Showing 114001 words to 117000 words out of 244445 words

Chapter 39 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16458

ta aikata Yasmeen d’in tace ‘’eh,Mommy”
sai kuma ta yi shiru kafin ta sake cewa “amma Mommy kina ganin Ya Yash ba zai fahimta ba?besides idan aka yi allurar ai za ta yi miscarriage kuma za‘a gani sannan za ‘a fahimci ciki gareta amma na yi k’arya nace babu.’’

Cikin fushi Mommy tace ‘’kin fi ni sanin abunda nake yi ne?tunda nace miki haka ayi kawai!mu samu mu fara yin maganin matsalar da ke a gaban mu gadan gadan,next..za mu san abun yi shima’’

Shirun da ta ga Yasmeen d’in ta yi ne yasa cikin tsananin fushi ta sake cewa’’za ki iya ko ba za ki iya ba!?”

Ahankali Yasmeen ta had’iye wani abu da take jin yana taso mata sannan tace ‘’Mommy!
i took an oath to help people!ba wai in kashe rai ba!,baya ga haka kuma
dukda ban so cikin nan ya kasance a jikin Manubiya ba na so ace a jikin Kausar yake amma no matter how na tsani Manubiya babyn jikin ta na Ya Yash ne..
Maganar gaskiya Mommy ba zan iya kashe Babyn nan tashi d’aya ba.Inaga in dai abunda kuke so kenan gara kawai a nemo doctor mu biya sa ya yi mata allurar amma ni kam a gaskiya Mommy ba zan iya kashewa Ya Yash baby tun kafin ya zo duniy…..”
Mahaukacin Marin da Mommy ta d’auke ta da shi ne ya hanata ci gaba da magana.
Cikin tsananin fushi da tashin hankali Mommy tace ‘’dan ubanki ni za ki nunawa jini!,kin bi kin wani hak’ik’ance Ya Yash!Ya Yash!Ya Yash d’in da bai damu dake ba tun farko sannan ana so a gyara Abu a had’a kanku kafin wata ta tarwatsa shine za ki yi mini wa’azi?ni za ki kunyata Yasmeen ni za ki yiwa taurin Kai???.”
Cikin huci ta fara ja da baya tana cewa
“Shikenan! na tsame hannuna
daga yau kowa ya yi ta kansa tunda kallon muguwa kika fara yi min’’

Da sauri Yasmeen tace ‘’A’a Mommy ba haka bane dan Allah…’’
Tun kafin ma ta gama magana Mommy ta fice daga d’akin ta banko k’ofa.
Ko gani sosai ba ta yi tsabar tashin hankali…tunda take bata tab’a Jin tsana irin ta yau ba.Da kyar ta samu ta k’arasa d’akin ta tana shiga ta fashe da wani irin kuka tana hango failure gadan gadan..
Tabbas Baba Larai ta yi gaskiya dan gashi tun da Manubiya ta shigo a hankali abubuwa suke going against her abubuwan da a da suke y’an k’anana a wajenta yanzu gashi suna shirin fin k’arfinta..duk yadda ta yi da Ummi sai ta botsare sam ta kasa ta shiga tsakaninta da Daddy Daddyn kansa da farko kamar sun samu kansa amma yanzu ya burkice ko su Yasira ba kasafai yake hira da su da Dariya kamar da ba,yanzu kuma gashi y’ar cikinta ta yi going against her!me ya fi wannan bak’in ciki?kuma ta san in ba da kyar ba sai su Yasmeen d’in sun dasa ayar tambaya a kanta duk a ta dalilin mak’urar da Manubiya ta kai ta. Tabbas sai yanzu ta sake fahimtar Baba larai dan gashi tun da Manubiya ta shigo rayuwar Yash duk abunda ta tsara baya tafiyi mata yadda take so,in banda fitina da b’acin rai da k’alubale babu abunda take fuskanta,a
tak’aice dai a hankali a hankali kenan Manubiya sai ta yi mata tumb’ir!!inaaa aikuwa ba zai yiu ba she won’t allow it wallahi sai dai a mutu!.


