Showing 219001 words to 222000 words out of 244445 words

Chapter 74 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16490

condition d’inta.

A tunanin Kausar Daddy zai koreta itama amma ko kallonta bai yi ba hakanan ya wuce ta ya fita wajen y’an sandan da suka k’araso yanzun domin ya sallamesu a ransa ya gama tsara’itama zai koreta ne but sai ta haihu tukunna bayan sun karb’i d’an sun bawa Manubiya….’

Yashjub tun d’azu yake ta jin k’arar bud’e gate ana rufewa shiyasa hankalinsa ya sake tashi dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi Allah dai ya sa ba harda Mommy aka bar gidan ba.
……
Duk yadda suka yi tunanin abun zai yiu a gida gagara ya yi dan bayan sun kai kayyakinsu,abun ya ci tura,sai da suka dangana Mommy da asibiti tukunna ta farfad’o da kyar.!
Ai kuwa tana tari tana hawaye hankali a tashe kamar tab’abb’iya ta shiga tambayarsu “ya ake ciki?a ina take?”
Ya’isha ce ta iya yi mata bayani Aikuwa cikin masifa da tashin hankali ta rufe su ta fad’a tace “dan meyaasa suka yarda suka fitar da ita daga cikin gidan??..”
Sai kuma ta fashe da kuka ta fara jero Allah ya isa a Hajiya Mama da Manubiya dan sam batajin haushin Daddy kamar yadda takejin masifaffiyar tsanarsu a cikin ranta!
Hatta su Yasira ma sai da ta dasa musu matsananciyar tsanar su Abhi da Hajiya mama a cikin ransu bayan ta Manubiya da suke zaune daram a kai.

Duk yadda suka so su lallashi Mommy sam abun ya gagara gashi dama suma a wuya suke shiyasa kawai suka fashe mata da kuka…ba ta damu da kukansu ba ballanta ta sarara musu magana kawai take yi kamar tab’abb’iya kuma ta nace akan Itafa sai sun d’auketa sun mayar gidan Daddy dan Kwata Kwata jikinta babu kwari itan so so ta kasa tashi da kanta,shiyasa kawai Yassir ya juya ya fita ya je ya kira likita yana zuwa ya yi mata allurar bacci da kyar dan sai da su Yassir d’in suka danneta tukunna aka samu aka yi sam ta k’i tsayawa.

Sosai Yassir yake jin tsanar Yashjub yana dad’a shigarsa ga tsoro ga tashin hankali…
Suma su Yasira sun ji haushin rashin zuwan Yashjub d’in asibiti ya ga Mommy matuk’a.

Sai chan dare tukunna Mommy ta farka…tashi d’aya komai ya dawo mata sabo wanda hakan ya sanya ta ji inama ba ta farka ba.
One by one ta fara kallonsu tashin hankalin ta yana sake hauhawa sakamokon yadda ta ga fuskokinsu sharkaff da hawaye dagaje dagaje kowa ta yi tagumi Yassir da Yassira kuma basa nan.
A d’an rikice ta tashi ta zauna ta kallesu tace “Ya’isha mai kuma ya faru??”

Sai a lokacin ma suka lura ashe ta farka dan haka daga Ya’ishan har Yusra haka nan suka nufeta da sauri suka fad’a jikinta suka fashe da wani irin kuka.

Zuwa yanzu jikin Mommy har wani irin karkarwa yake yi!
A hankali ta zaro su daga jikinta k’irjinta yana dukan tara tara tace”ku fad’a mini menene kafin zuciyata ta buga”
Sai da ta sake tambayar su!ta maimaita!!ta daka musu tsawa a karo na uku tukunna da kyar Yusra ta bud’e wayarta ta kai mata hoton ta mik’a mata tana wani irin kuka.
A hankali jiki na karkarwa Mommy ta saka hannu ta karb’a hoton…………..Babu idanuwa sannan an yanke nonuwa da private part da y’an yatsun k’afa da hannu amma hakan bai hanata gane Larai tashi d’aya ba.
Jifa ta yi da wayar a mugun tsorace sai kuma ta turesu ta mik’e ta d’aura Hannu a ka ta fasa wata razananniyar k’ara.

