Showing 126001 words to 129000 words out of 244445 words
ajiyar zuciya yace”Allah ya tsayar a iya ka hakan…”
Ahankali tace “ameen” hankalinta duk a tashe.
Cikin ruk’ota izuwa jikinsa yace”sannan kar ki damu businesses d’ina have been successful tun farkon shekarar nan har kawo yanzu dan inaga na samu abunda zan iya gina estate d’in ma biyar…ban saka komai a raina ba na karb’i k’addara.
Ko da ace ban samu income da ci gaba a business d’ina ba to banga dalilin da zai sanya in ji takaici ko in shiga damuwa saboda na rasa estate ba.
Ubangiji na ya yi mini ni’imomi masu tarin yawa a wannan shekarar…kinga na farko ya bani ke har da k’aruwa gashi mun samu,sannan abubuwa na da business d’ina sai bunk’asa suke yi
kina ganin dan estate guda d’aya ya k’one zan ji haushi?ai ya bani abunda ya fi estates dubu Baby tun da na same ki”.
A hankali Manubiya ta tafi jikinsa ta kwantar da kanta a kan k’irjinsa ta yi shiruuuu.
For the second time ta ji ya sake cewa “ki yi hak’uri a kan abunda Mommy ta yi miki dan Allah’’
Ahankali tace ‘’ba komai fa,iyaye basa laifi,sannan kai a matsayin ka na Mijina ka daina bani hak’uri ka fi k’arfin haka a waje na.”
Shiruu duk su biyun sukayi kowa da abunda yake tunani..
“Dan Allah ka kaini in ga Baba’’
Muryar Manubiya ta katse masa rikitaccen tunanin da yake yi.Shiru ya yi dama wallahi ba dan Mommy ta tambaya ba da ba zai fad’a mata ba
Su kansu su Innaa cewa suka yi kar ya gaya mata saboda kar ta d’aga hankalin ta.
Muryar ta ce ta sake katse masa tunani jin tana cewa
‘’Dan Allah” a hankali kamar za ta fashe da kuka.
Numfashi ya fesar kafin ya sake rungumeta da kyau yace’’ok zan kai ki amma maybe sai gobe kinga kema baki da lafiya yanzu bara in kira Doctor ya fara duba mini ku tukunna kin ji
ki kira su a waya kar ki sa damuwa zai samu sauk’i inshaaAllah….’’. Sai da ya lallab’a ta sosai tukunna da kyar ta hak’ura a kan goben za ta je dan haka ta d’au waya ta shiga kiran su ,ya ji sun yi magana da Jidda da Inna har ma da Siyama amma bai ji sun yi magana da Ya Musbah wanda tun da ya je gidan kafin su tafi kai Baba asibiti ake ta kiran sa yana cewa”gashinan zuwa”shiruu ya yi sai da ya gama had’a one plus one tukunna ya kalli
Manu yace mata “Ya Musbah bai je bane??har yanzu?”.
Diriricewa ya ga ta d’an yi dan ita kanta lamarin na Ya Musbahu ya fara d’aure mata Kai dan a bayanin Jidda ta fahimci su hud’u ne kawai a wajen Baban yanzu haka gashi idan ta kira sa a waya ba ya d’auka
Dukda shima yana fama anada tasa damuwar amma haka ya daure ya danne tasa cikin nutsuwarsa ya sake ce mata “akwai wani abun ne?is there anything I can do to help?saboda jinin Baba fa ya hau ne sosai”.
Tashi d’aya tun kafin ya gama rufe bakinsa ta fashe da kuka,cikin kukan tace “dan Allah ka kai ni in gansa”
Numfashi ya fesar yace”to bari in kira Doctor ya zo ya duba min ku,tukunna sai in ga ko zai iya barin ki ki fita yanzun”
Daga haka ya mik’e ya fice yana ganin dishi dishi tsabar tension…
Yana fita ta kira Jidda shi kuma ya na fita Ya Nafi’u ya kira dan tabbas ya lura family d’in Manu suna cikin damuwa…
Da farko ya Nafi’un b’oye masa yayi sai da Yashjub d’in ya nace tukunna ya zaiyyane masa komai halin da ake ciki,halin Baraka da yadda ta janye Ya musbah da kuma yadda y’an uwan Baba suka sako shi a gaba..ba su ajjiye wayar ba sai da suka yi wa tufkar hanci daganan suka yiwa juna sallama bayan ya Nafi’u ya yi wa Yashjub alk’awarin zai sanya Baki ya lallab’a su Baba su yarda su k’arbi gidan da Yashjub d’in ya basu su koma..
