Showing 165001 words to 168000 words out of 244445 words
yace”pls follow me!”
Daga haka ya wuce ya nufi office d’insa.
Da kyar Hajiya Mama ta iya kamo hannun Yash ta rik’e sa ta mik’ar suka nufi office d’in har da Ummi aka bar Munirat ta shige wajen Manu.
Suna shiga likitan ya kallesu one by one kamar ya ce Yash ya fita dan ya san maybe shine Mijin sai kuma kawai ya zab’i ya yi maganar a gabansa dan haka ya kalle su yace”have a seat”
Saida duk suka zazzauna tukunna ya ajjiye takardar da yake rubutu a kai a gefe ya cire glasses d’in idanunsa ya kalli Hajiya Mama yace”ke grandma d’inta ce?”
A hankali Hajiya mama ta jinjina masa kai alamun”eh”
tsura mata ido ya yi kafin chan ya sauk’e ajiyar zuciya ya fara magana”ya kamata ku da kuke manya ku dinga saka idanu a kan y’ay’ayenku da jikokinku,ku dinga gaya musu abunda ya dace da wanda bai dace ba..yanzu gashi saboda kyaliyarku da rashin kula Yarinyar nan ta je ta yi ta shan maganin zubar da ciki kuma mai k’arfi,we lost the Baby!!but ni babban tashin hankalina anan shine ba lallai ta k’ara haihuwa ba saboda maganin da ta dinga sha yana da k’arfi kuma ta sha sa over ne….
A hankali Yash ya tura kujerar sa baya ya mik’e ya juya ya fice….kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya fita daga asibitin ya hau titi ya kama tafiya ba tare da ya ma san inda zai je ba………….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 34
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Ya yi tafiya mai nisa sosai dan sai da ya kusan k’arasawa gida ma tukunna ya tari Napep ya shiga ganin jiri yana shirin zubar da shi.
Yana shiga gidan dai dai su kuma su Mommy suna fitowa har da Yassir domin zuwa asibitin.
Ba su kula shi ba shima bai kulasu ba dan sun riga sun fito shi kuma napep Tana ajjiyesa ya afka cikin gidan,yanayin sa ba k’aramin dad’i ya yi musu ba dan ko ba’a fad’a ba sun san cikin ya zube shiyasa ya zama haka.
Direct side d’insa ya nufa
yana zuwa ya rufe ko’ina ya turawa Siyama message yace ‘Manubiya ba lafiya’daga haka ya kashe wayoyinsa ya rufe ko’ina ya kwanta ya yi shiruu.
Su Yassir suna fita ya turawa Kausar message kamar haka”Yashjub is home,he looks weak
and terrible,this is the perfect time…get ready.”
Hajiya Mama da Ummi suka tarar a d’akin Manubiya tana kwance tana barci dan tunda aka fito da ita ba ta bud’e ido ba.
Hajiya Mama ba ma ta san sun shigo ba dan ta yi zurfi a tunani matuk’a,idan a kwai abu guda da za ta iya rantsuwa a kai shine Manubiya ba za ta tab’a shan kwaya domin ta zubar da cikin jikinta ba sannan tunda har Doctor yace magani ta sha cikin ya zube tou kuwa maganin ta sha ba tare da ita kanta ta san tana sha d’in ba bi ma’ana drugging d’inta aka dinga yi har cikin ya zube!
Daga ita sai Yasira Yusra da Yadira a cikin gidan sai gwaggwo sai Yashjub.”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun rajiun” ta shiga maimaitawa a cikin ranta dan suspects d’inta su Yasira ne!Tabbas Mommy ta cucesu ta cuci jikokinta muddin hakan ta kasance dan ta san ita ce ta koya musu wannan muguwar dab’iar.
“Maama Ina wuni,ya mai jikin?”
Muryar Mommy ta katse mata sak’e sak’enta.
D’agowa ta yi kawai ta zuba mata idanu wanda hakan ya sanya ta sha jinin jikinta ta hau dibi dibi…kallonta kawai Hajiya Mama ta ke yi tana sakewa a ranta tana mamakin how can someone be this evil!tun tana Uk take mugayen mafarkai akan su Yasira da Manubiya shiyasa tunda ta zo aka ce mata suna gidan sam hankalinta bai kwanta ba amma kuma dukda haka bata tab’a kawowa za su iya aikaata wannan mugun abu da take zarginsu da shi ba!.
