Showing 231001 words to 234000 words out of 244445 words

Chapter 78 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16454

kwana biyun nan daina hankali kawai. …Ta san watak’il akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ne da ya k’i ci ya k’i cinyewa (saboda ta ji anata maganar ciwon nata)
amma ita har ga Allah tsoron d’aukar wayar sa ma take yi,Shiyasa jiya da ta je gida ta tura Muhsin gidansu ya karb’o mata accnt number sa ta tura masa dubu d’ari amma kuma dukda haka Abbakar bai bar kiranta da tura mata sak’onni ba.


A b’angaren Kausar kuwa,tana nan cikin tashin hankali dan ga Yash da Manu a cikin gidan kusa da ita amma kamar basa nan…..ba ta Isa ta je inda suke ba kuma tun da suka zo
ko ganinsu bata yi ba,Yasmeen dai tana zuwa wajensu har Yadira idan sunzo amma shi kam saboda ita ko lek’owa bayayi itama Manu ya hanata shiga main cikin gidan kuma su Hajiya mama sun yarda da hakan,Daddy dai da asubah suke gaisawa Hajya mama kuma ta kan je musu da kanta…….

Tun daga kan Hajiya Mama har zuwa kan Yadira da suke yawan zuwa duk y’an gidan mamakinta suke yi dan ta ma fisu energy,Kwata Kwata ba ta jin nauyin cikin sannan babu alamun ciki ya d’auko tsufa a tartare da ita…….
Kwatsam yau suna zaune aka yi musu waya daga asibiti Kausar ta haihu ta haifi baby boy! Ba ma su san lokacin da ta fita ta tafi asibiti ba.

Ummi da Yasmeen ne kawai suka je asibitin…sai da Ummi ta firgita a lokacin da ta d’auki Yaron sakamokon tsananin kamannin da suke yi ita da Yaron hatta Yasmeen sai da ta lura da hakan dan haka kanta ya sake d’aurewa tamau da al’amarin Kausar da haihuwarta…

Basu dad’e da zuwa ba su Mommy suka k’araso dan haka suka yi mata sallama suka wuce gida kawai ko Yasmeen ma da Ummi ta yi tunanin zata d’an zauna bata zauna ba binta kawai itama ta yi.

Su kansu su Mommy sun yi mamakin tsananin kamannin Yaron da Ummi amma kawai sai suka bari a kan watak’il saboda tana yawan kallon ummin kullum ne,Mommy har da cewa”akwai wani d’an makwaftan su itama da ya tab’a yin kamanninta lokacin suna yawan shiga gidan!!”.
Daganan kuma suka hau murna aka fara zab’e zab’en suna aka zab’i ‘Alan’, ba kad’an ba sun ji matuk’ar dad’i da Yaron ya kasance Namiji dama tun tuni mommy take cewa ta yi scanning ita kuma tace bazata yi ba,gara kawai ta Haifa a gani.

Kausar ba ta b’oye musu abun da ta k’ullawa Manubiya ranar suna ba!
Su dai su Yasira basu ce komai ba,dan zuwa yanzu komai ya fita a kansu
Mommy ce ta bada goyon baya dama tana neman ta inda zata rage bak’in cikin Manubiya kafin a samu asirin ya kamata ta tafi forever…
Idan kuma ma ta mutu kafin ranar sunan to falillahilHamdu!!!

Daganan kuma suka shiga tattauna akan kud’in da zasu had’a bayan suna a samu Mommy ta ga likitan ido,dan suma zuwa yanzu al’amarin idon nata ya na tsorata su.

Bayan kwana d’aya aka kaiwa su Hajiya mama Yaron har gida ,Yash kuwa Ana ce masa za a kawo Yaron ya gani ya fita ya bar musu gidan sai dare tukunna ya dawo.Wanda hakan ya kusa haukata Kausar a lokacin da mai aikin nata ta dawo mata da Yaron take bata labari dan ita a tunanin ta Yaron ne zai sanya Yashjub ya zama close to her da ganan ta sameshi yadda take so……….


Itadai Yasmeen har gobe gaba d’aya mamakin lamarin haihuwar Kausar take yi ta lura kowa ma hakan take amma kawai ba a son yin maganar ne…kwata kwata jikin Kausar bai nuna alamun jego ba kuma duk girman Yaron ance bata samu tear ba sannan har zuwa ranar suna ruwan nono bai zowa Kausar ba hakanan akeya d’urawa Yaron madara.