Ba k’aramin lallashi likitan ya yiwa Yashjub ba da ya ji batun Manu har ta suma amma ba su sani ba,ya san ba laifin sa bane ko na nurses tunda sun gama yi mata allurai kuma ita da Mijinta suka barsu a d’akin sannan da aka zo fita ba a kira kowa ba amma hakanan ya yi ta bawa Yash d’in hak’uri dan ya lura ran sa a b’ace yake.
Dama ba so yake yi ta fita d’in ba aikuwa likitan yana zuwa da ya duba ta yace”ba zai yiu ta fita yau ba gaskiya jikin ta ba kwari”…
Hakanan da kyar ya samu ya sake lallab’ata ta hak’ura dan jikinta duk ya yi sanyi daga wayar data gama yi da Jidda yanzu
Dan Jiddan ta gaya mata komai itama…….
Yahanasu Yash ya kira ta zo
ta zauna da Manubiya yayinda shi kuma ya nufi estate d’innasa….
Sai da ya je Estate d’in nasa tukunna ya ga abunda ya faru da b’arnar da aka yi,tashi d’aya zuciyarsa ta aminta da zargin da yake ta yi tun d’azu ‘tabbas kashesa ake so a yi’ shi aka so a akashe da basaja sai Ubangiji ya kub’utar da shi kuma wannan aikin na jikin sa ne yake yi,da kunce masa tayar mota da aka yi da incidence d’in dole sai na jikinsa wanda kuma ya san shige da ficen sa ne zai iya yi,but who could it be???dan zuwa yanzu ya fahimci ba Kausar bace ba,wannan aikin sai dai aikin gayya ko kuma kwararren tantiri tunda har da y’an fashi a lamarin…gabansa ne ya yanke ya fad’i a tashi d’aya ya yi istighfari da ta’auzi dan kamar yadda d’azu kwakwalwarsa ta basa ‘Mommy ce ta turo Yasmeen ta yiwa Manubiya allura,’hakanan yanzu ma lissafinsa ya basa’ita da Kausar maybe da ko Yasira ne suka yi wannan aika aikar dan aikin ya wuce b’arnar mace d’aya’
Cikin runtse idanunsa ya shiga kokawa da zuciya da kwakwalwarsa dan sam bai ga ta inda mutuwarsa za ta zamo riba wa Mommy ba….ta ya ma zai yi tunanin hakan ita fa ta haifesa.
Still shi da kansa a cikin zuciyarsa yace”amma fa some facts cannot be denied,a iyaka d’azu kad’ai ya fahimci kamar ba ta tab’a shiga fushi irin na yau ba,ta ya za ace d’anki ya kusan mutuwa amma da kika gansa ya dawo safe and unharmed kwata kwata ba ki yi
farinciki ba instead sai fushi da bak’in ciki…kamar tana fushin ganin plan d’insu bai ci bane shiysa ta fusata ta kasa controlling kanta…..but y?me yasa suke son kashe sa me za su yi achieving?
A take zuciyarsa ta shiga aiyyana masa tana yi masa flashing yadda ba sa son Manubiya! kenan za su kashe sa saboda sun kasa raba sa da Manubiya kenan? Da sauri ya bawa kansa amsa ta hanyar cewa”noo it doesn’t make any sense!.”
Bai san lokacin da hawaye suka shiga ziraro masa ba yana mai jin wani irin yanayi na tashin hankai da bak’in ciki da rud’ani a ransa ya ce”Mommy ba za ta iya kashe ni ba but duk wata alama tana mini nuni ne da tsaf za ta iya aikata hakan….tun ba yau ba ya san ba ta sonshi sannan tunda ya d’auko maganar aure abubuwa suka sake tab’arb’arewa,ga kuma abunda ta yi yau.”
