Showing 138001 words to 141000 words out of 244445 words

Chapter 47 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16438

cikin zuciyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita…..

Ganin kuka ba zai fishsheta ba ne ya sanya ta share hawayenta ta mik’e jikinta yana wani irin karkarwa ta ajjiye abun ta shiga lissafin neman mafita.
Tashi d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji dan haka ta fito ta nufi side d’in Mommy jikinta har yana wani Irin karkarwa.



Su Mommy suna isa gida ta wuce sama d’akinta,Baba larai tana ganin haka ta bita da sauri…
Sai da ta kai k’ofar d’akinta tukunna ta lura da Baba larai dan haka tace”larai ki je kawai ina buk’atar space..”
Daga haka ta bud’e ta shiga tana k’ok’arin rufowa Baba larai ta sa hannu ta tare k’ofar ta shiga ta rufo,Mommyn tana shirin yin magana ta ji Baba larai tana cewa”Khadija zama na a cikin gidan na ya k’are dan haka na zo ne in yi miki sallama sannan in gaya miki abunda ya faru da kuma taimakon da na yi miki d’azu wanda ya taso na gaggawa.Daga nan ni kam yanzu ba sai anjima ba zan tafi!”.
Runtse idanuwa Mommy ta yi kafin ta bud’e tace”dan Allah Larai ki barni in huta tukunna we’ll talk anjima..”
Cikin tarar numfashinta tace “Au wai a tunaninki barazana ce nake yi?…wallahi wallahi na gama sakawa a raina Khadija barin gidan nan zan yi! Dan ba zan zauna rashin hak’uri da rashin lissafinki ya kaini prison ba!.Bari ki ji abunda ba ki sani ba d’azu kuna fita na ji Daddy yana waya,ko kin san wanene ya kirasa?”
Kallonta Mommy ta yi tukunna tace”A’a”
Sai da Baba larai ta sake ce mata “kin san wa ya kirasa?”Mommyn tace “a’a”
suka yi haka sau uku tukunna Baba larai tace”Mallan lawal!”
Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Mommy ya yi kafin cikin in Ina tace”mme yya ce mmasaa??”.

“Cewa ya yi yana son magana da shi inaga,dan ji na yi yana cewa”mallan lawal dama kana raye Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” sai kuma ya fara basa hak’uri kafin na ji ya yi shiru yana sauraronsa sai
kuma yace na godewa Allah nauyi d’aya ya sauk’a a kaina mallan lawal amma ba za ka iya gaya mini ta waya ba dole sai na zo??”

Daganan na ga ya fice compound ya nufi parking lot, to inaga case d’in Yashjub ne ya tsayar da shi ba dan haka ba da tuni yanzu yana garin Garin Mallan……
Cikin takaici Baba larai ta d’aura da cewa“wallahi Khadija in da ace ba ki tsaya dawo mana da aiki baya ba da tuni ba mu zo nan ba!,na gaya miki Yarinyar nan barinta tare da Yashjub masifa ne a gareki amma kin k’i ki bada goyon baya a samu a fitar da ita daga rayuwar tasa cikin sauk’i yanzu ga irinta nan! Idan kika ga yadda hankalin Daddy ya tashi ya rud’e za ki yi mamaki lokacin da ya ji mallan lawal yana a raye…kin san yanzu zai fara wasu wasin mutuwar Khadijah ko?”
A mugun rikice Mommy tace”larai shiyasa tun a lokacin na ce a kashe su kika ce A’a za ki san yadda za ki yi dasu yanzu ga irinta nan ai”
sai kuma ta fashe da kuka cikin gunjin kuka tace”wannan duk ba laifin kowa bane laifin Manubiya ne ita ce wallahi tun da ta zo ta lalatamin komai larai na gaji kashe Yarinyar nan zan yi wallahi kuma ba ki isa ki hanani ba…”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”ba za a yi haka da ni ba,in da ace zan barki ki kashe rai da tuni mun yi tun a kan Khadija..hak’uri za ki yi ki kwantar da hankalinki ki danne zuciyarki tukunna ki ci riba ba zan tab’a gajiya da gaya muku da ke da su Yassira ba saboda hakan ne kad’ai mafita”.

