Showing 201001 words to 204000 words out of 244445 words
za ta dawo ko su Larai d’in su nemota.Kuma indai Khadija ita ta haifi Yashjub ba zata bari Kausar ta b’ata masa suna ba,dan na san duk bakin su d’aya.
Abu simple very simple amma kuka gagara tsayawa ku yi lisssafi mai kyau sam saboda an had’a da asiri da wayo!!!
Saboda Allah kalli abunda kuka tafka!!ko
Shawara da ni bakuyi ba,kai da ake so a gyara gidanka a kub’utar da kai amma kalli yadda ka
sake damalmala komai!!!dan ba ka isa ka ce ka rabu da Khadija ba muddin Kausar ce matar Yash,ko ka kori Khadija a gidan nan indai Kausar tana a
matsayin Matar Yash wallahi ka yi ta banza ne…”
A hankali Abhi shima ya k’araso dan Daddy yana rik’e trolly ta sakar masa ta cigaba da zaro kayayyakinta rai a tsananin b’aci tana magana tana had’a kaya…cikin lallami yace”Hajiya mama ki yi hak’uri dan Allah mun yi laifi wallahi ni
kaina sai yanzu na ke ganin rashin dacewar hakan.”
Juyawa ta yi ta kallesa tace”kad’an daga aikin Khadija!ai ba za ku san lokacin da kuka d’aura ba dama…”
Cikin chanja topic d’in tace”ka
fara yi mini shirye shiryen tafiya meanwhile ka kama mini d’aki a hotel kafin komai ya kammala dan wallahi na gama zaman cikin gidan nan!”
“Innalilla wa Ina ilaihirrajiun”
Daddy yace kafin ya d’aura da cewa”Hajiya mama dan girman Allah ki yi hak’uri!!ina cikin garin nan da gidana amma ace kina hotel dan Allah ki rufa mini asiri,in dan har saboda Khadija ne to a yau za ta fita wallahi.”
Ya fad’i hakan kamar zai yi
kuka
Cikin b’acin rai tace”kar ka soma!!!ba zai you ka koreta saboda ni ba no matter what
sai dan halinta wanda na so in nuna maka ka runtse
Ido.
Ku zauna abunku kai da ita da surukarka Allah ya kareka daga sharrinsu zan dinga yi maka addu’a Ina daga chan…amma ba zan iya ci gaba da zaman a gidan nan ina tufka Khadija tana warware mini ba kai kuma kana biye mata!!ba zai yiu ba ba ni da wannan lokacin considering my age
yanzu lokacine da ya kamata ace na duk’ufa ibada da neman gafarar Ubangiji na.”
“Hajiya mama a yau Khadija za ta bar gid…”
Cikin fushi tace”wai
Ya ina magana ba ka ji nane??
Na ce maka ban yarda ba ko?
Ko shima taurin kai za ka yi mini ka nuna min iyaka ta?
A gaban yaranta za ka koreta saboda ni ko me??
Ka manta yadda muka yi ni da kai a asibiti ka manta abunda nace maka??
B’ata mini ran da ka yi ka k’i
jin maganata shiyasa zan tafi ka yi komai da kanka ni kam na tsame hannuna!ka bincika komai da kanka ka gyara gidanka ta hanyar da ta dace ba wai ka koreta haka kurum a gaban y’ay’anta saboda ni ba.”
Ya bud’e baki zai yi magana tace”Wallahi zan baka mamaki fa?da musu dakai kakeso
In ji ko da b’acin ran da kuka d’ura mini?”
A hankali Abhi ya d’an ruk’o hannusa alamun ya yi shiru dan ya san Hajiya mama yau kam ta riga ta gama kaiwa high!!!!
Daddy yana ji yana gani haka Hajiya Mama ta had’a kayanta tsaf tsaff ita da Junior suka tafi tsohon gidansa dan tace ko Abhi d’in ma kar ya biyo ta shima takaicinsa take ji idan kuma taga d’aya a cikinsu a inda take kafin ta wuce uk to sai dai ta k’arashe kwanakin ta a hotel har zuwa lokacin da za ta wuce uk.
