Showing 198001 words to 201000 words out of 244445 words
je mu dawo,incase idan Daddy ya tambaya ina ina kice na sha magani na kwanta Idan kuma sun ji an fita sun tambaya kuce su Yasira ne suka tafi siyowa Kausar magani…”
Tana gama fad’in haka suka saka sa kai suka fice su uku ragowar kuma suka ci gaba da lallashin Kausar.
Ya’isha ce ta biya side d’inta ta d’auko musu hijabai dan Mommy ba ta da kuzarin wannan,daganan ta taho da makullin motarta ta mik’awa Yasira…daga haka suka sauk’a k’asan.
Dama Yasira ta san gidan Yashjub suka nufa aikuwa tana kunna motar Mommy tace mata”gidan Yashjub za mu je.”MANNUBIYA
(Book 2)
Page 39
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Lokacin da su Mommy suka isa gidan,su Yashjub suna chan sama d’akinsa shi yana wanka Manubiya kuma tana zaune a kan sofa ta fara jiyo k’arar door bell!.
Kusan minti biyu suna a tsaya ba’a zo an bud’e ba, dan haka suka fara danna masa call ta wayar Mommy.
Wanka yake yi alokacin shiyasa Manu ta d’auko Hijab d’inta ta sauk’o.
Sai da ta lek’a ta y’ar b’ular jikin k’ofar tukunna ta sa Hannu ta bud’e k’irjinta yana wani irin bugu dan tana ganinsu Hankalinta ya tashi zuciyar ta ta shiga tsitstsinkewa.
Har k’asa ta durk’usa tace”Mommy Ina wuni”
Ba tare da ta kalleta ba ta wuce kawai ta nufi sama tana mai cewa”Ya’isha duba mini k’asan ko yana nan in baya nan ki hawo mu duba sama”.
Tana gani Ya’isha ta k’araci dube dubenta ta zo ta haye saman suka barta nan bak’in k’ofar a durk’ushe dan tun d’azu ta kasa tashi.
Da kyar ta samu ta mik’e ta tura k’ofar ta mayar ta rufe daga haka ta shige d’akin bak’i na nan k’asan tana shiga ta fashe da wani irin kuka….A yadda ta ga Mommy ta zo a zuciyen nan it’s either ta saka Yashjub ya mayar da Kausar ko kuma ta sa itama a sake ta.!
Ya fito kenan d’aure da towel kawai ya ga sun shigo su duka ukun.
“Subahanallah” ya ambata daga haka ya juya ya koma cikin closet d’in da sauri hankalinsa a tashe ransa a mugun b’ace….ita kanta Mommy yana da tabbacin ba ta tab’a ganinsa a haka ba da girmansa ballantana su Yasira
sannan yadda ya ganta a gidansa a cikin bedroom d’insa haka ya san ba alkhairi ne ya kawo ta ba amma fa yau sai dai duk abunda zai faru ya faru dan shima a high yake
Yana wannan tunanin ya zura jallabiya bai zare towel d’in ba ya fito fuskarsa a mugun murtuke kamar bai tab’a dariya ba.
Idanuwansa waenda har yanzu kalarsu bai daidaita ba ya zubawa su Yasira kafin yace”ku fita ku bani guri!!!”
“Ba inda za su fita su je!!
Ai idan za a yi tsinuwa ana buk’atar wasu a wajen saboda su bayar da sheda!!!”
Zuwa yanzu jikin Yashjub ya fara karkarwa…ya zubawa Mommy idanu kawai ya gagara cewa komai kafin ya yi taku biyar zuwa shidda ya k’arasa ya tsaya a daff da ita har tana jin hucin numfashinsa yace”Mommy saboda na saki Kausar shine za ki tsine mini????”
Ta d’an tsorata dan yanayinsa na yanzun yanayine na wanda yake cikin tsananin b’acin rai capable of anything sannan taga kamar furucin nata bai yi wani tasiri a kan sa ba,amma sai ta dake cikin sake son cin nasara a kansa tace”kwarai ma kuwa Yashjub!na rantse da girman Allah Wallahi Tallahi billahilazim idan har baka mayar da Kausar ba a yanzu a take sai na tsine maka ka bi duniya!!!
Tun muna daga mu sai kai tun kafin duniya ta ji su Daddy su ji ka mayar da Kausar matsayinta na matar ka idan ba haka ba sai na yi maka Allah ya Isa nonona da ka sha!”.
