Showing 108001 words to 111000 words out of 244445 words

Chapter 37 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16445

tata ta d’auko warkewa ma
Ba yabo ba fallasa ta amshi Manubiya har da y’ar tsokana
daga nan aka fita parlourn har ita.
Suna zama Abhi ya shigo dan haka suka shiga gaida shi, ya ji dad’in ganin su kuwa dan haka aka zauna har da shi aka shiga hira…
Dakyar kuwa Manubiya ta samu ta iya cin abinci a cikin su dan da har Yashjub ya d’auka zai kai mata d’aki da ya lura ba za ta iya ci a tsakiyar su ba amman sai Hajiya mama tace ya barri a bar ta ta saba ta sake da su ita batason wannan takurawa da ake kira da kunyar surukai…ta d’auketa kamar best friend d’inta.
Da wasa a dariya da raha haka suka dinga janta har ta samu ta d’an sake ta d’an ci abincin tana ta yaba kara da kirkin su
A ranta tace”inama ace sune family d’in Yashjub na Nigeria da ta more…”

Gashi dai sunada komai amma da ta basu tsarabar Cyprus ba kad’an ba ta ga murna a fuskokinsu nan ta sake tabbatarwa tabbas waennan sun san darajar d’an Adam.
Sosai take jin dad’in yadda Junior yake respecting d’in ta ba wai respect in the form of seniority ba no,respect ta yadda ko a kusa da ita baya zama kamar yadda Yassir yake yi
tsakanin ta da shi mutunta juna.
Hajiya mama kuwa da gaske take da tace wa Manubiya ta d’auke ta kamar babbar k’awarta dan janta ta ke yi a jiki suna hira sosai tun Manubiya tana nok’ewa har ta d’an sake dan Hajiya mama har labarin shagalin bikin ta ta bata tace “lokacin maman Mommy itace babbar k’awarta……..”


Kamar yau sukazo Uk sai gashi har sun yi two weeks gobe za su tafi tare da tarin alkhairin su Mom
Tabbas Manubiya ta ji dad’in zama da su ta ji d’adin yadda suka jata a jiki basu nuna kyama ko wani abun ba
Dan har gaisawa da Inna da Baba sukayi a waya kuma yanzu haka ma sunada number Innar
A bangaren mutumin nata kuwa abun ba a cewa komai
tana yin wanka ya ci gaba da honeymoon d’in sa babu kama k’afar Yaro dan shi ba ruwan sa da a inda suke sam bai damu da su Hajiya mama ba…


Haka nan ranar da za su tafi Hajiya mama da Mom suka had’awa Manubiyan goma ta arzik’i kayan alkhairi kala kala suna ji kamar kar su rabu da Yarinyar….Sai da Hajiya mama ta yi musu addu’o’i sosai tukunna suka yi musu rakiya compound d’in gidan Junior ya ja su ya kai su airport kamar yadda ya d’ukosu suka tafi da kewar su da kuma tsammanin su dan Hajiya mama tace “nan da sati biyu zatazo inshaaAllah”saboda akwai aikin da Junior zai yi anan kano har na tsawon shekara d’aya so za su taho tare da shi….”

K’arfe 2:00pm daidai jirginsu ya yi landing a Aminu kano international airport Nigeria….

3 months ago…
Da farko su Mommy b’oyewa Kausar batun tafiyar su Yashjub sukayi dan sun san zata d’aga hankalinta…

