Showing 99001 words to 102000 words out of 244445 words
basa da m burin raba aurenta da Musbahu murus rabuwa ta har abada kuma shi ba wai yanaso ta dawo baneba kawai dai a nasa b’angaren duk abunda Allah ya tsara tou zai yi maraba da shi…Kawai shi babban abun da ya b’ata masa rai shine yadda aka dawo da ita da wurwuri ba tare da ta gama gane mutuncin iyayensa ba
dan yanzu ba ta horu ba ya tabbatar ko da gidan gyaran Hali aka kaita bai ci ace ta yi hankali a cikin wata uku da y’an kwanaki ba.
Saboda Allah tsabar rashin lissafi ace wai duk kalar tujarar da Baraka ta yi amman Musbah ya maido da ita ko idda ba ta fita ba sai kace er gwal!.
Ba kalar fad’an da Baba bai yi ba,daga k’arshe ma kawai ya mik’e zai fita dan takaici yasa yake ji ba zai iya ci gaba da zama a cikin d’akin ba.
Yana Isa bakin k’ofa ya ci karo da Ya Musbah da mai sunan baba.Bai gama k’are musu kallo ba ya ga Baraka a bayan su…da farko so ya yi kawai ya zagayeta ya wuce amman kuma sai ya koma ya nemi guri ya zauna..
To dai Allah kad’ai ya san kalar turare da rubutun da Baraka ta yi ta sha dan tashi d’aya zuciyar Baba Inna da Jidda har ma da Muhsin wanda shigowarsa kenan daga d’akinsu ta yi sanyi.
Har k’asa da durk’usa ta bawa Inna hak’uri tana kuka tana cewa sharrrin shaid’an ne
haka shima ma Baba ta basa hak’uri.
Har Jidda sai da ta bawa hak’uri Akan abubuwan da ta yiyyi.
Daganan d’akin ya d’auki shiru
kafin Baba ya kalli Ya Musbahu yace “ka riga ka maida ita ko?”
Jin jina kai ya yi alamun ‘eh’
ya na mai jin kunya da nauyin Baba.
Ajiyar zuciya Baba ya sauk’e kafin ya ce”Sai ku tare da wuri,
Allah ya so naga gidan naka babu kowa a ciki”
Daga haka ya fara k’ok’arin fita.
Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya d’an yi gyaran murya yace
“Wai da sai nan da sati biyu tukunna dan itama ta samu ta bayar da kayayyakinta gyara nima kuma akwai y’an gyare gyaren da zan yi a gidan.”
Jin jina kai kawai Baba yayi daga haka ya mik’e ya ce “Allah ya yi albarka.”
Yana gama fad’in haka ya sa kai ya fice.
Sai chan dare tukunna Baraka ta tafi ta barsu da abubuwan mamaki…ko magana za ta yi da Inna sai ta sunkuyar da kai k’asa
Hatta Jidda yadda take janta a jiki abun sai da ya basu matuk’ar mamaki
Gashi tace za su tare ne tare da Muhsin
Shi dai Muhsin ya bita da to ne amman har ga Allah in ya tuno halayenta sai ya ji baya son bin su,matar da ada kwata kwata ko dariya ba ta yi masa bata jan sa a jiki yanzu kuwa tashi d’aya ta dawo kamar za ta goya sa dukda Yarone amma ya saka a ransa watakil dan ta ga Innaa ne kuma dan taga Gidan su ta zo shiyasa take ta faman lallab’asa ya san yana zuwa gidan ta zata fara cin k’aniyar sa.
Dukda yadda yanzun yake jinta har cikin ransa amman still yana iya tuno halayen Baraka a gidan ta….
Jidda kuwa Allah Allah takeyi Baraka ta tafi ta samu ta kira Manubiya,dan kanta ya rabu biyu
It’s either
Fad’a akayi mata a gida da kuma yanayin duniya da ta gani ta gane gaskiya ta yi dana sani ta shiryu da gaske
Ko
kuma dai
Wani abun ne a cikin zuciyarta dan Barakar da ta sani ba zata nutsu irin haka a lokaci guda ba tare da kwakkwaran dalili ba……
Sai chan dare su Manubiya suka isa Gida dan sai da suka biya suka ci abinci suka d’an zagaya suka fara rage siyayyar su tukunna suka nufi gida kowa a gajiye.Suna zuwa Yashjub ya cewa Yadira “ta zab’a d’aki”
Na nan saman opposite d’akin Manubiya ta nuna dan haka ya cewa drivern gidan da ya tayasu hawowa da kayayyaki “ya saka mata kayan ta a ciki”.
