Showing 27001 words to 30000 words out of 244445 words
ga Allah gaba d’aya Yash ya sa ta fara jin wani iri dan gaskiya ita dai hidimar ta yi yawa..tana fara masa godiya kuwa ya chanza topic d’in dan dama yace mata ta daina yi masa godiya ba ya so!ba k’aramin dariya ya bata ba da ta ji yace’’ta je aiki,ta na da report’’
da farko ta d’auka da wasa yake yi sai da taga ya dage tukunna ta tabbatar da gaske yake yi.
Aikuwa sai da ta yi da gaske tace’’ga skul da za su koma soon dan ba’a ba su wani hutu mai tsayi ba ga kuma hidimar biki dan Allah ya yi hak’uri ya bari ta tura masa kawai’’
tukunna da kyar ta samu ta shawo kansa ta lallab’asa ya d’aga mata k’afa amman da cewa ya yi sai ta je.
Daga nan ta ji ya yi shiruu kamar mai tunanin wani abun dan haka ta shiga tambayar sa menene,sai da k’irjin ta ya buga da ta ji yace‘’Abbakar ya tab’a cewa yana son ki ne??’’
Sai da ya sake cewa’’umm???’’
Tukunna da iyaka gaskiyarta tace’’A’a”
Numfashi ya fesar kafin yace’’can I ask you a favor???”
Ahankali ta samu da kyar tace’’sure!anything’’saboda yadda ta ji tashi d’aya muryarshi ta chanja sannan ranshi ya b’aci.
Cikin katse mata tunani ta ji
yace’’ko gaisawa ba na so ki sake yi da shi”
Sai da ya sake cewa”am I asking for too much?”tukunna ahankali tace”A’a”sai kuma tace”ba ma ya yi min magana fa,ya daina kulani”cikin tarar numfashinta yace”saboda kishi ne ai yasa ya daina yi miki magana saboda ya ji an fara maganar aurenmu yanzu kuma ya ga za’a koma skul shine ya je ya karb’i transfer,yanzunnan Najeeb yake gayamin ya samu transfer,bakiga kalar wahala da kud’in da ya kashe ba amman haka ya bi a gaggauce ya yi transfer”
Shiruuu Manubiya ta yi tana jin wani takaicin Abbakar yana taso mata a tunaninta da kuma ganinta sam alk’awari bai ce haka ba wato
ma gudun ta yake,a ranta tace”idan ma wani abun na yi mishi ai kamata ya yi ya neme ni da zancen mu sasanta bawai ya yi irin wannan abu haka ba’’ dan ita kwata kwata ba ta yarda da maganar Yash da ya ce “saboda kishi ne ya sanya shi ya yi transfer ba….”
Cikin son kawar da zancen Abbakar d’in Manubiya ta sako wata hirar dan ya b’ata mata rai ba kad’an ba,da
kyar kuwa ta samu mood d’in Yash ya chanja har yake bata labarin “ai Najeeb ma ya samu wani zazzafan appointment zai bar skul d’in”,ta kuwa yi murna sosai dan ko ba komai sir Najeeb ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta…..
Sai da Manu ta tabbatar Yash ya huce sosai tukunna suka yiwa juna sallama,kamar za su cinye juna don so haka nan su ka yi sallama ko wannen su cikin tsananin so da shauk’in d’an uwansa.
Tana gamawa su Siyama suka tisa ta a gaba da tsokana abun mamaki har da Muhsin,ita sai a lokacin ma ta fara data sanin yin wayar a gaban su.
Sai da Baba ya zo ta nuna mishi komai ya sanya albarka bayan ya gama fad’an hidimar ta yi yawa tukunna suka b’are wayar aka jonata a chargi
Dan jidda tace”tayi maza ta kwashe important abubuwa ta cire layinta a tshohuwar wayar ta bata dan ta ma riga ta zama tata……
Har k’ofar side d’in su Siyama suka rakata dan lokacin da ta zo tafiya dare yayi sosai,tukunna suka koma nasu d’akin..
