Showing 102001 words to 105000 words out of 244445 words
ba kowa ne ya dace ya dinga shiga ba kuma d’akin yana da girma zai isheku.
Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki cire komai a ranki sanann batun Kausar d’innan itama kar ki ma bari ta d’aga miki hankali ke dai ki dage da addua a ko da yaushe da sallar dare InshaaAllah ba su Isa su yi miki komai ba Wallahi….”
Ahankali Manubiya ta share hawayenta tana jin
sanyi da nutsuwa suna ratsata sakamakon shawarwari da kwarin guiwar da ta samu daga wajen Jidda.
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “na gode jidda”
kamar itace k’aramar.
Ko da ta yiwa Jidda zancen makaranta tace”ta ga kamar yanaso ya hanata ci gaba da karatu”
Tashi d’aya cike da bata kwarin guiwa Jidda tace
“Yashjub ba zai tab’a hanata ta k’arasa karatun ta ba.
Kawai yanzu tunda tafiya za su yi ta hak’ura ta bi sa su je su dawo ta san daganan zai
san abun yi kamar yadda ya fad’a maybe yace ta k’arasa Online tunda ya fad’a mata baya son cud’anyar ta da maza ne.
Amman ita kam tana ba ta assurance d’in ‘Yashjub ba zai hanata makarantaba’ tunda shima ya fad’a da kansa yace yanaso ta yi karatun kuma ai gidan su y’an boko ne so karma ta saka hakan a ranta…..”
Sai da Jidda ta kuma jaddada mata ta dage da addua tukunna suka yi sallama da juna suka katse kiran.
A hankali ta kife kanta akan gadon ta saki wani siririn kuka…
Sam ita ba ma ta san lokacin da Yashjub ya shigo ba sai da ta ji ya zauna nan bakin gadon kusa da ita.
A hankali ta d’ago da fuskarta…gaba d’aya sai hankalin sa ya kuma tashi sakamokon yadda ya ga fuskartata ta yi har ta kumbura idanuwanta sun yi luhu luhu.
Kamar zai fashe da kuka sannan kamar mai tsoron tab’ata haka ya matso ya ruk’o hannuwanta ahankali yace”I’m not supposed to make u cry dan Allah ki daina”
Ya fad’i hakan hawaye suna masu ciccikowa a idanuwansa.
A hankali ta share hawayen nata ta matsa jikinsa bai yi wata wata ba ya rungumeta yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya.
Haka kur’um sai ta tsinci kanta da jin tausayinsa da kuma jin kunyar sa da ta tuna yadda ta dinga turesa d’azu tana korar sa amma kalli sai da ya dawo…ahankali cikin sanyin murya tace ‘’ka yi hak’uri’’
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e mai tafe da
murmushi yana mai jin nishad’i da tsantsar k’aunarta suna ratsashi,d’ago ta ya yi ya yi cupping face nata a cikin hannunsa kafin yace ‘’Manubiya ba ta laifi a wajen Yashjub! ko ta manta ne?’’
Wani irin kuka ta saka ta sake cusa fuskarta a k’irjinsa..rungumeta kawai ya yi shima yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jejjere yana bubbuga bayan ta alamun rarrashi.
Sun jima a haka dan har ta yi shiru bata d’ago ba ta yi lamo kawai tana sauraron bugun zuciyar sa.Tukunna a hankali tace”Ina so zan koma d’akin naka,mu biyu kawai”
Murmushi ya yi kafin yace
“Whatever u say love..hakan za a yi”
Daganan ya gyara musu position suka kwanta a kan gadon ya shiga lallashinta kamar zai yi mata kuka……
Daman ba ta fara girki ba..kamar yadda Jidda ta gaya mata washegari da safe ta had’a kayanta har waenda ta rufe a jaka kaff ta kwashe Yash ya tayata kaiwa d’akin sa dan ta gama tsarawa akan ko sun dawo to ta bar d’akin ta muddin Yadira ta na gidan.
Tunda kuwa ta haye sama ba ta sauk’o ba dan hatta abinci delivery man yana kawowa idan ya bawa Yadira nata zai wuce da nasu sama…ba ta tashi sauk’owa ba sai bayan azahar lokacin da suka zo fita.