Mommy tana fita Yasmeen ta kalli Baba larai tace ‘’ Baaba ki yi mata bayani dan Allah”

Da sauri Yasira wadda k’arasowar su yanzu gurin tace
“Mai ya faru?
Kallon ta ta yi ta kalli Ya’isha kafin ta shiga zaiyyane musu abunda ya faru….
Kamar Ya’isha za ta rufe Yasmeen da duka haka ta shiga surfa ruwan bala’i tana cewa”Ashe baki da lisssafi ban sani ba? Har yaushe kika santa da har za ki tausaya mata dan wanann ba wai Yashjub kike tausayawa ba ita kike tausayi.
To bari ki ji in gaya miki idan har wanann Yaron ya zo duniya wallahi ko k’ofar gidan wata rana baki isa ki taka ba!,kin ga daganan sai in ga ta k’arshen zumunci da tausayin d’an d’an uwa!
Ki na gani dai kwanan ta uku tal a cikin gidan amma da muka je korar mu ya yi!
Ki bar ganin wai Daddy ya tsawatar masa yanzu ance mu je anytime wallahi a kwana a tashi watarana Daddyn ma bai isa ya ce komai ba,indai Yarinyar nan ba ta yi waje ba to ba mu da kwanciyar hankali a cikin gidan nan
Ke kin san su waye talakawa idan suka samu guri kuwa???
sai ta raba sa da kowa ta handame komai daga ita sai y’ay’an ta
gashi uban dukiyar family karakakaff duk tana hannun sa’’

Cikin son fahimtar da ita Yusra ma tace
‘’Yasmeen tunda har ga abunda Mommy tace miki ki yi kawai mana kin fi ta sanin daidai ne?’’

Ahankali Yassira wadda tun d’azu ba ta yi magana ba , ta fesar da iska kafin ta kalli Yasmeen ta ce ‘’ki rubuta za mu je mu siyo yanzu ni da Ya’isha…abun da Babba ya hango k’arami bai Isa ya hanga ba’’

Cikin rashin jin dad’i Yasmeen d’in tace
‘’Wai me yasa baza ‘a samu mutum d’aya a cikin ku wadda za ta kalli issue d’innan daga point of direction d’ina ba??”

Wani wawan tsaki Ya’isha ta ja kafin tace
“Ai dama na riga na sani,na san sai kin yi taurin kan naki da kika saba!
Yasira kawai ki zo mu je zan yi
browsing mu siyo kuma wallahi idan muka kawo dole sai kin yi
dan babu wanda kika Isa ki gwadawa taurin kai anan!.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice fuuuu zuciyar ta kamar ta b’ullo waje.

Still cikin son fahimtar da su Yasmeen tace
‘’in da ace mun san zamu aikata haka da bamu barta har ta rayu dashi a wata k’asa daban ba
Infact da bamu barta ma ta shigo gidan ba.”

Cikin tarar numfashinta Baba larai tace
“Yasmeen ke shaida ce wanne irin abu ne ba a yi ba amman sai da ta shigo
Y’an uwan ki da mahaifiyar ku sun fiki gaskiya fa….”

Cikin katseta Yasmeen d’in tace”to Baaba sai ku duba ku ga yadda akayi ta fama d’in amma sai da auren nan ya d’auru shin ba za ku yi lissafin watak’il wannan cikin shine rabon da ke a tsakanin su wanda Ubangiji ya k’addara sai sun yi auren kuma sai ya zo duniya ba??ba za ku yi tunanin mai za ta kasance da mu idan muka dage muka ce sai cikin ya fita ba??”

Shiruu kawai Baba larai ta yi tana kallon ta.
Ahankali Yasira wadda itama tun farko tsarin bai yi mata ba tace
‘’ Yasmeen ki yi abun da ake so ki yi kawai!!as far as I know Mommy ta fi ki sanin duk waennan abubuwan so definitely akwai abun da ta hango sannan kuma inaso ki sani duk yadda za ki so Yashjub bai kai yadda za ta so shi da shi da abun da zai Haifa ba,dan haka tun da har kika ji tace haka akwai dalili Babba!
We re suppose to stick together kar kanmu ya fara rabuwa tun a nan!
mun fi ki yawa dan haka Ina shawartarki da ki yi hak’uri ki yi abunda kowa anan yake so ayi.’’

