Showing 24001 words to 27000 words out of 244445 words
kallonta tana goge hawayenta kafin ahankali cikin sheshshek’a tace’’yi hak’uri dan Allah’’sai kuma ta sake rushewa da kuka.
Wani irin tausayin Mommy ne ya lullub’e Baaba Larai tashi guda..tun suna yara ita kanta ta san abunda yake saka Mommy kuka ba k’arami bane,shiyasa yanzun da ta ga tana kuka ta sake tausaya mata ta tausaya musu ta kuma yi wa kanta alk’awarin inshaaAllah ba za su kwashi kashin su a hannun ba….
Ahankali ta sa hannu ta janyota jikinta ta yi hugging nata ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi.
Kamar zuga Mommy ake haka ta shiga rera kuka kamar jira takeyi,cikin kukan ta fara magana tana cewa’’Larai na gaji,kuma na sad’akar,dan na san tunda har aka kai kud’i aka saka rana kuma matar nan ta riga ta zo to kamar an yi auren Yash ne an gama…shikenan mun yi failling we fail flat on our faces Larai!.
Sannan ga zuwan matar nan bana son ta a cikin gidana mutuwa zan yi Larai bana son ganinsu a cikin gidana zuciyata za ta buga ban san da wanne zan ji ba Larai abun ya yi yawa duka ta ko’ina ban san wanne zan tare ba…..’’
Ganin yadda take magana out of pain ne ya sanya Baaba Larai ta zaro ta da ga jikinta cikin sigar lallashi tace’’ban san mai zan ce miki ki sake yarda da ni wannan karon ba amma inaso ki yarda da ni ki yi putting trust d’inki in me inshaaAllah ba zan sake baki kunya ba,ni na san mai zan yi wannan karon ba za mu yi failing ba inshaaAllah ba za ayi auren ba not in 9days time not forever!
Sannan itama Hajiya Mama inshaaAllah sai sun koma inda suka fito da yardar Allah dan ba zan zuba miki ido in barki a hakaba ba zan iya ba y’ar uwata sannan ba zan zuba ido ina gani ake ci miki kashi a cikin gidan ki ba!sanann ga shi daga zuwanta na lura so take ta yi wa mutane handsfree a gaban idon kowa’’…
Gyara sosai Manubiya take sha dan a cikin cikin kwana d’aya da aka yi mata sau biyu safe da rana kawai har ta fara chanzawa in banda kamshi ba abunda yake tashi daga jikinta,fatarta har ta fara sumul sumul da yellow ta na d’aukar ido.
Yanzun ma na uku aka yi aka gama dan Mama ta ce ba su da lokaci dan haka a dinga yi
akai akai tunda ba su fara da wuri ba,ana gama gyaran jikin ta fad’a wanka tana fitowa kuma ta sake zama a kan kujerar tsugunno ba dan ta so ba sai yadda taga Mama ta dage akan sai fa ta sake zama a cewarta ‘’d’azu tana sane da ita ba ta zauna sosai ba ta fake da cin abinci’’,dariya duk suka yi har Manubiya wadda take Allah Allah ta yi ta shirya dan ta san anytime from now zai iya zuwa saboda ce mata yayi da yamma,already Jidda ta tambaya mata su Baba sun bata go ahead amma sun ce ta tafi da d’an rakiya shiyasa tun d’azu ta cewa Muhsin ya shirya.
Sai da ta kusan sakawa Mama kuka tukunna ta yarda ta ce shikenan ta tashi tana ta yi mata tsiya tana ce mata’’raguwa’’daga haka ta yi musu sllama ta tafi dan tana so ta je itama ta d’an huta.
Manubiya ta na tashi ta nufi wardrobe ta zaro kayan da za ta zata saka tukunna ta zauna ta shiga shiri…mai gyaran jikin tana gama shirin tafiya dai dai ita itama ta gama shirin ta kenan,kiran Yashjub ya shigo wayarta.