Ita a tunanin ta ma tare za su fita da Yadirar amman sai ta ga sun tafi iyaka su biyu kawai.
Haka suka je suka kammala komai na shirye shiryen tafiyar su.
Sai dare wajajen k’arfe takwas tukunna suka dawo.
Suna shigowa suka tarar da Yadira da Yassir a zaune a parlourn shi yana waya ita tana kallo
…..tabbas idan Yassir bai daina yi wa matar sa wannan d’an iskan kallon ba wallahi zai yi abun mamaki sai dai duk abunda zai faru ya faru
tsabar Iskanci har wani lashe Baki yakeyi gashi ya k’ank’ance idanu yana kallonta tun daga sama har k’asa
Tsabar takaici Yashjub bai san lokacin da yace mata “ta wuce ta tafi d’aki”ba
Sai a sannan Yassir ya yi murmushi ya mik’e tsaye ya k’arasa inda suke Manubiya tana shirin wucewa ya sa hannu ya karb’i ledar hannunta wanda sai da ya had’a da hannnunta da ledar ya runtse ya murza tukunna ya k’arba ledar yana wani kalar murmushi sannan yace “barka da dare antynmu”
Da kyar tace “lafiya”
Har ga Allah ta tsani Yassir especially ma yanzu da ta gama tabbatarwa d’an iska ne saboda kalar yadda ya runtse mata hannu ko ita Yarinya ce ta san kalar na y’an duniya ne har wani murzawa ya yi..
Shi kam Yassir laushi da taushin hannun nata ne ma ya fi komai d’aga masa hankali dakyar ya juya ga Yashjub wanda ya kafe sa da idanu yace “Ina wuni”
Yana wani killer smile.
Dakyar Yashjub ya iya danne fushin sa dan ya kul’e ba kad’an ba ya san case d’in Yadira ya Isa wajen Mommy da Daddy bashi da tantama dan Yahansu tace “tanada magana da shi in ya zama free ya kira ta”
Shiyasa kawai ya danne kan sa dan gudun kar a kuma yin wani case d’in.
Cikin kawar da kai yace “lafiya”
Kafin ya d’an kalli Yadira itama yace mata “lafiya”wadda sai da ta bari Manubiya ta wuce tukunna ta gaida shi,daga haka ya juya yana mai bin bayan Manubiya wadda ta wuce sama da sauri da kallo,kafin ya maida dubansa ga Yassir..da mamaki ya k’ura masa ido ya shiga k’are masa kallo dan idan idanuwan sa ba k’arya suka yi masa ba tou kamar kayan bacci yake gani a jikin sa shi sai yanzu ma ya lura sannan ya tuno bai ga motar sa a waje ba..
Cikin son fahimtar sa yace
“Banga motar ka a waje ba
ko dawowa za a yi a d’auke ka?”
Murmushi ya yi kafin yace
“Bello ne ya kawo ni ya koma
wai zan kai ku airport ne da safe gobe daganan sai mu wuce gida ni da Yadira”
Shiruu Yashjub ya yi a ransa yace ‘’a tak’aice dai kaima a nan za ka kwana!”
A fili kuma kawai sai ya jin jina kai ya sa hannu yace “bani ledar”
Da sauri Yassir yace
“No,ga guda biyu masu nauyi a hannunka,bari kawai in kai muku d‘aki
Cikin d’an tsare gida Yashjub yace ‘’bani nan, sai da safe’’
Ya fad’i hakan yana sa hannu ya k’arba ledar…
Ba dan Yassir ya so ba ya basa
daganan ya zura wayar sa a aljihu ya wuce d’akin bak’i na nan k’asan zuciyar sa tana turiri…so ya yi ya d’an fara k’addamar da shirin sa akan Manubiya tun yau!ya so ace ya
bata ajiyar sak’o mai nauyi mai tsayawa a rai wanda har ta je honeymoon d’in ta dawo yana mata yawo a rai.Ya san rik’e mata hannun da ya yi ma wani abu ne amman ya so ace ya yi wanda ya d’an fi haka…
Bai kamata ya dinga jin kishi ba tunda ba Kausar baceba amman har ga Allah haushi yakeji idan ya tuna Yashjub zai tafi honeymoon da ita wata uwa duniya!anya kuwa ba k’aunar Manubiya yakeyi ba kuwa!
dan yanzu haka ma da ya tuna da cewa tare za su kwana ita da Yash wani irin tafarfasa zuciyar sa takeyi….