Rud’ani rikici da kuma rashin sanin gaskiyar lamari ne suka sanya ya runtse idanuwansa da mugun k’arfi still a cikin ransa yace “i’m definitely missing something here…akwai abunda ban gani ba kuma ban sani ba!what is it????”.
Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya san mai basa amsar ba!.
Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e ya dafa sa ganin yana hawaye sannan ya runtse idanuwa yace”Yash sai hak’uri fa!na san me kake tunani amma ka kwantar da hankalinka ka ci gaba da addu’a bawa bai Isa ya yiwa bawa abunda Ubangijinsa bai yi ba”
A hankali ya bud’e idanunsa da suka koma kamar garwashin wuta ya zuba su a kan Najeeb
Jin jina kai Najeeb ya yi yace”yeah tun Akan incidence na accident d’inka na fahimci akwai wanda yake harin rayuwarka kawai na yi shiru ne saboda na ga kaima ka sani amma ba ka son tada maganar,yanzu kuma duba da yadda motarka tana shigowa suma suka baiyyana suka rufe gate suka fara kashe mutumin suka kunna wuta,ya sanya na sake tabbatarwa…amma kar ka damu a hankali zan taimaka maka za mu yi bincike ko dan rayuwakan mutane kusan d’ari da aka b’atar inshaaAllah za a kama whosoever is behind it…..
“A hankali jikin Yashjub ya fara kararwa duk yadda ya so hana kansa yin kuka sai da hawaye suka balle masa sosai..yanzu a ta dalilin sa aka kashe duk waennan mutanen….how can he ever forgive himself??
Ga kuma zargin Mommy da yake yi wanda ya sake hautsina sa…MANNUBIYA
(Book 2)
Page 30
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Duk yadda Yassir ya so ya jira ya d’an saisaita kansa kafin ya fuskanci Kausar kasawa ya yi…ba ya so ya tunkare ta yanzu dan tabbas zai iya illatata amma kuma zuciya da bak’in cikin rashin samun nasarar kashe Yashjub da kuma kishi ne suka k’i su barshi ya jira d’in dan haka kawai ya nufi gida gadan gadan.
A b’angaren Kausar kuwa
A rikice ta shiga gidan itama
sakamokon wani amai mai k’arfi da ya hanata sukuni yake ta faman yunk’uro mata…ta na shiga d’akin ta kuwa ya taho da mugun k’arfi..
Da gudu ta nufi toilet amman tun kafin ta k’arasa ta fara sakinshi.
Ta jima tana yi kafin ta samu ya d’an sarara mata ta shiga mayarda numfashi…Yanayin k’arnin aman ne ya firgitata ya tsoratata,haki ta shiga yi tana addu’a a lokaci guda ta shiga hargitsa toilet d’in tana neman pts.
Da ikon Allah kuwa ta samu
dan haka ba ta yi wata wata ba ta auna kanta.Bata iya ajjiyewa lokaci ya cika ba hakanan ta shiga safa da marwa a cikin band’akin da abun a hannunta idanunta kyam a kai,gaba d’aya ta hargitse ta ma rasa tunanin me za ta yi…tun da take ba ta tab’a
jin tsoron shigar ciki da fargaba da tashin hankali kamar na yau ba!.
Aikuwa tashi d’aya ta fara ganin alamun positive…kafin ma ya gama tabbatar mata da hakan ta fashe da wani irin kuka ta durk’ushe a wajen tana kallon yadda abun yake yi mata nuni da tana d’auke da ciki ne.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
ta shiga maimaitawa a cikin zuciyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita…..
Ganin kuka ba zai fishsheta ba ne ya sanya ta share hawayenta ta mik’e jikinta yana wani irin karkarwa ta ajjiye abun ta shiga lissafin neman mafita.
Tashi d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji dan haka ta fito ta nufi side d’in Mommy jikinta har yana wani Irin karkarwa.