Shiruu d’akin ya d’auka kafin chan Yasmeen ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ahankali tace”okay!bara in rubbuto”
daga haka ta juya ta fita.

Ahankali Yasira ta fesar da iska…ta rasa ganin ta inda abunda suke shirin aikatawa ya kasance daidai ya kuma dace ace su yi!
Tabbas itama a cikin zuciyar ta a bayan Yasmeen take d’ari bisa d’ari
Amman kuma akwai abunda Mommy ta hango tabbas!
wannan shine dalilinta na bin bayan Mommyn dan ta san in dai Mommy za ta iya cewa a kashe d’an d’an cikin ta
to tabbas lamarin Yashjub da Manubiya ya wuce tunanin su,ya fi k’arfin iyakar abunda ta gaya musu suka sani.
………..

Bayan kamar 40 minutes,
Su Yashjub suna zaune har da Yahanasu wadda ta kawo wa Mannubiya tea take sha suka ji ana knocking.
Sai da Yashjub ya kalli wayar sa ya ga likitan bai kira sa ba tukunna ya kalli Yahanasu yace “ta bud’e maybe su Mommy ne”
Ai kuwa tana bud’ewa suka yi
Ido biyu da Yasira Yasmeen da Ya’isha.Ba musu ta matsa musu suka shigo..sai da suka fara yi wa Manubiya ya jiki tukunna Yasmeen tace “Mommy ce tace ta zo ta duba ta”
Cikin tarar numfashinta Yahanasu tace
“Ai Likita yana hanya”

Murmushi Yasira ta yi ta matsa kusa da Yashjub da Mannubiya da suke zaune a bakin gadon tace’’Manu ya akayi kika bari ya kira Dr bayan gamu da soon to be consultant a gida?Yasmeen matso ki duba ta Mommy tana jira,ta ce in ta kama sai a wuce asibiti.
Gaba d’aya hankalinta har mu duk a tashe yake…aman da ta yi ai dole a dubata da wurwuri in ma k’arin ruwa ne a yi mata dan na san she’s weak’’.

Shiruu Yashjub ya yi kafin chan ya d’ago ya cewa Yasmeen d’in “matso mana mai kike jira?”
Sai kuma ya kalli Ya’isha yace
‘’ki je ki cewa Mommy jikin nata fa da sauk’i ta kwantar da hankalinta”.

Murmushi duk suka yi banda Yahanasu da gaba d’aya hankalin ta yake a tashe
Har ga Allah ta gama shiryawa akan ko da ace cikin ne to za ta san yadda za ta yi ta lallab’a Yashjub su b’oye har sai ya d’an yi kwari tukunna a fad’a
amma gashi yanzu su ne ma za su fara sani
Sannan yadda suka dad’e a saman nan ba su sauk’k’o ba bata da tantama plan suka gama had’awa….
Tana wannan tunanin ta ga Yasmeen ta matsa kusa da su ta shiga duba Mannubiya dama har da abun auna hawan jinin ta ta taho da ragowar abubuwa.
Duk wani gwajin da ya kamata sai da Yasmeen ta yi mata.
….Tun a kan pulse d’in Mannubiya Yasmeen ta jiyo alamun ciki ga kuma ragowar gwaje gwajen da ta yi mata waenda suma suke nuni da hakan
shiyasa tashi d’aya gaban ta ya yanke ya shiga fad’uwa dan ba ta san ya za ta yi ba sannan ba ta san ma ta Ina za ta fara ba…

Cike da murmushi da tsantsar farin cikin da ya baiyyana a iyaka kan fuskar ta Yasira ta matso ta ce ‘’good news ko?pls tell me I’m about to become an aunt.’’
Ta k’arashe maganar tata da y’ar guntuwar dariya kwance a kan fuskarta.

Murmushi Yashjub ma ya yi yana jira kawai ya ji ance masa Mannubiya na d’auke da ciki ne amma instead sai kunnuwansa suka jiyo masa muryar Yasmeen d’in tana cewa’’A’a gaskiya ba ciki bane ba, dan in da ace shine da zan ji yanayin pulse d’in ta ya d’an chanja sannan ragowar gwaje gwajen da na yi mata suma duk ba su yi detecting pregnancy ba,inaga gajiya ne da fever…
But first bari in fara yi mata allurar tsaida aman nan dan da na duba idonta gaskiya she’s very weak sannan ba ruwa a jikin nata zata iya fainting anytime from now.!”