Dama wayar tana hannunta yau kam babu wani maganar jan aji dan ita kanta kawai gani ta yi ta d’auka ta kara a kunnenta…..shiruuu ta ji ya yi da farko kafin chan ta ji yace‘’Ina k’ofar gida.’’
Da kyar ta iya cewa ‘’tam’’daga haka ta kashe ta k’arasa wajen inna ta d’an durk’usa ta gaya mata daga nan ta mik’e ta d’auki mayafi me kyau da girma da kauri sosai ta d’aura akan doguwar riga y’ar kantin dake a jikinta.
Har za ta fita sai kuma ta dawo ta k’ara turare har da d’an lipstick pink ta d’an goga sannan ta gyara zaman hular ta,ta na juyawa suka had’a ido da inna dan haka gaba d’aya duk sai kunya ta rufeta,da sauri ta juya da niyyar cewa Jidda Ina Muhsin yayi amma sai suka had’a ido da shi ya d’ago labule,dan haka ta yi gaba bayan ta ce musu ‘’sai sun dawo‘’suka fita ita da Muhsin da mai gyaran jiki….
Suna fita ta yi mata sallama
ta wuce ita kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 10
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Suna fita ta yi mata sallama
ta wuce ita kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su.Dukda ba ta riga ta ga na ciki ba dan motar tinted glass gareta amma tashi d’aya jikinta ya bata shine.
A b’angaren Yash kuwa tunda ya zo ya yi parking a k’ofar gidan yake sake k’arewa gidan kallo yana sak’e sak’e a ranshi…tun ranar farko da suka zo shi da Najeeb yake tunanin ta yadda zai siya musu gida su yarda su karb’a dan ya san tabbas da wuya su amince da hakan,amman zai gwada ya gani saboda har ga Allah daga arean har gidan basu kwanta mishi ba,a take tashi d’aya tausayinta da k’imarta suka lullub’e shi
a ranshi yace’’yanzu a nan ta girma ta yi wayo amma kalli yadda abun duniya da kwad’ayi sam ba su rufe mata ido ba.’’
Yana wannan tunanin ya ganta sun fito su uku,sun yi wa d’ayar matar sallama ta wuce ita kuma sun tsaya itada
Muhsin.
Murmushi ya yi kafin ya d’ago wayarsa ya shiga kiranta so yake ya ga yadda za ta yi shiyasa ya k’i fitowa balle ma taga inda yake,tana d’auka kamar d’azu yace’’ki shigo mana’’kawai.
Shiruu ta d’an yi sai da ta ji yace’’Come in pls’’tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta kashe wayar suka nufi motar ita da Muhsin.
Su na zuwa ta bud’ewa Muhsin gidan gaba,sai da ya shige ya zauna ta rufe masa tukunna ta nufi baya ta sa hannu a kan handle d’in.
Dariya sosai ce ta ke tasowa Yash wanda yake zaune a gidan baya,dama ya san hakan za ta yi tun lokacin da ya ga sun fito ita da Muhsin he just can’t wait ya ga reaction d’inta idan ta shigo gidan baya suka yi ido biyu da shi,yana wannan tunanin yaga ta d’aura hannunta a kan handle d’in dan haka ya yi saurin matsawa ya bud’e mata tun kafin ta murd’a.
Ta d’an yi mamakin ganin yadda k’ofar ta bud’u tun kafin ta murd’a amma sai ta yi tunanin maybe Yash d’in ne ya bud’e mata ta gaba inda yake zaune.
K’amshin mayatacccen turarenshi da sanyin ac ne suka fara yi mata sallama,har ga Allah sam ba ta lura da shi a ciki a zaune ba dan motar da d’an duhu,sai da ta d’an sunkuya ta shiga ta zauna ta
mayar da k’ofar ta rufe tukunna ta d’an zabura ta d’ago ta kalleshi sakamokon kamshinsa wanda ta ji ya k’aru sosai a cikin hancinta da kuma alamun mutum da ta ji a zaune a gefen ta.
