Showing 147001 words to 150000 words out of 244445 words

Chapter 50 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16435

cannula!to Allah ya kyauta..””Bismillah”daga haka ta juya ta nufi ciki suka mara mata baya.

A zaune suka tadda Muhsin yana assignment Baba kuma yana zaune a kan gadon jinyarsa yana kallon k’ofar da alamun shigowar tasu yake jira dan ya ji Inna ta ambaci sunan ‘Manu!’.

A hankali ta k’arasa ta d’an durk’usa ta gaida sa tukunna ta zauna a kujerar mai jinya ta shiga tambayarsa ya jikinsa..
Murmushi ya yi duk da bai so ta fito ba duba da yanayin jikinta amma kuma ya yi matuk’ar jin dad’in yadda ta damu ta taho dukda itanma a kwance take…
Cikin fesar da numfashi ya yi ta’auzi ya kawar da shed’an d’in da ya fara comparing masa himmar Manubiya da Ya musbah a kansa,tukunna yace”ya jiikin naki?”
A hankali tace”Alhamdulillah”
“MashaaAllah Allah ya inganta”ya ce kafin ya d’aura da cewa”ki kira mijinki ku koma Manu dare fa ya yi,ai na warke ma Alhamdulillah”
Murmushi ta yi tace”ya tafi siyo abu sai ya dawo za mu tafi..”
Jin jina kai kawai Baba ya yi daga haka suka d’an tattauna Akan batun su Uncle,Manubiya ba ta so ace Yashjub ne ya bawa iyayenta gidan da za su zauna a ciki ba,amma ba ta da choice tashinsu a kusa da su Uncle shine mafita dan abun nasu ya yi yawa..shiyasa har wani sanyi ta ji da ta ji Baba yana gaya mata ai Ya Nafi’u ya yi masa batun maganar da suka yi shi da Yashjub shi kuma
ya amince,inshaaAllah yana fita daga asibiti za su tare,dan d’azu ma Yash d’in ya zo ya d’auki ya Nafi’u suka je ya basa gidan tare da makullai da takardun.Da Nafi’un ma har yana cewa zai zo ya kawo yanzu to sai nace ya barshi kawai dare ya yi..ma had’u gobe.A gidan ma har da b’angaren Musbahu Allah ya sa dai Baraka ta yarda ya dawo gidan su zauna….”


Ahankali Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace zai dawo inshaaAllah Baba,ku dinga yi masa addu’a kar ku bar b’acin ransa a cikin zuciyoyinku fushinku a garesa masifa ne.”

Jin jina kai Baba ya yi kafin yace”ki na da gaskiya kam,Allah ya sa mu dace.”

Knocking suka ji dan haka Muhsin ya mik’e ya je ya bud’e k’ofar….cikin girmamawa ya gaida Yash ya amsa masa da kulawa tukunna suka k’araso cikin d’akin a tare bayan Muhsin ya maida k’ofar ya rufe.

Sai da Yashjub ya d’an russuna tukunna ya gaida Inna da Baba suka amsa ya tambaya ya k’arfin jikin yace”Alhamdulillah”

Wallahi dama shiyasa d’azu bai shigo ba yanzu ma kawai ya ga dare sosai ne shiyasa ya shigo tafiya da Manubiya kar ya barta tana yawo ita d’aya da dare…Sam ba ya so su Baba su yi masa godiya amma suna gama gaisawa suka hau yi masa godiya har da su Jidda wadda itama sai yanzun ne ta ji batun daga bakin Baba.

Kamar zai nutse k’asa haka ya ji,hakanan ya sunnar da kai yana ta faman cewa”Ameen Ameen.”


Ba su wane dad’e ba,suka yi azamar tafiya,Saida duk ta yi musu sallama tukunna ta yi hugging Jidda ta ba ta atm card d’inta da ta d’auko
daga jaka tace gashi,karb’a Jidda ta yi tukunna ta fara shirin rakasu,murmushi Yashjub ya yi ya ce “ta barshi ai su biyu ne.”
Daga haka suka tafi Yashjub yana tunanin
“Ba dan suma a asibiti suke ba da sun tafi da su Jidda”.


A mota Manubiya ma ta so yi masa tata godiyar amma ya yi kicin kicin”wai idan ta yi sai sun yi fad’a”
Har wani turo baki wanda hakan ya sa ta fara dariya….