Gagarumin suna aka had’a na gani na fad’a suka gaiyyace Manubiya…ita Manubiya da cewa ma ta yi bazata je ba shima Yashjub yace “ta huta kawai”
Saboda yau zasu je gida jibi arba’in d’in inna amma sai su Anty Umma sukace ta je kawai tunda sunan da yamma ne kuma ma har sun gama shirye shiryen sadakar da za a yi jibi…saboda idan bata je ba kowa mummunar fassaara zai yi mata tunda har sun gaiyyace ta to ta je kawai.
Dan haka ta tashi ta fara shiri.
Yash ya yi mata waya ya taho tanata sauri tana cikin shiri kiran Abbakar ya shigo wayarta a karo na ba adadi…..tun d’azu basu zauna ba shiyasa bata samu ta saka wayar tata a charji ba dan haka yana kira wayar ta katse ta mutu gaba d’aya!
Tabbas zai ga kamar kashewa ta yi kuma Abbakar bai yi deserving wulak’anci daga gareta ba ko ba komai yadda ya dinga d’awainiya da Inna da Baba bai kamata ta banzatar da al’amarin tasa mahaifiyar ba..har harbinsa aka yi a ranar da akayi case d’in black snake duk saboda ita da ahalinta…..tana cikin wannan tunanin Muhsin ya shigo cikin d’akin kamar ba zata yi ba sai
kuma kawai ta karb’a wayar hannunsa mai tochila ta saka sim d’inta a ciki ta kira asalin layin Abbakar….ga mamakinta yace mata dan Allah ta fito
da ma ya zo
ganinta ne yana neman alfarma a wajenta.”

So ta yi tace ya shigo amma ta san su Aisha ma sai sun yi mata magana muddin suka gansu tare shiyasa kawai ta fita tanata jero istighfari….A nan wajen ta samesa zaune a kan machine d’insa yana hangota ya mik’e ya nufota wanda hakan ya sanya jikinta sake d’aukar karkarwa….
Gaisawa kawai suka yi daga haka ta fito masa k’iri k’iri
tace “dan Allah ya daina yawan kiranta Mijinta baya son mu’amalarsu ya yi hak’uri kar ya janyo mata matsala….
Sosai ya nuna mata ya fahimta yace”ta yi hak’uri dama godiyar kud’in da ta tura masa ya zo yi mata sannan ta k’ara hak’uri da shi amma kud’in basu kai ba..aiki za a yi mata a zuciya yanzu haka dai cikin kud’ad’en da yake ta tarawa saura dubu d’ari biyu…..”

A take ta sake tura masa kud’in ya cika tace ya yi
hak’uri ta san yayi mata halaccin da bazata iya k’irgawa ba amma dole ta yanke alak’arsu har abada ta yi saving aurenta,idan yana buk’atar wani abun ya gayawa Muhsin shi kuma zai gaya mata”
Hakanan suka rabu yanata jera mata godiya zuciyarsa k’all dan chan ya hango Yashjub ya danno kan motarsa tun d’azu amma da ya gansu sai ya tsaya ya ja ya yi parking ita kuma Manu sam ba ta lura da shi ba.
Tunda ta fito yake ta addu’a Yashjub ya zo dan Kausar tace masa mai gadin yace”tun d’azu ya fito……”
Tun a jiya ya tura masa mesaage ta inda yake cewa”a tunaninka sharri na yiwa matarka ko?to yanzu haka halinda ake ciki kud’i take bani nake tarawa zan siya mana gida,mu ja jari kafin ta ta rabu da kai.Manubiya ni take so ba Kai ba za ta iya yin komai saboda ni….idan Baka yarda da maganata ba ka duba alert a wayarta.”
Shiyasa tunda Manu ta fito yake ta addu’ar Yash d’in ya zo saboda ya samu ya sake k’ulleta idan Yash d’in ya gansu tare.