Su Mommy suna isa gida ta wuce sama d’akinta,Baba larai tana ganin haka ta bita da sauri…
Sai da ta kai k’ofar d’akinta tukunna ta lura da Baba larai dan haka tace”larai ki je kawai ina buk’atar space..”
Daga haka ta bud’e ta shiga tana k’ok’arin rufowa Baba larai ta sa hannu ta tare k’ofar ta shiga ta rufo,Mommyn tana shirin yin magana ta ji Baba larai tana cewa”Khadija zama na a cikin gidan na ya k’are dan haka na zo ne in yi miki sallama sannan in gaya miki abunda ya faru da kuma taimakon da na yi miki d’azu wanda ya taso na gaggawa.Daga nan ni kam yanzu ba sai anjima ba zan tafi!”.
Runtse idanuwa Mommy ta yi kafin ta bud’e tace”dan Allah Larai ki barni in huta tukunna we’ll talk anjima..”
Cikin tarar numfashinta tace “Au wai a tunaninki barazana ce nake yi?…wallahi wallahi na gama sakawa a raina Khadija barin gidan nan zan yi! Dan ba zan zauna rashin hak’uri da rashin lissafinki ya kaini prison ba!.Bari ki ji abunda ba ki sani ba d’azu kuna fita na ji Daddy yana waya,ko kin san wanene ya kirasa?”
Kallonta Mommy ta yi tukunna tace”A’a”
Sai da Baba larai ta sake ce mata “kin san wa ya kirasa?”Mommyn tace “a’a”
suka yi haka sau uku tukunna Baba larai tace”Mallan lawal!”
Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Mommy ya yi kafin cikin in Ina tace”mme yya ce mmasaa??”.
“Cewa ya yi yana son magana da shi inaga,dan ji na yi yana cewa”mallan lawal dama kana raye Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” sai kuma ya fara basa hak’uri kafin na ji ya yi shiru yana sauraronsa sai
kuma yace na godewa Allah nauyi d’aya ya sauk’a a kaina mallan lawal amma ba za ka iya gaya mini ta waya ba dole sai na zo??”
Daganan na ga ya fice compound ya nufi parking lot, to inaga case d’in Yashjub ne ya tsayar da shi ba dan haka ba da tuni yanzu yana garin Garin Mallan……
Cikin takaici Baba larai ta d’aura da cewa“wallahi Khadija in da ace ba ki tsaya dawo mana da aiki baya ba da tuni ba mu zo nan ba!,na gaya miki Yarinyar nan barinta tare da Yashjub masifa ne a gareki amma kin k’i ki bada goyon baya a samu a fitar da ita daga rayuwar tasa cikin sauk’i yanzu ga irinta nan! Idan kika ga yadda hankalin Daddy ya tashi ya rud’e za ki yi mamaki lokacin da ya ji mallan lawal yana a raye…kin san yanzu zai fara wasu wasin mutuwar Khadijah ko?”
A mugun rikice Mommy tace”larai shiyasa tun a lokacin na ce a kashe su kika ce A’a za ki san yadda za ki yi dasu yanzu ga irinta nan ai”
sai kuma ta fashe da kuka cikin gunjin kuka tace”wannan duk ba laifin kowa bane laifin Manubiya ne ita ce wallahi tun da ta zo ta lalatamin komai larai na gaji kashe Yarinyar nan zan yi wallahi kuma ba ki isa ki hanani ba…”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”ba za a yi haka da ni ba,in da ace zan barki ki kashe rai da tuni mun yi tun a kan Khadija..hak’uri za ki yi ki kwantar da hankalinki ki danne zuciyarki tukunna ki ci riba ba zan tab’a gajiya da gaya muku da ke da su Yassira ba saboda hakan ne kad’ai mafita”.
Cikin wani irin kuka Mommy tace,Baba larai yanzu to
ba Manubiyan ba,shi mallan lawal d’in Baba larai mun bashi second chance amma kinga yanaso ya tona mana asiri na rok’e ki da giraman Allah ki taimaka mini ki rufa mana asiri a kawo k’arshen sa dan wallahi na san gaskiyar lamari zai fad’awa Daddy idan har suka had’u if not menene zai sa yace yana son ganinsa?…”
Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”kar ki damu..Daddy yana fita na kira mutumin da muka ce ya saka mana ido a kansa,ashe ciwon hanta ne ya ke damunsa likita yace ba shi da sauran lokaci shiyasa yake neman Daddyn ya samu ya gaya masa gaskiya.”