Suna had’a ido ya yi mata gwalo yana mai jin kamshin da take yi yana shirin zautar da shi da kyar k’asa k’asa ta yadda ya tabbatar ita kad’ai ce za ta ji yace’’an guje min kuma anzo an taddani,a clear reminder to you wifey’destiny will forever bring us together,har abada muna manne da juna InshaaAllah’.’’
Shiruu Manubiya ta yi dan ita ta ma kasa magana,sam tunaninta bai sa ta tuna da hannunshi ba sai da suka yi ido biyu da shi ta kalli hannun tukunna ta tuna ba fa zai iya tuk’in ba.
Ahankali ta d’ago ta d’an kalleshi kafin tace’’Ina wuni’’
Da kyar ya iya cewa lafiya idanunsa a kanta yana mamakin mai ya same ta haka da ta k’ara wannan azabb’en kyan cikin k’ank’ani lokaci a gefe guda kuma na zuciyarsa yana jin takaicin kasancewar drivern da ke gaba da ke a cikin motar dan ya san shima tabbas ya shak’i wannan sumamman k’amshin da take ta zubawa,addu’ar sa d’aya kar yazo gaisheta yace zai juyo ya k’are mata kallo dan arayuwarsa bayason abunda zai sa ake kalle masa ita balle yanzu da shi kansa yake jin numfashin sa yana shirin d’aukewa…..yana cikin wannan tunanin yaji ta cewa drivern’’ina wuni’’
Cikin girmamawa da yin k’asa da kai drivern ya gaisheta ba tare da ya juyo ba daganan ya kunna motar bayan Yash ya fad’amasa Ina suka nufa,suka d’au hanya…..
Dukda drivern ne ya kamata ya gaidasu amman sai Yash ya ji dad’in yadda Manu da Muhsin suka girmama dattijon mutumin dan ko Muhsin ma bayan sun gaisa sai da ya gaida drivern shima,hakan ya nuna sun san girman d’an Adam da farin gemu unlike su Yasmeen.
A k’ofar shagon wata shaharariysr mai d’inki suka yi parking kafin drivern ya kashe motar ya fita haka ma Muhsin,bai yi gigin bud’e musu ba dan bai san ko za su tattauna ba kafin su fito dan haka ya koma gefe ya ja ya tsaya haka shima Muhsin.
A hankali cikin wata murya kamar ta wanda ba ya son yin magana yace’’mu je ko?’’
Jin jina kai ta yi tukunna ta sa hannu da niyyar bud’ewa amma sai ta gagara,ta juyo da niyyar yin magana ta ga ya bud’e side d’insa ya fita ya zagayaya.Da kansa ya bud’e mata dan ko da drivern ya matso ma d’aga masa hannu kawai ya yi ya tsaidashi.
Ahankali duk tanajin kunya da nauyi sun lullub’eta haka ta sa k’afa ta fito,sai da ta gama fitowa tukunna ya rufe marfin motar ya ja mata mayafinta daya d’an zame yana shirin sauk’a da ga kanta tukunna suka nufi k’atoton shagon suka bar driver cikin tsananin mamakin yau Oga ya zama driver!amma har ga Allah ya ji dad’i kuma sun matuk’ar burgesa,hatta Muhsin ma da yake Yaro sai da suka burgesa,bai bisu har ciki ba ya tsaya a wajen driver suka shiga hirar su.
Suna shiga wajen taga ashe har ya bayar da kaya wajen kala ashirin majorments d’inta kawai ake buk’ata…dan haka suka shiga wani d’aki matar ta aunata aunin kwakwaf dan ba abunda ba ta gwada ba saboda wai za’ayi d’inkin nikkah wanda zai yi fitting ragowar ma duk ana so su yi fittng tunda a lefe ya ce mata za’a saka so kayan dole su fito rasss!!!hakanan ta yi ta janta da hira dan matar professional tailor ce
mai kirki kanta a waye shiyasa kamar za ta goya ta.
Manu ta ji dad’in yadda Yash ya yi respecting decision d’inta dan tunda ta ji matar tace ‘’iyaka d’inkin nikkah,ragowar kuma na lefe” to ta san ya yarda shi da y’an gidansu babu wani event d’in da za su yi kenan.