A hankali Yasira wadda jikinta ya yi sanyi ta fara tsorata dan sam ba ta kawo abun da suka zo yi kenan ba,ta matso jiki ba kwari tace”Mommy kar ki yi haka,a nemo wata mafita amma banda wannan.”
Wani irin kallo Yashjub ya yi mata kamar zai yi magana sai kuma ya kauda kai yace”Mommy ni da kaina na tab’a kama Kausar da Yassir a side d’inmu shiru kawai na yi muku ban fad’a ba!ta ya kike so
In yi zaman aure da dadiron k’anina?
Kausar ta haramta a gareni dan Allah ki ma janye wannan maganar saboda anzo in da ba zan tab’a yin abunda kike so ba.”
Jin jina kai ta yi kafin tace”ko da ace zan tsine maka ko?”
Cikin d’an d’aga murya yace”Mommy are you not listening to me?
Kama ta fa na yi red handed ita da Yassir on bed,ta ya zan rayu da ita??”
“Allah na tuba kana Ina Yaya yake rabuwa da mace k’ani ya aura?!ai ba wai ance haramun bane kawai dai ana barin Halak ne dan kunya.Dan haka dan ka ga Kausar da Yassir wannan tsakanin su ne su da Ubangijin su,kai kuma kai ne wanda duniya ta sani a matsayin mijinta dan haka wannan duk bai shafeka ba!!!!”
Mommy ta fad’i hakan tana huci.
Cikin d’aurewar kai haushi bak’in ciki da tsananin mamaki yace”bai shafe ni ba idan Kausar ta kwanta da k’anina???
bai shafeniba dan ta kasance karuwa??Mommy wacce irin uwa ce ke!?da kike k’ok’arin ignoring duk waennan facts d’in saboda kawai ki farantawa Kausar.”
A hankali yana kallonta yace”anya Mommy kin san ciwo na kuwa??kin san zafi na kuwa?wannan rashin adalci haka har ina?ko dai inada wata uwar daban ba ke ba??!!!”
A rikice ta d’ago tashi d’aya ta d’aukesa da wani gigitaccen Mari sai kuma ta fashe da kuka…
Cikin kukan tace”Wata tara ciff ka d’auka a cikin cikina,bayan dogon laulayi mai wahalarwa haka na kawo ka duniya bayan na sha tsananin wahalar nak’uda! na shayar da kai na tsawon shekaru biyu,kashinka fitsari tumbid’i duk ni mai wankewa mai gyarawa,sai da ka yi watanni shidda a duniya tukunna ka fara baccin dare wanda a ta dalilin hakan ne ya janyomini na kamu da ciwon hawan jini tsabar rashin samun ishashshen bacci. Idan baka da lafiya in kwana a zaune in wuni a zaune cikin damuwa har sai naga ka warke!k’iriniyar k’uruciyarka babu kalar wadda ban gani ba babu wadda ban sha ba amma yau ni ce nake gaya maka abu kana yi mini musu Ina fad’a kana fad’a Yashjub har ta kaimu ga kana iya kallon cikin tsabar idanuna kana cewa ‘ba ni na haifeka ba!!’
Ka san yadda maganar nan ta sanya ni na ji kuwa?
Auren Kausar fa a k’arshe duk kai na ke k’ok’arin yiwa gata amma ka kasa fahimtata!”
Ta k’arashe maganar tata cikin fashewa da wani Irin kuka.”
Duk shiruu suka yi kafin su Yasira su fara rarrashinta..ganin yadda shima ya yi shiru kamar maganganunta sun yi tasiri akansa ne ya sanya ta goge hawayenta tace”tunda ka ce ban yi maka adalci ba ka saurara ka kasa kunne ka ji ga adalci nan zan yi maka…
It’s either ka sake Manubiya itama,ko kuma ka dawo da Kausar!
A cikin biyun nan ka zab’i d’aya ka aiwatar na baka mintuna biyu kawai kacal idan ba ka yi ko d’aya ba mintuna biyun nan suka cika Yashjub Allah ya Isa ban yafe maka ba!”
Runtse idanuwa Yashjub ya yi da mugun k’arfi a take wasu hawaye suka zubo masa.