Cikin wani irin kuka Mommy tace,Baba larai yanzu to
ba Manubiyan ba,shi mallan lawal d’in Baba larai mun bashi second chance amma kinga yanaso ya tona mana asiri na rok’e ki da giraman Allah ki taimaka mini ki rufa mana asiri a kawo k’arshen sa dan wallahi na san gaskiyar lamari zai fad’awa Daddy idan har suka had’u if not menene zai sa yace yana son ganinsa?…”

Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”kar ki damu..Daddy yana fita na kira mutumin da muka ce ya saka mana ido a kansa,ashe ciwon hanta ne ya ke damunsa likita yace ba shi da sauran lokaci shiyasa yake neman Daddyn ya samu ya gaya masa gaskiya.”
Numfashi ta fesar kafin ta ci gaba da cewa”tunda dama mutuwa zai yi shiyasa kawai na cewa mutumin ya k’ara masa gudu zamu bashi naira miliyan d’aya,to dai a halin yanzu Ina tabbatar miki mallan lawal ya tafi kai balance dan mutumin a lokacin ce mini ya yi a take zai aiwatar da aikin dan gidan dama ba kowa shi mallan lawal d’in ne kawai da shi da jikarsa ita take jinyar sa to alokacin ya ga ta tafi kasuwa……yanzu miliyan d’ayan za a tura masa dan naga ya kirani d’azu Ina asibiti shiyasa ban d’auka ba.!Muna tura masa ni kuma zan kama gabana dan ba zan zauna ki ci gaba da lalata m….”
Cikin Jin dad’in maganganunta Mommy ta rungume Baba larai wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa abunda take cewa,wani kuka Mommy ta fashe dashi tana cewa”na gode Larai na gode sosai ki bani accnt number miliyan biyu ma zan bashi wallahi….sannan zan gyara wallahi zan yi yadda kike so dan Allah kar ki sake cewa za ki tafi.”

Da kyar Mommy ta lallab’a Baba larai ta hak’ura da tafiya,daganan suka kira mutumin ya shaida musu cewa”Mallan lawal yana ma shirin shiga k’asa a halin yanzu dan wanka ma ake yi masa.”
Naira miliyan biyu Mommy ta tura masa a take daga nan ta nutsu tana sauraron hud’ubar Baba larai.


Da sallama Yasira ta turo k’ofar d’akin ta shigo,kafin ta k’araso ta zo ta tsaya a gabansu.
Kallonta kawai Baba larai ta yi ta maida hankalinta ga Mommy kafin tace”a baya da kika iya kwantar da Kai wacce kalar riba ce ba ki ci ba?yanzu kuwa kinga ai komai lalace miki yake yi saboda rashin tunani da lissafin da kika bawa ragamar rayuwarki,kuma bari ki ji ba ni da tantama a yau Yash ya dasa ayar tambaya a kanki wallahi saboda abunda kika yiwa Manubiya a gaban kowa ya na nuni ne da kin tsaneta dama tun asalin farko wanda hakan zai sanya ya fahimci dama chan pretending kike yi kuma bakin ku d’aya ke da su Yasira duk ba son matarsa kuke yi ba!dan haka yanzu ko ciwon yatsa Manubiya ta yi Ina mai baki tabbacin Yashjub ke zai zarga tunda dama ba wata shak’uwa ce a tsakaninku ba balle ya ki zarginku,kuma ko su Yasira sun je gidan ido zai sanya musu ya dinga d’arr d’arr da su ta yadda ba su isa yin komai ba shikenan kina ji kina gani Manubiya zama daram!
Hakanan abubuwa za su yi ta faruwa da mu,tunda kink’i ki bada goyon baya mu samu a yi abunda za ta tafi.
Shiysa na yanke shawarar in tartara ya nawa ya nawa in kama gabana tun kafin bomaboman da za su iya hallaka ni su fara fashewa.”