Da kyar ta iya cewa”lafiya Alhamdulillah.Jiki da sauk’i.”
Shiruu duk suka yi suna so su tambaya su tabbatar da cikin ya zube ne amma kuma suna shakkar kar Hajiya Mama ta gano wani abun dan iyaka kallon da take yi musu kad’ai sun sha jinin jikinsu,shiyasa suka ja bakunan su suka yi shiru.
Baba Larai ce tace”itakam wannan cikin nata mai laulayi ne,Allah dai ya raba su lafiya!”.
Sai da Hajiya Mama ta d’an k’ura mata ido kafin tace”Ciki kam wanda ya bayar ya karb’a ,sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo masu albarkaa Allah ya sa wannan d’in mai ceto ne.”
Guntun murmushin da Ya’isha ta yi da kuma ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Hajiya Mama ta gani ta ji dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa kawai ta hau salati a cikin ranta kanta yana wani irin juyawa..Tabbas an zo gab’ar da ya zamo mata dole ta shigo
rayuwar cikin gidan Daddy ta san abun yi,Mommy rub’abb’en seed ce da ya zamo dole ta b’intike ta tun kafin ta fara kisan gilla,ta riga ta cucesu ta yi poisoning mind d’in su Yasira ta kafa musu muguwar d’abia a ciki amma it’s not too late tana da yak’inin za ta ita gyara jikokin ta muddin Mommy ta yi nesa da su.
A hankali ta d’ago kanta ta kalli Mommy wadda sai a lokacin tace”To Allah ya kawo masu albarka”
Ita da su Yasira.
Cikin rashin son ganinta tace”ki tafi ki je wajen Yashjub!yana da buk’atar ki,za mu kula da Manubiya.”
Babu musu tace”to shikenan Hajiya Mama”dan itama so take ta gudu ta san tshoho duk inda yake ya fika wayo shiyasa take so ya yi nesa da ita gudun kar ta gano wani abun game da su dan wannan kallon da taga tana yi mata ta san ba na lafiya bane ba.
“Allah ya k’ara sauk’i.” Tace daga haka tayi musu
sallama suma su Baba larai suka yi musu daga haka duk suka fice zuciyoyinsu fess! kamar an yi musu bushara da gidan Aljannah.
Hatta Ummi sai da ta dasa ayar tambaya a kansu itama ta fara zarginsu dan yadda suka yi da yadda suka nuna halin ko in kula gameda batun zubewar cikin dole abun ya saka duk wani mai hankali a shakku.
Shiruu d’akin ya d’auka bayan fitarsu,kafin daga baya Ummi ta ce”Bari in je in yi girki kafin ta farka.”
“Sannu Ummi Allah ya yi miki albarka”
Hajiya mama tace dan gaba d’aya jikinta ya yi sanyi ta kad’u kwarai.
Jaka Ummi ta d’auka daga haka ta fita itama jiki babu kwari.
Baya ta fara dubawa dan ya ci ace Munirat ta kammala shanyar kayan Manu da suka tafi yi,ga mamakinta sai ta ganta ta fito daga lab tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,sai da ta zo daff da ita tukunna ma ta lura da ita.Da mamaki ta tsaya take kallon idanunta waenda suka kumbura kamar wadda ta sha kuka..”Ummi za mu wuce ne?”
Ta yi mata tambayar ba tare da ta had’a idanu da ita ba.
“Kuka ki ka yi?”
Itama ta jeho mata da tata tambayr.
“Cleaner d’ince ta d’an watsa mini hypo a ido garin wanke zanin Manu shine na je lab d’in suka duba mini sun ce ba komai bai ma shiga idon ba.”
Wata bahaguwar ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e saboda da har ta fara tunanin wani abu daban.
Sai da itama ta sake duba mata idon tukunna suka nufi gida.
Ummi tana fita Hajiya Mama ta kira Daddy a waya tace”ya zo yanzunnan tana da buk’atar ganinsa.