Ba tare da ya bud’e idanunsa ba ya ce mata”ki yi hak’uri!!na dawo da Kausar.”
Cikin tarar numfashinsa tace”na gode!kuma inaso ka sani Muddin ka sake sakinta b’acin ran da za ka fuskanta sai ya fi na yau wallahi!!!”
Sannan gobe inshaaAllah za ta tare,ba ma buk’atar ka yi sabon gida ballanta ka tafka rashin adalci a nan za ta zauna d’akin ta kusa da na Manubiya idan na ga kamun ludayinka daga nan zan yi deciding idan ware gida za a yi,ko kuma Babba za ku chanja wanda ya fi wannan….”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice su Yasira ma suka mara mata baya..Yasira jiki ba lakka Ya’isha kam abun ba k’aramin dad’i ya yi mata ba.”
Har suka fita bai bud’e idanunsa ba yana nan a yadda yake…..har Manu ta hawo saman bayan ta ga fitar su ta je ta rufe k’ofa,yana nan bai motsa ba.
Yanayin yadda ta gansa kad’ai ta san ba lafiya ba.
Ta dai san ba sakinta ya yi ba dan da tuni su Ya’isha sun nemota a gidan sun yi mata tujara..amma in ba da kyar ba tanada tabbacin Mommy ta saka shi ya maido da Kausar ne.
A hankali cikin tsananin k’arfin hali ta k’arasa ta kamo hannayensa duka biyu ta ja shi…
Bai yi mata musu ba ya bita suka zauna a kan sofa ta yi hugging d’inshi a hankali cikin son kwantar masa da hankali tace”all will be fine,wata rana sai dai labari..ka kwantar da hankalinka…”
Cikin tarar numfashinta yace”Mommy ta saka na mayar da Kausar,cewa tayi idan ban mayar da ita ba za ta tsine min.”
Tunda ya fara magana Manubiya ta fara hawaye..he can feel yadda jikinta yake vibrating k’irjinta yake bugawa shiyasa tashi d’aya wani matsanancin tausayinsu ya lullub’esa.
Manubiya ji take yi kamar za ta mutu..kishi tashin hankali da komai ma duk sun lullub’eta amma kuma ba za ta biyewa son kan ta ta je ta kai Mijin da take masifar kishi da so wuta ba!
Indai har tana son Yashjub da gaske to za ta so su rayu har a Aljannah a tare ba wai ta bashi kwarin guiwar da zai tafi wuta ba,dan haka ta tattaro duk wata jarumta da k’ok’arinta da juriya ta fara magana”Ya Yash duk abunda ka ga Allah ya tsara hakan shine mafi alkhairi,ni kam na hak’ura babu komai zan zauna da kishiyar,dan Allah kar ka sake yin jayayyya da su Mommy ba zan so ka tafi wuta ba….”
Wani irin kuka ne ya taho mata wanda ya katse mata maganar tata ,dama tunda ta fara maganar muryarta ta shiga rawa tana kakkatsewa.
K’ank’ameta Yashjub ya yi k’irjinsa yana wani irin mahaukacin gudu.
Sun jima a haka kafin yace”ki fara had’a kayanki”
Da farko ba ta fahimci inda zancen nasa ya dosa ba sai daga baya,dan haka tace”Ya Yash we can’t just pack up and leave..ko ba komai Kausar matar ka ce akwai hakki…”
Cikin tsananin b’acin rai ya zuba mata jajayen idanunsa yace”idan kika sake cewa Kausar mata ta ce za ki ga b’acin rai na”.
Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa wanda hakan ya sanya ya ruk’o hannunta duka biyu yace”Mannubiya we deserve to be happy!
Annabi Muhammad sallahu alaihiwasallam da kansa a lokacin da aka nuna ba a sonshi Hijara ya yi daga Mecca ya koma Madina!.
Ki duba fa kiga Yassir is after my life..Mommy tana so ta had’a ni dole in yi zaman aure da dadiron brother d’ina sannan sisters d’ina suma bangama yarda masoya na bane ba.
Ki gaya mini abu guda d’aya reason kwaya d’aya tak da zai sanya in ci gaba da zama a cikin mutanen nan,sun nuna ba sa so na ba sa sonki so kike yi mu cika gaba da zama a haka har sai bak’in ciki ya kashe mu???”