Ya na shigewa Yadira ta girgiza kai a ranta tace
‘’Ya Yassir kenan!”
Shi yasa fa ta k’i yarda da Junior saboda duk kusan halinsu d’aya da shi da Ya Yassir sai dai Ya Yassir ya fisa sosai dan nasa kam ya fara zama disorder….babban dalilin da ya sa bataji haushin Kausar a lokacin da ta yi futun futun tace ba ta son Yassir ba shine
ta san shima ba ita kad’ai yake kulawa ba kuma duk macen da take son zaman lafiya da kwanciyar hankali da ruhi to ba za ta tab’a zab’ar Yassir a matsayin Mijin aure ba…
Dan Tabbas idan aka bincika Ya Yassir tou yanada matsala it’s either psychological ko kuma asiri aka yi masa da mata dan tunda take bata tab’a ganin confused d’an iska kamar Ya Yassir ba….za ta iya cewa indai mace sunan ta mace tou Ya Yassir yanaso..
Ta san Kausar yakeso da aure amman fa y’an matan da yake so da lalata sam ba za su k’irgu ba kuma shi sam babu ruwan sa da class ko wani abun..
Yanzu haka a iyaka cikin gidan su kawai ta lura akwai abu a tsakanin sa da Munirat ga Kausar yanzu kuma yadda ta ga tun d’azu da ya zo yana ta faman tambayar ta Manubiya ta fahimci akwai matsala dama tun jiya yadda ta ga yana ta shishshige mata ta san da walakin.
Bata san mai yake damun sa ba bata tab’a ganin Namijin da bashi da tsayayyen choice irin Yassir ba wani zubin tana lura da shi idan ya ga mata jikin sa har karkarwa yakeyi,gashi yanzu tsabar idanunsa sun rufe matar yayan sa yake shirin farmawa!”aikuwa za’ayi murder!indai ya Yash ne”ta fad’i hakan a chan k’asan ranta kafin kuma ta tab’e baki ta mik’e tanajin haushin Manubiya yana ratsata
a hankali a fili tace ‘’su suka sani’’
daganan ta nufi sama d’akin ta…….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 26
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Dukda Manubiya a k’ule take da Yassir amman sam sai ta k’i yiwa Yashjub maganar sa dan kamar yadda Jidda ta gaya mata inshaaAllah ba za ta sake basu k’ofa su zamo silar b’acin ranta ko na mijinta a rayuwar aurensu ba sannan ba za ta sake da su ba….addu’a kuwa tun a jiya ta duk’ufa da yi dan ko shiru ta yi to a zuciyarta addu’a takeyi….
shima Yash d’in bai yi mata maganar Yassir ba
shiyasa ita bama ta san a gidan zai kwana ba.
Hira kad’an suka tab’a daganan sukayi nafila suka tofa addu’o’i suka bi gado.
Tun k’arfe uku ta tashi ta yi wanka ta fara shiri,har breakfast yau ta d’an had’a musu ta ajjiye wa su Yassir nasu a k’asa na ta da Yash kuma ta hau sama da shi ta ajjiye a d’akin…
Yassir kuwa wanda yake ik’irarin ya zo kai su airport ne sai da Yashjub ya zo tafiya sallah tukunna ya tashe sa da kyar…
Doguwar rigar abaya ta saka bak’a ta yafa mayafin..babu kwalliya ko k’adan a fuskarta amma ba k’aramin kyau ta yi ba.