Wanka kawai ta yi ko sallah ba ta nutsu ta yi ba ta d’auki abunda su Mommy suka bata ta fito.
A zaune ta sami Manubiya tana waya da Jidda tana bata labarin Baraka.
Kamar Manubiya za ta had’iyi zuciya kuwa haka taji..ashe dama shiyasa ta ga yanata tunani for the past few weeks,d’azu kuma ita a tunanin ta ma ko kukan da ta yi ne ya b’ata masa mood d’in sa ya saka shi a damuwa ashe shi tunanin shegiya Baraka yakeyi.
Taya Ya Musbah zai so Baraka ta dawo wanne irin abu ne haka!…a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e kafin ta d’ago ta kalli Yadira tace “zauna mana”
Sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tace “zan kiranku Jidda”daga haka ta katse wayar,tana mai jin kanta yana wani irin juyawa tsabar takaicin Baraka da Ya Musbah.
Tsaki Yadira ta yi kafin tace
“Ai ko ba ki fad’a ba!”
Sai kuma ta zauna tace”duk fushin da mutum zai yi nan gani nan bari..zama daram babu inda zanje”
Ahankali Manubiya ta d’ago ta kalle ta har za ta bata amsa sai kuma kawai ta mayar da kanta k’asa.
Ba tare da b’ata lokaci ba
kawai ta ga Yadira ta mik’e tafad’a toilet d’inta wuff!
A shirye da shirin ta na bacci tsaff ta ganta shiyasa abun ya bata mamaki ta shiga tunanin ‘to mai ta shige za ta yi…’
A b’angaren Yadira kuwa ba kalar barbad’en da batayi ba a b’an d’akin dukda ta ji ba dad’i kuma tana ganin abun somehow amman hakanan ta rufe ido ta yi ta bankawa tana yi tana jin wani iri dan kusan kullum a makaranta ita da k’awayenta basu da aiki sai zagin masu asiri da uwar da take koyawa yaranta asiri sai gata yau tsulum a cikin harkar dumu dumu…
Tunda ta shige Manubiya ta saki baki dan Yarinyar ta bata mamaki sosai
Ita ba ma wai batun zargi ko wani abun ba audacity d’in Yarinyar ne ya fi bata concern.
Tashi d’aya kuma sai ta ji gabanta ya yanke ya fad’i tsigar jikinta tana tashi dan haka Yadiran tana fitowa ta mik’e tace
‘’Dakata Yadira’’.
Ko kallon ta Yadira bata yi ba haka ta juya ta kama hanyar fita…tsabar takaici Manubiya bata san lokacin da ta matsa da sauri ta ruk’ota ba dan a ganinta wannan k’arshen rainin wayo kenan
Ta shigo ta gaya mata magana ta mik’e ta shige mata toilet kuma ta fito ko sallama ba ta yi mata ba zata fice
Shiyasa ta na ruk’ota ta juyo da ita cikin fushi tace
‘’akwai band’aki a k’asa na bak’i akwai a dakin ki akwai a corridor d’in saman nan sannan akwai a d’akin bak’in dake a k’asa,duk wani uzurin ki ki je ki yi a chan ko da wasa kar in sake ganin kin shige mini band’aki,bamuyi wannan sabon ni da ku ba as far as I know da kuma yadda kuke nunawa ‘kun tsaneni!’.’’
Cikin fushi Yadira ta fincike hannunta sannan tace
‘’Eh lalle Manubiya kin auri mai kud’i, Allah sarki d’an Adam mai manta gobe, yanzu ke har kin manta yadda ke da uwarki da ubanki kuke sharing band’aki shine yanzu har kike da bakin cemin wannan personal toilet d’inki ne…..”
Mahaukacin marin da Manubiya ta d’auke ta da shi ne yasa ta gagara ci gaba da magana dai dai nan ne kuma
Yashjub ya shigo cikin d’akin.