“Shine amma baka gaya mini ba?”

“Na san zugawa za ki yi ai ki hana,shiyasa na zagaye ki!”
Ya bata amsar yana mai d’an juyowa ya kalleta.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace”da Ya Nafi’u kuka yi magana kenan?”

Sai da ya d’an yi shiru tukunna yace”ni ne na tambayesa na nace shi ne ya gaya mini komai”

Cikin mutuwar jiki tace”ba lalle ai ya Musbahn ya yarda ya tashi daga gidan da yake d’in ba.”

Kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace”na sa a nemo mini number landlord d’in nasu,kar ki damu zai tashi.”

Shiruuu ta yi haka shima Yash d’in daga nan har suka k’arasa asibiti.Kowa da tunanin da ya ke yi,Yashjub gaba d’aya hankalinsa yana a kan wayar Manubiya ne ya lura wayar a silent take kuma sai faman kiranta ake yi tana rejecting shiyasa ya tafi tunanin ko dai wannan wanda ya kira ta ta k’i cewa komai jiya ne?
To kenan ta san waye tunda har take k’in d’auka…bai yi expecting za ta b’oye masa wani abun ba shiyasa shima ya yanke a kan ba zai tambayeta ba,zai danne kansa ya ga iyakar gudun ruwanta.Amma fa yadda zuciyarsa take yi sakamokon kishin da ya ke tunzurosa hatta jijiyoyin gaban goshinsa sai da suka fito rad’au!.

A b’angaren Manubiya kuwa Abbakar ne yake ta nacin kiranta da messages na ban hak’uri wai yana son magana da ita yana neman taimakon ta,ta ji zafin yadda ya banzatar da ita amma kuma babban dalilin ta na ignoring d’insa Yashjub ne! Ba ta so su samu matsala ita da shi saboda wani Abbakar kuma he made it pretty clear to her cewa ba ya son relationship d’inta da Abbakar d’in kwata kwata ko gaisawa ba ya so su yi!…ta san ba ya son shi saboda yana tunanin kamar son ta yake yi kuma ta tuna b’acin ran da ta ji a muryar sa ta kuma gani a fuskarsa duk a ta dalilin Abbakar d’in,shiyasa yanzun ta ke jin tsoron gaya masa ‘Abbakar d’in ya na ta kiranta,ya turo mata message yana buk’atar taimakonta.’Ta zab’i kawai ta rabu da shi da zarar ta nutsu za ta nemo yadda ake block ta yi blocking d’insa gaba d’aya,ta san Abbakar ya taimaka mata ba adadi ya kamata ace ta taimakesa yanzun itama amma Yashjub comes first a komai na rayuwarta kuma tunda ya nuna ba ya son ko gaisawa ne su yi da shi inashaAllah za ta yi masa biyayya…..…..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 31
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.


Sai dare tukunna Baba larai ta tambayi Mommy ya suka yi da Daddy…duk yadda suka yi ta zaiyyane mata,tashi d’aya Baba larai tace mata”bugar cikinta ya yi amma tunda ta ga bai yi mata komai ba yana so ya yi confirming ne dan haka ta nutsu ta sa ido sosai ta yi taka tsantsan.”
Tashin hankalin da Mommy ta shiga ba zai misaltu ba dan sai da Baba larai ta yi mata bayani dalla dalla tukunna itama ta fahimci tabbas bugar cikin nata yayi..yo Ina zata fahimta?gaba d’aya d’azun duk a rud’e take hankalinta a tashe.


Sai wajajen k’arfe sha biyu na dare tukunna Yassir ya yi sneaking daga d’akin Kausar ya tafi side d’insa a lokacin ya san kowa ya yi bacci babu mai ganinsa….
Ba k’aramin mamakin ganin Munirat a zaune a cikin d’akinsa ya yi ba…shaf ya manta da lokacin da ya bata makullan side d’in nasa shiyasa yace”ta ya kika shigo?”
Murmushi ta yi ta mik’e tace”har ka manta lokacin da ka mallakamin makullan d’akinka har ma da na zuciyar ka kenan??”
Sai kuma ta girgiza kai tace”hmm..of course you do”

