Showing 162001 words to 165000 words out of 244445 words

Chapter 55 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16440

time d’in inshaaAllah”

Yana shiga gidan da ya so ya yi mata bayani ta k’i fahimta sam ta rufesa da fad’a a ranar dai ba su yi bacci ba,kwana ta yi tana bala’i kuma ta tabbbatar masa da babu inda za ta je…..
Shi dai ya Musbah a hankali a hankali ya dinga kwasar kayansa da shi da mai sunan Baba suna kaiwa sabon Gida sannan ya je ya biya kud’in registration d’insa ya ci gaba da zuwa makaranta ranar da sati d’aya ya cika ya zo ya yi mata sallama yace”za su tafi shi da mai sunan Baba”

Da kyar Baraka ta fita daga shock d’in Musbahu wanda tana tunanin ta riga ta saka a kwalba bai Isa ya yi mata haka ba,ta fahimci akwai matsala shiysa ta danne zuciyarta kawai dan ta san dole sai ta sake sabon shiri kuma a yadda ya botsare mata idan tace za ta yi turjiya kanta za ta jawa shiyasa kawai ta ce “ba komai ya jira ta ita ma za ta bishi…..”
Sai washegari aka gama kwashe kaya….a plan d’in Baraka idan ta je sai ta yi abunda shi da kansa zai ce su bar gidan kuma sai ta had’a sa da su Inna wannan karon ta kissa asiri da komai za ta had’a…sai dai kuma tun da ta je ta ga d’ankareran gida ta ce ba ta ga ta tashi ba,ta san kuma fitar da su Inna a gidan aiki ne ko da zai yiu to ba yanzu ba….gashi ya Musbah gaba d’aya ya juya mata baya aikin ma ya daina tasiri a kansa Kwata Kwata ba ya sauraronta ba ya jin maganarta,dan yanzu ma k’iri k’iri so take ya d’aga katanga tsakaninsu da su Inna ya fitar musu da gate d’insu a daban tama ce ita da kanta za ta bayarda kud’in amma yace”ba ta Isa ba!”
“Idan kuma ta sake yi mishi wannan maganar shirmen wallahi sai ranta ya yi masifar b’aci”
Shiyasa gaba d’aya hankalinta yake a masifar tashe,ta sake dagewa gidan kullum idan ka shigo banda k’aurin hayaki mara dad’i babu yake yi dan haka suma su Inna suka sake dagewa da rok’on Allah.

Jiya da daddare Hajiya Mama da Junior suka zo….Shiyasa yau da safe su Manu suke ta shiri akan za su je.
Kana ganinta ka san ta ci kuka dan fuskarta duk ta kumbura shiysa tunda su Yusra suka ganta a haka farin cikin su ya nunku ya gagara b’oyuwa har sai da ta d’an lura..a b’angarenta kuwa fad’a suka yi ita da Yash jiya abunda bai tab’a shiga tsakaninsu ba kenan!
Tun bayan sati biyu da ya nemeta ta k’i bashi had’in kai ta fara kuka shikenan bai sake neman wani abu a wajen ta ba,abun ya yi mata matuk’ar ciwo dan a tunaninta sun wuce haka ita da shi ba ta tab’a expecting zai yi irin wannan fushin da ita ba mutumin da a ko da yaushe ya ke cewa”Manubiya ba ta laifi a wajen Yash,he loves her morethan life itself”amma shine wai zai yi irin wannan fushin da ita!
Ba wai fushi na k’in magana ba dan suna wasa suna dariya yana kula da ita yadda ya kamata kawai dai ko hannunta ya daina rik’ewa…..
Dama da haushin hakan a ranta yau kuma k’iri k’iri da ta yi masa maganar makaranta ba kunya ba tsoron Allah yace”ba za ta ci gaba ba!”
Daga haka ya shige toilet ya barta a tsaye kuma ko da ya fito ya ga tana kuka bai tsaya ya rarrasheta ba instead shima sai ya had’e fuska tamau ya ci gaba da shirinsa ko a jikinsa…hakanan yana ganinta har ta gama kukan ta ta sauk’a k’asa had’a breakfast bai ce mata komai ba.