Dai dai nan Yassir da Yasira suka shigo da sauri suka k’araso suka rik’eta Yasira itama cikin kuka tace”addu’a za ki yi mata Mommy dan Allah ki yi salati ki daina ihu…”
Sai a lokacin Mommy ta shiga ambaton innalillahi wa inna ilaihirrajiun ba k’akk’autawa a gigice tana wani irin kuka jikinta yana karkarwa.

Shiruu duk suka yi suna kuka kafin Ya’isha tace”an baku ita?”
Jinjina kai Yassir ya yi yace”Tana mortuary sun yi saurin saka ta a k’ank’arar saboda ta kumbura gawar ta fara wari!zuwa gobe da safe inshaaAllah sai a yi mata wanka a binne ta!”

Wani irin kuka mai k’arfin gaske Mommy ta fashe da shi
Haka suma su Ya’isha,babu mai rararahin wani kowa kawai kuka yake yi gaba d’aya d’akin ya birkice dan ko kusa da d’akin ka zo a wannan dare sai ka fahimci an yi musu rasuwa.
A tsaye ranar suka kwana babu wanda ya runtsa.
Washegari da sassafe suka nemi sallama aka sallami Mommyn daga nan suka d’auki Larai suka wuce da ita gida domin su yi mata wanka a mik’ata gidanta na gaskiya!!!.


Kamar yadda su Yasira suka ci karo da labarin gidan tsafin da jami’an tsaro suka binciko a garin kano tare da hotunan victims d’in ta watsapp hakanan yau suma su Daddy suka gani har da Kausar…Hankalinsu ba k’aramin tashi ya yi ba..Yashjub ma yana idar da sallar asubah ya gani..
Daddy ya so ya hanashi zuwa inda suke amma kawai sai ya rabu da shi ya tafi Hajiya Mama kuma ta kira Yusra da Yasira ta yi musu gaisuwa tace ta mik’a gaisuwarta zuwa ga su Ya’isha.

Motocin su Yasira suna gama yinparking a k’ofar gidan Momy wanda ke a tudun yola dai dai nan Yash ma yana k’arasowa kamar had’in baki, da ma ya san nan d’in suka nufa.

Mommy tana hangosa ta fito a fusace ko ya kan su Yasira da suke ce mata “ta tsaya su shiga ciki tukunna sai a yi” ba ta bi ba hakanan ta nufi Yashjub tana zuwa ba ta yi wata wata ba ta zabga masa wani Irin rikitaccen mari……….

Da mamaki ya dafe wajen yana kallonta kawai ya ma kasa magana.
Ita kanta sai da ta mareshin ta d’an ji sanyi a cikin ranta tukunna ta ta yi tunanin considering the fact that Yassir fa da kashe sa ya so yi bai kamata ace ta maresa ba,dan haka tace”tsabar kai dak’ik’i ne Yashjub ace a had’a video da voice d’in d’an uwanka amma ka gagara gane k’arya ne aka shirga?ina karatunkka da ilimin ka suke?sannan ka tartaro mini su Hajiya mama ka sako su cikin case d’in nan saboda baka san ciwon kanka ba?”
Ba ta jira jin ta bakinsa ba ta d’aura da cewa
“To bari ka ji ba ni ka wulak’antaba wallahi kanka ka wulak’anta kuma inaso ka sani wallahi tallahi muddin baka je ka wanke d’an uwanka ka shiryasa da mahaifinka ka gyara abunda ka lalata ba ni da kai har abada!!
Ka b’ace mini daga gani duk ranar daka gyara b’arnar da ka yi sai ka zo gareni!”
Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta wuce ciki ta shiga ta gate d’in da su Yasira suka bud’e suke ta k’ok’arin shiga da motocin.

Har suka gama shigewa Yash yana nan yadda yake ya ma kasa motsi..”shin da gaske Mommy ta yi believing sharri aka yiwa Yassir kokodai son Yassir ne ya sanya ta yi masa wannan borin??”
Ya yiwa kansa tambayar a cikin ransa, Saboda ya tabbatar ko k’aramin Yaro idan ya ga video d’innan da voice da shaidu ya san ba had’awa aka yi ba.

Juyawa kawai ya yi ya shige cikin motarsa ya kunna ya wuce,yana tafiya ya turawa Yasira mesaage ya yi mata gaisuwar rashin da suka yi,dan Mommy tana shiga ya ga ta fito za ta zo wajensa shi kuma ba zai iya sake ci gaba da tsayuwa a k’ofar gidan ba zuciyar sa za ta iya tarwatsewa
..Tabbas Mommy ta tsaneshi!!!