Ko da labarin ya je mata ba ta yi komai ba dan zuwa yanzu tama kasa kuka amma fa sai da ta yi kwana uku bata runtsa ba..sai da Yasmeen ta yi mata prescribing magani tukunna aka samu ta yi bacci..gabad’ayan su tausayi Kausar d’in ta ke basu ta zama so silent kamar ba Kausar ba,wani zubin har sai ka zo ka na yi mata magana amma ba ma ta sani ba ko kuma kawai ta zuba maka ido ta yi ta kallon ka har ka gama baza ta iya cewa komai ba.
Lamarin ta ba k’aramin sake d’agawa Mommy hankali yayi ba gashi ita ta ma kasa lallashin ta dan batasan mai za ta ce mata wannan karon ba
Ita tace ta yi hak’uri kar ta yi komai zata nema musu solution amman sai da Manubiya ta basu mamaki
saida ta shigo gidan yashjub..amma ba komai!dan wallahi ko da ace za ta bada ranta ne wallahi ba za ta tab’a bari kud’iranta ya tafi a banza ba,enough is enough kome zai faru along the way sai dai ya faru bata damu ba dan sai ta cimma manufarta.
Hankalinsu bai sake tashi ba sai da suka ga su Manubiya sun yi fiye da sati biyu amma shiru ba su ma da niyyar dawowa…dukda Mommy ba ta kasance mai yawan laulayi ba amma sai ga ta a asibiti wannan karon jininta ya hau matuk’a,matar da ko a ciki ba ta laulayi iyaka ciwon nak’uda kawai ta sani.Sai da suka shafe sati d’aya cur ba su zauna ba sunata jerawa Yash da Manubiya kiranye amma ko kyallin dawowarsu ba su hango ba,ganin Mommy tana shirin susucewa ne ya sa Baba larai nemo musu sabon solution ta inda ta kawo shawarar kawai su yi wa Manubiya ajiya a ciki sannan su cire mata Yash d’in a rai kwata kwata ta yadda duk nacin sa ba za ta tab’a bashi kanta ba. A ganinta wannan kad’ai ce mafita dan ta san maganar kunce jini da tayi zuwa yanzu har sati uku ba lalle ya yi musu yadda suke so ba…
Dan tsabar bala’i a jeji Mommy da Baba Larai suka je suka binne abunda suka yi,a ranar suka yi wa Daddy k’arya suka ce masa an yi musu rasuwa a k’auye suka je suka kwana washegari da yamma suka dawo sunata murna su ala dole sun yiwa Manubiya ajiya a ciki sannan sun saka mata tsanar Yash a rai.
A tunanin su su Manubiya bai fi su k’ara sati d’aya ba daga haka su dawo amman har fiye da wata biyu suka ji shiru hakan ya sa Mommy ta sake d’aga hankalinta a ganinta indai har abubuwan da suka yi suna aiki ai Yash da Manubiya bai kamata ace sun yi zaman su a chan shiruu kamar haka ba cike da assurance Baba larai tace”ta kwantar da hankalinta watak’il har yanzu jinin da aka kunce mata tun farko bai daidaita ba maybe yana on and off saboda ita dai bata karya abun da ta yi ba dan haka watak’il sunachan sunata yawon neman magani ne amman ba dai honeymoon ba.

A b’angaren Yassir kuwa yana nan zargin Kausar ya dasu a ransa fiye da ko yaushe dan ya lura Yashjub yana tafiya ta fara rashin lafiya….sai dai kuma Maganin da take sha na saka bacci ba kad’an ba ya ke taimaka masa dan in ta sha ta kwanta haka zai shige d’akin nata ya yi ta bidirin sa wani lokacin ta nuna masa bata so wani lokacin kuma kawai ta rabu da shi dan ta san ba hak’ura zai yi ba ita kuwa bata da k’arfin hana sa ko yin fad’a da shi a wannan lokacin…rannan kad’an ya rage Yasmeen ba ta kama sa ba tsabar yadda yake zirya ba d’aga k’afa sam,amma ko a jikinsa bai damu..yana sonta kuma hakan yana taimakawa wajen kawar masa da damuwar da yake a ciki saboda kamar yadda damuwa ta yi wa Kausar d’in yawa hakanan shima damuwa ta yi masa k’ad’abaibai
Shi babban tashin hankalinsa a yanzu shine Yashjub yana chan yana hutawa tare da kyakykyawar matar sa shi kuma yanannan duk wani plan d’in da ya had’a sai ya tarwatse dan a tafiyar nan da Yashjub d’in ya yi sau uku yana k’ok’arin yashe sa amman ya kasa
Har company d’in sa yaje amman komai thumbprint ne bayan thumbprint d’in kuma hadda password
Sannan ga zargin sa a kan Kausar ga Munirat da ta fara k’ular da shi da nacin ta….