Ajiyar zuciya Yasira ta sauk’e kafin tace”Mommy nima gaskiya abunda kika yi yau ban ji dad’in sa ba….”
Cikin tarar numfashinta Baba larai tace”Yasira yo
ai har da ku!”
Jin jina kai Yasira ta yi kafin tace”ni kam zuwa yanzu Baba larai duk yadda kika ce inshaaAllah hakan za ‘a yi,saboda hakan ne kawai mafita,gara in yi tolerating d’inta in nuna ina sonta in ja ta a jiki na wata d’aya ko biyu akan mu rayu da ita har abada muna fama da ita tana janyo mana masifu kala kala,na tabbatar kashe Ya Yash da aka so yi a yau shima duk a cikin masifun da take tafe da su ne!.”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta kamo hannun Baba larai ta ci gaba da cewa”dama ai ya san za mu je mu tayata gyaran gidan ko?”ba ta jira jin mai Baba laran za ta ce ba ta d’aura da cewa”zan yiwa su Yasmeen magana da su Yusra na yi miki alk’awarin inshaaAllah daga yau mun chanza zani,amma Ya’isha ba za ta bimu ba dan na san za ta iya b’ata mana komai…ki had’a duk wasu abubuwa da ya kamata inshaaAllah this time around ba za mu baki kunya ba ,za ki sha mamaki…”


“Allah ya yi miki albarka Yasira,zuwa dare zan ganku ke da su Yasmeen d’in kafin ku tafi”

Jin jina kai Yasira ta yi kafin ta kalli Mommy tace mata”Daddy yana son ganinki…”
Daga haka ta juya ta fita ta rufo musu k’ofar….

Tana fita Baba larai ta saki murmushi dan tabbas ta hango jajircewa a idanun Yasira,ta san kuma su Yasmeen ma za su yi mata biyayya inshaaAllah wannan karon akwai nasara….cikin jikin Manubiya za su fara farma a yadda Yash yake ji da cikin nan ta san easily za su samu matsala da shi da ita idan har suka nuna masa kamar Manubiyan ce ta zubar,but tayaya za su nuna masa hakan??dole su nemo reason da zai yarda da shi……
Tana wannan tunanin ta ji Mommy tace”bari in je…”
Kallonta Baba larai ta yi kafin tace”Juyin duniya!Khadija kar ki kuskura ki bari ya fahimci kin san wani abun”
Jinjina kai Mommy ta yi gabanta yana dukan uku uku ta juya za ta fita…cikin son kwantar mata da hankali Baba larai ta ruk’o hannunta tace”ki kwantar da hankalinki…”
Hawayen da suka b’allewa Mommy ne suka sanya ta kasa ci gaba da magana,a hankali ta rungumota ta shiga lalllashinta..fashewa Mommy ta yi da kuka cikin kukan tace “dan Allah dan annabi larai kar ki sake cewa za ki tafi,a wannan worst situation d’in larai idan kika tafi kika barni Ina makomata??…”

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e ta cikata tace”ba bu inda zan je amma Khadija kema sai kin chanja zani!kamar yadda su ka yi alk’awari dan Allah kema ki gyara…mu samu Yarinyar nan ta tafi daganan mu aura masa Kausar bayan shekara d’aya ko biyu idan ta haihu muka samu abunda muka so sai mu k’arasa shirin mu a samu a rufe chapter nan wallahi na gaji,sai abu d’aya ake yi yau kusan shekara nawa amma ba riba!”

Ajiyar zuciya Mommy ta fesar kafin tace”Larai I can’t trust Kausar with Yashjub anymore,a da na d’auka soyayyar da take yi masa mai sauk’i ce ko kuma lust ko wani abu makamancin haka shiyasa na yi tunanin idan suka yi shekara d’aya ko biyu ta samu abunda takeso ta haihu ta d’an zauna da shi ya fara fita a ranta to za ta iya yi mana abunda mukeso dan na san tunda ba ya sonta musguna mata zai ta yi…amma yanzu na fahimci masifaffiyar soyayya take yi masa,no matter what she’ll stick around and always love him unconditionally….abunda Yasmeen ta yi mini akan batun zubar da cikinnan ya sanya na fahimci Yaran nan ba za a dad’e ba kowacce za ta fara fito da nata view d’in tana jayayya da ni,kuma indai har Yasmeen y’ar cikina za ta iya yi mini hakan to abu mai sauk’i ne ga Kausar dan ta bijere mini,shiyasa na gama yankewa akan’babu maganar Kausar da Yashjub za mu san yadda za mun yi amma I can’t trust Kausar akan wannan Lamarin gaskiya…..”
Shiruu Baba larai ta yi kafin tace”to amma kuma ta ya za mu samu wanchan abun kenan?ko mun b’ata shekaru a banza kenan?ki duba future d’in Yassir ki sake tunani….”shiruu Baba larai da maganar ta d’an yi tunani kafin tace”to ko Manubiya za mu jira ta haihu idan ta haifa sai mu rik’e…….”

