Showing 168001 words to 171000 words out of 244445 words
a lokacin ya warware ragowar igiyar aurensa d’aya da ta yi saura a kanta,dama kwanaki tun farko da ta hana auren Yassir da Kausar ta taso masa da maganar Khadija ya sake ta ba tare da ya fad’a mata ba gudun ma kar ta tada masa hankali, ya bari a kan sai ta fita daga idda tukunna zai sallameta,tausayinta ya ji ta kuma ci darajar y’ay’anta shiyasa kawai ya mayar da ita a wannan lokacin yanzu kuwa ya riga ya rufe ya gama babu sauran aure a tsakanin su shi da ita kuma sai ya zo korarta tukunna zai sanar mata ya dad’e ma da sakin ta.!…
Awa biyu su Inna suka yi suka tafi ita da Muhsin suka bar Siyama,suna tafiya Yahanasu ta zo,itama tsoro da tsananin tashin hankali sun rufar mata dan ita kam tana tsaka mai wuya ne a wannan al’amarin saboda itama Ummi tana gama gaya mata lissafinta da zarginta akan Mommy ya dira.
Ita ta zauna a wajen Manu ita da Hajiya Mama da Siyama,dan ita Hajiya Mama ma tace”a asibitin za ta kwana da Manubiya”
A chan gida kuwa zuwan Kausar biyu side d’in Yash amma a rufe,gashi duk wayoyinsa a kashe,dan haka ta gayawa Yassir shi kuma yace”kar ta damu…gasunan zuwa idan suka zo dole zai bud’e daga nan sai su san abun yi.
After 3 hours
Su Mommy ne suka fara dawowa sai
Ummi da ga baya Daddy…babu kalar bugun da ba a yiwa Yashjub ba amma ya k’i bud’ewa.Najeeb ma ya zo shi da Yahanasu dan zuwa yanzu Manubiya ta farka kamar yadda ta yi bacci da sunansa a bakinta tana farkawa da sunan sa ta fara.
Daddy ne ya je ya nemo spare key da kyar ya samo ya zo ya bud’e k’ofar suka shiga amma wani abun takaicin iyaka waiting parlour da corridor kawai suka tarar dan ya rufe k’ofar shiga da ma duk wasu k’ofofi.
Zuwa yanzu sun fara tsorata shiyasa Daddy ya ware murya ya shiga kwala masa kira….
Tun a bugun farko Yash ya ji su duk kuma abunda suke yi yana jinsu kuma ya saka a ransa ba zai kula kowa ba he needs some time alone….
Sun fi minti ashirin a wajen Daddy da Najeeb har ma da Yassir da Junior waenda suka zagaya ta baya saitin d’akin sa suna ta faman kwala masa kira!
Jin muryar Daddy har ta dashe yana kiransa yana haki da nishi su Najeeb kuma suna cewa bari kawai a nemo masu b’alle k’ofa ne ya sa kawai ya mik’e ba don ya so ya nufi k’asan.
Ta cikin glass door d’in suka hangosa ya taho dan haka hankalinsu ya d’an kwanta,yana zuwa ya d’auki key d’in a jikin k’atoton frame d’in da ya mak’ala ya saka ya murza ya bud’e musu ya koma cikin parlourn ya nemi guri ya zauna,dan bibbiyu yake gani wani Irin mahaukacin jiri yake yi.
Jiki a salub’e hakanan suka shigo suka nemi guri suka zazzauna.
Kasa magana duk suka yi kowa ya yi shiru suna mamakin yadda ya rame tashi d’aya fuskarsa ta yi jazir ya yi wujuga wujuga.
Yahanasu ce tace”Yash bawa fa baya wuce k’addararsa,duk abunda kaga bai zama naka ba it wasn’t yours to begin with!Allahn da ya baka ya karba shi zai mayar maka da mafi alkhairi,don’t torture yourself ka rungumi k’addara mana!you have to stay strong Yash ita ma Manubiya tana da buk’atarka a gareka za ta samu support da kwarin guiwa if you are this weak ta ina zaka fara bata support ka kwantar mata da hankali??”