Gaba d’ayan su jikinsu sanyi ya yi especially ma Yashjub wanda ya gama kwallafa rai ya gama yarda akan kawai cikin ne, ganin yadda Mannubiyan ta yi ne ya sa cikin son bata kwarin guiwa ya samu dakyar ya aro jarumta yace’’ok,dama nima na yi tunanin gajiyar ce, a ina za’a siyo allurar?
A samu a yi mata da wuri a samu ta d’an ci wani abun ta kwanta ko?”

Cikin tarar numfashinsa Yahanasu tace‘’Ina ga gara dai a jira Doctor d’in ya zo shima ya dubata tun da kaga shi Babba ne!
sai a san da me da me ya kamata a bata.”

Da sauri Yasira tace ‘’ba ki ji abuna itama Yasmeen d’in tace ba?
Iyaka allurar tsaida amai za ta yi mata saboda itace emergency ana buk’atar a tsayar da gaggawa.’’

Cikin katseta Yahanasu tace’’Yasira allurar tsaida amai fa tanada k’arfi sosai! ki bari a yi kwak’kwaran bincike kafin a fara d’irka mata abubuwa’’

Murmushi Yasmeen ta yi sannan tace”Na yi duk gwaje gwaje fa
In da ace akwai ciki ko na sati d’aya ne to da zan gani zan kuma fahimta, kar ki manta Gynea na yi specializing a.
Also allurar da zan yi mata yanzu ba ta da wani k’arfi iyaka tsayar da aman za ta yi.’’

Zuwa yanzu ran Yahanasu ya b’aci kuma ta sake tabbatarwa akwai abunda suka shirya dan haka tace
‘’Ai nima ba cewa na yi ciki ba cewa na yi ki tsaya dai a yi kwakkwaran bincike dan wannan gwajin da kika yi bai kai ace ya yi detecting komai b..’’

A hankali cikin katseta Yashjub yace
‘’Yaha Mommy ce ta aiko su kar k….’’
Juyawa kawai ya ga Yahanasun ta yi ta fice daga d’akin da alamun ranta ya b’aci.
Shiruu kawai Yashjub ya yi,
sam bai ji dad’in abun da ya yi mata ba amma kuma ba ya so Mommy ta yi fushi..
Shiyasa ya bari akan idan su
Yasmeen d’in sun gama zai je ya bata hak’uri,gara ace ita ta yi fushi ta bar case d’in akan su Yasmeen su je su gayawa Mommy ta ga kamar ya sace mata guiwa ne daganan ta yi fushi.
Tunda sun ce ita ta turo su kuma ta na chan hankalinta a tashe ya san idan ya hana su bazata ji dad’i ba…
Gara Yahanasu ya san ita za ta fahimcesa idan ya je ya bata hak’uri zuwa anjima…

As far as he knows,su Yasmeen ba za su tab’a yi masa k’arya ba kuma ba za su cutar da shi ko Mannubiya ba…dan ko kwanaki da aka yi ta case yanzu ya fahimci saboda Kausar suka yi ta abubuwa amma yanzu gashi da ya dage da addu’a ai sun shiryu sun dawo saiti dan yadda suke yiwa Manubiya tun zuwansu har kawo yanzu ya ji dad’i kwarai ya fahimci suna sonta yanzu….shiyasa har ga Allah tunda suka ce ‘babu ciki’ya yarda kuma ba ya so ma wani likitan ya zo ya kuma duba ta ya ce ‘babu cikin’ saboda shi kad’ai ya san kalar disappointment d’in da ya ji a lokacin da Yasmeen tace ‘babu cikin’….
ya san kuma a b’angaren Manubiya itama haka ne…..

Da waya Yasmeen ta kira Yusra tace ‘’dan Allah ta duba cikin bed side d’inta na left akwai wata green Leda ta d’auko ta kawo mata
Allurar tsayar da amai ne a ciki da su paracetamol”.