A b’angaren Yash kuwa..dalilin da ya sa ya d’aga mata k’afa kwana biyu ba ya so ya cika nagging ne ya je garin haka ya fara fita a ranta shiysa ya hak’ura akan har sai yaga she’s ready tukunna…..sannan yana so ya yi k’ok’ari ya ga ya kawar da duk wani abun da zai sa ya yi zarginta ko ya ji haushinta.

A yadda ya ji tana waya dole ko ma waye ya dasa mata ayar tambaya amma shi kuma k’ok’ari yake yi ya goge zargi ya bawa hakan kyakkyawar manufa…

Ya san dole idan ta koma makaranta he’ll be restless tunda ga issue a tsakaninsu dana ba su gama sorting out ba!sannan ga ciki a jikinta da ake buk’atar ace ta huta,shiysa yanzu da ta yi masa maganar yace mata”A’a”kuma ya had’e rai.
Sannan har ga Allah ya na kishi shiyasa ya ga dacewar gara kawai ta yi online…
Kukan ta ya tab’a sa sosai amma ya san idan ba hakan ya yi mata ba,ba za ta hak’ura ba!.

Har ta kai masa breakfast ya ci ya fita,sam fuskarsa babu walwala.
Sai wajajen 11 bayan sun gama girki Yasira ta ja su ta kai su gidan ita kuma ta wuce office da so ta yi yau ta zauna amma sai Daddy ya kirata.

Shiruuu gidan ba kowa dan haka Manubiya suka ajjiye flask d’in girkin da suka yo suka nufi sama side d’in Mommy,kamar ko da yaushe ita da Baba larai sai Ya’isha suka tadda a parlourn nata..zuwan Hajiya Mama ba notice ya d’aga musu hankali matuk’a ga kuma Daddy wanda yake bin diddigin Mommy kamar ba gobe…
Ba yabo ba fallasa suka gaisa kafin Mommy ta kalli Yadira tace”ta raka Manubiya wajen Hajiya Mama su gaisa.”
Suna fita ko tambayar ta su Mommyn ba su yi ba Yusra tace”yanzu haka ma cikinta ciwo yake yi,ba ta dai fad’a ba amma tun safe take rik’e ciki idan ya murd’a har sai ta durk’usa”
“MashaaAllah,Alhamdulillah!!”
Baba larai tace cike da farin ciki,kafin ta d’aura da cewa”tunda na ga matar nan da safe hankalina ya tashi dan na san tsaf za ta iya cewa ku dawo gida..”
With full confidence Yusra tace”ai aikin gama ya riga ya gama yanzu kam..dan duk wani ruwa nata muna sakawa a ciki ita kuma tass take shanyewa.. yau sati biyu ta shanye sachet biyu fa!.
Ragowar abubuwan ne dai da na toilet da na d’aki duk ba mu samu damar yi ba ai dama na gaya miki..saboda ya Yash ko k’afar benen sa bai bamu fuskar mu tab’a ba k’iri k’iri ma yace mana “ko ba ya nan kar mu shigar musu d’aki. Na abinci ita kuma ba ta yarda da mu ba! dan ko girkin mu ba ta ci kuma tana yawan addu’o’i so na san turaren shima ko ta shak’a ba lalle ace ya yi wani tasiri ba dukda dai na lura kwana biyu rikici suke yi but gaskiya ba lalle abubuwan namu bane dan ba ta cin duk wani abu da muka bata…maybe wata rigimar tasu ce daban.”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”Allah ya shige mana gaba,tunda har suka fara rikici su kad’ai ai sun sauk’ak’a mana kinga….sannan ba komai dan ba ku samu kun yi waenchan d’in ba indai komai ya tafi yadda muke so,maganin da kuka saka da chatting d’in sun ishi komai.Yanzu Ya’isha ki kirawo Abbakar kice masa zai iya tunkarar Yashjub a yau!”

Shiruu Ya’isha ta yi kafin tace”amma bai yi wuri ba?”
Murmushi Baba larai ta yi tukunna tace”kina ji fa Yusra tace ta fara ciwon ciki!ai this is the perfect time,dan tunda ta fara ciwon cikin nan ba za ta kai jibi da shi a jikinta ba.”

“Tam shikenan,bari in kirasa…”
Daga haka ta d’au waya ta kirasa….a gaban su suka tattauna kafin daga baya suka yi sallama,zuciyar kowa fesss!!!.


