Showing 159001 words to 162000 words out of 244445 words

Chapter 54 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16475

ta ce yace “kowa sai ya ji kansu shi da ita,har Yahanasu”.A ganinta idan ba ta samu damar shak’uwa da Yahanasu ta bata tarbiyya da kulawar da ta kamata ba bai kamata ta bada gudun mawa wajen goga mata bak’in fenti ba!Yahanasu mace ce aure za ta yi ta san muddin ta bawa Imam k’ofa ya tozartata tabbas abun sai ya shafi rayuwar y’arta.
Mommy Uwa ce ta gari kuma za ta iya rantsuwa a kan soyayyarta ta gaskiya ga Yahanasu shiysa ta zab’i ta bisu ta addu’a dama rayuwa ba a yi ta dan ka samu komai perfect yadda kake so ba…tsakaninta da lawal Allah ne kad’ai zai Isar mata dan ya cuceta ta koina,Imam kuma ya tarwatsa ta gaba d’ayanta!kaico!da rashin sa’ar Miji na gari wanda zai tsaya mata ya bugi k’irji ya yi shaidar ta ya kareta a gaban kowa,asalima shi harin rayuwarta da duk wani sauran farin ciki da darajarta yake yi…
ko maganar tozarcin da wannan rana ta k’unsa ba ta so ta tuna ballanta a yi mata terere a bainar jama a a gaban y’arta.
Dan haka ta zab’i ta bi y’arta da fatan alkhairi kawai tare da addu’ar samun Miji na gari dan tabbas duk macen da ta yi rashin sa’ar Mijin kwarai a rayuwa to ta yi babban rashi…..shiyasa tun jiya Hankalinta yake a tashe take addu’ar Allah ya kawo abunda zai tarwatsa maganar auren Jidda da Yusuf dan tabbas Yusuf bai dace da Jidda ba mutumin da ba a san silar arzik’in sa ba ta ya za a d’auki y’a a basa saboda Allah…………..

Sallamar su Manubiya ce ta katsewa Mama dogon tunanin da ta lula!a hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta shiga goge hawayen da ita kanta sai yanzu ta san suna zubo mata.Sai da ta gama goge fuskarta tukunna ta d’ago ta kallesu tana mai amsa sallamar tasu.
Cikin tsananin mutuwar jiki Manu ta k’arasa inda take suka gaisa da Mama da Aisha da Anty Umma,ta gaida Ammi wadda daga ita har Siyama suka yi mamakin ganinta a parlourn nasu tukunna tace musu “Ina su Inna”
Aisha ce ta mik’e tace”mu je wajen nasu”
Daga haka ta yi gaba suka bi bayanta.

Su biyu kawai suka tarar a cikin d’akin,Jidda ta rame a cikin kwana d’aya tak ta fita a haiyyacinta..
Suna zaune Inna ta na yi mata nasiha a haka su Manu suka shigo suka tarar da su.
A gefen gadon suka zazzauna suka sakata a tsakiya kowa idanunta ya cicciko.
Bayan gaishe gaishe Inna ta yi sauri ta mik’e ta ce”ga su Manu Aisha ku yi mata fad’a kuma Baba yace ana d’aurawa za a wuce a kaita gidanta.”
Siyama ce ta iya cewa”Inna kuma babu abunda za a yi?”
Murmushin da ya ki fi kuka ciwo Jidda ta yi ta rik’o hannunta tace”ba komai Siyama,Allah ya sa hakan ne ya fi alkhairi”
Siyama na shirin yin magana suka had’a ido da anty Umma wadda shigowarta kenan dan haka ta yi saurin d’aura yatsanta a kan labb’anta alamun ta yi shiru kafin ta kalli Manubiya tace”Manu d’an zo”
Suna fita ita da Inna suka ce mata “tunda har Jiddan ta yi shiru ta hak’ura itama to kawai su ci gaba da kwantar mata da hankalli,kar wadda tace wani abun da zai d’aga mata hankali a cikinsu.
Baba ya riga ya yi nisa ba zai ji kiran kowa ba ga Ammi Chan a parlour har ita aka had’u aka dinga bashi hak’uri d’azu amma ya k’i hak’uri dan haka kawai su zuba mishi ido.Zab’in Allah suke nema a ko da yaushe ba su san meye a k’asa ba,su dai su ci gaba da addu’a kawai…”