Ga mamakinsu kawai sai suka ga hawaye ya shiga sintiri a kan fuskarsa babu k’akk’autawa abunda dayawansu ba su tab’a gani ba dan haka suka shiga al’ajabi Mommy kuwa kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha ita da Baba larai,cikin jan hanci da share fuskarsa da tafin hannunsa ya juya ya kalli Daddy yace”Daddy I want to be alone!dan Allah.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e shi kad’ai ya san me yake ji ji yake yi kamar ya yi super ya damk’i wuyan Mommy har sai ya ga ta daina numfashi.Cikin jinjina kai yace”okay Yash,but kar ka sake kulle k’ofofin ka.”ya d’an yi tapping kafad’ar sa tukunna ya mik’e yace”kowa ya fito”ba tare da ya yarda ya kalli direction d’in Mommy ba,daga haka ya sa kai ya fice.
Haka nan duk suka fita one by one aka bar Yashjub Najeeb sai Yahanasu,Yusra da Yadira tun kafin a je koina har sun fara dana sanin abunda suka aikata dan basu yi tunannin d’an uwan nasu zai shiga wannan halin ba,a tunaninsu kawai zai sake ta ne ta tafi shikenan a wuce gurin ba su yi tunanin zai tsaya yana turturing kansa har haka ba su sai yanzu ma kwakwalwarsu ta yi lissafin tabbas fa zai shiga damuwa da tashin hankali dan a yadda yake son Manubiya dole ya shiga masifa idan aka ce ta yi betraying d’insa…..also! they are not supposed to feel sorry for her amma yadda suka ganta a asibitin a kwance rai a hannun Allah ga ciki ya zube haka nan sai ta basu tausayi,shiyasa gaba d’aya suka shiga wani yanayi har sai da su Mommy suka lura.Ya’isha kam ko a jikinta daddana wayarta take yi tana bawa Yassira wadda take office update dan ita da Yasmeen ne kawai babu a wajen sun tafi aiki.Tana gama tura mata ta ja ta tsaya jiran fitowar Najeeb su kuma suka wuce.
Suna gama fita Najeeb ya k’arasa ya murza key ya dawo ya zauna a kusa da shi,cikin tattausan lafazi yace”Yash akwai wata matsalar ta daban ne?”
Ya yi masa tambayar yana mai kafe sa da ido,d’agowa shima Yashjub d’in ya yi ya zuba masa shanyayyun rinannun idanunsa kafin yace”Najeeb tunda nake a rayuwata ban tab’a kwallafa rai a abu kamar Manubiya da Babyn da na rasa a yau ba,a ganinka hakan bai Isa ya jefa ni a damuwa ba?”
Numfashi Najeeb ya sauk’e kafin yace”sorry for your lost Yash,Allah ya sa mai ceto ne ya baka masu albarka.”
Sau kuma ya sake fesar da numfashi kafin yace
“Yashjub baka tab’a b’oye mini komai ba sai yau dan tabbas na san bayaga b’arin da Manu ta yi akwai wani abun da yake damunka,if not Yashjub d’in da na sani ba zai bar Manubiya a asibiti ita kad’ai a wannan lokaci da tafi buk’atar sa ba.”
Runtse idanuwa Yashjub ya yi ba tare da ya bud’e ba yace”Najeeb ka je kawai,kaina ya na ciwo ina da buk’atar kasancewa ni d’aya!”
Cikin d’an b’acin rai Yahansu tace”Yash amma ka bani mamaki matuk’a!dan inda ace wani ne ya gaya mini cewa ka hau ka zauna akan abunda Doctor ya gaya maka wallahi ba zan yarda ba.”
Da sauri ya mik’e tsaye yace”Yaha plssss.Not now!”
Ya fad’i hakan cikin d’an b’acin rai.
Itama cikin b’acin rai tace”yanzu zamu yi Yash!yanzu za mu yi saboda yanzu nake so in tabbatar kaine kuwa ko ko dai wani ne mai kama da kai ya zo mana dan Yash d’in da na sani ba zai yarda da k’azafin da Likita ya yi ba.”
Cikin rashin fahimta Najeeb yace”Yahanasu me kike cewa?me kike nufi kun bar ni a duhu.”
Sai da ta gama zabgawa Yash harara dan ji take yi kamar ta rufesa da duka,tukunna ta juya ga Najeeb tace”Nima d’azu Ummi take gaya mini,Doctor d’in cewa ya yi maganin zubar da ciki ta yi ta sha har cikin ya zube.”