Sosai Manubiya ta ji dad’in ganin Hajiya Mama haka itama Hajiya Maman…bayan gaishe gaishe Hajiya Mama ta bata tsarabar da ta yo musu ita da Yash ta karb’a tana ta murna da godiya.
Dai dai nan Ummi ta shigo dan haka suka zauna su uku gwanjn ban sha’awa bayan Ummi da Manubiya sun gaisa.
Hirarsu suke sosai,dukda Manu murmushi da eh ko a’a take ta cewa amma hirar tana yi mata dad’i.
A bakin Hajiya Maman take jin maganar Yadira da Junior ta inda take cewa”ta cewa Daddy kawai ya tsayar da date dan al’amarin Yaran gidan ya fara bata tsoro dan haka tunda har Junior ya nuna Yadira yake so gara kawai a saka rana a yi aure ragowar suma za ta bincika musu Miji a cikin jikikon k’awayenta na nan Nigeria da suke in contact with!ya zama dole a tashi a tsaya a kansu sun rik’a dayawa.”
Ita dai Manubiya murmushi ta yi tace”Allah ya tabbatar da alkhairi”
Dan zuwa yanzu ciwon cikin da ya addabeta sama sama tun d’azu ya k’ara k’arfi!
Tana ji Ummi tana cewa”ta ji suna cewa Yadiran fa ba ta son Junior d’in…!”
Ita kuma Hajiya Maman tace”Wallahi ko za ta mutu sai ta auresa!,Junior ba shi da wani mugun Hali dan haka dole da aure sa.”

“Washh!”
Manu tace sakamokon wani mahaukacin murd’awa da cikinta ya yi.
Da sauri duk suka kalleta sai kuma suka rufar mata sakamokon yadda suka ga ta rik’e ciki ta runtse idanuwa da mugun k’arfi.

Sannu suka shiga jera mata bayan Ummi ta rik’eta Hajiya Mama kuma ta fara k’ok’arin kiran Yashjub.

Yadda Manubiya ta fashe da wani irin kuka ta shiga kiran sunayen Allah ne ya sa Hajiya Mama ta ajjiye wayar ita da Ummi suka fara k’ok’arin kinkimarta dai dai nan Junior ya shigo.
Da sauri Hajiya Mama tace”ya fito da mota ga su nan sauk’owa zai kaisu asibiti.

Munirat da Ummi ne suka sauk’ar da ita suka sakata a mota suna ta faman jera mata sannu,Junior da Hajiya Mama da Manubiya sai Munirat da ta d’aura kan Manu akan cinyar ta,ne suka fara yin gaba suka nufi asibitin,Ummi kuma sai da ta koma ta sanarwa su Mommy tukunna ta bi bayansu a motarta,da taimakon kwatancen Munirat da suke waya ta Isa asibitin……



Yashjub yana zaune a office gaba d’aya tunani ya yi masa yawa dan sai yanzu ya ke ganin rashin kyautawar sa ga Manu…waya ya d’auko da niyyar kiranta amma sai shigowar Racheal ya katse masa hanzari…..

Cikin takunta ta k’araso tace”Sir,a guy named Abbakar is here to see you!he said he’s a friend of your wife.”
A take k’irjin Yashjub ya buga,
sai da ya d’an d’au lokaci kafin ya samu ya d’ago a hankali ya kalleta yace”send him away”.
Duk wani Abu da zai kawo matsala tsakaninsa da Manu ba ya so,gudan sa yake yi.
Ya san ya tsani Abbakar,yana kishinsa saboda Manubiya shiyasa ya zab’i k’in ganinsa.

Har ta juya za ta fita sai kuma ta juya tace”Sir he said it’s very important and urgent,he need to see you!..”

Wannan karon cikin d’an fushi yace”Racheal!send him awayyy!!!”

“Ok sir”
Ta ce,daga haka ta juya ta fita.

Dafe kansa wanda zuwa yanzu ya fara sara masa ya yi…ya d’an jima a zaune kafin ya gama deciding ya mik’e da niyyar zuwa gidan nasu ya samu Manubiya,shiruu da kyaliya bai kamata ace ya fara shiga tsakaninsu tun yanzu ba…abunda ya yi kwata kwata bai kyauta ba….