A b’angaren Yash kuwa kwata kwata bai yarda da maganar Abbakar ba! Haba mana!!abu kamar wasan Yara,amma fa da ya gansu tare ya kusan suma a cikin motar dan ko last week sai da ya ce mata ba dai ta kula Abbakar ba ya fakewa da zuwa musu gaisuwa ko?ita kuma tace masa “eh”
Sai gashi yau ya gansu tare a tsaye a waje ba ma a cikin gida ba kamar wasu masu zance!!!

Su Siyama sun tafi Umrah Jidda kuma bata da lafiya shi kuma Muhsin da shi ake aikin kimtsa gida ga aike shiyasa ba ta samu me rakata ba…Bata dad’e da komawa cikin gidan ba Yash ya kirata yace”ta fito ya zo!”
Peach colour lace ne a jikinta da white vail takalmi da y’an kunne da agogo…Bata yi kwalliyar komai ba amma sosai ta yi kyau shiyasa da ta fito ya tuna a haka fa ta ga Abbakar ya ji zuciyarsa kamar zata fashe….
Tana fitowa ta bud’e motar ta shiga suka gaisa sama sama ya kunna motar ya ja suka yi gaba fuskar nan a tamke kamar bai tab’a yin dariya ba,wanda hakan ya d’aure mata kai matuk’a…ya kan yi shiru ya yi ta tunani amma bai cika had’e rai kamar haka ba..

Duk da alhinin rasuwa da take a ciki haka ta daure ta dinga yi masa magana..wanda daga um sai um um kawai ya dinga binta da shi…..
A haka har suka k’arasa wajen..
iPhone d’inta ta zaro ta jona a jikin motar tasa dan ta ga bashi da niyyar shiga ita kuma ta d’auki purse d’inta ta fara k’ok’arin fita bayan tace masa ta gode
Kamar da ga sama ta ji yace”muga wayarki!”

A hankali tace”gata nan tana charji wanna kuma ta Muhsin ce na saka layi na a ciki”
Ta yi maganar tana mik’a masa wayar”
Karb’a ya yi kanshi tsaye ya shiga message ya duba.
Yadda ya mik’o
Mata wayar sai da ta tsorata tana karb’a yace mata”jeki!!”
da d’an k’arfi!
A ransa yana ji inama bai duba ba…shiyasa fa tun d’azu yake ta tausar kansa amma zuciya ta tunzurashi sai da ya duba!!!
Ya san maganar abbakar k’arya ne dayace tana basa zai siya musu gida to amma kuma meyasa ta tura masa kud’i ba tare da ta tambayesa ba sannan meyasa ta fita waje wajensa……
iPhone d’inta da ta kawo haske ya shiga ya duba nan ma yaga ta tura masa..
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun me yasa manubiya zata yi masa haka??”
Ba shi da mai basa amsa a take kawai ya ji hawaye sun b’alle masa dama ga masifar dayake a ciki tun kwanaki talatin da bakwai baya yanzu kuma ga kishin da yake shirin tarwatsa masa zuciya da kwakwalwa.shiyasa kawai ya kafa kansa a kan sitiyarin motar ya fashe da wani irin kuka.

Ya jima yana kuka kafin ya shiga jero istighfari ya goge fuskarsa ya d’ago yana maida numfashi dai dai nan ya ji ana knocking masa gilashin motar tasa….

Ba k’aramin mamakin ganin Aslam M T ya yi ba (Abokinsa da suka yi karatu tare a Uk)
Abunda bai sani ba kuwa wajen taff!! cike yake da Abokansa dan Kausar diary d’insa ta tsinta a d’akin Mommy hakanan ta turawa kaff friends d’insa da invitation na ranar sunan!!!

Yana fitowa Aslam ya yi murmushi yana kallonsa yace”Yash ya akayi ka yi aure?”
D’an guntun murmushin da ya fi kuka ciwo Yashjub ya yi kafin ya d’aura kwayar idanunsa a kan matar da ke gefen Aslam d’in yana rik’e da hannunta yace”kai ya akayi ka yi aure?!”
Duk dariya suka yi har ita Hudan..dai dai nan wasu friends d’insu su biyu suma suka k’araso wajen d’ayan yana cewa “da ikon Allah Yash da Aslam sun rigani aure gaskiya ku nema mini mata”
Dariya d’ayan ya yi kafin yace”ai Yash matansa har biyu amaryar ce ma ta haihu!!”
Ai kuwa nan suka tusa shi a gaba har Aslam wanda duk suka yi mamakin magana da walwalar sa dan hakan ba d’abiarsa bace ba kowa ya shaida…sun d’an jima a wajen suna ta tsokanar Yash kafin suka yi masa murna suka nufi cikin hall d’in gaba d’ayansu..
Shi dai Yash bai so shiga ba sam amma haka suka tilasta masa gashi ba zai yiu ya yi musu bayani ba,ga tashin hankalin da yake a ciki shiyasa ya ji kamar ya d’aga Hannu ya d’aura a ka ya yi ta kurma uban ihu….