Ba zai yiu Yashjub ya fi sa komai ba sannan ya fi sa kwanciyar hankali ba…shiyasa kawai ya gama deciding rufe chapter Yashjub as soon as possible dan ya gaji da nad’ar takaici…tunda yayi yayi ya kasa to zai b’arar kawai kowa ya rasa…
Wallahi ko sunansa ba ya so ya ji an ambata Allah Allah ya ke ya ga babu shi a doron k’asa,ba don he can’t stand him anymore longer ba da zai so ace ya fara tura masa bak’in cikin da watak’il ma shi ne zai zamo ajalin sa dan tabbas idan akace Yashjub ya mutu da takaici bak’in ciki da kuma tashin hankali abun zai fi yi masa dad’i fiye da komai.…tsabar yadda Yassir ya kwallafa rai da son ganin bayan Yashjub har wata y’ar rama ya yi…..

Today.

Daddy Yash ya gayawa time na landing d’insu
Yaso ace driver d’insa aka turo masa amma suna fitowa sukayi ido biyu da Yassir.

Sai da Yassir ya ji numfashin sa ya d’auke na y’an dak’ik’u tukunna ya dawo da kyar sakamokon hango Manu da yayi..ta yi wani irin fari ta yi fresh ta k’ara kyau
kamar ka sace ta ka gudu!.
Da kyar ya d’auke idanuwan sa daga kanta ya maida akan Yash yace ‘’Wlcm”
Sai kuma ya yi musu jam’i yace
“Ya hanya?”

“Alhamdulillah”suka ce daganan suka nufi motar da ya faka Yashjub yana mamakin yadda ya ga jikin Yassir d’in yayi wani irin sanyi kamar mara lafiya..

Sosai Jeep d’in ta cika taff da kaya dan sun yo tsaraba ga kuma kayyakin su da suka tafi da su…Ana gama lode kayayyakin a cikin motar suka shiga ya ja motar suka yi gaba.
Har suka d’au hanyar gidan Daddy Yassir ya kasa magana,
wani irin kishi da zafi da takaicin Yashjub yake ji ta koina,ji yakeyi kamar ya juya ya shak’e sa kokuma ya cika sitiyarin kowa ma ya mutu
Amma da ya tuna ya kusan kawo k’arshen Yash d’in sai ya yayyafawa zuciyar sa ruwan sanyi dan ya riga ya gama had’a plan d’insa Allah Allah kawai yake ayi ayi lokaci ya cika bayason ganin sa baya son jin ko da muryar sa ne ya kag’u ya rufe chapter d’in Yashjub ya fad’a wata sabuwa dan a yadda Manubiya take yi masa d’innan ya san zai d’an sha fama da ita kafin ta yarda ta auresa bayan mutuwar Yashjub.

“Ya naga ka d’au hanyar gida?”
Muryar Yashjub ta katse masa lissafin sa
Sai da ya d’an d’au lokaci tukunna ya juya ya kalle sa ya ce
‘’Mommy ce tace in kai ku chan ku huta.Zuwa gobe sai su Yasira su je gaba d’aya a tayata gyaran gida dan ta san ba za ta iya ita kad’ai ba’’

Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya ji gaban sa ya yanke ya fad’i..shiruu kawai ya yi a ransa yace
“Allah ya rufa asiri”
Daga nan motar ta d’au shiru tsit kawai kakeji har suka k’arasa bakin mansion d’in aka bud’e musu suka shiga ba wanda ya sake cewa komai.

Tun kafin motar ta tsaya ya ga sun fito gaba d’ayansu
Har Kausar Ummi da Munirat..shine ya fara fitowa tukunna ya bud’ewa Manubiya gidan baya itama ta fito..kallon Kausar take yi tana mamakin kwalliyarta ta cikin glass d’in shiyasa ma ta kasa fitowa.
Gashi kayan jikinta k’anana ga hula ta d’aura a kanta amma ba ta cusa gashinta a ciki ba instead ta fito da shi duka yana reto gefe da gefe da baya ko k’aramin ribbom ba ta mak’ala ba ga wani irin high makeup da ta yi kamar wadda za ta je gasar saurauniyar kyau!
Ko ba a fad’a mata ba ta san saboda Mijinta ta yi wannan kwalliyar da shigar shiyasa ta kasa hana kanta jin kishi,dama tun d’azu a jirgi take jin amai da ciwon Kai ga zazzab’i yanzu kuma ganin Kausar ya sake b’ata mata rai shiyasa gaba d’aya ta shiga jinta wani iri sosai sosai.
Ahankali yake nazartar ta kafin yace”muje mana”
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin ruk’o hannunta,gudun magana yasa ta d’an janye da style ta d’aga masa Kai alamun ‘to’
daga nan suka nufi inda dandazon su Mommy suke a tsatstsaye.