Yana wannan tunanin ya sauk’a ya shiga motarsa yana shirin kunnawa Abbakar ya k’araso wajen…tun da ya fito ya gansa dama dan haka ya sake tamke fuska tamau.

With full confidence Abbakar ya k’araso ya na zuwa ya d’an yi knocking glass d’in motar wajen mai zaman banza kafin ya bud’e ya shiga ya zauna.

Shiruu Yashjub ya yi sai kuma kawai ya kunna motar ya ja ya fice.

Sai da suka d’an yi nisa tukunna ya faka ya juya ya kallesa yace”I made myself pretty clear kuma na san Racheal ta gaya maka..”

Cikin tarar numfashinsa Abbakar yace”I have to see you,shiysa ka ga na yi hakan..”

Yashjub ji yake kamar ya bud’e motar ya hanakad’a Yaron dan ya yi tunanin idan ya yi masa hakan zai fita amma sam baiga alamun shakka ko shirin fita daga garesa ba ,shi kuma har ga Allah he can’t stand him.. ko sunan shi ba ya so ya ji an kira wallahi…ga kuma gudun zuciya..

“Am…Yashjub ban yi
Mamakin yadda kake treating d’ina ba, dan na san haushina kake ji kamar yadda nima nake jin haushinka!”
Muryar Abbakar ta katse masa tunani..
Juyawa kawai ya yi ya zuba masa jajayen idanunsa..wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yiwa Abbakar ba dan ya hango trigger…

Cikin sauk’e numfashi yaci gaba da cewa”A da na so in b’oye maka kamar yadda Manu ta buk’ata amma kuma sai na ga rashin dacewar hakan dan bai kamata mu yi ta b’atawa kanmu lokaci ba shiysa na zab’i in tunkare ka…”

Cikin katsesa da tsananin fushi Yashjub yace”Kaii!dan ubanka na yi maka kama da Yaro???ni za ka zowa da wannan shirmen?fice mini a mota kafin na illataka!!!”

Murmushi ya ga Abbakar d’in ya yi kafin yace”idan ni ban maida kai Yaro ba ai Manubiya ta maida kai Yaro jariri ma kuwa..gashi kuma ina k’ok’arin wayar maka da kai amma kak’i ka saurare ni!.”

Kama sitiyarin motar Yash ya yi da mahaukacin k’arfi ya d’aura kansa a kai ya shiga karanto addu’o’i dan ya san tabbas tsaf zai iya kai Abbakar lahira muddin ya ce zai biye sa…

Tsabar b’acin rai zuwa yanzu sama sama yake iya jin Abbakar d’in yana cewa”Tun Yarinta muka taso ni da Manubiya..ba ta yi tunanin Ina sonta ba shiyasa ta karb’i soyayyarka…yanzu kuma ta fahimci Ina k’aunarta she’s ready to leave you for me Yash!saboda tace ko dan family d’inka ma ba za ta iya rayuwa da kai ba gashi ba ta son ka…kawai matsalar itace tace mini ba ta san ta yaya za ta gaya maka ba!tana jin kunyarka har gida ka siyawa iyayenta…ganin duk mu uku muna ta b’atawa kanmu lokacine ya sa na yanke shawarar tunkarar ka a yi ta ta k’are.”

A hankali Yashjub ya zare makullin motar ya d’ago kansa ko kallon Abbakar bai yi ba haka ya bud’e ya sa kai ya fita,dan tabbas shaid’an ya fara kad’a masa ganga maganganun Abbakar sun fara tasiri a kansa gashi zuciya
In banda tunzuroshi ya rufarwa Abbakar babu abunda yake yi shi kuma ya san muddin ya biye Yaron a halin nan da yake ciki to sai dai wani ba shi ba.

Bai san shima Abbakar d’in ya fito ba sai hannun sa da ya ji ya kamo ya saka masa wayar sa yace”idan baka yarda da ni ba ka duba wannan.”