Numfashi ya fesar a ransa ya aiyyana”lokaci ya yi da zai yi getting rid of Yarinyar nan fa”
Dan haka ya kalleta yace”ki je ki yi bacci please,kaina ciwo yake yi..kar ki sa raina ya b’aci”
Wani irin kuka ta fashe da shi tace”you snake!!ashe dama duk yaudara ce Yassir??yau ni ce zan b’ata maka rai?ka manta yadda kake cewa ba ka iya bacci idan ba na kusa da kai,ka manta duk kalolin k’aryayyakin da ka dinga zuba mini Yassir yau ni kake wulak’antawa kake pushing away Ina kiranka ba ka d’auka ba ka replying messages d’ina saboda ka riga ka samu abunda kake so???”

Runtse idanuwa ya yi da k’arfi kafin ya bud’e ya matso daff da ita tukunna ya ce”ki fad’a ko nawa kike da buk’ata zan biyaki fansar budurcinki”
Wani mahaukacin mari ta zabga masa wanda sai da jinsa ya d’an d’auke na y’an sakanni.
Cikin tsananin b’acin rai ya d’ago ya zuba mata manyan idanuwansa da suka yi jazir yace”zan baki mintuna biyu kacal Munirat! ki fice ki bar mini side d’ina if not wallahi zan baki mamaki….aikin banza!!! ba ma ki kai yadda na yi expecting zan same ki ba amma kin bi kin wani d’aga mini hankali sai kace wadda kika ba ni ranki!”

Kallonsa kawai take yi jikinta yana wani Irin karkarwa kamar mazari idanuwanta suna zubda ruwa kamar fanfo….maganganun cin mutunci da cin zarafi ya ci gaba da fad’o mata dan haka kawai ta wuce sa ta nufi k’ofa tun kafin ya sa zuciyarta ta buga,har ta fice bai daina magana ba sai da ya tabbatar da ta yi nisa tukunna ya yi tsaki ya fad’a bathroom……

Washe gari da sassafe ta rubuto masa doguwar wasik’a da tsinuwa da Allah ya Isa kala kala ta had’o masa da makullayensa da duk wasu gifts da ya tab’a bata ta kai side d’insa ta ajjiye ta.Tabbas Yassir ya koya mata lesson a rayuwa kuma ya cuceta har abada,amma ba komai ya je zai gani……



Da safe Dr ya sallami Manubiya dan jikin nata Alhamdulillah sai d’an abun da ba a rasa ba.

Direct gida Yash ya kaita bayan ya tsaya ya siya musu abinci a hanya…sai da suka yi wanka suka ci abinci suka huta tukunna ya ce “bara ya je ya d’auko mata Jidda da Muhsin su taya ta zama kafin ya je ya d’auko mata gwaggwo mai aiki.”
A take kuwa farin ciki ya wanzu a fuskarta,murmushi kawai ya yi yai kissing forehead d’inta ya fice bayan ya tabbatar ba ta buk’atar komai.

Ko da ya je Inna ta so ta hana su Jiddan zuwa dan ta san halin k’annensa da mahaifiyarsa kar zuwan na su ya zamo case amma sai Baba ya ce”ba komai su je kawai”
Dan a duniyar nan Baba bai ga alfarmar da Yashjub zai nema a wajensa ya k’i yi masa ba muddin bai fi k’arfin sa ba.
Hadda Siyama aka taho dan a lokacin ita da anty Umma sun je duba Baba Yash d’in ya je
hakanan ita da su Ya Nafi’u waenda suka zo da makullan gida suka ta yi masa godiya suma..Anty umma ta na saka masa albarka…..



Sai da ya kai su gida yace”su d’ebi kaya”dan a cewarsa “kwana za su yi”tukunna suka kama hanyar nndc quaters. Ba sa so su yi jayayya da shi,shiyasa kawai suka ce masa to suka d’ebo kayan amma sun san ko da ace suna son kwanan ma su Inna ba za su bari ba….

Yana hanya Najeeb ya kirasa ya ce masa yana k’ofar gidansa dan haka ya ce”ya basa 5 minutes yanzu zai k’araso shima inshaaAllah”.