Ba bu maganar deposite dan Yash complete ya juyewa matar kud’in d’inkunan kaff a account,har suka fito suka shiga mota suka fara tafiya kan Manubiya bai daina juyawa ba…sai da aka tura kud’in tukunna ta ji amma wallahi ba dan haka ba to da ba za ta yarda a yi wannan uban b’arnar kud’in a iyaka d’inkuna ba….
Ba gida suka koma ba wajen jewelries da shoe and bag d’in da za ta yi amfani dashi sukaje
suka sissiya,daganan
suka biya mudassir,ya riga ya sayi komai amma akwai d’akin dama da ya ware akan itace za ta zab’a da kanta sai kuma deco da kayan kitchen da yake da bukatar ta k’ara choices d’inta akan waenda ya sissiya,shiyasa ya kaita ya ce ta tayashi zab’e dan ya kasa..
Siyayya sosai kuwa suka yi dan har sai da ta fara tunanin maybe ko harda iyayenshi zai chanjawa kayan kyale kyale da kitchen saboda bikin dan uban kayan da suka d’iba wasu aka yi order abun ba ‘a cewa komai.
Tabbas ta yi mamaki matuk’a
amman da ta tuna yawan estates d’in shi da business d’in da yake yi sai
taga kud’in da suka bata tsoro waenda suka kashe a iyaka yau kad’ai ba komai bane a wajensa.Ta san Yash yana sonta kuma ta san so gaskiya ne amma yadda taga yake rawar k’afa da waensu abubuwan duk akanta wasu lokutan har tsoro da mamaki takeyi…duk wani kud’i! dukiya!class! ajjiyewa yakeyi a gefe
ya sauk’ar da kanshi k’asa sannan ya kawar ya goge the fact that ‘she and him sam class d’insu ba d’aya bane’.! Yadda yake treating d’in ta a gaban kowa da koina kamar wata queen tabbas hakan yana bata alajabi,gashi dai ya san itan ma tana sonshi
ballantana tace ko campaign yake yi….Tabbas ta yarda ta amince she’s fortunate infact she’s morethan fortunate…….
Sai chan dare tukunna suka d’auki hanyar gida bayan ya loda na lodawa ya kira wani driver d’insa ya yi assigning an tafi kai kayan da za a kai gidan amarya…ta gaji lik’is dan haka ta na gishingid’ewa bacci ya kwasheta.
Ahankali ya d’an tab’o Muhsin wanda suke ta hira da drivern dan har sun saba sosai kamar wasu sa’anni,sai da ya juyo tukunna Yash ya d’aura yatsarshi akan bakin sa alamun su yi shiru kar su tasheta,jinjina kai Muhsin yayi ya juya yana murmushi bai gama sanin meye so ba amman yana jin dad’in yadda ya Yash ya damu da Addar su,shima drivern ya gani kuma ya fahimci mai Yash yake nufi shiyasa ya yi shiruu ya bada himma a tuk’in da yake yi.
A hankali kamar mai shirin d’aukar cracked egg haka Yash ya d’auki wata suite d’insa dake a cikin jakar kujerar driver ta baya ya d’an matsa kusa da ita kad’an ya lullub’a mata dan ya lura ba ta son sanyin.
Manu bata da nauyin bacci
shiyasa yana rufa mata ta farka amma ba ta bud’e idanunta ba…ta ji dad’i a ranta,duba da yadda yanzun suka gama fad’a kuma yayi fushi da ita amma kalli yadda yake kula da ita,ba ta son yin fad’a da shi amma ta lura idan ba hakan ta yi masa ba to ba zai hak’ura ba ba zai bar maganar ba!. Saboda Allah ta ya dan su Baba sun aura masa ita sai kuma kawai aga sun kwashe kaya su koma gidan da ya ce ya basu,a ganinta hakan ba dacewa bane ba,ta san sun zama family amman kuma idan suka yi haka ai sun sake da yawa,idan ma zai basu gida gaskiya ba yanzu ba besides ta san ma Baba ba zai tab’a yarda ba…
Tana wannan tunanin ta ji an yi
parking an kashe motar,ta na ji Muhsin ya yi musu sai da safe da godiya ya jidi laidojin gabansh ya fita dan haka ta yi saurin bud’e idanunta dan ta lura ba shi da niyyar tashinta,dai dai nan drivern ma ya fita kenan..da sauri tace’’mun gode sai da safe daga haka ta fara kokawa da shegiyar handle d’in da ta rasa dalilinta na k’in bud’uwa a koda yaushe idan ta ja.