Da “to” kawai Manubiya ta amsa su daga haka ta nufi d’akin da ke opposite na Jiddahn dan ta san watak’il shine na Inna,tana shiga ta mayar da k’ofar da rufe dan har ga Allah ba ta son had’a idanu da Jidda ba za ta iyaba,she can’t believe wai Jidda za ta auri Yusuf amma ba abunda za ta iya yi a kai.
Waya ta d’auko ta kira Yashjub,a tunaninta har yanzu za ta ji fushi a muryarsa amma sai ta ji sa wasai kamar ba ta yi masa laifi jiya ba har yana tambayarta akwai abunda take so ya siyo ya taho mata da shi?yana hanya Daddy ya d’an kirasa zai je ya dawo.”
“A’a”kawai tace.
Daganan ta tambayesa ya suka yi da Baba,komai ya gaya mata daga haka shima yace su yi ta addu’a he’ll call her back yana shiga office d’in Daddy yanzun”
Sallama suka yi ta ajjiye wayar tana tunani barkatai a cikin ranta.

K’arfe 10:30am guri ya cika taff da jama’a dan Yusuf da kaka mallan sun yi gayya ba laifi,cikin gida kuwa kowa hankalinsa a tashe yake suma su Ya Nafi’u hankali a tashe dan yanzu suka dawo daga kai gado shiyasa suka kuma tabbatarwa eh fa Jidda Yusuf za ta aura…kaff wajen daga y’an gaiyyar sod’i da suka ga anata sauk’e kulolin abinci da lemuka da snacks da kajii sai Yusuf da kaka mallan ne kawai suke farin ciki dan hatta Baba hankalinsa ba a kwance yake ba ba a son ranshi zai aurawa Jidda wanda ranta ba ya so ba especially ma yanzu da Baban Al’Ameen ya zo ya ja sa gefe ya basa hak’uri yace”a shirye yake ya aurawa Al’Ameen Jidda a yanzu.Ya yi trusting Al’ameen har ma da ita kanta Jiddan amman indai har zargin su yake yi kamar yadda labari ya iske masa to tabbas babu wanda ya fi chanchanta Jiddan ta aura idan ba Al’ameen d’in ba.”
“Ya je ya sake tunani,da shi da wakilin Al’ameen suna nan babu inda za su je,fatan Allah ya sa su ji alkhairi.”

Tun daga nan jikin Baba ya yi sanyi tun ba ma da Baban Al’ameen yace”ya yi trusting har ita kanta Jiddan” ba!
A take a lokacin ya ga rashin adalcinsa ga Jidda…..tabbas ya biyewa dokin zuciya ya yanke d’anyen hukuncin da har abada zai dinga damunsa dan ya san zuwa yanzu kam ba zai yiu ya chanja d’aurin auren nan daga kan Yusuf ya koma kan Al’ameen ba….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 34
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

“Na gaya miki dama,ni ne Mijinki…in da ace ba ki tsaya b’ata mana lokaci ba da tuni abubuwa da dama basu faru ba!.
Allah ya bamu zaman lafiya Jidderty”
Yusuf yana gama turawa Jidda message kamar haka ya juya ya nufi cikin masallacin yana zuba wani faffad’an murmushi yana ji kamar an yi masa bushara da Gidan Aljannah.
A gefen Baba ya nemi guri ya zauna,idaunsa a kan Baban Al’ameen wanda tun d’azu ya ke ankare da shi yana sane da shi ya san so yake a fasa auren a bawa d’ansa,har ga Allah bai yi niyyar yiwa Baban Al’ameen ko Al’ameen d’in wani abun ba amma abunda mutumin yake ta yi tun d’azu ya sa ya k’ullacesu kuma sai ya nuna musu waye Yusuf! bari a gama d’aura masa aure da Jidda a kaita gidansa lafiya Wallahi sai ya b’atar da su.
Ana shirin fara d’aurin auren.
Sojoji da y’an sanda masu fararen kaya sun fi mota ashirin suka danno kai cikin layin a dai dai wannan lokacin.