Sai da ya shiga cikin ma tukunna ya had’u da ragowar friends d’insa hakanan aka had’u aka yi ta murna kowa yana cewa Yash ya kyauta da ya had’a musu wannan reunion d’in dan sun dad’e basu had’u ba.


Hannu bibbiyu su Mommy suka amshi Manubiya kamar za su goyata daga ita har Kausar d’in…ita dai Yassira binsu take yi da ido amma wallahi tsaf sai ta tona musu asiri saboda ta gaji gashi zargin Mommyn ma ita takeyi da rufe musu Baki dan kwata kwata ta gagara yin maganar Ya’isha a kowa.

Bayan sun shiga ne Yash ya nuna musu Manu wadda ke zaune a chan gefe yace musu “ga wife d’insa chan!”
Huda dama she’s uncomfortable a tsakaninsu shiyasa tace masa bari ta je wajensa….
Mommy d’ayan Abokin nasa ya hango dan haka suka je suka gaida ita suka dawo suka ci gaba da tsokanar Yash wanda shi ya k’i yarda ko kallonta ma ya yi….hakanan itama Kausar ya k’i amincewa su je wajenta ko jaririn ma ya k’i basu fuskar su d’auka saboda shi har yau bai ko kalli fuskar Yaron ba hud’uba ma Junior ne ya yi masa…su Daddy kuma basuce komai ba har yanzu wanda hakan ya sake fusata Kausar ta san duk dan Manubiya ne hakan take faruwa da ita shiyasa da ta tuna a yau zata kawo k’arshen ta sai kawai ta basar ta d’an ji sanyi a cikin ranta.

Manubiya tana zaune Huda ta zo ta zaune a kusa da ita suka gaisa tace mata”sunan ta Huda matar Abokin Mijinta Aslam”
Itama Manu ta ce mata sunanta Manu daga nan suka sake gaisawa suka zauna tare suna kallon masu rawar k’oroson da aka d’auko suke ta chasewa…
Ita dai Huda har ga Allah kwata kwata Kausar ba ta yi mata ba..ta wani zauna a kan kujerar alfarmar ta had’e rai kana ganinta ka san bata da mutunci gashi ita da Manubiya sam babu had’i shiyasa take ta tunanin dalilin da yasanya Yash ya auri Kausar bayan Allah ya basa Manu a matsayin mata……


Suna zaune aka kira Hudan a waya akwai kid’a sosai ta san ba za ta ji ba shiyasa ta mik’e tacewa Manubiya bari ta amsa call ta dawo……ba ta yi mintuna uku da fitan ba ta dawo kusan a tare suka shigo ita da Kausar wadda ta shigo ita kuma ta k’ofar kusa da seat d’inta…tun kafin ta fita ta ga Kausar d’in ta mik’e ta fita kuma bata ga lokacin da ta fita da jaririn ba amma tabbas yanzu da Yaron ta ganta ita da wata maid a wani dogon lungu inda ta je zata amsa waya itama…bata ma yi wayar a wajen ba ta chanja waje saboda kana ganinsu ka san basu da gaskiya kuma ba sa so a gansu sannan tabbas indai har she’s not mistaken to kamar a buhu ta ga suna shirin saka Yaron!
Noo it can’t be!babu uwar da zata saka jaririn d’anta a buhu ba bu ita!amma kuma what are they up to???”
Ta yiwa kanta tambayar kanta yana sake d’aurewa…..