Yashjub yana gama waya da Manu dai dai ya shiga bedroom d’inshi kenan kiran Daddy ya shigo wayarsa,yana d’auka ya ji muryar Daddy yana cewa”ka zo parlour na,Hajiya Maama na son magana da kai”
Yadda Yashjub ya ji murya Daddy dama sai da gabansa ya yanke ya fad’i shiyasa ko wanka ya gagara yi tashi d’aya ya juya ya nufi side d’in Daddyn yana jin yadda k’irjinsa ya ke bugawa akai akai.
A zaune ya same ta ita da Daddy da Ummi da mom da Abhi.
Sai da ya gaishesu one by one suka amsa tukunna ya nemi guri ya zauna.
Yana zama Hajiya Mama ta yi gyaran murya tukunna cikin lallashi tace”Yash! da ni da iyayenka gasunan mun yanke shawarar za’a d’aga bikinka za’a k’ara wata uku a kai sakamokon matsalar gocewar k’ashi da ka samu kar ka yi gaggawa ka bi komai a hankali a je a samu a duba ka sosai dan a gaskiya ban gama yarda da gyaran da suka yi maka a nan ba,ka yi hak’uri ka bari a d’aga bikin,lafiyar ka ta fi komai ka warke garau tukunna sai a yi komai cikin nutsuwa da kwanciyan hankali ka ji d’an albarka”
Hajiya Mama ta k’arashe maganar cikin tsananin lallami.
Tunda ta fara magana idanun Yash suka cicciko da hawaye.
Kamar wani d’an Yaro haka ya d’aga kai ya kalli Abhi da Daddy Irin ‘ku sa baki mana’ d’innan,ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace‘’Yash it’s for your own good in banda kai da abunka ina kai ina yin aure a haka saboda Allah fa,tunda har mukazo aka yi tambaya aka yi komai aka baka yarinyar nan a ganina dan an k’ara wata uku ba komai bane kamar yau ne,ka yi hak’uri ka bi Junior da mom d’inku ku je a duba maka hannun sosai ka warke garau! In yaso sai ayi auren I promise you zan tsaya maka ka auri Manubiya under any circumstances,Ina nan har 3 months da ni da Hajiya Mama inshaaAllah sai an yi auren an kai maka amaryarka tukunna za mu koma.
Cikin bashi assurance Daddy da Hajiya Mama ma suka mishi alk’awarin duk rintsi inshaaAllah zasu tsaya masa ya auri Manu haka ma su Ummi.
Zuwa yanzu Yash har wani dishi dishi yake gani tsabar tsaka mai wuyar da ya shiga manya sun sakashi a tsakiya suna so a d’aga for his own good sannan sun yi masa alk’awarin tsaya masa duk rintsi a yi auren,on the other hand kuma gani yakeyi kamar idan aka d’aga wani abun ka iya faruwa infact kwata kwata baya k’aunar abunda zai janyo a d’aga auren nan.
Ahankali Hajiya Mama tace’’ka yi hak’uri ka kwantar da hankalinka ka samu lafiya tukunna fiancé d’inka tananan tana jiranka babu inda za ta je kana dawowa za’ayi auren ka ji ko?”
Cikin son jin amsar da za ta fito
daga bakinsa Abhi yace”kai muke jira Yash,a matsayinmu na iyayenka ga abunda muka ga ya dace,na yi magana da friend d’ina already, za a yi
maka booking appointment so ya kamata ku tafi soon a je a dubaka da wuri,ko?’’
Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa da kyar muryarsa har wani karkarwa take yace”…….”MANNUBIYA
(Book 2)
Page 1 1
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa da kyar muryarsa har wani karkarwa take yace”duk yadda kuka ce Abhi Allah ya sa hakanne ya fi alkhairi.”
Ba k’aramin dad’i suka ji ba kuwa dan haka suka shiga saka masa albarka tare da fatan alkhairi.
Ganin yana shirin fashewa da kuka a gabansu ne yasanya ya mik’e har wani jiri jiri yake ji yace musu”sai da safe”daga haka ya sa kai ya fice yana mai ji kamar ya kurma uban ihu,so yake ma ya yi kuka amma sam ya kasa,shiyasa ya nufi side d’insa ya na zuwa ya shige d’aki ko bi ta kan Junior bai yi ba ya shiga ya rufe kanshi ya kashe wayoyinsa…….