Da sauri ya k’arasa inda suke a tsaye yana cewa lafiya??!Baby mai ya faru har kika mareta haka?..”
Ihun kukan da Yadira ta fasa ne yasa ya kasa cigaba da magana,da sauri ya juya ya kalleta ya shiga duddubata yana kallon yadda shatin y’an yatsun Manubiya suka fito rad’au a fuskar ta..cikin kid’ima da tashin hankalin ya shiga addu’a a cikin ransa’Allah ya sa kar Yadira ta gaya wa su Mommy an daketa’ dan idan akwai abunda Daddy ya tsana to shine ka tab’a masa Yaro”
Cikin d’an fushi ya juya ga Manubiya yace‘’ next time idan ta yi miki laifi u report to me!kar ki sake marin ta.”
Daga haka ya ja hannun Yadira suka fice tanata uban kuka tana kiran sunan Mommy.
Suna fita Manubiya ta share zafafan hawayen da suka zubo mata ta durk’ushe a wajen….anya auren Yashjub ba mistake bane ba kuwa!
anya zata tab’a samu farin ciki a cikin gidan nan, gashi tun ba a je ko ina ba ta fahimci kamar so yake ya hanata karatu!da farko yace mata ba ya son chud’anyar ta da maza yanzu kuma ya zo yace”ya riga ya yiwa Najeeb magana zai sanar da ex colleagues d’insa su yi mata chuku chukun deferring zuwa nan da lokacin da za su dawo. Zai yi tunani kafin nan…”
Ta jima a tsugunne a wajen kafin ta mik’e ta fad’a toilet domin ta wanke fuskarta…
Tana shiga cikin band’akin lokaci guda ta ji duk duniya babu wanda ta tsana sannan ba ta son kallon ko da fuskarsa ne kamar Yashjub
Ita tunani ma ta fara yi wanne dalilin ne ya sa ta aure shi in the first place dan ta nemi soyayyar da take yi masa tashi d’aya ta rasata….
Suna shiga d’aki Yadira ta juyo tana kuka tace
“Wallahi Ya Yash ban yi mata komai ba!”
Cikin katseta Yashjub yace”ban tambayeki ba!.Yadira kin bani mamaki…ashe haka kika zama haka kika koyi k’arya?Manubiya mahaukaciya ce da za ta dake ki ba tare da kin yi mata komai ba?dama zuwa kika yi ki kashe mini aure? ashe bakya sona a matsayina na d’an uwan ki ni ban sani ba..”
Tashi d’aya ya fahimci yadda jikinta yayi sanyi k’alau dan haka ya sake tabbatarwa tabbas akwai abunda ta yiwa Manubiya….a tunanin sa su Mommy sun turota cid ne amman yanzu ya fahimci an turota ne ta kashe masa aure!
mai yayi wa su Mommy ne da har suke son rabasa da Manubiya su had’a sa da Kausar dan ko shi Yarone tou ya kamata ace zuwa yanzu ya fahimci manufarsu kenan
Mai yayi musu da zafi haka mai yasa duk yadda yake k’ok’ari wajen ganin ya shafe laifukan Mommy dole ita kuma sai ta san yadda ta yi ta nuna masa bafa ta son shi…..
Kasa ci gaba da tsayuwa a d’akin ya yi dan haka kawai ya juya ya fita zuciyar sa tanata faman tafarfasa.
Kitchen ya fara zuwa ya zauna a kan dining table d’in ya yi shiruu kafin chan ya nufi fridge
ya d’auki ruwan sanyi ya b’alle murfin ya kafa a baki sai da ya shanye tukunna ya ajjiye robar yana mayar da numfashi….ya jima kafin ya fito ya nufi sama d’akin Manubiya.
Yana shiga daidai ita kuma tana fitowa daga band’aki…d’auke kai tayi ta turo baki gaba ta yi kamar bata gan sa ba.
Murmushi yayi ya k’arasa inda take anan gaban madubin ya rungomata ta baya.
Yadda Manubiya ta ji ita kanta saida abun ya bata mamaki dan ji ta yi kamar wani k’aton arne ne ya rungumeta,saida ta yi da gaske tukunna ta lallashi zuciyarta da take azalzalarta akan ta hankad’e sa.