Suna isa tsabar sauri Siyama ko gama parking Yash bai yi ba ta fito da sauri ta nufi entrance..ta ci sa’a kuwa dan Manubiya tana k’asa dama tana jiransu…murnar ganinsu da oyoyo d’in da Manubiyan ta tsaya yi ne ya sa ba ta samu ta shige d’aki ba har Najeeb d’in ya shigo shi da Yashjub.Allah ya so da ma Manubiya ta hijab d’inta dan ba ta dad’e da idar da sallar azahar ba.

Sama suka nufa Yayinda shi da Najeeb suka zauna a nan k’asan….ba k’aramin tausayi Najeeb ya bawa Yashjub ba dan ya fahimci komai kuma ya lura ko kallonsa Siyama ba ta son yi dan haka ya gama shirya yadda zai yi ya samu ya ceto rayuwar Abokinsa saboda in banda tsantsar so da k’aunar Siyama ba bu abunda yake hangowa a tartare da shi….

Siyama da Jidda har ma da Manubiyan ne suka sauk’o suka yi musu fried rice da coslo mai d’an karen dad’i itakam Manubiya kafin a gama ta jigata dan wani irin amai da zazzab’i take ji gashi aman ya k’i fitowa……

Ana gama cin abinci Yashjub ya kira Manubiya yace “ta turo masa Siyama”
Da d’an mamaki Najeeb ya kallesa sai kuma ya yi shiru kawai ya ci gaba da tunanin da tun d’azu yake ta yi dan ko da suka zauna ma Yash d’in ne yake ta magana.



Cikin nutsuwarta ta k’arasa cikin parlourn inda suke ta sake gaida Yash tukunna ta zauna a kan one seater da ya yi mata nuni yace “ta zauna”
Kamar ba za ta kula Najeeb ba sai kuma kawai tace”Ina wuni”
Saida ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”Alhamdulillah,kwana biyu…”

Ta san jan magana yake so
,shiyasa kawai ta sharesa.

Shiru parlourn ya d’auka kafin taji muryar Yash ta d’ira a dodon kunnuwanta kan sa tsaye yana cewa”Siyama mai yasa ba kya kula Abokina?ki ke ta bashi wahala..ko kwata kwata ba kya son shi?”

Nauyi tambayar ta yi mata gashi ba ta yi expecting hakan ba..shiyasa ta sunkuyar da kanta ta yi shiruu ta gagara cewa komai.

Jan numfashi Yashjub ya yi,kafin yace”a da ban yi niyyar saka muku Baki ba amma naga abu har wajen 4 months ya k’i gyaruwa sai gara mini Aboki kike yi shi kuma na san ba hak’ura zai yi ba!”
“Na san watak’il a kan Ya’isha ne kuka samu sab’ani da shi…wanda ko baki auri Najeeb ba na san ba zai auri Ya’isha ba tunda ba sonta yake yi yanzu ba kinga an yi biyu babu kenan.
Kasancewar ni yaya ne ga Ya’isha ba shi zai sa in k’i bin bayan gaskiya ba,Maganar gaskiya Ya’isha ita ta yi neglecting Najeeb har ya zo ya had’u dake kuma na san kin san negligence ya kan kashe har aure ba wai iyaka soyayya ba….”

“Wannan itace gaskiyar maganar Ya’isha da Najeeb dan haka the choice is yours amma ni dai ina baki shawarar ki saurari Najeeb ki auresa saboda na san yana son ki tsakani da Allah kuma Najeeb is a very good kind and nice person.”

Shiruu parlourn ya d’auka kafin Yash ya mik’e ya ce “Bari na baku guri…”daga haka ya wuce chan sama d’akinsa.

A hankali Najeeb ya mik’e ya k’arasa ya zauna a gefenta kan three seater da ta ke a zaune yace”what more reason kike buk’ata Siyama na ci gaba da azabtar da zuciyata?na garu haka dan Allah ki ji k’aina….”

Shiruu ta yi ta kasa cewa komai kafin tace”zan yi tunani akai”

Wani sanyin farin ciki ne ya lullub’e Najeeb a hankali yace”sai an ja mini rai kenan yanzun ma..”

Murmushin da yaga ta d’an yi ne ya sa ya ji kamar an tsunduma sa a aljannah dan haka a fili ya ce”Alhamdulillah”
“Yanzu ko zuwa anjima idan na zo za ki fito ko???”