Sojoji uku da ss guda d’aya ne suka shigo cikin masallacin suka ce “kowa ya fito!”cikin dakakkiyar murya,aikuwa tashi d’aya waje ya hautsine,
cike da fargaba jama’ar suka fara kiciniyar fita ana hayaniya da tambayar “mai ya faru”
Baba ne ya juya da niyyar cewa Yusuf”mu je mu ji mai ya faru,a samu abun ya lafa sai a dawo a d’aura”..amma kamar walk’iya da ikon Allah sai ya ga babu Yusuf babu mai kama da shi bayan yanzunnan suka gama magana.

A b’angaren Yusuf kuwa tun da ya ga Sojoji hankalinsa ya yi masifar tashi,tsoro ya rufesa in banda dukan uku uku babu abunda k’irjinsa yakeyi, dukda kuwa ya san cewa fuskarsa is not known a cikin yaran black snake kuma he’s not wanted amma hakan bai hanasa tunanin watak’il shi aka zo nemeba,dan yanzunnan yaga message d’in Abokinsa ta inda yake cewa”an zo kama Black snake a airport ya yi yunk’urin guduwa an harbesa ya mutu sannan an bud’e wayarsa an fara binciken neman yaransa,dan haka a duk inda yake ya gudu kafin a samu komai ya lafa.”
Yana gama karanta message d’in ko numfashi bai ja ba ya ga Sojoji sun shigo shiyasa ana fara hayaniya ya sulale ya bi ta k’ofar liman da sauri ya fice amma yana fita yaci karo da wasu a ta gaban k’ofar saboda dama zobe suka yiwa masallacin….tashi d’aya suka damk’esa dan an raba musu hotonsa shiysa suka yi saurin shaidasa.

Baba Yashjub wanda k’arasowar sa kenan sai su Ya Musbah sojojin suka yiwa bayanin arresting Yusuf da aka yi……
…..”A cikin wayar black snake suka hararo Yusuf ta hanyar bibiyar chat d’insu da suka yi,an gano yana d’aya daga cikin manya manyan yaransa masu tayashi safarar kwayoyi da y’an mata dan yanzu haka ma a wannan ranar if not ba a kamasu ba to suna shirye shirye ne a kan shi Yusuf d’in zai taimaka a sacewa Black Snack wata Yarinya ‘Mannubiya’…..”
Dan haka za su tafi da shi kuma babu bailing har sai sun gama interrogating d’insa daganan idan suna so za su iya d’aukaka k’ara zuwa kotu kafin a yanke masa hukunci….

Suna ji suna gani aka datsawa Yusuf ankwa wanda yake ta turje turje aka wuce da shi,shi dai Baba bai gama gasgatawa ba amma su Ya Musbah da Yashjub wanda yake ji kamar ya bisa ya fara nad’a masa shegen duka tun a nan saboda tunanin sace masa mata ma da ya yi,duk sun yarda.

Kaka mallan kam har da kukan sa a take ya nemi adaidaita sahu ya nufi gida yana tafe yana kiransu Baba Habu a waya…..



Limamin ne ya matso ya yiwa Baba jaje kafin yace “yanzu a yi sanarwa Akan an fasa d’aurin auren kowa ya watse kenan?ko za a d’aura ko babu shi?”
Murmushi ya Nafi’u ya yi ya kalli Baban Al’ameen wanda ya k’araso yanzun yace”za a yi d’aurin aure yanzu amma ba da wanchan Angon ba,an chanja sabon Ango.”

Jinjina kai Baba ya yi yana jin wani nauyi yana sauk’a daga k’irjinsa dan har ga Allah da ya d’aura auren nan yau da bai san ta ya zai kalli Jidda ba,cike da kwarin guiwa ya kalli Limamin yace”sunan sabon Angon Muhammad Al’ameen Muhammad.”

Murmushi mahaifin Al’Ameen ya yi a fili yace “Alhamdulillah”
Daga haka suka d’unguma izuwa masallacin.

Jidda ne kawai da Siyama sai Muhsin wanda shima ya yi jigumm a cikin d’akin….
Kamar a mafarki ta ji ana sanarwa a loudspeaker”An d’aura auren Muhammad Al’ameen Muhammad da Maijidda Musa akan sadaki naira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba….
Wani irin bahagon numfashi ta fesar ta sake kwantar da kanta a kan cinyar Siyama wasu zafafan hawaye suka shiga gangaro mata a ranta tace”shikenan na zauce!!gashi dai k’iri k’iri da Yusuf aka d’aura auren nan na riga na sani amma sunan Al’Ameen nake ji…..”
“Jidda kin ji abunda kunnuwa na suka ji kuwa???”