Ba abunda ya fi d’agawa Mommy hankali irin farin da ta ga Manubiya ta yi dan har wani d’aukar ido ta ga tanayi
Ta san sun yi mata ajiya a ciki
amma she can’t help it but to think ko dai cikine da ita,har Manubiya ta k’arasa inda take tsaye ta d’urkusa ta na gaida ita ba ma ta sani ba saida Baba larai ta d’an zungureta tukunna ta dawo cikin haiyyacin ta
Ahankali ta dafa kan Manubiya ta ce “lafiya y’ar albarka ya hanya?”
“Alhamdulillah”kawai Manubiya tace daga nan ta gaida Baba larai itama ta amsa mata da kulawa kafin ta mik’e ta nufi Ummi tana shirin durk’usawa Ummin ta rik’eta tace
“Sannu ya hanya”
cikin tsananin ganin girman matar Manubiya tace “Alhamdulillah”daga nan ta gaida ita sai kuma suka hau murna da hugging juna ita da su Yahanasu yayin da Yashjub yake chan suna gaisawa da su Mommy Baba larai tana tsokanarshi da ‘ya yi k’iba.’

Ko kallon Kausar bai yi ba
ko da ta matso ma tana kwarkwasa ta gaida shi bai amsa ba sai da Mommy tace’’Kausar fa tana gaida kai,”tukunna yace ‘’Alhamdulillah’’ba tare da ya kalle ta ba, dukda haka bata damu ba haka ta matsa kusa da shi sosai ta tsaya ana magana wanda hakan ba kad’an ba ya sake tunzura lissafin Yassir.
Sosai ran Ummi ya b’aci itama duba da yadda Kausar d’in ta matso kusa da Yashjub sosai
kuma Mommy ta rik’e masa hannu ta hanasa matsawa ana hira ana dariya it’s like so take ma Manubiya ta gani.
Shiyasa tun kafin Manubiyan ta juya ita kuma ta kamo hannunta suka yi ciki su da Munirat da Yahanasu.
Bata barta ma ta zauna a parlourn ba chan sama side d’in ta ta kaita har bedroom d’in ta tace “ta huta”daga nan ta cewa Munirat ta kawo
mata abincin da suka yi..
Sai dai a ga shishshiginta amman ba za a yi wannan cin kashin a gaban idanunta ta ta kyale ba
Dama tunda ta ji su Mommy sun dage a kan Yassir ya kawo su nan ta fahimci akwai abun da suke son yi….kuma ita har ga Allah girkin da Mommyn ta yi musu ba ta yarda da shi ba dan haka ba za ta bari ta ci ba shiyasa ta cewa Munirat ta kawo wa Manubiyan wanda su suka dafa.