Sai washegari da safe tukunna Manubiya ta ji labari,duk yadda take ta cewa itadai 2weeks ya yi kad’an a d’aga amman sai ta ji ba dad’i musamman ma da Yash ya kira ta ta ji kamar kuka ma yake shirin yi mata…gaba d’aya sai ta sake gigicewa.
Suna kashe wayar itama ta nemi fashewa da kuka sai da Jidda ta d’an kwantar mata da hankali ta had’a da tsokanarta tana cewa”au dan an d’aga aurenta shine za ta yi kuka?”
Tukunna ta wayance ta fake da borin kunya.
Dukda su Mommy sun ji kuma sun san d’agawa kawai aka yi ba wai fasawa gaba d’aya ba amman hakan bai hanasu shiga cikin tsananin farin ciki ba ji suke yi kamar su zuba ruwa a k’asa su sha dan Baba Larai tace’’d’agawan da aka yi hakan ma nasara ne,kuma za su samu enough time d’in da za su tarwatsa maganar inshaaAllah,dan wata uku is more than enough for them su yi abunda ya dace,”Shiyasa murna a wajen su har kasa b’oyuwa ta yi tun daga kan Baba Larai har izuwa kan Yadira kowannen su in ka kalla tashi d’aya za ka san yana cikin tsananin farin ciki wanda hakan ba k’aramin sake ingiza Hajiya mama ya yi ba dan tabbas ta sake tabbatar da cewa ‘dukkansu ba son auren suke yi ba.’
A b’angaren su Manubiya kuma kaka mallan ne yaketa b’ab’atun sa shi kad’ai duk inda ya zauna ya tashi sai ya sanar ai an fasa auren Manubiya a cewarsa ‘’babu wani d’agawa da akayi Yaron ne ya fasa saboda ya gama lalubeta dan kusan kullum sai ya zo ya d’auketa sun fita kuma basa dawowa sai dare…tun mutanen layi basa biyeshi har aka fara k’usk’us dan in ya zauna har rantsuwa yake yi yana cewa”Yaron nan fa ba zai auri Manu ba tunda ta kasa rik’e kanta ta bi kud’i ta bashi abunda dama ya kawo sa wajenta,dan wallahi akwai ranar da a gaban idanunsa suka dawo da daddare har da Muhsin amman sai aka cewa Muhsin d’in ya fita shi da driver su kuma suka zauna a bayan mota wallahi wallahi sun fi awa uku a cikin motar har motsi yaga motar tanayi,shikam daga k’arshe ma hak’ura ya yi ya shige ciki bai san lokacin da suka gama ta shigo gida ba.”
Duk wannan gulmace gulmace da gutsiri tsoman da yake yi hakan ba ta ishe sa ba sai da ya sa aka kira masa Ya Musbah takanas yace masa”ai ga irinta nan,ranar a masallaci sune har da yi masa rashin mutunci saboda yaga y’ar uwarsa ta shiga daula to ga irinta nan ai tun kafin a je koina saboda abunda suka yi masa gashi an fasa auren,waye waye..”
Hakanan dai ya yi ta b’ab’atun sa,uffan!ya Musbah bai ce da shi ba har ya yi ya gama,sai da ya dasa aya tukunna ya mik’e yace”Allah bamu alkhairi”daga haka ya sa kai ya fice.
Sati d’aya da d’aga bikin Yashjub ya zo yi mata sallama.a cikin sati d’ayan nan zazzab’i sosai yake yi shiyasa ko iya fita ma bayayi balle ya je wajenta sai dai kullum suna waya.
Ko da ya zo a waje ya tsaya ta fito,tashi d’aya hankalinta ya yi tsananin tashi dan ba kad’an ba ya rame sosai ashe shiyasa
kullum take jin muryarsa wani iri idan kuma ta tambayesa sai yace mata”ba komai.”
Cikin tsananin mutuwar jiki ta k’arasa ta gaida shi da kyar ya iya amsawa har da d’an k’ak’alo murmushi duk dan kar ta gane.