Shiruu ta yi kafin ta tashi a mugun zabure ta mik’e ta zauna sakamokon abunda ita da Siyama da Muhsin suka ji an sake fad’a ana kuma maimaitawa a loudspeaker dai dai nan su Anty Umma suka shigo Anty Umma tana shigowa ta rungume ta haka ma Aisha wadda take waya da Nafi’u domin ta tabbatar….
Sai da ta yanke wayar tukunna ta sanar da su komai abunda ya faru…
Nan waje ya kaure da murna Jidda kuma ta fashe da kukan da kowa ya san na farin ciki ne…
Har cikin d’akin Ammi ta shigo ta rumgume Jidda ta sake neman yafiyarta tukunna tace”Bari ta tafi ta fara shirye shiryen tarbar amarya…”
Tare suka tafi ita da Mama domin su je su d’anyi shirye shirye….Zuwa yanzu Mama ta tabbatar Yashjub dai d’an gidan Imam Manubiya ta aura dan tana ganin su Yusra ta ga kamanni,ta dad’e da yiwa kanta alk’awarin fita daga harkar Imam da zuri’arsa amma kuma tana so ta ji ya Yahanasun take,dan haka ta tsara a kan za ta ke tambayar Manubiya halin da y’ar tata take ciki ba tare da ta bari ita kanta Manubiyan ta fahimci wani abu ba….


Akwai tafiyar da Al’ameen zaiyi zuwa Dubai nan da sati d’aya shiyasa ana gama d’aurin auren Mahaifinsa ya cewa Baba”sai nan da sati d’aya tukunna za su d’au amarya inshaaAllah daganan direct sai a wuce da ita airport”kamar ya sani sai ya d’aura da cewa”amma dai za su fara magana da Angon yanzun duk yadda suka tsayar zai kira sa.”
Aikuwa albishir yana zuwar ma Al’ameen bayan ya gama kukan farin ciki ba kunya ba tsoron Allah ya ce shifa kawai a kawo masa matarsa yau su zauna a nan kafin su wuce”
Dariya su Ammi suka yi suka kira su Inna suka sanar musu….k’arfe takwas dai dai aka kawo amarya Jidda side d’in Al’ameen da ke cikin gidan.
Sai da kowa ya watse tukunna ya shigo…farin ciki da tsantsar nishad’i masoyan suka tsinci kansu a ciki mara musaltuwa….tunda ya shigo ya yi hugging d’inta suka yi shiruu da kyar ya cikata suka yi nafila suka d’anci abinci daga haka ya ja ta ya sakata a jikinsa yana sauk’e ajiyar zuciya yana hamdala suka kwanta…..Jidda har ta fara fargaba..ganin awa d’aya awa biyu bai yi yunk’urin yi mata komai ba ya sa ta kwantar da hankalinta tana mai sauraron yadda k’irjinsa yake bugawa da k’arfi har zuwa yanzun,a haka suka kwana ranar in ka gansu kamar wanda aka cewa wani zai kwace masa ita ne,ita kam Jidda jikinta har ya fara tsami tsabar yadda ya ruk’umk’umeta…..