Sai da Yasira ta bari Yassir da su Yusra sun shige ciki tukunna ta yi saurin ruk’o hannun Mommy k’asa k’asa tace”Mommy videos d’innan da gaske ne fa!!Yassir da kansa jiya ya yi mini confessing…….da kin sani ba ki yiwa Ya Yash haka ba gaskiya,jiya dai na ji haushinsa da bai zo ya ganki ba amma yau ai da mun tsaya mun sauraresa tunda ya zo.”

Shiruuuu ta ga Mommyn ta yi..ba ta da wani choice da ya wuce ta tubure kawai tace sharri aka yiwa Yassir dan haka ta cewa Yasirar ‘
rikicewa Yassir ya yi jiya shiyasa yace mata shine amma tabbas sharri aka yi masa……’
Rabuwa da ita kawai Yasira ta yi ta bari akan sai an kai Baba Larai zafin mutuwar da komai ma ya fara raguwa r mata tukunna sai su yi magana da ita ta fahimtar juna.
….
Gaba d’ayansu kashe wayoyinsu suka yi saboda Mommy tace ba ta son y’an gaisuwa su san tana nan bama ta buk’atar ganin kowa a halin yanzu…da kyar da mugun kyar suka samo matan da suka yarda suka yiwa Baba larai wanka dan a k’ank’arar da aka sakata jiya ya sanya yanzu kuma duk sai ta lagwab’e da k’ank’arar ta narke dan ko jikin nata kana tab’awa sai ka ji kamar zai biyoka ga uban wari!
Suma Matan dai daga k’arshen wankan kawai ruwa suka yayyafa mata aka yi mata sutura.
Sai la’asar tukunna suka samu aka sallaci Baba Larai aka kaita makwancinta…

Ana dawowa daga kaita
Mommy ta cewa Kausar ta tafi,ita tsoranta d’aya kar itama Kausar d’in Daddy ya koreta dan tabbas suna da buk’atar ta a gidan…tare suka tafi ita da Junior Yasmeen da Yadira…..
Suna tafiya Yassir shima yace musu”zai wuce za su ci gaba da zama da wani Abokinsa kafin komai ya yi settling”
Mommy ta so ta tsayar da shi gudun kar wani abun ya same sa amma da ta fahimci video d’in a iyaka family ne ya yi circulating hukuma ba su riga sun gani ba sai kawai ta rabu da shi ya tafi….ba ta kuma yi masa maganar ba saboda ta lura kamar ba ya son zancen!
Har ga Allah ita she’s proud of Yassir saboda ya yi yunk’urin kawar mata da matsalar ta
(Dama ita tun a wajen da abun ya faru ta so ta fahimci shine ta kuma fusata da Yash d’in bai mutu da gaske ba)
dan haka ta bisa da kyawawan addu’o’i da fatan alkhairi su Yasira kuma ta ci gaba da yi musu borin ai sharrin aka yiwa Yassir d’in.


Sai da Yash ya je ya ga Manu tukunna ya wuce gida saboda dama tun jiya take rok’ansa ya barta ta yi kwana uku tunda gida ma za su chanja ai kuwa da ya barta ta ji dad’i kwarai amma kuma tana ganin yanayinsa ta fahimci akwai matsala dannhaka ta hau tambayarsa bai b’oye mata ba ya gaya mata cewa”Daddy ya kori Yassir kuma k’arshen abun bai yi dad’i ba dan har da Mommy itama sai da ta bar gidan”
,sosai Manu ta tab’u daga jin zancen da kyar ta taushi kanta sannan ta yi namijin k’ok’ari wajen kwantar wa da Mijin nata hankali tukunna suka rabu ya wuce gidan Daddy shi da Najeeb dan yana gidan suka zo shi da Siyama.

Ita Manubiya ba ma ta yi tunanin da Siyaman aka zo ba dan basu dad’e da yin waya ba bata gaya mata ba sai da su Yash d’in suka wuce tana shiga parlourn nasu daga parlourn Baba ta ganta a zaune ai kuwa nan suka hau murna har da hawayen farin ciki.