Suna gama magana Inna Siyama da Muhsin suka shigo,har da Sir Najeeb wanda ya je zance ne ya ji zancen shine ma ya kawosu.
Cike da girmamawa suka gaida Hajiya Mama ta amsa da kulawa kafin suka shiga jaje da tambayar jikin nata.
Cike da alhini Hajiya Mama take sanar dasu ai cikin ma ya zube har sun yi mata wankin ciki…gab’a d’aya shiruu aka yi jiki da zuciya duk ba dad’i.
Hawaye kawai suka ga yana bi ta k’uncin Manu wadda shigowar su Inna ne ya farka da ita ba ma su sani ba.
Numfashi Hajiya Mama ta fesar kafin ta tura kujerar ta dai dai saitin kan Manubiya a hankali ta shiga rarrashinta tare da yi mata nuni da ta karb’i k’addararta hannu bibbiyu,Allah ya na sane da ita shi zai sake bata wani.
Da kyar ta samu ta iya bud’e idanuwanta da suka yi mata nauyi,tukunna da taimakon Siyama da na Hajiya Mama aka samu ta tashi ta zauna still hawaye sun k’i su daina sintiri a kan fuskarta.
Ya jiki suka yi mata ta gaida Inna daga haka ta shiga kallonsu
One by one idanuwanta suna masu begen son ganin fuskar Yashjub ta samu su ta ga halin da yake ciki su koka tare su rarrashi juna tare,amma sai ta ga babu shi babu mai kama da shi…
Siyama ta tambaya Siyaman tace mata”ita ma yanzu suka shigo,ba ta gansa ba”
Dan haka ta juya ta fara laluben wayarta still hawaye suna sintiri a kan fuskarta sun k’i tsayawa ko na second d’aya.
Kallonsu Hajiya Mama wadda ta gama cewa Najeeb ya je ya Kira Doctor ta yi,tace”me kike so Manu?”
Ta yi mata tambayar cike da tausayawa don yadda take hawaye jikinta har yana karkarwa dole ta baka tausayi!
A hankali Inna ta matso ta ruk’o hannunta da niyyar yi rarrashinta aikuwa kamar jira take yi tashi d’aya ta fashe da wani irin kuka ta fad’a jikin Inna ta k’ank’ameta.
Duk dauriyar Hajiya Mama sai da ta yi hawaye….duk kalar kunya da kawaici irin na Manubiya kalli yadda take kuka a gabansu ita da Inna ai kuwa tab’uwa ta yi tab’uwa,kuma ta sake tabbatarwa ba ita ta zubar da cikin da kanta ba zubar mata aka yi,tabbas Mommy ta zalinci baiwar Allah nan amma ba ta Isa ta ci b’agas ba wallahi……wani irin tausayin baiwar Allahn ne ya lullub’eta a haka ma ba ta ji abunda Likita ya ce ba, tashi d’aya ta shiga addu’a Allah ya sa kar maganar sa ta tabbata Allah ya sa Manubiya za ta haihu shiyasa ma ba ta gaya wa ko su Inna ba kuma za ta cewa su Ummi suma su b’oye gudun ma kar baki ya yi yawa a zancen ya tabbata,inshaaAllah Manubiya sai ta haihu,babu abunda ya samu mahaifarta.
Kuka sosai Manubiya take yi kamar ranta zai fita dan zuwa yanzu ta kasa b’oye kawaicin ta,shigowar Najeeb da Likita ne ya tsagaita hak’urin da su Hajiya Mama suke ta bata suka d’an matsa gefe domin ya yi aikinsa.
A karon farko ya tabbatar musu jininta yayi mugun hawa,sannan she needs more rest dan haka bari ya yi mata allurar bacci.
Cikin kuka tace”ya fara jira Ya Yash ya zo tukunna sai ya yi mata,tana son ganinsa.”
Kallonsu Likitan ya yi zai yi magana Najeeb yace”ka barta tukunna bari in kira sa.”
With full confidence ya shiga gwada numbobin Yashjub amma duka hud’un da ya ke amfani da su a kashe!