Tun a wajen kai amarya Yusra ta kira Ya’isha tace”to fa babu abunda aikin Baba larai ya yi dan ga Najeeb da Siyama nan kamar za su cinye juna!”
Dabass!!!haka Ya’isha ta zauna a kan kujerar parlourn Mommy sai kuma hawaye suka fara bin fuskarta…
Da mamaki Mommy da Baba larai waenda suke cikin tsananin farin ciki suka shiga kallonta don yanzunna ta dawo daga ganin Abbakar take ce musu”Da farko ya d’an so ya yi zurfin ciki amma daga baya ya amince d’ari bisa d’ari it’s like ya ma fi su son mutuwar auren Manu da Yash d’in,kuma yace’ba ya buk’atar sisin kobo kawai su kular masa da mahaifiyarsa su biya duk wasu kud’ad’en asibin ta.”
Hakanan suna ta murna ita da su to kuma me ya saka ta kuka tashi d’aya haka…
Mik’ewa Mommy ta yi ta k’arasa inda take ta shiga tambayarta,da kyar ta iya ce mata”ai Najeeb da Siyama aka
gani tare har yanzu suna tare ba su rabu ba….”
Sai kuma ta mik’e ta fice da sauri tana kuka.
Shiruu Mommy ta yi ta fad’a duniyar tunani,har ga Allah tana mutuwar son Najeeb ya auri Ya’isha gashi abun na Y’an matan nata xuwa yanzu ya fara damunta..Jiya ta ga d’aurin auren d’an k’awarta wanda suka shirya ita da k’awar tata a kan za a had’asa shi da Yasira,tsabar abun da munafurci ko gaiyyatar ta bikin ma ba a yi ba sai kawai d’aurin aure ta gani….
“Ki kwantar da hankalinki,inshaaAllah duk za su yi aure,Najeeb kuma shima ki barni da shi bari mu fara gamawa da Manubiya tukunna”
Muryar Baba ta katse mata tunaninta.
A hankali tace”Baba larai idan kuma ya kai kud’i kafin a gama da Manubiyan fa?”
“Kar ki damu ba zai kai ba,ai ita Manubiya inaga ba lalle ta k’ara sati biyu a cikin gidan nan ba!komai a shirye yake kuma yana tafiya a kan tsari ga kuma wanchan Yaro d’an albaraka Abbakar shima yana side d’in mu,dan haka kawai ki kwantar da hankalinki a kan komai…kar ki damu Najeeb will come around sannan shima wanchan na Yasirar ko a ta biyu ne za ta shiga inshaaAllah……”
“Allah yasa”
Kawai Mommy tace,daga haka ta yi shiruu haka itama Baba larai.

Bayan sati biyu!.

Satin su Jidda d’aya a Nigeria suka wuce Dubai ita da Al’Ameen dan cikin sauk’i ta samu visiting visa.


Najeeb da Siyama abu ya yi k’arfi da shi da Yashjub har sun je sun nemi izinin zuwa zance a wajen su Baba Habu wanda hakan idear Baba ce,yanzu haka kuma maganar kawo
Kud’i da saka rana ake yi…..

Yusuf kuwa babu shi babu labarinsa an hana ma ganinsa,sai dai hakan kms ya sake ruru wutar bala’i tsakanin Baba da y’an Uwansa a cewarsu”tsabar mugunta a gabansa shi da Yashjub aka tafi da Yusuf amma ba su yi komai ba instead ma su d’aurin aure suka ci gaba da yi.”


Ya’isha Yassira da Yusra kuma suna gidan Manu har yanzu sun kafa sun tsare,da farko ba sa samun damar yin chatting da Abbakar ta wayar Manu kamar yadda suka tsara sai da aka yi sati d’aya suka samu Siyama ta tafi tukunna….sai sun daidaici ta tada sallah za su d’auki wayartata su yi abunda suka ga dama su goge su ajjiye mata wayar kafin ta idar dama shima Abbakar ya san time d’in da suke samun chance shiyasa he’is always available……Ana gamawa za su goge gudun kar ta gani shi kuma Abbakar yana chan yana tarawa a tasa wayar.


A b’angaren Baraka da Ya Musbah kuwa,tunda ta ji labarin tashi tashin ma zama gida d’aya da su Inna tace ba ta san zance ba,gashi kuma tun a ranar aka basu notice akace su tashi daga wannan gidan da suke a ciki in one week time mai gidan ya siyarwa wani…
Sai da aka yi fad’a da ita a k’ofar gida tace”ai ba a tab’a bada notice d’in da ba na shekara d’aya ba dan haka ko ubanwa ya siyarwa gidan wannan tsakaninsu shi da sabon mai Gida ita kam ba za ta tashi ba sai ta cinye shekara d’ayar ta sannan ba za ta karb’i refund ba,da kyar aka rabata da mutumin dan shima d’an a yi ne,sai da ta koma ciki tukunna mutumin ya bawa ya Musbah kud’in hayar sa ya sake bashi hak’uri yace”ya taimaka su nemi gida su tashi ga kud’insa nan complete ma ya bayar”
Ya Musbah dama yana so ya ci gaba da makarantar da ya soma kuma har ga Allah zuwa yanzu yana son zama a kusa da su Baba shiyasa shi abun ma dad’i ya yi masa dan haka ya karb’a yace”ba komai za su tashi in one week

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login