Duk yadda Yashjub ya so ya yi k’ok’ari kar ya kalli wayar sai da ya kalla…chat d’inta ne da Abbakar har yana ce mata shifa yana kishi gaskiya ta daina yarda da yash ita kuma ta yi masa alk’awarin ta daina sannan tace”ba za ta iya haihuwa da shi ba ba za ta iya haifar niece ko nephew d’in su Yasira ba shi kuma ya yi mata recommending magani ya ce ta dinga sha kullum guda d’aya a hankali cikin zai zube………
Kafin yashjub ya gama karantawa ya had’a wata uwar zufa fuskarsa ta yi jaa…how dare he! ta yaya ma zai fara mishi wannan shegen zancen on top of that har yana da guts d’in nuna mishi kamar Irin shi ne ya saka Matarsa ta ke k’aurace masa sannan har yana da bakin yin magana akan cikin jikinta HOW DARE He!!!…..
Cikin son k’aryata zancensa kafin ya ci ubansa ya shiga bincika wa yana dubawa da kyau sai dai kuma duk ta inda ya so ya k’aryata d’in abun ya gagara…..ya duba number ya fi sau a k’irga amma number Manubiya ne da komai nata…
Gashi kuma tabbas wannan itace number da take ta kiran Manubiya amma ba ta tab’a d’auka a gaban sa ba!dan ya ga number ya haddace tsananta bincike ne ba ya so shiyasa bai tab’a kira ba.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Yashjub ya shiga maimaitawa a cikin zuciyarsa yana jin wani kalar gagarumin tashin hankalin yana yi masa k’awanya.


“Actually wannan sirrin mu ne bai kamata in gaya maka ba but I have no choice..…dalilin da ya sa na nuna maka na san idan ba gani ka yi ba ba za ka tab’a yarda ba,ni kuma har ga Allah na gaji dan tun kuna Cyprus ake Abu d’aya shiyasa ita kanta Manu d’in ma na shalllake ta na yi gaban kaina gara ka san gaskiya mu daina b’atawa kanmu lokaci.…
Mahaukacin Marin da Yash ya d’aukesa da shi ne ya saka shi a silent…ba ji ba gani ya rufe sa da duka sai da ya ga ya daina motsi tukunna ya tsallakesa ya shige cikin motarsa yana jin abunda bai ma san me ya ke ji ba!!…..

Tafiyar mintuna uku ya yi ya ja ya faka dan wani irin duhu duhu yake gani…ji yake kamar ya koma ya cinnawa abbakar wuta ko ya ji sauk’in abunda yake ji a cikin zuciyarsa…he can’t believe guts da audacity na Yaron!d’ayar zuciyarsa kuma tana ta faman tunzurashi da son tabbatar masa da maganganun Abbakar d’in saboda gashi har gudunsa da take yi Abbakar d’in ne kenan ya hanata ashe,adduarsa d’aya kar maganar zubar da ciki ya zamo gaskiya infact Allah ya sa ma mafarki ne yake yi ya samu ya farka a yanzu ko kuma ya ga wani abun da zai nuna masa wannan al’amarin k’arya ne…..


Wayar sa ce ta d’auki k’ara a karo na bakwai…. da mugun kyar ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kasheta gaba d’aya amma sai ya ga sunan Hajiya Mama yana yawo a kan screen d’in dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce komai ba.


“Ka zo! Yanzunnan..muna asibiti Manu ba ta da lafiya….”
Daga haka ta gaya masa sunan asibitin da kwatance ta kashe dan suma hankalinsu gaba d’aya a tashe yake ganin yadda jini ya kuncewa Manubiya….


Ikon Allah ne kawai ya kai Yashjub asibitin dan shi kansa gani kawai ya yi har ya iso amma ya ma manta ta Ina da Ina ya bi.

Yana shiga ya tarar da su carko carko a reception,da sauri Hajiya Mama ta k’araso tana zuwa yace”menene yake damunta??”
Ya yi mata tambayar yana addu’ar ya ji tace zazzab’i ko wani abun amma sai kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar ta taana cewa”ciwon ciki ne yake damunta…”
A hankali ta sake cewa”yanzu kuma ta fara bleeding!.”

Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Yash ya shiga yi bai san lokacin da ya durk’ushe a wajen ba kamar wani zararre….babban abunda zai tarwatsa shi a halin yanzu ya burkitashi shine idan aka ce cikin nan ya zube! Allah kad’ai ne ya san kalar tsantsar so da k’auna da kuma yadda ya kwallafa rai a cikin nan…..

Dai dai nan Dr ya fito ya kalli Hajiya Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login