Ahankli ya d’an sunkuyar da kansa ya yi kissing wuyanta kafin yace “ki yi hak’uri Yadira Yarinya ce,um…”
ya fad’i hakan ya na sake rungumarta sosai izuwa jikinsa .
…Inaa she can’t take this anymore dan haka ta juya da sauri ta hankad’esa!ba dan Yashjub yana da k’arfinsa ba da sai ya zube a wajen.
K’ura mata ido ya yi sai kuma ahankali ya d’an matsa ya kamo hannunta yana kallon fuskarta da serious face yace “are u okay??”dan har wani jaa yaga idanuwanta da kan hancinta sunyi irin mutum yana cikin tsananin tashin hankali da b’acin ran nan.
Ba ta kulasa ba kuma yaga alamun bazata kula shin ba
dan haka ya sake matso ta a hankali da kyar kamar wanda yake jin tsoro yace”mai ta ce miki?
Mayene ya faru dear tell me menene matsalar??”
Tashi d’aya ta fashe da wani irin gigitaccen kuka wanda ya gigita Yashjub yana shirin sake matsowa tace
“Kar ka tab’ani ka fita kawai banason ganin ka!”
Kamar zai fashe da kuka yace
‘’baby ni d’in ne bakya son gani?ki yi hak’uri komai zai yi daidai yanzu sai kin d’anyi hak’uri da su am…”
Cikin katseshi sannan da k’arfi tace
“Ka fita nace!!”
Da k’arfi kamar ba mijin ta take yi wa magana ba.
Ahankali ya lumshe idanuwan sa ya bud’e kafin yace “to mu je d’akina sai mu yi magana ko??..in bakya son zama da ita a kusa ne mu je sama d’akina ki kwashi kayanki ma gabad’aya daga nan sai ki koma chan da zama ko?”
Wani kuka ta sake rushewa da shi ta durk’ushe a wajen tace
“Dan Allah ka fita bana son ganin ka!”
Wani irin bugawa zuciyar Yashjub ya yi dan kalamanta sun shige sa sosai…shiruu ya yi kafin kawai ya juya kamar mara lakka a jiki haka ya fice ya rufo mata k’ofar.
Sai da ya biya d’akin Yadira yace mata”Ko da wasa kar ta kuskura ta je inda Manubiya take ko sun had’u daga nan har gobe bai yadda ta yi mata ko da kallon banza ba
Infact ta zauna a d’akin ta ma kar ta kuskura ta fita koina sai gobe ai taci abinci..”
Da “to” kawai ta amsa shi daga haka ya juya ya fita.
Yana fita Yadira ta yi wani murmushi dan da da farko ta d’an ji tausayin sa ta ji babu dad’i amman taba tuno hud’ubar su Mommy da Yasira sai ta ware.
A take ta d’auki hoton fuskarta Inda shatin hannun Manubiya ya fito,tun daga kan Daddy har zuwa kan Yusra babu wanda bata turawa ba tace”Manubiya ta mare ta daga zuwan ta yau!”
Daga nan kuma ta kira su Baba larai tace “ta zuba abunda aka bata successfullly.”
Yashjub yana fita Mannubiya ta sake sakin wani irin kuka kamar ranta zai fita.
Ta jima tana kuka kafin ta mik’e da kyar ta fad’a toilet sai a lokacin ta lura da gari gari a zuzuube a cikin bathtub d’in ta da kuma k’asan tiles d’in..
Tashi d’aya ta fahimci mai ya faru a wajen ta kuma fara tunanin ko dai shiyasa ta ji ta tsani Yash lokaci guda
kawar da tunanin tayi da sauri ta yi ta’auzi da isthigfari a ranta tace”Mutum bai Isa ya yiwa bawa komai ba sai abunda Ubangiji ya riga ya tsara”
Sai da ta fara yin fitsari ta zuzzuba a duk wajajen da ta ga garin daganan ta wanke band’akin ta yi wanka ta d’aura alwallah ta fito still tana jin b’acin rai da takaicin da kuma tsanar Yash amma ba kamar
d’azu ba….