Gashi kowa ya tsura masa ido yana jira…shi abun ma mamaki ya basa Anya kuwa Yashjub ne ya aikata haka?Manubiya ba lafiya tana asibiti ba ya wajen sannan ya kashe gaba d’aya wayoyinsa!something is wrong,definitely…
A hankali ya d’ago ya kallesu cikin in ina yace”wayoyinsa ba sa tafiya bari in je gidansa in duba”
Shiruuu Manubiya ta yi hawayen idanunta suka k’afe ta shiga wani irin rikitaccen yanayi,dama ta san Ya Yash sai ya shiga tashin hankali amma ba ta yi tunanin zai yi abandoning d’inta ba ko wanne Hali yake a ciki ta yi tunanin zai taushi zuciyar sa ya zo gareta!,to ko dai bai san ta yi b’ari ba? Inaa ya sani ta san he’ll be the first person da su Hajiya Mama za su kira.
Tana wannan tunanin Likita ya kamo hannunta ta cikin cannula ya juye mata ruwan allurar bacci wanda tun kafin ya gama zarewa bacci ya yi awon gaba da ita.
Ba ta dad’e da yin baccin ba Daddy ya zo dan haka bayan sun gaisa da su Inna suka fita shi da Hajiya Mama.
A garden d’in da ke cikin asibitin suka nemi guri suka zauna.
Cikin fahimtarwa ba tare da b’oye b’oye ba Hajiya Mama tace”Manubiya ta yi b’ari,kuma Likita ya tabbatar mana magani ta yi ta sha watak’ila ma ba lallai ta haihu ba.na san ka shiga ka ga halin da Yarinyar nan take ciki kuma ka san ko da wasa ba ita ta yi yunk’urin zubar da cikin nan ba,dan haka inaso ka gaya mini me lissafinka ya baka a halin da ake ciki yanzu?.”
Shiruu ya yi ya fi minti ashirin duk su biyun suka yi shiru babu mai cewa komai kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace”ina riba ga su Yasira idan sun zubar mata da ciki?”
Lumshe idanuwanta ta yi ta bud’e tace”mashaaAllah Imam,na gode Allah da soyayyar y’ay’anka ta daina rufe maka idanu daga ganin gaskiya.
Ina so ka san cewa su Yasira ba su da riba dan sun zubar da cikin Manu amma Khadijah fa?”
A mugun zuciye ya mik’e yana wani irin huci tashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi jazir cikin fushi yace”now everything makes sense”
Ya fad’i hakan yana mai mik’ewa had’i da shirin barin wajen….da sauri Hajiya Mama ta mik’e itama ta ruk’o sa,cikin hikima tace”Imam idan ba ka iya kama b’arawo ba fa shi sai ya kama ka.Yanzu ka gaya mini hujja d’aya da zaka nuna ka kamasu da laifi?babu!
Kuma idan ka yi haka ka sake dulmiyar da y’ay’anka mata ka saka a halaka mazan kuma har abada ba za su tab’a yafe maka ba,ka ga ta raba ka da su kenan har abada.”
Cikin rashin fahimta yace”Hajiya Mama ni ne Uba ni zan fad’a a ji da ni da ke duk mun san ita ce do we really need to prove anything to them?”
Girgiza kai ta yi kafin tace”dad’ina da kai kenan idan zuciyarka ta motsa Imam ba ka ji ba ka gani!
Wallahi d’azu da na fahimci abunda Khadija ta saka yaran nan suka yi sai da na yi hawaye,Imam su Yasira y’ay’anka ne jininka ne kai ya kamata ka tashi ka tsaya ka gyara tarbiyyar su da lissafinsu da aka lalata,yanzu idan ka kori uwarsu kana tunanin za su rabu da ita ne?
Za ka sha mamaki idan suka kwashe kayansu suka yi maka yaji suka koma gabanta gaba d’aya tunda bakinsu d’aya kalli fa abunda ta tura su suka aikata meye kake tunanin ba za su iya yi mata ba?kaga da ga nan sai abunda Hali ya yi hakanan za ta lalata maka zuri’a Allah kad’ai ya san abunda Hali zai yi.Su kuma mazan ba za su tab’a yafe maka ba cewa za su yi ka kori uwarsu saboda kawai ba ka sonta.