Cikin katseta da d’an b’acin rai Mommy tace”haba larai!ke fa da kanki ki ka sanar da ni illar kasancewar Manubiya a tare da Yashjub kuma gashi muna gani muraran!…besides ko dan masifar da wannan cikin da Uwarsa da Ubansa suka sakani a ciki wallahi dole sai ya fita!ko ana ha maza ha mata……”



K’ausar tana hawaye,a haka ta k’arasa side d’in Mommy ta shiga ta wuce parlourn ta nufi bedroom,har za ta tura k’ofar d’akin ta shige ta ji Mommy tana cewa”za dai mu san abunyi za mu nemo mafita amma cikin jikin Manubiya ya zama dole ya fita,sannan ba zan tab’a bari Kausar ta auri Yashjub ba!.”
Wani irin duhu duhu dishi dishi Kausar ta fara gani…ita da ta zo a kan ta cewa Mommyn ‘mai zai hana a yi tricking Yash ta samu ciki ta yadda dole sai ya aureta…’
amma shine take jin wannan batun daga bakin Mommy??
Dama ita ba ta yi shirin gaya mata tana da ciki ba dan ta san ba za ta yarda a aurawa Yash ita da cikin Yassir a jikinta ba,shiyasa take so ta bata wannan idear ta yadda ko shi Yassir d’in bai Isa ya san cikin nasa bane kawai kowa a tafi a kan cikin Yash d’in ne,ta samu ta rufawa kanta asiri burinta ya cika.Sam ba ta yi expecting haka daga Mommy ba,wato ta barta ta gama lalacewa shine yanzu take kyamar ta had’a d’anta da ita kenan ko yaya?
tabbas blood is thick! Ita kuma ta tabbata all alone….
Wani Irin kuka ne ya taho mata dan haka ta yi sauri ta juya gudun ma kar su jiyo ta ta nufi k’ofar parlourn hannunta a kan bakinta tana mai k’okarin hana sautin kukan nata fitowa.Kusan karo suka yi ita da Daddy wanda ya turo k’ofar parlourn ya shigo.
Shi ya wuce ya nufi d’akin ita kuma ta fice ta nufi d’akinta tana kuka kamar ranta zai fita.

A tsaye ya same su ita da Baba larai….sum sum haka Baba larai ta sa kai ta fice bayan ta yiwa Mommy wani kalar kallon da su kad’ai su ka san me take nufi.

Tana fita ya lumshe idanuwansa ya d’an bud’e kafin ya k’arasa kusa da ita yana mai kallon cikin idanuwanta yace”mallan lawal ya rasu”
Gefe da gefe ta kalla kamar irin tana tunani d’innan kafin tace”Daddy mai ya faru??? Kai fa ka ce a daina maganar nan kuma yau kai da bakinka ga shi ka kawo ta?”

K’ura mata ido ya yi,dama yana so ne ya ga reaction d’inta ko zai iya kamata da laifi amma babu alamun hakan a tartare da ita!
Ya san yadda Mommy ta kula da mahaifiyar Yahanasu suka zauna lafiya idan ya zargeta a kan incidence d’innan to bai yi mata adalci ba,amma kuma tunda mallan lawal ya kirasa d’azu ya fara basa hak’uri yana cewa yana son magana da shi to tun daga nan ya fahimci anya ba sharri aka k’ulluwa Khadijansa a wannan lokacin ba kuwa! sannan kuma kan sa ya d’aure matuk’a ta inda yana da tabbacin mallan lawal d’in ya mutu tun shekaru wajen ashirin da bakwai baya amma yanzu gashi ya ji sa a raye dan ko a mafarki idan ya ji muryar mallan lawal sai ya gane,shiyasa tashi d’aya ya tabbatar akwai k’umbiya k’umbiya a cikin al’amarin..
Khadija ba ta shiga ko mak’ofta sai tare da Mommy kuma ko hayaniya ba ta tab’a yi da kowa ba ita ba ma ta iya fad’an ba,duba da haukar da Mommy ta yi a lokacin da yace zai k’ara aure da kuma yadda ta shiryu lokaci guda ta rungumi Khadija tashi d’aya dama tun a wannan lokacin ya ke zarginta kuma ya ke ganin kamar akwai abunda ta ke shiryawa amma bai yi tunanin za ta iya yi mata wanchan sharrin ba!