D’aukar wayarta ta yi da niyyar kiran Jidda taci karo da text na rashin mutunci daga Ya’isha ita bata ma san wa ya bawa Ya’ishar numberta dan itama ba ta da tata sai da taga ta rubuta sunanta a farko kafin ta d’aura da zage zage…hatta kakanninta saida ta zage tass gori kala kala zage zage kuwa har da ashar haka ta dinga rubutu sunan musu tana danna masa zagi…kuma ta tabbatar mata wallahi ko budad’e ko bujuma sai ta ramawa Yadira marin da ta yi mata…
A zuciye Manubiya ta fara typing d’in reply kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta ta tsaya ta danne yatsar ta akan delete ta goge tass!
Hawaye ne suka fara sintiri akan kyakkyawar fuskarta kafin ta yi jifa da wayar a kan gado ta zube a wajen ta fashe da wani irin kukan wanda ta dad’e rabon ta da tayi irinsa…
Ta jima tana kuka kamar ranta zai fita kafin ta d’auki waya ta kira Jidda…
Jidda tana zaune kiran Manubiya ya shigo wayarta dama ita take jira dan d’azu bata kaiga tambayar ta daliin kukan da suka sameta tana yi ba Manubiyan tace mata tana zuwa za ta kirata…
Tana d’auka ta kara a kunneta tace”assalam alaikom”
Muryar jidda da Manubiya ta ji ne ya sa ta sake fashewa da wani sabon kukan.
A rikice Jidda ta mik’e tsaye sai kuma ta d’an kalli Inna ganin tana baccinta ya sa ta fita da sauri.
Tana fita tace “subahannallah Adda Manu mai ya faru???..dan Allah ki yi shiru.”Ta fad’i hakan wasu hawaye suna zubo mata itama……
Da kyar Jidda ta samu Manubiya ta yi shiru ta shiga gaya mata abunda su Yasira su ka yi mata tun safiya har izuwa yanzu.
Sai da Jidda ta yi da gaske tukunna ta iya hanta kanta kuka dan ta san tana fara kuka za ta karya wa Manubiya kwarin guiwa ne.
Ahankali cikin rarrashi tace
“Adda Manu sai da su Innaa suka gaya miki zaman aure dama duk hak’uri ne…ki yi hak’uri kar ki d’aga hankalinki ki yi k’ok’ari ki cinye jarabawarki…kuma ni har ga Allah na d’an ji sanyi a raina tunda matsalar ba daga ya Yash take ba.Su waennan sisters d’in nasa nasan dolen ki ne su amman tunda basuda kirki sai ki ja jikinki ki rabu dasu gaba d’aya,ita kuma Yadira idan nice ke Allah sai na ga dama zan had’u da ita.
Karki d’aga hankalin ki ki lalata rayuwar aurenki tun kafin ki soma saboda su.
Idan suka zo inda kike ki yi musu iya ka mutuncin da ya kamata da zarar sun fara miki rashin mutunci ki tartara su ki watsar ki shige d’aki nasan ya Yash zai fahimta.
Sannan kamar yadda kika fara yau karki basu fuskar shige miki d’aki dan nan ne turakarki nan ne kaff gidan zaki shige ki zauna in sun fara haukar su ba tare da sun biyo ki ba wannan ni kaina na baki goyon baya ki tsaya ki sanar wa ya Yash kar su dinga shigar miki anyhow.
Sannan maganar fad’uwar gaba da garin da kike tunanin ta zuba miki kar ma ki saka haka a ranki balle ya yi tasiri..babu bawan da ya isa ya yiwa mutum abunda Ubangiji bai k’addara ba. Ke dai kawai ki yi ta addua ki dage da Azkar zan turo miki da wasu addu’o’i ma dana gani an turo a group na y’an class d’in mu sannan zan san yadda zan yi in sanar wa Inna ba tare da ta fahimci komai ba itama ta dinga yi miki addua.
Sannan dan Allah Adda Manu abunda kika ce kin yi masa muna gama wayar nan ki tashi ki je ki basa hak’uri tunda ma ya nuna cewa ki tafi d’akin nasa ni a gani na kawai ki kwashe kayanki ki koma chan saman sannan ki ce masa ba kyaso kowa ya dinga shigar muku,idan ya yarda hakan ya fi tunda dama ai turakarku