…Already dama sun riga sun gama had’a plan d’insu shiyasa suna gama wayar su Baba larai suka yi sauri suka bawa Yusran ledar allurorin da su Yasira suka je suka siyo,ta karb’a ta sauk’o ta nufi d’akin Yahanasu da shi….

Ita dai Mannubiya ta yi shiruuu tana ta istighfari a cikin ranta dan lokacin da Yasmeen tace ‘bata da ciki!’ kad’an ya rage ba ta yi sab’o ba….haka shima Yashjub ya yi shiruuu ran sa a mugun dagule….yayinda Yasmeen take jin inama akwai wani waje da za ta gudu ta b’uya dan wallahi har ga Allah ba ta son yin allurar! ba ta son ta kashewa Yashjub Baby!,she can’t believe wai yau itace take shirin yin kisan kai,that too Babyn yayanta.!

Suna a haka Yusra ta yi sallama ta shigo ta mik’awa Yasmeen laidar allurorin.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 28
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.


Yahanasu tana fita ta nufi sama side d’in Daddy…dan wallahi sai dai fa a yi ta! a cikin gidan nan amma ba za ta bari Yasmeen ta d’irkawa Mannubiya allura ba tare da an tsaya likitan kwarai ya zo ya dubata ba
Ya za’ayi mace tana irin wannan aman ga jiri ga fever sannan kuma amarya amma tace wani ‘ba ta da ciki!’
Ta san ba ta yi aure ba kuma bata da experience amma tanada shekaru da hankalin da zata iya banbance mace mai ciki da mara ciki.
In banda tsabar rainin wayo a ta ina aka tab’a tabbatr da ciki da rashin sa ba tare da an yi test na jini ko na fitsari ba!…

Ba b’oye b’oye tana zuwa ta cewa Daddy “ga Yasmeen chan za ta yiwa Mannubiya allurar tsaida amai ba tare da ta duba ta ko ta bari Likitan da aka kira ya zo ya dubata ba.”
“Kuma allurar tana da k’arfi sosai!ba a cika son yin ta anyhow ba”.

Shiruu Daddy ya yi kafin ya mik’e ya ce “mu je wajen nasu.”

Kusan a tare Daddy suka k’arasa bakin k’ofar shi da Mommy wadda duk yadda ta so yin fushi ta bar Yasira ta yi dealing da Yasmeen sam ta kasa hak’ura sai da ta sak’k’o a yi komai a gaban idanunta.
Tun ba ma da Yasmeen d’in ta kira Yusra tana cewa ta kawo mata ledar ba dan a lokacin sai da Mommyn tasa Yusra ta tambayeta tace “akwai?”
Ita kuma tace mata ‘yh’kawai ba tare da ta bari su Yashjub d’in sun gane ba.
Shiyasa sam ta gagara sukuni ta sake burkicewa ta sauk’o ta nufi d’akin Yahansun a gigice a hakan ma wai Baaba larai ta ce mata ta nutsu ta yi controlling kanta…


Su Daddy suna shiga itama ta shige
dai dai Yasmeen tana shirin zurmuk’awa Manubiya allura a cinyar hannu.

D’an dakatawa ta yi ta tsaya kawai tana kallon su
Suna had’a ido da Daddy yace
‘’Yasmeen an yi duk wasu gwaje gwaje da suka kamata ne???ku je asibiti a yi test har na jini mana’’
Wani kalar kallo Yassira ta shiga jifan Yahanasu da shi dan ta san ita ta je ta kirawo Daddy.
Mommy kuwa ta fi jin haushin Yasmeen! ji takeyi kamar ta je ta rufe ta da mahaukacin duka dan in da ba ta tsaya delay ba da tuni komai ya kammala.
Sannan yanzu da ta ga sun shigo tun da har ta riga ta kai allurar kan cinyar hannun Manubiyan meye nata na wani tsayawa ta d’ago instead of kawai ta soka ta juye mata ruwan allurar..dama chan ba ta son yi ai shiyasa ta lalata musu komai!…
Har wani duhu duhu take gani tsabar tashin hankali,ganin bakin Yasira take yi yana motsi alamar tana yiwa Daddy magana amman ba ta san ma mai take fad’a ba dan ba ta jin komai tsabar masifar da ta shiga.
Tana k’ok’arin ta bud’e Baki ta san dabarar da za ta yi su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login