Numfashi ta fesar kafin ta ci gaba da cewa”tunda dama mutuwa zai yi shiyasa kawai na cewa mutumin ya k’ara masa gudu zamu bashi naira miliyan d’aya,to dai a halin yanzu Ina tabbatar miki mallan lawal ya tafi kai balance dan mutumin a lokacin ce mini ya yi a take zai aiwatar da aikin dan gidan dama ba kowa shi mallan lawal d’in ne kawai da shi da jikarsa ita take jinyar sa to alokacin ya ga ta tafi kasuwa……yanzu miliyan d’ayan za a tura masa dan naga ya kirani d’azu Ina asibiti shiyasa ban d’auka ba.!Muna tura masa ni kuma zan kama gabana dan ba zan zauna ki ci gaba da lalata m….”
Cikin Jin dad’in maganganunta Mommy ta rungume Baba larai wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa abunda take cewa,wani kuka Mommy ta fashe dashi tana cewa”na gode Larai na gode sosai ki bani accnt number miliyan biyu ma zan bashi wallahi….sannan zan gyara wallahi zan yi yadda kike so dan Allah kar ki sake cewa za ki tafi.”
Da kyar Mommy ta lallab’a Baba larai ta hak’ura da tafiya,daganan suka kira mutumin ya shaida musu cewa”Mallan lawal yana ma shirin shiga k’asa a halin yanzu dan wanka ma ake yi masa.”
Naira miliyan biyu Mommy ta tura masa a take daga nan ta nutsu tana sauraron hud’ubar Baba larai.
Da sallama Yasira ta turo k’ofar d’akin ta shigo,kafin ta k’araso ta zo ta tsaya a gabansu.
Kallonta kawai Baba larai ta yi ta maida hankalinta ga Mommy kafin tace”a baya da kika iya kwantar da Kai wacce kalar riba ce ba ki ci ba?yanzu kuwa kinga ai komai lalace miki yake yi saboda rashin tunani da lissafin da kika bawa ragamar rayuwarki,kuma bari ki ji ba ni da tantama a yau Yash ya dasa ayar tambaya a kanki wallahi saboda abunda kika yiwa Manubiya a gaban kowa ya na nuni ne da kin tsaneta dama tun asalin farko wanda hakan zai sanya ya fahimci dama chan pretending kike yi kuma bakin ku d’aya ke da su Yasira duk ba son matarsa kuke yi ba!dan haka yanzu ko ciwon yatsa Manubiya ta yi Ina mai baki tabbacin Yashjub ke zai zarga tunda dama ba wata shak’uwa ce a tsakaninku ba balle ya ki zarginku,kuma ko su Yasira sun je gidan ido zai sanya musu ya dinga d’arr d’arr da su ta yadda ba su isa yin komai ba shikenan kina ji kina gani Manubiya zama daram!
Hakanan abubuwa za su yi ta faruwa da mu,tunda kink’i ki bada goyon baya mu samu a yi abunda za ta tafi.
Shiysa na yanke shawarar in tartara ya nawa ya nawa in kama gabana tun kafin bomaboman da za su iya hallaka ni su fara fashewa.”
Ajiyar zuciya Yasira ta sauk’e kafin tace”Mommy nima gaskiya abunda kika yi yau ban ji dad’in sa ba….”
Cikin tarar numfashinta Baba larai tace”Yasira yo
ai har da ku!”
Jin jina kai Yasira ta yi kafin tace”ni kam zuwa yanzu Baba larai duk yadda kika ce inshaaAllah hakan za ‘a yi,saboda hakan ne kawai mafita,gara in yi tolerating d’inta in nuna ina sonta in ja ta a jiki na wata d’aya ko biyu akan mu rayu da ita har abada muna fama da ita tana janyo mana masifu kala kala,na tabbatar kashe Ya Yash da aka so yi a yau shima duk a cikin masifun da take tafe da su