“Cikin kuka sosai kamar ranta zai fita tace”Rayuwarmu a nan take,bani da dream d’in zuwa k’asar wasu in yi rayuwa..a nan muka had’u da kai ba ni da burin da ya wuce in rayu a nan in tsufa a nan..”
A hankali ya yi cupping face d’inta a cikin palm d’insa duka biyu yace”Mannubiya idan akwai lokacin da nake buk’atar support d’inki to yau ne dan Allah dan Annabi kar ki yi mini turjiya.
Ba na buk’atar musu ko wani sabon Abu negative, na cika dayawa! level na tolerance d’ina ya kai k’arshe….please ko me nace kawai ki ce mini ‘to’dan Allah”
Ya fad’i hakan hawaye suna masu zubo masa.
Wani irin kuka ta sake fashewa da shi ta rungumesa ta na mai jinjina kanta alamun ‘to’.
……..
Najeeb Yashjub ya kira yace msa “dan Allah ya zo yana da buk’atar ganinsa”.Daga nan ya fara nema musu flight d’in Abuja kafin ya yi musu arrangin barin k’asar gaba d’aya.
…
Komai na company d’insa na nan Nigeria ya d’aura Najeeb d’in a kai yace masa”zai yi tafiya na tsawon wani lokacin ya rik’e masa amana.”
Najeeb bai yi niyyar yi masa maganar ba dan kunya da tausayinsa yake ji amma kuma sai ya ga bai kamata ya b’oye masa cewa ya sani ba, dan haka cikin tsananin jin tausayin Abokin nasa ya dafa kafad’arsa yace”ba a kan ka aka fara ba!komai ya yi zafi maganin sa Allah.”
D’an k’ura masa Ido Yash ya yi kafin ya d’auke kai ya fesar da iska yace”kai ma sun tura maka kenan!”
Jinjina kai Najeeb ya yi yace”a tare suka tura mana!
Na san ba za ka so ka zamo wanda zai fallasa a kashe Yassir ba shiyasa na yi shiru ban yi maka maganar ba kawai! haka suma masu bincike ban ce musu mun gano komai ba amma dai na ari bakinka na ce musu mun zare hannunmu a bikincen sai dai kuma family’s d’in victims d’in Estate d’in naka gaskiya sun kunno wuta dan bincike sosai suke yi cewa ma ya yi ko mu mun janye yanzu haka sama da mutane ashirin ne tsaye tsayin daka a kan case d’in.”
A hankali Yashjub ya sunkuyar da kansa k’asa ya yi shiruu kafin ya d’ago ya ja hanci yace”kar ka gaya wa kowa inda nake dan Allah…ba wai iyaka Yassir ne dalilin da ya sanya zan tafi ba”
Sai da ya yi shiru ya sake jan hanci tukunna yace”Yau su Daddy suka aura min Kausar….”
Dalla Dalla ya gayawa Najeeb bayanin komai da dalilinsa na k’in zama da Kausar…tashi d’aya Najeeb d’in ya yi supporting d’insa d’ari bisa d’ari.
Sai asubah tukunna suka gama shiryawa da had’a kan komai..
Kamar kar su rabu Najeeb har da hawayensa dan mugun mugun tausayin Yashjub yakeji hakanan suka yi sallama daga haka driver ya d’auke su zuwa hotel bayan Yash ya damk’awa Najeeb makullan gidan yace da safe ya kaiwa su Mommy dan tace za su kawo Kausar.Dalilin ma da ya sanya ya k’i amincewa su zauna a cikin gidan kenan,gudun kar su ce za su kawo masa ita da safe.
Sai washegari da safe tukunna Ummi ta samu courage d’in confronting Hajiya Mama…har ga Allah Hajiya Mama ta yi tunanin Ummi wasa take yi mata da farko dan kwata kwata ba ta tab’a yin tunanin su Daddy za su tafka wannan kwab’etar ba!that too ba tare da sun shawarceta ba.
Sai da ta saka Ummi ta rantse mata tukunna ta yarda,Hankalinta a mugun tashe ranta a masifar b’ace ta kalli Ummin da ta fara dibi dibin bata Baki tace”ke kanki kinsan babu ta inda za ki ce mini hakan ya dace ko?”
Shiruu Ummi ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa.
Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”to ki yi shiruu kawai kar ma ki bawa kanki wahala.”