Sai da su Yash suka kama hanya tukunna ya tuna bai sanarwa su Manubiya rasuwar Baba Larai ba,dan haka ya bari a kan sai zuwa anjima sai ya gayamata ya san dole za ta kirasu ko ma ta je addu’arsa d’aya Allah ya sa kar Mommy ta yi mata abunda ta yi masa itama da ma gashi ba ta sonta.

A b’angaren Kausar kuwa zuwa yanzu ta gama sanin abun yi dan haka jimamin Baba Larai yana d’an sakinta ta kira Ya’isha tace”tana so ta had’ata da Abbakar akwai abunda zai yi mata”
Da kyar Ya’ishan ta had’ata da shi kuwa
Saboda last time Abbakar d’in ce mata ya yi “kowa kawai ya yi ta kansa daga yanzu!
dan plan d’in da suka had’a last time bai yi masa ba gashi ba su yi winning ba gashi kuma sai da yayi watanni uku a asibiti…”
Hakanan dai ita Kausar ta nace sai da aka had’ata da shi saboda shi ne kawai ta ga intention d’insu ya zo d’aya tunda yana son Manu itakuma tana son Yash dan haka za su taimaki juna,ta zauna ta yi tunani sam ba za ta wani biyewa Mommy ba wallahi!
Ba za ta iya hak’ura da Yashjub ba…kowa kawai ya yi ta kansa……….

Ita dai Yasira tana jinsu suna wayar da Ya’isha har aka tura number tana mamakinsu a ranta tace”wato dai wanda ya mutu ya riga ya tafi!duniya kuma kowa sai ya ci gaba da abunda ya saka a gaba.
Kalli yadda suka ci gaba da k’ulle k’ullensu kamar ba yanzunnan aka dawo daga kai Baba Larai kabari ba.”

Ita ma Yusra lissafin da take yi kenan.
Ita sam ba ta yi tunanin Kausar d’in ta san da issue d’in Abbakar d’in ba ma maybe Ya’ishan ce ta fad’a mata.

Su Yassir suna gama tafiya Mommy ta cewa su Yasira su zo su raka ta…su sun yi tunanin ma kayan abinci da abubuwan buk’ata za su sissiyo sai da suka ga ta d’auki hanyar inda za su je tukunna suka fahimci inda suka nufa…
Aikuwa suna isa suka shaida wajen…
Mutumin tsoho tukuff idan ka gansa ba za ka yi tunanin yana gani ba ma tsabar tsufa..hakanan ya k’araso inda suke dan suna yin parking suka ga ya fito yana zuwa yace”lale marhaba Khadija yau kuma ina Larai??”
Sunkuyar da kai Mommy ta yi ta girgiza kanta a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata….

Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata idanu kafin yace”Allahu Akbar amma an yi babban rashi..Allah ya ji k’anta!mu je daga ciki”
Daga haka suka nufi ciki.

Shi wannan tsohon!wanchan bokan na k’auyen su Baba larai shi ne ya had’ashi da ita tun asalin farko kafin ya rasu kafin ta baro ma k’auyensu ta da who nan Kano inda yake…..idan abubuwa suka shige masa duhu ya kan tambayeta itama haka,har nan suna zuwa ita da Mommy idan aikin da suke son yi ya had’a da wanda mace ba zata iya yi ba sai su kawo shi ya yi musu.
….
Sai da ya sake yi mata gaisuwa ta amsa tukunna ba tare da b’ata lokaci ba tace masa”Yashjub ya yi aure ba ta samu abunda take so ba har yau kuma Yarinyar ta zo da farar k’afa mutuwar Baba larai na daga cikin masifun da Manubiya ta zo mata da shi saboda dama Baba larai tace
muddin aka aurota to fa an yi ta ganin bala’i kala kala.Yanzu haka ma ba ta gidan Daddy jiya ya yi musu korar kare ita da Yassir….”

Salati tsohon ya yi kafin ya janyo wata tukunya fall ruwa yana duba cikinta yana jimami….

Sun fi minti ashirin a haka kafin chan ya d’ago ya kalleta yace”ai kin yi kuskure!irinsu waennan ba a barinsu a doran k’asa!ai idan aka yi aiki ya k’i ci ya k’i cinyewa rabasu da duniyar ake yi tunda sun fi k’arfinka to ta ya zaka tsaya fafatawa da su ai ba zai you ba!”