Da Yamma Yashjub ya turo mata da message ta inda yake cewa”Jiya an d’aura masa aure da Kausar ba tare da yardarsaba a jiyan ya saki Kausar to kuma a jiyan Mommy ta zo ta sanyashi ya mayar da ita…yana da babban dalilin da ya sanya ba zai
Iya zama da Kausar ba sannan akwai abubuwa da dama a halin yanzu da suke damunsa waenda suka sanya ba zai iya ci gaba da zama a gari d’aya da su Mommy ba dan haka yana da buk’atar space da time dan Allah kar su nemeshi yanada buk’atar break daga fitinar family d’insa.”
Sai da Hajiya mama ta yi kuka da ta karanta message d’in Yashjub sosai ya tab’a mata zuciya,ace mutum shi da k’asar sa shi da gidan Ubansa amma fargaba da fitintinu sun hanasa ya sake ya rayu a wajen!!wannan wanne irin abu ne haka!!
Allah ya Isa tsakaninta da Mommy wallahi!…
Junior ta kira tace”ya je gidan ya duba mata idan sun riga sun tafi ko driver ne ya tambaya watak’il su gano inda suka nufa,ba wai binsa ko fad’an inda yake za ta yi ba kawai dai taana so ta san inda yake for her peace of mind..saboda itama ta goyi bayan tafiyar da zaiyi d’in d’ari bisa d’ari.
Har daren ranar Hajiya
Mama a fusace take ta k’i
ta kula kowa ta k’i ta saurari kowa kuma tace in banda Junior ba ta so ta ga kowa a inda take,hatta Yahanasu da ta je ba ta samu ganinta ba dan ta rufe d’akin ma da take ciki abubuwa da tunani sun yi mata yawa.
…….Tun ranar da su Mommy suka haifi Yashjub da Yahanasu ta kasa gane abu guda d’aya game da Mommy;kwata kwata ba ta d’aukarsa ya dad’e a hannunta kullum tana mak’ale da Yahanasu,a tunaninta kunyar Haihuwar fari ce takeyi amma sai ta lura kamar ma haushin Yaron take ji tun ba ma da ta ce a bashi madara ba wai ruwan nononta bai zo ba amma Likita yana zuwa da aka tilastata aka matso sai ga ruwan Nono fall yana zubowa…
Tun daga wannan lokacin ta saka mata ido dan tashi d’aya kwakwalwarta ta bata ko dai saboda maganar dukiya da Imam ya yi ne ya sanya Khadija ta musanya y’arta da d’an kishiyarta!!saboda a lokacin Yahanasu da take jaririya kamanninta sun yi shige da na Baba Larai da ta fara girma ne dai ta koma kamannin Daddy.
Shi kuma Yashjub da Daddy yake kama da yana jariri amma yana fara yin wayo har kawo yanzu da Khadija amaryar Daddy yake kama,sam ba ya kama da Mommy.
Har kusan shekara d’aya zuwa biyu Hajiya mama ba ta gano wata hujja da zai sanya ta ce Yashjub ba d’an Mommy bane saboda yanzun kuma yadda Mommyn take yi masa babu wanda ya Isa yace ba ita ta haife sa ba,kuma a wannan lokacin ba ta san Mommy da mugayen halaye ba,shiyasa kawai ta kawar da komai ta cire shakku ta cigaba da addu’a ta mik’awa Ubangiji lamuranta ta barshi ya yi ikonsa dan har yanzu zuciyarta ba ta daina yi mata wasi wasin ‘anya Yashjub dan Mommy ne kuwa!!?’Gashi ita Babba ce ba zai yiu ta tada husuma akan wannan gagarumin al’amari haka ba azo a yi bincike aga ba haka bane gashi Ubangiji da kansa yace “kar ka tsananta bincike”
Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru ta ci gaba da addu’a,A lokacin ne kuma Mai gidanta ya rasu mahaifin su Daddy dan haka zaman ta ya dawo Gidan Daddy tunda shine Babba.