Ahankali Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya k’araso ya tsaya a gabanta a hankali ya amsa gaisuwar ta kafin ya yi shiruu ya shiga kallonta,sai da ya gama k’are mata kallo tukunna yayi cupping face d’inta a cikin tafukan hannunsa yace‘’I’ll forever love you!a ko da yaushe inaso ki yi ruk’o da wannan kalmar dan daga zuciyata da ruhina ta taho babu hijabi’’ya karashe maganar tasa yana mai sakar mata light kiss a saman lab’b’an ta.A hankali Manubiya ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya dan kamar yadda yace mata maganar ta taho daga zuci da ruhinsa itama haka maganar ta shiga cikin zuciyarta ta samu mazauni dan har kwalla sai da suka d’an taru a idanunta.
Cikin nutsuwa ya d’auke lips d’insa ya mannna mata wani light peck a kumatunta da forehead kafin yayi hugging nata yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sun d’an jima a haka tukunna
ya cikata dakyar ya d’an gyara tsayuwar tasu ya koma gefenta ya sak’ale hannunsa na dama a cikin na hagun ta yace “shall we?’’
Yayi mata tambayar yana mai d’aga mata gira sama.
Murmushi ta yi tana jin tsananin son mijin nata da k’aunarsa suna ratsata dan har wani irin kallo Yash ya ga tana yi masa mai tafiya da imani da zuciyar wanda akeyi ma wa.Ahankali ya ce
‘’Baby wannan kallon fa?so kike ki sumar da ni?’’
Ahankali itama yadda yayi mata maganar kamar mai rad’a tace
“Ka yi kyau yau sosai,sosai!!’’
Ta fad’i maganar cik’e da shauk’i.
Wani irin blushing Yashjub ya shiga yi mai had’e da dariya
yana jin sa a sama……
“Mu wuce ko’’?
Muryar Yassir ta katse musu dogon kallon kallon da suke yi wa juna suna masu murmushi,mai cike da shauk’i da sak’onni.
Runtse ido Yashjub ya yi yayin da Manubiya ta yi saurin zare hannunta a cikin na Yashjub ta d’an matsar gefe kad’an.
“Babu alamar hankali ko sanin ya kamata a tsarin Yassir kwata kwata”
Ta fad’i hakan a k’asan ranta tana mai sake had’e rai sannan ta d’an chuno baki
Hakan da ta yi kuwa ba ta sani ba ba k’aramin burge Yassir ta yi ba…k’arasa shigowa cikin d’akin ya yi sarai ya lura da kallon mamakin da Yashjub yakeyi masa amman ya watsar da shi ya k’araso gaban su ya tsaya yana mai cewa
“Waenchan ne luggage d’in ko?bara in fara ragewa.
Antynmu Ina kwana”
Dakyar tace”lafiya” daga nan ta ja k’aramin trolley d’in da yake a gefenta ta fice daga d’akin.
A parlourn chan k’asa ta had’u da Yadira bata ko sake kallon inda take ba itama Yadirar haka bata kalleta ba bata kuma kulata ba.
Haka Manubiya ta fice ta Isa parking lot d’in gidan ta tsaya dan ba ta san a cikin motoci ukun a wacce za su fita ba.
Ta yi mamakin ganin har da Yadira a y’an kwaso kaya dan tana tsaye taga sun sauk’o gaba d’ayansu. Ba ta yi mamakin ganin Yadira ta fito da iyaka akwati d’ayan da ta zo da shi ba instead of biyu saboda dama ita ta san ba tafiya zatayi ba gaba d’aya kuma dama bata d’auka a ka ba k’ark’ari dai abunda ta sani shine bazata d’auki raini ba kowa ya tsaya a iya matsayin sa idan kuma ta ga rawar kan mutun ya yi yawa tou zata dawo da shi saiti,ta yi musu na bak’unta kafin ta gama sanin alk’iblar su yanzu kuwa tunda ta riga ta fahimta shikenan…
Bazata wulak’anta su ba ba za ta k’i su ba tunda dangin mijin ta ne amman fa bazata tsaya a taka ta ba.