Da sauri Yash ya lumshe idanuwansa ya koma ya zauna dab’asss a kan kujerar yana jin kansa yana wani irin juyawa,dan Yahansu tana fara maganar ya ji komai ya dawo masa sabo ciwon da zafin da zuciya da kwakwalwarsa sukeyi sun sake hauhawa.
Cikin rashin jin dad’i sannan a hankali Najeeb yace”and you believed him?”
Ya yi maganar yana kallon Yashjub.
Cikin tarar numfashinsa Yash ya kallesa yace”Nima ban sani ba!iyaka abunda zan iya fad’a kenan ‘nima ban sani ba’!”
“Ka yarda kenan!ka yarda mana idan ba haka ba da baza ka shiga wannan halin ba!da ba za ka k’i zuwa inda take ba Yash wallahi ka bani mamaki.”
Cewar Yaha.
Kallonta ya yi zuciyarsa tana wani Irin tafarfasa yace”kin san me na gani?kin san me na ji?”
“Sai ka fad’a!”
Ta bashi amsa cikin takaici…
Tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda suka yi da Abbakar a yau kafin ya je asibiti…..
Cizan labb’a Najeeb ya yi bai jira ya kai aya ba ya katsesa ta hanyar cewa”Tabbas Yash ba don na san gigin giyar kishi ce take d’awainiya da kai ba wallahi da sai na rufe ka da duka!
Bari ka ji abunda ba ka sani a kan Abbakar ba…za ka iya tuna ranar da ka zo ka same ni akan mu je gidan su Manu kanason magana da ita urgent muka kira Abbakar ya yi mana kwatance,bayan y’an mintuna ya kira yace sun tafi k’auye?”
Bai jira jira jin me zai ce ba yace”to k’arya yake yi dan a ranar ma sai da Manubiya ta yi exams kuma ai kaga abunda ya faru next na case d’in black snake wanda hakan yake sake nuni da bbu inda taje tana cikin garin amma ya yi mana k’arya saboda son ta yake yi mata sam ba ya so ka rab’eta!.
A ranar da na bashi katin ka na yi masa bayani nace ya bata tun daga ranar na fahimci son ta yake yi ban gaya maka ba saboda gudun irin wannan abun da ka aikata da zargi a tsakaninku Ashe na yi ta banza tunda gashi Yaro k’arami ya juya maka lissafi!
Saboda ita fa ya nemi transfer dan tunda aka fara maganar aurenku ya gudu aashe kwanciyar kura yayi ya je ya yi sabon shiri ya dawo da niyyar tarwatsa ku!.
A gaskiya Yash ka bani kunya dan ban yi tunanin za ka yarda da …..”
Cikin tarar numfashinsa Yashjub yace”Najeeb I saw there chat!”
Kamar Yahanasu za ta rufe sa da duka tace”kuma sai ka yarda ita ta yi?”
“To wa ya yi? Wayarta ce kuma number ta na gani da dp da komai nata ga chats nan na gani waye ya yi idan ba ita ba?besides not just chats,na ji ta tana waya da shi tana cewa,sai da na fita tukunna ta samu damar yin wayar….da asubah! Sannan kusan kullum yana kiranta ina gani ba ta d’auka a gabana…”
A hankali Najeeb yace”me ka gani a chats d’in?”
Sai da ya share hawaye tukunna yace”Najeeb shiyasa tun farko da ka tambayeni na ce muku ban yarda ba!saboda i can’t believe wai Manubiya zata yarda ta yi maganata da shi sannan har ya yi mata prescribing maganin da za ta sha ya zubar mata da ciki na da ke a jikinta.”
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Najeeb da Yahansu suka ce a tare kafin Yahanasu ta matso ta zauna a gefen sa ta kamo hannayensa tace”Yash look at me!”
Sai da ya juyo ya kalleta tukunna tace” da ka ji Manu tana waya da asubah ba da kowa take waya ba da ni ce!”
Da mamaki ya kalleta wanda hakan ya sa ta jinjina masa kai tace “tabbas…na yi wa Manubiya alk’awarin ba zan fad’a maka ba amma yanzu kam ya zama dole in fad’a maka….”