Sai dai ko sati ba ta iya yi a gidan ba ta ji komai ya fita a kanta ta tsani gidan ta tsani jama’ar gidan hakan ya sanya ta koma Uk da zama.Dukda tana so ta d’an saka ido akan zaman Daddy da amaryarsa saboda a lokacin dukda Daddyn ba ya yiwa Amaryarsa abubuwa a gabanta amma ta fahimci akwai matsala sai dai kuma ba zata iya zama a gidan ba dan haka ta hak’ura ta tafi bayan ta had’a su su biyu Daddyn da Amaryartasa ta tambayesu Daddy yace mata babu komai ba fad’a suke yi ba.
Itama amaryar haka.
Bayan shekara biyu ta zo hutu,a wannan lokacin ne ta ci karo da layu da abubuwa a d’akin Mommy k’asan gadonta lokacin Yashjub yana wasa ya tura Abun wasan nasa a k’asan gadon ya isheta sai da ta zo ta duba ta d’auko masa dan su Khadijan duk basa nan sun fita barka…
Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba saboda har da tsaka mai rai a cikin kwalba da abubuwa na tsafi kala kala ta gani a k’asan gadon Yarinyar da kusan rainon ta ma ita ta yi.
A lokacin Mahaifiyar Mommy itama ta rasu,kasancewar Hajiya Mama babbar k’awa ga mahaifiyar Mommy kafin rasuwar ta ya sanya ta ga ba laifi bane ba idan ta kirata ta zaunar ta yi mata magana ta kub’utar da ita daga kan Hanyar b’ata da halakar da ta d’auka wanda ba ya b’ullewa.
Dan haka suna dawowa ta nemi ganinta, sai da suka keb’e iyaka su biyu kawai tukunna tace mata“ta ga abubuwan da ta ajjiye a d’akin ta a k’asan gado”….nasiha sosai Hajiya mama ta yi mata tace “ ta rik’e Allah da addu’a shi zai sa Imam ya so ta ba wai tsafi ba,a duk lokacin da ka yiwa mutum tsafi ya so ka to fa idan abun ya karye tsanar da zai yi maka sai ta fi ta farko….”
Kan Mommy a k’asa lokaci da Hajiya mama take yi mata nasihar kuma daga ‘to’ sai ‘inshaaAllah’ kawai take ta cewa amma tana ji Daddy ya shigo tashi d’aya kawai sai ta fashe da kuka kuma ya yi tambayr duniyar nan ta k’i magana,ita kanta Hajiya mama kasa magana ta yi tsabar shock. Sai daga baya tukunna da kyar ta bud’e baki ta gayawa Imam d’in cewa “nasiha take yi mata akan biye biyen malamai”ita ba ma tace masa ta ga abu a k’asan gadon Mommyn ba!,
Ita Mommyn ce da kanta tace”ai Hajiya maman tace ta ga kaza ta ga kaza a k’asan gadon ta waye waye…”
Har da abunda Hajiya Mama bata ce mata ta gani ba duk sai da ta lissafo kaff abubuwan da suke a k’asan gadon nata
Tana magana tana kuka! kukan da duk wanda ya gani sai ya tausaya mata.
A take Hajiya mama ta ga alamun b’acin rai a fuskar Imam amma dai bai ce komai ba ya yi shiru,ganin Yarinya tana shirin shiga tsakaninta da d’anta ne yasa tace “to a je a duba”
A take with full confidence Mommy ma tace “ta yarda a je a duba”
Tun daga nan jikin Hajiya mama ya yi sanyi dan sai a lokacin ta tuna ba ta gyara katifar sosai ba dan ba zata iya ba ta yi nauyi,maybe Mommy ta gani sun gane an duba wajen watak’il sun kwashe….ai kuwa hakan ne dan ana zuwa in banda k’ura da akwatuna babu abunda aka gani a k’asan gadon Mommy.
Daddy bai ce mata komai ba,sai bayan kwana hud’u Allah kad’ai ya san mai da mai Mommy ta yi masa ta kuma fad’a masa tsabar an shanyesa hakanan ya zo yana ce mata wai”akwai wani Likita da zasu je ta gani idan mutum yana hallucination shi ake gani a kaff garin he’s the best”
a lokacin kacha kacha ta yi amsa ta koresa amma tundaga ranar daga ta ga k’adangare a d’akinta sai ta ga maciji kuma idan ta je ta tattaro mutane aka zo aka duba ba’a ganin komai! Hakanan za ayi ta kallonta ana mata kallon tab’abb’iya.