“Ina shi Yashjub d’in yake ya sani??a gaban sa shima aka d’aura??”
A hankali Ummi tace”a’a..na dai kira na gaya masa nace ya zo a san abunyi, to dai tun jiyan bai zo ba yau kuma inata kiran wayarsa daga shi har Manubiyan ba ya tafiya.”
Jinjina kai Hajiya Mama ta yi,fuskarta har ta yi jaaa!
Ta kalli Ummi tace”ki kirawomin su Imam d’in ki ce na ce su zo yanzunnan!”
“Tam”Ummi tace daga haka ta mik’e ta sa kai ta fice.
Ba’a yi mintuna goma ba,Daddy ya shigo da shirin tafiya office Abhi kuma da jallabiya.
Ko gaisuwar su ba ta amsa ba ta kalli Daddy tace”ashe har kana iya tafiya office bayan masifar da ka k’ulla a gidanka jiya??”
A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”ki yi hkr Hajiya Mama da ma yanzu nake shirin shigowa mu tattauna kafin in wuce!”
Cikin fushi tace”Imam tattaunawa kuma ta nawa?
Sai da ka gama yanke decision da kai da munafuka!muguwa!!makirar matarka!!!!tukunna za ka zo ka ce mini za mu tattauna saboda ka raina ni??
Me za mu tattauna???
Ina sauraronka gaya mini menene ya rage wanda ba ka riga ka yanke hukunci ba?”
Shiruu ya yi ya gagara cewa komai.
Cikin tsananin b’acin rai ta kallesu su duka biyun tace”da ni da ku duk mun shirya a kan za a sakawa Khadija ido a bincike ta a gano ta a nunawa Yaranta illarta da illar d’abiar da ta d’aurasu a kai tukunna a sallameta a cikin gidan nan,amma saboda tsabar ku d’in ba jajurtattun maza bane ba a cikin awannin da basu wuce biyu ba Yarinya y’ar k’arama Kausar da Khadija sun juya muku tunani kun aurawa Kausar Yashjub!!!
Daga ta yi y’ar drama da shirmenta shikenan har kun kamu??”
Da kyar Abhi ya iya cewa”Hajiya mama cewa ta yi za ta tafi da Yaron shi kuma Yashjub ko
Maganar mu ba ya ji iyaka maganar Manubiya ya ke bi da farincikin ta..a jiyan fa cewa ya yi wai sai abunda ta yanke tukunna za a yi”
Sakar Baki kawai Hajiya mama ta yi ta na kallonsa har ya dasa aya tama kasa cewa komai.
Da kyar ta iya cewa”idan na fahimce ka, kishi kenan kuke yi da Manubiya kamar wasu mataa!!!shiysa kuka aura masa Kausar saboda kar Manubiya ta yi dominating d’insa ita kad’ai ko?”
“This is the dumbest thing da na tab’a ji tunda uwata ta kawo
ni duniya wallahi tallahi!
Ina tunaninku ya tafi ina hankalinku ya tafi??
Kausar faaa!!”
Cikin son yi mata bayani Daddy yace”ai Kausar d’in ba fa wai mun aura masa ita forever bane mun aura masa ita ne akan idan ta haihu sai su rabu”.
Mik’ewa kawai Hajiya mama ta yi ta nufi wajen kayanta ta fara fito dasu tana cewa”Bari
Ka ji in gaya maka,Indai Kausar ce to ba za ta tab’a rabuwa
da Yashjub ba ba za ta yarda ba!
Barr ganin wai da Yassir kuka santa,a yadda Khadija ta tsani Manubiya ba za ta bari Kausar ta bar Yashjub ba,
A tunani na auren ka da Khadija ya isheka ishara ya Isa ka gane idan aka auresa ba sa fita tunda tun yaushe kake so ka saki Khadija ta saku???”
Ta yiwa Daddy wanda ya matso ya rik’e trollyn hannunta tambayar.
Ba ta jira jin amsar shi ba tace”kuma saboda ku wawaye ne kuke tunanin Kausar za ta yarda a saketa?
Wai ma shin ina lissafin ku ya tafi da Kausar d’in tace za ta tafi kuka biye mata kuka yarda??
Khadija fa kad’ai sai Larai gareta a kaff fad’in duniyar nan,Wallahi ko ta tafi k’ark’ari ta yi wata biyu zuwa uku nasan ita da kanta