Abunda ya kamata mu yi yanzu shine mu nutsu mu karance su sai mu san abun yi saboda wallahi Imam akwai abubuwa da dama da bamu sani a kan Khadijah ba kuma idan muka ce za mu yanke hukunci cikin fushi tou kuwa za mu kwafsa dan indai har Khadija za ta iya kashe d’an cikin Yash to akwai wasu abubuwa da yawa game da ita wanda mu ba mu sani ba.
Sannan yanzu idan aka yi hayaniya ta tafi ba za mu tab’a sani ba sannan yaranka bamu samu mun gyara abunda ta b’ata ba wanda na tabbata Wallahi ko gidan miji ba su Isa su iya zama da wannan mugun halin ba…daga karshe su yi muguwar rayuwa!Imam yaran nan amana ne Ubangiji ya baka kuma zai tambayeka ranar gobe k’iyama fa!…ka nutsu ka yi abunda nace sai ka ga an dace”
A hankali ya koma ya zauna ya dafe kansa da hannu bibbiyu,kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace”Mamaa ba zan iya ci gaba da zama a inuwa d’aya da matar nan ba,ta yi mini abubuwa da dama ta cuce ni da yawa,Hatta lamarin Khadija ba ni da tantama itace wallahi….”
Tiryan tiryan ya zaiyyano mata yadda mallan lawal ya kirasa da yadda ya mutu kafin ya samu ganinsa,sannan ya ce”ya yi hacking wayarta but yana ga kamar ta gane dan ta ma chanja layi ta kashe wanchan,kenan definitely ba ta da gaskiya.”
Waje Hajiya Mama ta nema itama ta zauna ta kamo hannun Imam wanda zuwa yanzu yake kuka kamar k’aramin Yaro,cikin tsananin rashin jin dad’i tace”ka yi hak’uri Imam,da ni da mahaifinka mu muka tilasta maka aurenta,ka yi hak’uri ka yafe mana mun had’aka da…..”
Da sauri yace”ba laifinku bane Mama,na san ba ku yi tunanin za ta zama haka ba ai,saboda da ba hakan take ba,na san tana da masifar kishi amma sam ban yi tunanin zata zamo haka ba.”
Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”kaga ire iren abunda na ke gaya maka ko?kaga lamarin Khadija ma har da sa hannunta sannan recent mutuwar lawal ma muna zargin itace..Ni tunda na ga abunda ta aikata a Yash na san ta yi abubuwa da dama waenda bamu sani ba shiysa ka ji na ce maka mu bi komai a sannu mu bincike ta kafin mu san abunyi idan ba haka ba ba za mu ci ribar al’amarin ba…..”
Sun jima sosai a wajen da kyar Hajiya Mama ta yi convincing Daddy ya hak’ura suka tsayar akan za su saka ido a kan Mommy kuma su san yadda suka yi suka nunawa su Yasira abunda suke yi is wrong su dawo da su hanya….
Ba dan Hajiya Mama ce ta rok’esa ba wallahi da ba zai k’ara kwana d’aya da Mommy a cikin gidansa ba kuma sai ya wulak’antata ya k’ask’antar da ita dukda ya san ba shi da tsayayyiyar hujja da zai nuna ya ce ita ta yiwa Khadija sharri sannan ita ta yi sanadiyyar zubewar cikin Manu amma ya san itace kuma shi kawai he can’t tolerate her anymore a cikin gidansa ya tsaneta! sai dai kuma abunda Hajiya Mama ta fad’a gaskiya ne shiyasa da kyar ya aminta ya kuma zab’i su biyo mata ta yadda ta bi da su ta hakan ne za su yi nasara a kanta…idan ya koreta yanzu bai rabata da su Yasira ba ai aikin banza kenan kuma ya barta da gatan ta.Shi kuma so yake yi ta wulak’anta ta shiga masifar da sai ta zab’i mutuwa akan rayuwa sai ya rabata da duk wani kwanciyar hankali da jin dad’i kamar yadda ta yi masa.
A take