Cikin rashin jin dad’i tace”ba ka da lafiya ne?”
Murmushi ya yi kafin ya girgiza mata kai kawai,ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”gobe da asuba za mu tafi,”
Sai
Da ya sake fesar da numfashi tukunna ya gyara tsayuwarsa sannan yace”ni kam har ga Allah na fara da na sanin amince musu da na yi,kawai inaga gara a d’aura mu wuce tare,na so in same su da maganar amman sai na ga gara in fara yi miki maganar in ji ta bakinki,but still dan Allah baby kar kice A’a kawai kema ki amince a d’aura a yau dan hakan nake so”
Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.
Da kyar Manu ta iya danne kukan da ya taho mata ta d’ago idanunta da suka cika taff da kwallah tace”na san ba za ka ji dad’in abinda zan fad’a maka ba amma hakan shine daidai….ana barin halak ko dan kunya,kai fa da kanka ka ce min kawaici da alkunya ne suka sanya ka amince da buk’atar su,yanzu kuma kawai sai ka zubar ka je ka samesu ka ce ka chanja shawara?
Kuma kowa gani zai yi saboda ka zo ka yi magana da ni ne”
Cikin sanyin murya yace”baby gani nake yi kamar idan aka d’aga wani abun zai iya…”
Cikin katsesa tace”duk abunda ka ga ya faru to muk’addari ne daga Ubangiji,wayonmu ko saurin mu bai Isa ya k’ara ko ya rage lokacin da ubangiji ya riga ya tsara za’ayi ba….dan Allah inaso kamar yadda ka ji kunyar su ka yi kawaici a farko to yanzun ma ka zauna akan bakarka ka yi musu biyayya baka san dad’in da hakan zai sanya su ji ba, amman yanzu idan ka bijire kowa rashin hak’uri da karar mu zai gani,kuma hakan ne. Dan haka gara kawai mu yi musu biyayya mu yi hak’uri mu mik’awa ubangiji komai inshaaAllah za mu dace”
Ganin yadda ya yi shiruu ya kasa cewa komai sannan idanunsa suka yi jajir yasanya manubiya ta kawar da kunya direct daga cikin zuciyarta tace masa”inshaaAllah i’ll forever be yours,no matter what”
Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya dan ba kad’an ba kalamanta sun yi tasiri a kansa.
Cikin tsareta da lumsassun idanunsa da suka k’ank’ance suka yi jaa yace”promise??”
Ahankali tace”I promise”
Lumshe idanunsa ya yi wanda hakan ya bawa kwallar da yake ta k’ok’arin rik’ewa damar zubowa, da sauri Manubiya ta kauda kanta ta sunkuyar k’asa dan tashi d’aya itama taji tata kwallar tana shirin zubowa.
Ahankali ya share idanunsa ya d’an ja hanci kafin yace”3 weeks zan yi in dawo na san kuma zan koma follow up kamar sau biyu haka kafin auren namu”
Cikin yin k’asa da murya yace”I’m going to miss you so much,take care of yourself ki dinga rik’e wayarki always pls”
Ahankali ta d’ago ta kallesa tace “inshaaAllah”
Cikin wata kalar kasalalliyar murya ta ji yace”I love you,always and forever”
Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa duk yadda ta so ci gaba da rik’e kwallar kasawa ta yi da n tashi d’aya suka zubo mata, gudun kar ya gane yasanya ta sa hannu ta goge a hankali tukunna itama tace”I love you too”
Murmushi ya yi daga haka yace”see you in 3 weeks time”
Ahankali ta d’ago ta ce”bye”
Waving nata ya yi shima yace”bye”
Daganan ta yi sauri ta juya ta shige cikin gidan dan tabbas Idan ta ci gaba da tsayawa a gabansa tou za ta yi kukan ne mai yawa ba d’an kad’an ba.