Yashjub ya so su zauna a side d’in sa amman sai Mommy tace”tunda na kwana d’aya ne kawai su zauna a guest room gobe sai su wuce”
“To”kawai yace ba dan ya so ba dan 3 months ago Yahanasu ce masa ta yi ya zauna da matar sa kawai a uk har abada
In kuma hakan bai yiu ba to kar ya kuskura ya dinga favoring d’inta sannan ya d’an rage nuna mata soyayya a gaban su Mommy…..shima ya fahimci hakan kuma dama ya sa a ransa ba kwana kusa za su dawo d’in ba but no mattter yadda yaso ya dad’e ya yi kamar 2 years haka sai ya ji ya kasa kuma bazai ma yiu ba aiyyukan sa duk suna nan shiysa ya fara shirin dawowa to a wannan time d’in ne ma Daddy ya kira sa wanda kiran da ya yi masa da yanayin yadda ya yi masa magana da sanyin murya gaba d’aya ya kashe masa jiki duk abunda ya shirya ma zai fahimtar masa kuma zai yi a kan su Yassira gaba d’aya sai ya ji ba zai iya ba dan Daddy d’in sounds so disturbed it’s like Irin ya gaji da damuwa da cases d’innan tunda har ya sauk’o da kansa,kuma kamar akwai abunda ya taso masa yake damunsa maybe case d’in marigayiya…shine babba a ganinsa bai kamata ace shine zai saka Daddy a damuwa ko
ya k’ara masa damuwa ba..kwanaki ya yi masa wuta wuta yanzu kuma tunda ya sauk’o to Alhamdulillah shi kuma inshaaAllah ba zai taimaka wajen sake d’aga masa hankali ba,shiyasa ya yanke a kan zai yi ta addu’a kawai komai ya daidaita kuma inshaaAllah ba zai yi abunda Manu za ta kwana a ciki ba…


Baba larai ce tace “mu shiga ciki mana ku gaisa da Daddy a ci abinci ko?
Naga su Manubiyan ma har sun wuce.
Tun safe Mommyn naka take yi muku girki..babu wanda ya ci abinci ku ake ta jira”.

Murmushi ya yi ya kalli Mommy yace ‘’Thankyou Mommy’’
Daganan duk suka shige cikin parlourn Yashjub ya nufi chan sama wajen Daddy yayinda su Mommy suka fara rarraba idon neman su Manubiya
Da sauri Baba larai ta matsa kusa da ita k’asa k’asa tace
“To!Ummi ta yi sama da ita kuma in ba da kyar ba ta cika mata ciki da nata abincin kinga shikenan mun yi shiri da wahalar banza kenan….”
A zabure Mommy ta nufi sama d’akin Ummi.


Tun d’azu dama Ummi ta lura kamar Manubiyan bata jin dad’i dan haka suna zama da Munirat ta tafi d’ebo abinci ta kalle ta tace
“Baki da lafiya ne?”

Sai da ta d’an sunkuyar da kanta k’asa dan gaba d’aya kunyar Ummin take ji gashi ta hanata zama a k’asa kan kafet ta d’aura ta akan gadon ta d’are d’are
tukunna tace
“Zazzab’i nake ji da amai”

Wani kalar murmushi Ummi ta yi kafin tace “Sannu..
Inaga flight d’in ne ya ja miki hakan,akwai pottage na san za ki ji dad’in sa sosai yanzu Munirat za ta kawo sannu ko”

Ahankali ta jinjina Kai tace “Nagode Ummi”
Daganan ta d’auko wayarta ta shiga kiran su Innaa, tun a mota Jidda ta kirata tace mata sun iso
amma ita Jidda tana skul ta kira Innar kuma bata d’auka ba shine yanzu take sake gwadawa.


Ummi na cikin gaisawa da inna Mommy ta shigo…sai da ta basu mamaki sakamokon ganin ta a hargitse da suka yi,
dan haka sukayi sallama da Inna tukunna Ummi ta bata dukkannin attention d’in ta tace”ya na ganki a gigice ince dai lafiya ko?”

Tabbas zuwa yanzu Ummi ta fara kai Mommy bango da yanayin maganganunta masu harshen damo marasa respect.
Ba ta ita take ba yanzu
amman tabbas za ta samu lokacin ta soon .
Shiyasa kawai ta k’ak’alo murmushi da kyar tukunna tace “lafiya k’alau Ummi,
naga ban ganku a k’asa bane shine na biyo d’aukar y’ar tawa”.

Ita kanta Manubiya sai da ta ji bambarakwai dan yanayin kulawar da su Mommyn suke ba yau ta musamman ce saboda ko a waya idan za su gaisa da ita ba ta cika yi mata irin haka ba.

Murmushi Ummi ta yi tana shirin yin magana Munirat ta shigo d’auke da tray..cikin
tattausan lafazi tace
“Ai ni kam wai da har na yi shishshigi na sa Munirat ta d’ebo mata abinci,ki bari kawai ta ci anan naga duk kunya take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login