Tiryan tiryan ta zaiyyano musu komai game da yadda Manu tace mata ta taimaka mata suma su yi participating a case d’in estate d’insa,ba za ta nad’e hannu ta zuba ido ana wasa da rayuwar mijinta ba! Da binciken da suke yi akan case d’in da kud’ad’en da Manu ta bayar duk dan a yi bincike duk sai da ta gaya musu komai ba ta b’oye ba tukunna ta d’aura da cewa”wallahi ka godewa Allah Yash dan samun mata irin Manu ba kowa ba Manu mace ce tam kar dubu!Allah ya zab’e ka kar ka yi masa butulci.
Maganar chats da shan magani kuma ni na san aikin su waye amma ba zan fad’a maka ba saboda wani dalilinawa kawai Ina so ka tsananta bincike a kai ka duba cctv ai akwai a gidan ka ka yi bincike sosai ta nan ne za ka gano waye ya d’auki wayarta,waye yake saka magani a abunshanta ko cin ta duk za ka gani.”
Ahankali Najeeb ma ya zauna a gefe suka saka shi a tsakiya yace”Yash shaid’an ya tsani ya ga ana zaman lafiya an yi aure ana soyayya tsakani da Allah,nan za ka ga ya fara saka zargi da abubuwa a zuk’atan maaurata,bayan Abbakar da sharrin zubar da ciki da chats Yash akwai shed’an dan Allah ka daure ka yi trusting matar ka duk rintsi! ba fa a aure da zargi babu kyau ka daina dan Allah kar ka sake wannan tab’argazar shi kuma Abbakar ka bar ni da shi sai na ci uwarsa wallahi zai san Ina ya zo”.
“I don’t think he’s still alive dan dukan da ni yi masa ba lalle ya rayu ba”
Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin yace”mu yi addu’ar ya rayun dai”
“InshaaAllah ya mutu”
Yash ya fad’a cikin d’aci yana jin tsanar Abbakar tana sake taso masa.
A hankali Yahanasu tace”ai yanada magoya baya shi kad’ai ba zai iya aikata wannan b’arnar ba…..”
Shiruu duk suka yi Hatta Najeeb shima zuciyarsa sisters d’in Yash d’in ta zarga tunda it’s obvious ba sa sonta,amma kuwa da sun cika dabbobi dan in har za su iya kashe d’an wansu to kuwa abun nasu Azimun ne!ya godewa Allah da ya rabu da Ya’isha bai aureta ba…….
A b’abgaren Yash ma yadda Yahanasu ta yi masa bayani da komai ba bu wasu waenda suka zo kansa sai su Yasira tunda tare suke da su a cikin gidan,sai dai kuma no matter what so yake ya maida zarginsa akan gwaggwo saboda yanzu haka a cikin tashin hankalin binciken estate d’insa yake yana jin tsoron sakamokon shiyasa yake addu’a Allah yasa idan ya yi binciken ya gano gwaggwo ce kawai ba y’an uwansa uwa d’aya uba d’aya ba.!…
Yahansu ce ta ce”Manu da sunan ka ta yi barci a bakinta…ka tashi ka j….”
Tun kafin ta rufe bakinta yace”Bara in je in ganta…..”
Murmushi duk suka yi cikin tsananin jin dad’i suka mik’e Najeeb yace”na san ba zaka fad’awa kowa ba but pls Yash misunderstanding d’innan da kuka samu da abunda Doctor yace inaso ya tsaya a iyaka mu uku!sannu kamar yadda yaha tace ka yi bincike,Allah ya sa mu dace.”
Jinjina kai Yashjub ya yi yana jin wani sanyi yana lullub’esa kafin yace musu”thanks,alot”a hankali.
Murmushi duk sukayi suka ce ya dage da addu’a ya cire komai a ransa daga haka suka wuce shi kuma ya hau sama domin ya d’auko makullin motarsa……
Har wannan lokacin Ya’isha tana tsaye tana jiran Najeeb.
Sallama ya yi da Yahanasu ta wuce shi kuma ya d’auke kai ya yi kamar bai ganta ba ya had’e rai ya nufi motarsa da sauri wanda hakan ya sanya itama ta nufosa da sauri amma kafin ta k’arasa tuni ya shige ya bata wuta ya yi reverse an wangale masa gate ya fice da mugun gudu.