Ai kuwa tana shiga ta zauna a d’an dakalin hanyar d’akin su ta saki kukan ta, ta yi k’ok’ari ta kwantar wa da Yash hankali bayan ta san tabbas ta fisa shiga damuwa dauriya ce kawai take yi…ta jima ta na kuka mara sauti mai cin rai kafin da ga bisani ta goge fuskarta ta tashi ta shige cikin d’akin,a da ba ta ganin nisan watanni dan nan da nan indai aka saka rana sai ta ga lokaci har ya yi,amman tabbas a yanzu watannin ukunnan da aka k’ara jin su take yi kamar shekaru d’ari uku…..
Bayan wata uku.
Kwanci tashi…..yau gashi har wata ukun da aka k’ara a kan bikin su Manubiya ya cika cif cif….wasu suna cikin tsananin murna wasu kuma suna bak’in ciki yayinda waensu suka ji kunya….Cikin nasara Yash ya je aka duba masa hannusa aka yi masa duk wasu abun da ya kamata,kafin wata biyu ya ware sosai shiyasa a lokacin Hajiya mama tace ko za’a d’aura kawai amman sai su Daddy suka ce kar ma ta bari yaji kawai a jira dan dai wata d’aya da kwana 7 ai kamar yau ne….yadda auren ya sake taho wa su Mommy suka fara d’aga hankalinsu sai da kowa a cikin gidan ya lura,shiyasa Hajiya mama da dage ta tsaya tsayin daka a kan al’amuran gidan dan matar nan da ta kira ta yi musu feshi kwanakin baya yanzu kusan kullum sai ta zo haka aka dage da addu’o’i a cikin gidan ba kama hannun Yaro. Idan kuwa anayi Baba Larai ji take kamar ta mutu dan har ga Allah ba k’adan ba Hajiya mama take b’ata mata aiki gashi ta kasa korar ta a gidan.
Kamar yadda Yash ya fad’a sau biyu ya je follow up a UK..a yau ya gama da ganin likita shiyasa suka tarkota har da mom suka nufo Nigeria.
Suna zuwa aka shiga murna da oyoyo Hajiya Mama tana ta tsokanar Yash tana cewa”ba ga shi lokaci har ya yi ba,amman da har da kwallar sa da aka ce za’a d’aga auren,Itafa gaskiya tana kishin wannan kishiyar tata tun kafin ta zo dan yadda yake wannan rawar k’afar ta san tana zuwa zai manta da ita”
Dariya duk akayi banda Mommy wadda take jin kamar zata mutu,cikin tafiyar tsofaffi Hajiya Mama ta nufi kitchen..yau dan rigima da kanta ta dafawa Yash jalof d’in taliya dan ta san yanaso ba yadda Ummi ba ta yi da ita akan ta kawo ta yi ba amma tace “ta yanka mata albasa kawai”(shima saboda matsalar idon ta ne)
daganan ta girka abunta tsaf kuma ya yi dad’i sosai.
Mom da Ummi ne suka bi bayan Hajiya Mama yayinda Daddy da Abhi suka nufi waje dan suna da wajen zuwa,junior kuma ya bi bayan Yadira da ya ga ta nufi garden alamun waya take yi.
Yash yana zaune yana murmushi ya ji kawai an damk’i hannunsa yana d’agowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya kawai yana kallonta…dan tun d’azu da ya shigo bayan ya je sun gaisa ko ‘ya hanya’ ba ta ce masa ba,kamar ma fushi ta ke yi da zuwan na sa,kuma a cikin watanni ukun nan ya lura kamar ma gudun sa take yi dan idan ya je k’ofar ta kullum a kulle. Yana cikin wannan tunanin ya ji tace “biyo ni,Inada magana da kai”
Daga haka ta juya ta nufi parlourn bak’i.
Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya mik’e ya bi bayanta,yana wucewa su Yasira da Baaba larai suka yi sama dan kar ma a zo a tambayesu yana ina.
Yash ba k’aramin shock ya shiga ba dan yana shiga parlourn Mommy ta rufesa da fad’a kamar za ta had’iyi harshe abunda ba ta tab’a kwatantawa ba kenan,babu abunda ya fi b’atawa Yash rai kamar akan abunda take yin fad’an,in da ma wani abunne ya faru recently har ta kai ta ga