Dariya ta yi wannan karon ta d’aga masa kai alamun”eh”sai kuma ta mik’e da sauri ta haye sama….dama chan tana son Najeeb she’s just waiting for someone da zai ba ta genuine reason d’in da za ta auresa dan ba shi kad’ai ba ita kanta ta garu..yanzu kuwa da ta ji komai ta fahimci komai InshaaAllah za ta rufe ido ta goge babin Ya’isha daga rayuwarsu…

Ko da su Manubiya suka ji labarin a take suka goya mata baya d’ari bisa d’ari suna ta murna suka kira Aisha itama ta ji dad’in batun matuk’a….

Najeeb kuwa farin cikin da yake a ciki ya k’i b’oyuwa…Tana wucewa ya kira Yash yace masa “zai tafi”
Yana sauk’owa ya kallesa yace”har kun gama?”

Jin jina kai ya yi kafin ya mik’e yace”Yash Ya’isha kar ta zamo silar…”
Dariya ya ga Yash d’in ya fara kafin yace”Najeeb if I were in your shoes da gudu zan bar sistern ka fa in zab’i Manubiya,na san menene so!”

Sai kuma ya yi tapping shoulder d’insa ya ce”laifin Ya’isha ne,na dad’e da fahimtar hakan,kar ka da mu!”

Ganin still Najeeb d’in bai sake ba yasa cikin zolaya yace”Allah ya sa nan da next week mu je mu yi gaisuwar iyaye”
Da sauri Najeeb ya ce”Ameen”
Dariya Yash ya yi yace”an zo
wajen da za ka yi magana kenan…..”
“You are welcome”
Daga haka suka fad’a zancen case d’in estate d’insa…akwai haske sosai dan ana ta samun ci gaba,soon inshaaAllah suna ganin za a kamo culprit d’in….



Ba su san waye ya gaya wa su Yasira sun koma gidan ba sai kawai ganinsu suka yi har da babbar jaka…Yasira da Yusra da Yadira,dan Yasmeen ma cewa ta yi ba za ta bi su ba wannan karon,tace ita babu ruwanta saboda zuwa yanzu da ta zauna ta yi lissafi ta fahimci tabbas idan ba su daina biyewa Baba larai ba sai ta goge musu duk wani ilimin addini da suke da shi,she can’t believe wai Yassira tana wani ce mata”ai da ma Baba larai ta duba ta gani Manubiya za ta taho da masifu ita za ta ga bayan Mommy tou kuwa gashi alama sun fara nunawa dan haka dole su tashi su tsaya…dama ai duk abunda Baba larai ta fad’a sai ya zama gaskiya”.
Bayan ba su san sakawa da suka yi a ransu ne ya sanya Allah ya barsu da halin su shiyasa suke ta ganin masifun suna zuwar musu kamar yadda sukai zato,idan ba haka ba wacece Baba larai da za a ce duk abunda ta fad’a sai ya tabbata???…
Shiyasa Yasira tana gama zaiyyane mata tace”ita dai babu ruwanta,ba za ta hanasu ba dan ta san ba za su hanu ba idan kuma ta fad’a ta san za ta samu matsala da Mommy amma kar su sake sakota a cikin zancensu….”

Shiyasa Yasirar ta kad’o kan Yadira da Yusra suka taho bayan Baba larai ta cika musu jakankuna da kayan barbad’e barbad’e dan tunda suka je asibiti aka ce an sallamesu ta fara harhad’awa.

Ba iyaka su Manubiya ba hatta Yash ya fahimci kissa ce da k’arya su Yasira suka zo da ita wannan karon…dan yadda suka yi suka chanja gaba d’aya tashi d’aya abun dole ya baka mamaki…hatta Yasira da murmushi ta gaida Manubiya ta shiga tambayarta ya jiki kamar za ta goyata har da zama a kusa da ita,tukunna tace”Mommy ce ta ce su zo
su tayata gyare gyare.”

Shi dai Yash ba don kar ya ce su tafi abun ya zama case ba da tuni ya sallame su dan gaba d’aya haka kurum hankalinsa bai kwanta da su ba.
Ya san watak’il idan gwaggo ta zo za su tafi shiyasa yace bara ya je ya d’aukota amma ko alamun gezau bai gani ba shiyasa kawai ya fita yana jimami.

Suma shiruu suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login