Ganin Mommy tana shirin haukatata ne ya sanya ta tattara kayanta ta d’auki Yashjub tace zai je ya yi musu hutu ta tafi da shi,dan abunda Mommy ta yi mata ya sanya ta fahimci tabbas za ta iya aikata fiye da chanjin Yaro ma.Tun da ga lokacin ta san yadda ta yi ta d’auke Yashjub gaba d’aya daga gabanta dan indai harshashenta daidai ne to kuwa ta san tsaff Mommy zata iya cutar da shi ko ma ta kashe sa,tunda indai saboda dukiya ne ta musanya Yaran to kuwa bata ga reason d’inta da zai sa ta barshi a raye ba yanzu dan yanzu kam dukiya ta dawo hannunta,ita da su Yassir………
Yanzu kuma da Mommy ta tura su Yasira suka zubar wa da Manubiya ciki hakan ya sake assasa zarginta ta fahimci komai,shiysa ta cewa Daddy ya barta a gidan su yi bincike a kanta sosai saboda tana so ta gano gaskiyar lamari da kuma duk wasu abubuwan da ta aikata a b’oye su samu evidence a kanta ta yadda za su fi hukunta da hujja, dan tabbas ta san Mommy ta dad’e tana cutarsu ba tare da sun sani ba..to shi kuma Daddy gashi yanzu ya sake k’ak’abawa Yashjub Kausar.
Ta san ba laifin su bane ba amma she can’t help it dole ta fusata saboda abun ya tab’ata sosai.Dan Auren Kausar da Yashjub kamar an sake kafe Mommy a cikin zuriarta ne….
Sallamar Junior ce ta katsewa Hajiya Mama tunanin da take yi,
A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta kallesa tace”ba sa gidan ko?”
Jinjina kai ya yi yace”driver d’insa na samu yana tartare kayansa yace mini wai an sallameshi ne saboda Yash d’in yace masa “sun tashi daga gida”
Yau da asubah wai ya kaisu hotel d’azu kuma ya je ya d’aukesu ya kaisu airport,yace bai san jirgin Ina suka bi ba.
Ajiyar zuciya ta sauk’e tace masa”ba ni wayata”kawai.
Yana mik’a mata ta nemo number Daddy ta danna call ta kara a kunnenta.
Ko gaisuwarsa ba ta amsa ba tace
“Yashjub ya tafi ba ya nan,ya turo mini message ya gaya mini abunda Khadija ta je gidansa ta yi Jiya,yace min dan Allah kar a nemesa.
Dan haka Ina mai baku umarnin kar wanda ya bibiyesa kamar yadda ya buk’ata,
ku bar shi ya huta da bala’in Khadija da y’ay’anta.
Ka ja mata kunne ka jawa su Yasira kunne sannan ka gaya wa d’an uwanka shima ya sani.”
Tana gama fad’in haka ta kashe wayar ta ajjiye a gefe zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Daga wajen Hajiya mama direct gida Yahanasu ta nufa dan tana son magana da Mommy yau kam ba za ta yi shiru ba!abun ya yi yawa.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 40
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
A d’akin su Yadira ta same ta ita da su suna hira…
Tana shigowa duk suka d’ago suka kalleta sai kuma suka d’auke Kai babu wanda yace mata ci kanki hakanan suka ci gaba da hirar su,Mommy tana shirin yi mata magana ita Yahanasun ta riga ta ta hanyar cewa”Ina so za mu yi magana!”
Sai da gaban Baba larai ya yanke ya fad’i dan in ba da kyar ba a yadda ta ga Yahanasu yau kam tabbas za ta iya fasa mata kwai a wajen Mommy kuma ta san Mommyn za ta ji haushinta.
Kallon Yahanasu Mommy ta yi kafin ta d’an kalli Baba larai sai kuma ta mik’e ta nufi Yahanasu n ba tare da ta saurari
Yusra wadda take cewa”eh lallai rainin hankali ma kenan.”ba.