Ajiyar zuciya Mommy ta sau’ke dan ba k’aramin dad’i ta ji da jin wannan batun ba saboda dama ita takanas abunda ya kawota kenan!!a yi ta ta k’are kawai.
Cikin k’aguwa tace”aikin gaggawa nakeso ka yi mana,ba na so Larai ta kwana uku a kabari ba tare da Yarinyar nan ta bi ta ba!”
Cikin tarar numfashinta Yasira tace”Mommy wai kisan Kai kike nufi??”

Murmushi tsohon ya yi kafin yace”to ai hakan kawai ce mafita!saboda Wallahi Allah muddin Yarinyar nan tana raye tou fa bala’i da masifu yanzu kuka fara gani!!!”.

K’ura masa ido Yasira ta yi kafin chan ta d’auke kanta ta mayar ga Mommy tace”Mommy mu je gida ma yi magana Plss dan Allah ki bar maganar nan!”.

Girgiza Kai kawai Mommy ta yi kafin ta ce”Yasira har yanzu ke Yarinyace..dan gashi duk abubuwan da suke faruwa a gaban idanunki ba kya gani!inaga sai na mutu kin binne ni tukunna za ki fahimci abunda muke nufi!!!”

Da d’an zafi Yasira tace”Mommy Manubiya b….”
Cikin katseta da tsawa sosai Mommy tace”za ki yi mini shiru ko kuma in kora ki waje????”

alamun ta yi shiru su Ya’isha suka yi mata dan haka kawai ta yi shiru ba dan ta so ba kuma wallahi wannan tab’argazar ba da ita ba ba za ma ta bari a yi ba…

Sai da Mommy ta yi kusan minti d’aya tana hararar Yasirar tukunna ta mayar da kanta ga tsohon wanda shima yake cewa Yasirar “ki tsaya ayi abu a nema muku mafita hatta rashin aurenku duk itace gashi nan na gani a nan!ko ba kwanan nan wanda za ki aura ya yi aure ba???”

Ita dai Yasira banza ta yi da shi Yayinda Mommy da Ya’isha suka aminta da maganar ta shi d’ari bisa d’ari…

Murmushi kawai ya yi ya mayar da dubansa ga Mommy yace”kar ki damu komai ya zo k’arshe inshaaAllah!”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace”yanzu nake so a yi aikin..saboda na gaji na tsani…”

Cikin tarar nunfashin ta yace”sai dai a yi aikin a yau da daddare gobe a tashi babu ita!!”

Jin jina kai ta yi tace”hakan ma ya yi”

“To Alhamdulillah” yace kafin ya d’aura da cewa”yanzu akwai yadda za a yi in samu hularta???”

Kallon juna suka yi ita da Ya’isha suka yi shiruu kafin chan Ya’ishan tace”eh!!
Da me kuma??”

“Iyaka hula,kawai!
Ki tabbatr tana cirewa daga kanta kin kawo mini kai tsaye ba tare da kowa ya saka ba!
Shikenan abunda na ke buk’ata.”
Cikin yin serious da fuska sosai,ya ture tukunyar gabansa ya mayar gefe ya kallesu sosai yace”da farko dai inaso ku fahimci cewa shi RAI!!
Bayar da shi da karb’arsa wannan Ubangiji ne kad’ai ya isa bi’ma’ana Ubangiji ne kad’ai yake bayar da Haihuwa yake kashewa bayan shi babu wanda ya isa,duk bala’in mutum bai Isa ya kashe ko ya raya ba…”
Jimm Mommy ta yi tana jin wani sabon tashin hankali yana rifeta, kar dai mutumin nan yace ba zai iya yi mata komai ba kuma!!!
Tana wannan tunanin ta ji ya ci gaba da cewa”Abunda mukeyi idan matsala irin taki ta taso shine wannan aikin da zan yi muku a yanzu ammafa yanada matuk’ar hatsari kuma yana buk’atar taka tsantsan!”
Sai da ya sauk’e numfashi tukunna ya d’aura da cewa”ita wannan hula da za’a kawo itace nake so a kiyaye kar a samu matsala wani ya saka bayan ita Yarinyar saboda idan aka samu matsala to fa shi wanda ya saka bayan itan da wanda ya kawo duk su biyun aikin zai fad’awa kuma idan aka yi ba’a janyewa bima’ana idan aka yi an riga an yi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login