Murmushi ya yi kafin yace’’kar mu rabu muna fad’a mana,ai tunda kin nuna bakyaso ba zan sake yin maganar ba,amma ki yi tunani akai pls’’
Jin jina kai kawai tayi ta ci gaba da k’ok’arin bud’ewa
Murmushi ya yi yace’’ba fa za a bud’e k’ofar nan ba sai kin yi min murmushi.’’
Jin tayi shiru yasanya cikin wata kalar kasalalliyar murya ya ce’’kin san Allah zan yi miki cakulkuli’’
Sai da ta zabura sosai kamar ya riga ya yi mata cakulkulin tukunna ta juyo kamar za ta fashe da kuka tace’’dan Allah ka yi hak’uri,dare fa ya yi ka bud’e min’’
Ganin yadda ta fara fita a haiyyacintane ya sanya ya fahimci kad’aicewar nasu ne ba ta so,dan haka tashi d’aya ya sa hannu ta gaba ya bud’e mata sannsn ya bud’e tashi k’ofar ya fice da niyyar za gaya wa domin ya bud’e mata amman tuni ta yi wuff ta fice dai dai shikuma ya zagayo,tashi d’aya ya ji ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi
y’ar tsere,murmushi kawai ya yi yana mamakin yadda daga sun zauna a mota iya su biyu duk ta bi ta gigice a ranshi yace’’Yarinya za ki yi bayani ne’’.
Duk taurin kanta kuwa sai da ta yi masa murmushin nan tukunna ya kyaleta.
Da shi da ita da driver suka yi jidon ragowar siyayyar da ya yi mata har soro ya ajjiye mata
yana sake mamakin gidan tukunna ya bata wata jaka mai d’an karen kyau yace”invitation ne a ciki ta bawa su Baba zai turo mata na waya ma sai ta tuttura shi kam ba wanda bai riga ya turama a cikin friends d’insa ba”
Karb’a ta yi tana mamakin zumud’i irin na Yash kafin yayi mata sallama
suka rabu yana jin kamar ya d’auke ta su koma.
Tabbas inda ace irin wata d’aya d’in nan aka saka aurensa da Manubiya tou da sai ya bai san ya zai yi ba kafin ta zo….wata kalar zazzafar k’aunace ta ke d’awainiya da shi the more yana getting to know her the more k’aunar ta take sake dagargaza mishi lisaafi! tunani! da zuciya…..
Sai da ta zo shiga kuma tukunna ta fara fara kame kame,ba k’aramin dad’i ta ji ba da bata ga Baba a d’akin ba,amma dukda haka sai da ta d’anji nauyi dan kasa had’a
Ido ta yi da inna illa kawai sai
taje ta durk’usa ta gaida ita daganan ta cewa Jidda ta zo ta tayata d’aukar kaya dan Muhsin yana shigowa ya fad’a toilet.
Ahanya take tambayar Jidda ko su Baba sun yi fad’an daren da ta yi amman sai ta ji jiddan tace mata a’a besides ai ba ta yi dare sosai ba.
Sai a sannan ta sake,su ka kwashi kayan suka kai ciki.
Sai da Jidda ta je ta kira Siyama tukunna hankalinta ya kwanta,tare suka ware ledojin da komai,ita Manubiya sai da suka ware ma tukunna ta ga gift d’in Muhsin(agogo mai tsananin kyau na maza)da wayar da ya saka mata ba tare da saninta ba
iPhone mai kyau k’irar wadda ake yayi,shiyasa a take ta kirasa domin ta yi masa godiya har