K’amewa kawai ta yi a wajen ta kasa motsi kafin da kyar ta ja k’afafuwanta ta wuce garden tun kafin ta gama shiga ta fashe da wani irin kuka.
Junior kam yau ya samu fuska a wajen Yadira ba laifi dan suna shiga Yusra ta wuce sama su kuma suka zauna a main parlourn…gaba d’aya jikinta ya yi sanyi shiysa ya sameta yau ta d’an sake da shi wanda murna da farin cikin sa sam suka gagara b’oyuwa.A rayuwarsa yana mutuwar son Yadira so ba na wasa ba,Allah ya jarabcesa da masifaffiyar k’aunarta.
Ummi tana zuwa za ta d’aura girki ta tarar gwaggwo har ta kusan kammalawa dan haka ta sa hannu ita da Munirat suka yi na duka gidan suka gama daga haka suka wuce asibiti suka je suka kai musu bayan ta had’a na Yash a daban daban ta ajjiye.
Babu yadda ba ta yi da Hajiya Mama ta hak’ura ta koma gida ba tunda ga Siyama amma tace”ba komai za ta kwana da Manubiya da safe sa chanjeta.”
Yashjub yana hawa sama aka fara kiran sallar Magrib,dan haka ya ce bari ya kama ruwa ya yi alwallah kafin ya wuce.Zuciyarsa ta yi sanyi zuwa yanzu amma ciwon da kansa yake yi ba kad’an bane ba,yana buk’atar ya sha magaani
Amma a yadda yake jiri a yanzun ya san idan ya sha babu komai a cikinsa wahala zai sha gashi a side d’in babu cima tunda ba zama ake yi a ciki ba kuma ba zai iya tsayawa cin abinci ba ya san zai d’auki lokaci, dan haka ya kira gwaggwo a waya yace”ta had’o masa coffe dan Allah yanzu da sauri zai sha ya sha magani da shi kafin ya wuce sallah.”
Lokacin da ya kira ta tana shirin kawo masa abunci dan haka ta ce “to shikenan”.
Daga haka ta katse ta ajjiye basket d’in ta shiga had’a masa coffee d’in.
Kausar tana kitchen d’in a wannan lokacin dama tana tunanin ta yadda za ta aiki gwaggo ta samu ta ajjiye basket d’in Yash ta juye abinda ta k’unso a cikin abuncin nasa a kai ta ji ya kira ta.Ba k’aramin dad’i ta ji ba da ta ga gwaggo ta fara had’a coffe saboda dama ta riga ta yi
diluting abun kuma ta san idan ta zuba akan farar shinkafa ko miyar agusin da suka yi zai gane,coffee d’in will be perfect wajen yi mata sauk’in juyewa……
Yana fitowa daga band’akin ya chanza kaya zuwa jallabiya ya d’auki wayoyinsa ya kunna,sai da ya gwada layin Manu akace masa tana barci tukunna ya zuba a aljihu ya d’au makullin mota ya nufi k’asa dai dai gwaggo tana shigowa da basket.
“Yauwa sannu gwaggo iyaka coffee d’in kawai za ki zuba mini,ya fad’i hakan yana mai sauk’owa daga stairs d’in a gurguje.”
Itama da hanzari ta shiga zuba masa kafin ya k’araso cikin parlourn har ta gama zubawa.
Sai da ya nemi guri ya zauna tukunna ya karb’a yace “sannu gwaggo”
Daganan ya fara k’ok’arin kaiwa Baki.
Gani yayi ta tsaya tana kallonsa dan haka ya ajjiye cup d’in ya zuba mata dogayen idanuwansa kafin yace
“Lafiya dai ko gwaggwo?
Akwai matsala ne!?”
Da sauri ta yi firgigit kafin tace”laa a’a ba komai”sai kuma ta juya ta fice ranta duk ba dad’i…ba ta so ta taso da case kuma a zo a yi bincike
aga ba komai ta shiga masifa
amman haka kawai
ta ji ba ta yadda da Kausar ba!
Ta gama had’a coffee d’in kenan Kausar d’in ta ce mata”ta je sama ta d’auko mata