Dan Khadija ko y’an uwa ba ta da shi balle ace wani ne ya yi mata sharri tabbas wannan aikin Mommy ne…
Sannan a cikin gidan ya yi waya da Mallan lawal ya san maybe Baba larai ce za ta gaya mata,shine ta kashe sa kenan??gudun kar asirin ta ya tonu?Tabbas kuwa indai hakan ya tabbata to bai ma san wanne kalar hukunci zai yanke mata ba!
Matsalar guda d’aya shine yadda ta yi d’innan ba dan shi da kansa gaba d’aya alamomi suna masa nunin kamar ita ce master ba,to ba dalilin da zai sanya ya zargeta.

A b’angaren Mommy kuwa in banda lugude babu abunda zuciyarta take yi!k’arfin hali ne kawai yake amma a mugun Muhsin hargitse take tun da ya shigo ta firgice…

“Daddy ka yi shiru”
D’in da tace ne ya katse masa tunani…
A hankali yace”yanzunnan ya rasu”
Wata zabura ta yi tace”innalillahi wa inna ilaihirrajiun,
Daddy dama chan bai rasu ba??me ya faru?kiranka ya yi?”.
Ta fad’i hakan ita kanta ba ma ta san ta fad’a ba tsabar rashin sanin tudun dafawa,kar ta yi shiru ya zargeta shiyasa ta zab’i ta yi maganar da ta zo mata.

Wani kalar mahaukacin bugawa zuciyar Daddy ta yi dan tabbas Mommy ta k’ulle kanta da kanta..ta ya aka yi ta san kiransa ya yi?

Jin jina mata kai ya yi yana jin kamar ya shak’e ta ya kashe ta right away,da kyar ya iya cewa”kira na ya yi ya ce in yafe masa yana buk’atar gani na da gaggawa.”

Zuwa yanzu yadda Mommy ta fara gumi ya gama tabbatar masa da komai,dama abunda ya zo tabbatar wa d’in kenan shiyasa ya zo mata a haka,cikin son sake ganin reaction d’inta yace”tun lokacin da ya kira ni ya fara magana gaba d’aya hankalina ya karkarta ne a kan watak’ilan Khadija ma tana raye.”

A take ya ga idanuwanta sun fara ciccikowa da hawaye kamar za ta yi kuka…da kyar bakinta yana wani irin karkarwa ta samu tace”Noo Daddy it can’t be,idan shi ya rayu ita ba zai yiu ta yi rai ba,ko ka manta yadda ita d’in da hannunka fa ka c….”
Yadda taga idanuwansa sun yi jaaa a take ne ya sa ta had’iye maganarta ta sunkuyar da kanta,kafin da kyar ta sake d’agowa tace”amma ban sani ba sai dai mu fara bincikenta,watak’il itanma she made it out alive..saboda ka san dama na gaya maka wajen yadda ya koma ba mu iya detecting ko da biro ba ballantana gawa komai ya kone k’urmus ruwa kawai muka yayyafa aka yi musu salla a haka…..”

Wuff kawai ta ga ya juya ya fita zuciyarsa ta na wani irin tafarfasa dan ya san tabbas idan ya ci gaba da zama to zai iya aikata abun ban mamaki ga Mommy…Mommy ta yi masa abubuwa daban daban tun daga kan yadda ta tilasta masa aurenta har kawo yanzu kullum a cikin b’acin ranta ya ke,amma bai tab’a tunanin za ta iya aikata haka ba,sannan gashi still k’ok’arin b’oyewa amma ya san ta yadda zai kamata dumu dumu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login