kallesa yace
‘’Wajen mai sunan baba na je, ko ban Isa na je naga d’ana ba??”
Cikin katsesa sannan cikin tsananin fushi Ya Nafi’u yace
‘’ba za ka tsaya ka gaya min gaskiya ba? Yau nine na zama wanda za ka yiwa wannan k’umbiya k’umbiyar???
Shikenan ka je ka yi ta yi,dama shawara ce zan baka amma tunda na ga bakaso fine!
In dai Baraka ce bismillah,ga ka ga ita amma inaso ka san cewa ba za ta tab’a chanza zani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’arin zare makullin motar ya fita.
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’d’an tsaya Nafi’u.”
Shiruu Ya Naif’un ya yi kamar ba zai kula sa ba sai kuma ya juya yana kallon sa tare da basa dukkan nin attenbtion d’insa.
Ahankali Ya Musbah ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Ina son ta,har yanzu’’
Wani irin kululun takaicin Baraka da tsantsar tausayin Ya Musbah ne suka lullub’e Ya Nafi’u a lokaci guda.Da kyar ya had’iye abunda ya ji ya tokare masa mak’oshi yana shirin yin magana ya ji Ya Musbah ya ci gaba da cewa
“Har gobe inason Baraka,har abada!.Kai Abokina ne kana fahimta ta akan komai dan Allah ka fahimceni ka bani goyon baya akan wannan ma.
Itama ta shiryu ta ce min za ta gyara halayyarta sannan tana so ta zo ta bawa su Inna hak’uri kuma tace za ta rik’e Muhsin.
Har yanzu ba ta riga ta fita a idda ba shiyasa da ni da ita muke so a had’u a gyara abun nan kafin ta fita idda kaga ba sai an yi sabon d’aurin aure ba.
Wannan shine abunda yaketa damu na, na rasa wa zan gayawa kuma ni a ganina Baraka za ta zauna lafiya da ni da kowa ma tunda yanzu Ina aiki kuma Inada rufin asiri.”
Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace
‘’Musbahu duk matar da ba ta zauna ta ci talaucinka ba to bata yi deserving arzik’inka da kai kanka ba.
Musbahu Baraka bata da kirki ta raina ka ta raina iyayenka…..”
Shiruuu ya Nafi’un ya d’anyi ya tsagaita da magana ya dafe kansa saboda ciwon da ya ji ya fara yi masa a sakamokon b’acin rai da takaicin Ya Musbah da Baraka.
Ya d’an jima bai ce komai ba kafin ya cika kan