Duk idanu suka zuba musu Baki sake har suka fice daga d’akin.
Side d’in Mommy suka nufa suna shiga Mommyn ta kalleta tace”ya aka yi ??Yahanasu”.
Har ga Allah ta san bai kamata ta dinga jin haka game da uwar da ta kawota duniya ba amma she can’t help it!
Wani Irin haushi da takaicin Mommy take ji,ba ma ta jin za ta iya tsayuwa su yi wata doguwar magana dan haka cikin k’aguwa da son barin inda take ta d’an matso kusa da ita tana kallon cikin idanunta tace”ki cewa Yashjub kin janye maganar tsinuwa sannan ki daina treatning d’insa da tsinuwa idan ba haka ba wallahi tallahi sai na gaya masa cewa ‘ba ke ce kika haife sa ba’!”.
Wani irin zabura Mommy ta yi jikinta ya d’au karkarwa gaba d’aya ta fice a haiyyacinta tashi d’aya fuskarta tayi jazur.
D’an k’ura mata ido Yahanasu ta yi kafin tace”as I suspected..ba ki san na sani ba ko?to kuwa wannan karon Baba larai ta munafurce ki.”
Hawayen da suka zubo mata ne suka sanya ta yin shiru itama Mommyn hawaye ta ke yi sosai zuwa yanzu.
Da kyar Yahanasu ta tsayar da hawayenta ta goge fuskarta ta ce”A ranar da kuka dawo daga makarantar mu!a ranar da kuka je kuka had’a guiwa da principal d’inmu kuka saka ta shirgawa Mama k’arya kuka ce Daddy ne ya fad’a!to a ranar ne na ji komai.
….” Tun lokacin da Mama ta fara zuwa wajena a makaranta na so in fad’a muku ke da Daddy amma sai ta ce mini ba ta so ku sani wanda a da laifinta na gani da ta nemi in b’oye muku amma da na ji abunda kuka yi kuka saka aka ce mata Daddyn yace! ne ya sanya na fahimci dalilinta na cewa in b’oye muku.
Tana zuwa wajena a kai a kai har ta fara yi mini maganar tana so za ta d’auke ni in zauna a wajenta zan bita?!’ni kuma na ce mata ‘eh’. A wannan lokacin shekaruna ba su haura takwas a duniya ba amma sai na yi lissafin cewa idan na b’oye muku wannan al’amari to
kamar na munafurceku ne,dan haka na yanke shawarar gaya muku ke da Daddy saboda daga ke har shi kuna nuna min tsananin soyayya shiysa na ga rashin dacewar b’oye muku zancen.
Ina zuwa dai dai k’ofar d’akin ki na ji muyarki cikin fushi kina cewa”Larai!!wannan yana d’aya daga cikin dalilan da suka sanya na ce miki kar mu fitar da Khadijah har ma da mallan lawal d’in amma kika k’i yarda kika ce ba za ki iya bari su mutu ba!
Yanzu ai ga irinta nan inda ace Daddy ne ya fara jin labarin zuwan da Khadija take yi wajen Yahanasu ya san cewa ta na raye har yanzu ai da mun shiga uku!!!kuma dan mun ce wa principal ta ce mata ga abunda Daddyn yace ke kina tunanin za ta hak’ura ta daina bibiyar y’arta ne?dan kawai ance za a tona mata asiri?ina ce farrak’u kika ce kin yi mata da duk ahalin gidan nan sannan kin kafeta a duk inda take?to ya akayi ta fito?”
Kai na ne ya d’aure dan ban gama fahimtar me kike nufi ba sai da na ji batun Baba larai tukunna na fahimta,ta inda take cewa”Kar ki damu akasi aka samu amma zan gyara sannan saboda Allah Mommu yanzu ace duk Irin taimakon da lawal ya yi mana sai mu barshi ya mutu??ba dan shi ba ai da tuni Khadija har yanzu tana tare da Imam…”
A lokacin I was 8 amma tashi d’aya na fahimci abunda kuka yi na fahimci komai saboda a ko da yaushe cewa ake yi gobara ne ya