Dole sai dai a yi mota biyu dan haka Yashjub ya bawa drivern d’ayar motar aka saka akwatin Yadira a ciki,su kuma akwatunan su a boot d’in motar da za su shiga..har zai
hana Yassir ya tuk’asu zuwa airport d’in yace kawai ya zauna shima a motar driver da Yadira sai kuma ya kyalesa
suka zauna a gaba su biyu Manubiya tana a baya…
Hakanan suka musu rakiya zuwa mallan Aminu Kano international airport,sai da sukaga jirgin su yana shirin boardin tukunna Yadira da Yassir suka nufi gidan Daddy
shi kuma drivern ya maida wa Yashjub motarsa guda d’aya ya fakata ya rufe harabar gidan da aka bar masa makullin ya kama gaban sa dan Yassir yace masa”kar ya damu zai ajjiye d’aya motar Yashjub d’in a gidan Daddy kawai.”
Yashjub so yake yi su dad’e sosai a tafiyar nan su fahimci juna da shi da matarsa dan ya san su Yasira har ma da Mommy ba za su ba su wannan chance d’in ba…Shiyasa ya riga ya gama tsarawa akan ba za su dawo kwana kusa ba sai sun huta sun sha soyayyarsu kafin nan kuma ya san inshaaAllah Daddy ya huce dan ya san yanzu haka ya sake hawa game da case d’in Yadira dan haka ba fahimtarsa zai yi a kan komai ba,shiyasa zai bar shi ya huce ya d’an yi nesa da su kafin su dawo ya samu ya taka wa y’an gidan su burki ba tare da Daddy ya ja masa layi ba,dan ba zai iya rayuwar da suke so ya yi ba ba zai zuba ido yana kallon hawayen matarsa a kullum saboda su ba dole a chanza tsari…
Kasancewar Airline na Cyprus ba ya zuwa Nigeria a ya sanya tafiyar ta su ta kasance da transit a Egypt dan egypt air d’in suka bi..
A babban hotel na Egypt suka sauk’a dama Yashjub ya san sai sun d’au lokaci ai kuwa ilai sai da sukayi awanni dan sai cikin dare wajajen 2 tukunna komai ya yi settling suka d’auki hanyar Cyprus.
Flight d’in su yana landing suna fitowa suka samu mota…
Tare suka saka kayayyakin a boot da shi da drivern daga nan suka d’au hanya bayan Yashjub ya basa adress d’in inda zai kai su.
Ita kam Manubiya ta yi laushi
shiyasa suna shiga motar da ya janyota ta gishingid’a a jikin sa sai bacci.
Sai da suka k’arasa tukunna ta ji ana tashin ta a hankali…cikin
kulawa kamar ya samu kwai haka yake lallab’ata yana tashin ta kamar baya so dan ba dan drivern na jiran su zai
koma ba da ba dalilin da zai
sanya ya tashe ta yadda yaga tana baccin ta peacefully ya san ba k’aramin dad’i baccin ya yi mata ba.
Tana bud’e ido suka yi ido biyu dan haka ta sakar masa wani lallausan murmushi kafin ta d’an gyara ta mik’e ta zauna
Cikin kulawa yace mata “mun iso bara in bud’e a rufe ne gate d’in.
“Tou” kawai ta ce.
Ta na jinsa da shi da drivern suka fita suna ta faman zuge gate sai da aka gama parking motar tukunna ya lek’o ya mik’o mata hannu yace “muje ko”
Jin jina kai ta yi a hankali kafin ta bi bayan sa suka fice daga bayan motar.dama tunda yace mata zai bud’e gate ta yi mamaki dan ita a tunanin ta za ta ga hotel ne amman sai ta ga gida flat mai d’ankaren kyau mai d’auke da d’an madaidaicin compound..
Murmushi ta yi suna fitowa dan gidan ba kad’an ba ya d’auki hankalin ta ya burgeta gashi dai d’an mitsitsi amman ya k’ayatu iya k’ayatuwa. Sai da driver d’in ya taya Yash suka gama kai kayan bakin k’ofar shiga drivern ya tafi ya rufe gate d’in tukunna ya dawo.
Yana zuwa ya sunkuya ya d’auke ta in a bridal style
Murmushin ta yi ta zagaye hannunta a wuyansa,a haka suka k’arasa bakin k’ofar..
Tumb d’in sa ya saka wata murya tayi welcomin d’in shi had’e da fad’ar sunan sa daga nan ya tura suka shige cikin k’ayataccen parlourn
Saida ya kai ta kan