Ita kam Manu al’amarin Yash damuwa alhini da kuma halin da take a ciki ne suka sanyata a gaba ta ma kasa magana ga kuma ciwon cikin period d’in da take yi sannan gashi ta ji kamar har ta fara b’ata jikinta tsabar yadda pad d’in jikinta ya jik’e!
Ba ta k’aunar chanjin pad a unguwa Idan ta fita amma ya zame mata dole!
Allah ya so ta ta zo da pad d’inta dan haka a gaban idanun Huda ta bud’e jakarta ta d’auka bak’ar ledar mai zip da ta sako pad d’in a ciki ta mayar ta rufe ta bata tace ta rik’e mata jakar bari ta je ta dawo….
Ba ta dad’e da fita ba itama ta dawo…tana zama baba ya kirata suka yi magana sai da ta kashe tukunna ta cewa Huda jibi sadakar arba’in d’in Mahaifiyarta
Sosai Huda ta tausaya mata nan ta yi mata gaisuwa tanata bata Baki…

Kwatsam y’an sanda da sojoji tare da masu gadin event centre d’in suka danno kai cikin hall d’in gadan gadan wanda hakan ya tada hankalin kowa matuk’a…gasu kuma rik’e da jaririn da ake sunansa wanda jama’ar wajen kaff basu ga lokacin da aka fita da shi ba a tunannin kowa Yaron yana chan a cikin gadonsa ne.

Mik’ewa tsaye suma su Manu suka yi ita da Huda dan mutane sun fara hayaniya da guje guje kowa ya nufi k’ofa…
Da gudu Kausar ta je ta karb’e Jaririn daga Hannunsu ta fashe da wani irin kuka…
babban sojan da aka zo da shi ne ya d’auki mike ya yi harbi sama yace kowa ya zauna wanda hakan ne ya nutsar da mutanen wajen…maid d’in da suka kama da Yaron ya saka aka kawo masa gaban hall d’in itama..dalla dalla yayi musu bayani akan cewa”satar sark’a aka yiwa ogar su matar da suke gadin ta to kuma suna shirin shigowa ne suka kama wannan maid d’in da jaririn zata fita da shi a buhu…tace musu sakata aka yi aka bata mak’udan kud’ade,dan haka kowa ya zauna za ta nuna wadda ta turota!!”

Ko da wasa sam Manubiya ba ta yi tunanin ita zata nuna ba…a cikin zuciyarta tanata alhinin rashin imani irin na masu satar yara….
Kawai tana k’ok’arin zama kwatsam tana d’agowa taga maid d’in ta yi pointing saitin ta!!
A rikice ta juya ta kalli gefe da gefenta amma babu kowa ita d’ince dai….Bata Ida fita daga shock ba mutumin ya nufota gadan gadan har da ankwarsa……

Aslam ne kad’ai ya rage zuwa wannan lokacin a cikin Abokan Yash bai tafi ba dan ragowar k’uluwa suka yi da attitude d’in Yash d’in kawai suka yi masa sallama da barka suka wuce!ya k’i dariya ya k’i basu baby su gani ya k’i tsayawa a yi hoto,sannan gaba d’ayansa a rikice yake kana ganinsa…shiyasa kawai suka basa space suka wuce……..

Da sauri Aslam ya nufi sojojin da Manu dan ya lura Yash bashi da niyyar yin komai!!!
Kawai ya tsaya ne ya k’ame….

Yana zuwa ya warce ankwar ya yar yacewa sojan”Atleast ka yi bincike sosai mana dan kawai ta fad’i abu shikenan sai mu hau kai mu yarda?ka san wacece wannan d’in da kake shirin arresting?”
Da gudu Kausar ta yo kan Manubiya tana kuka wai zata daketa da kyar aka rik’eta aka hanata tab’ata su Mommy suka janyeta aka fita da ita tana cewa”Allah ya isan Yaronta da ta saka mata a cikin buhu wallahi Allah sai ya yi musu hisabi muguwa azzaluma saboda ita bata haihu ba shine zata kashe mata nata!!!”

Ita dai Manu uffan ba ta ce da su ba tunda sojan nan ya nufota da ankwa har kawo yanzu kawai ta k’ame a wajen ta kasa cewa komai!!babu wanda ya fi bata mamaki kamar Yashjub wanda kawai ya tsaya ya kafe su da idanuwa ya gagara cewa komai!!!

Shi kuwa Yash bak’in cikin Kausar ne ya ke jin kamar zai kashesa,bayan jama’ar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login