Showing 72001 words to 75000 words out of 244445 words
ta jirasa a d’akinsa”
Ita kuma ta yi masa biyayya ta wuce d’ingui d’ingui ta tafi.
A b’angaren Yassira kuwa ta riga ta gama kai wa wuya!Wallahi Daddy ya kunna wuta a cikin gidansa da hannunsa,dan wallahi sai dai in ya koreta a gidan amman da Manubiya da Munirat da Yahanasu da Ummi sun shiga uku a hannunta…ita kanta tanajin tsoron abubuwan da zuciyarta take aiyyana mata ta aikata wa su Ummin!wallahi duk sai sun ci ubansu…..
Babu yadda Baba Larai bata so ta fahimtar mata da amfanin kissa da siyasa ba amman tashi d’aya tace”wallahi ita ta gama kissa da siyasa dan bata ga anfani da ribar yin hakan ba!saita nunawa ummi da Munirat nan fa gidan ubanta ne wallahi hatta Yahanasu sai ta gane kuranta,sai ta sake fahimtar cewa’ba ta fa da uwa!ba ta da gata!sun fi ta power a cikin gidan’.”
Cikin takaici Baba larai tace”Yasira wai ya Ina baki kina k’in karb’a ne?duk fa inda mata suke mata ne kuma dole kowacce da tata kalar power ku daina ganinsu kamar k’ananan alhaki za su baku mamaki!yanzu kalli abunda aka aikata muku duk a ta dalilinsu,kuma ina mai tabbar muku muddin kuka ci gaba da wannan shirmen wallahi wallahi this is just the begining….dan haka daga yau tunda har ga abunda ya fara faruwa to indai zan baku shawar ku d’auka hatta Manubiya dan Allah inaso daga yau ku nemi zaman lafiya da ita a gaban idanun su Daddy daganan sai mu san abunyi ta kark’ashin k’asa…”
Cikin katseta Ya’isha tace”Baba larai munfa gama siyasa,mu da gidan uban mu!?amman ki ce sai mun yi musu siyasa?sun shigo sun mak’ale ta k’arfi da yaji and still ace ba mu isa mu fad’a a yi ba kenan?so kike a taka mu a maida mu gefe kenan?ko ya kike nufi?”
Cikin fushi Baba larai tace”wai ta ya zan yi muku bayani ne ku fahimceni?…ai ba su Ummi na ce ku yiwa siyasa ba!Daddy ne ba na so ya lura ko su fahimci kune masu takalo fad’a sannan suma kuma su Ummin ba wai b’aro b’aro za ku yi musu ba dole a sakaya wani abun idan ba hakan aka yi ba wallahi ina mai tabbatar muku shi Daddyn naku sai ya maidaku gefe su Ummin kuma su taka ku,idan bai zab’a muku mazaje ko kuna so ko bakwa so ya yi muku aure kun bar masa gida ba kenan!,kuna abu kamar wasu marasa lissafi!ki duba fa ki ga yadda muka gaya masa abunda ya faru a gidan su Manubiya d’azu da muka dawo amman ya ajjiye namu ya d’auki na Ummi saboda ita ta fi ki iya kissa!,dan ba ni da tantama itace ta zuga sa saboda tunda ta dawo ta haye b’angarensa ban sake ganinta ba sai yanzu da ta ji hayaniya tukunna ta sauk’k’o.”
Cikin tarar numfashinta Yadira tace”tun da suka dawo take samanshi.”Da sauri Baba larai tace”kin ji ko?ai na sani dama tunda na ji yana dukanki yana cewa”kina Babba amma ke ce mai janyo magana,ba za ki b’ata masa sunan family ba”na san cewa Ummi ta fad’a masa wani abun.
Dan Allah ku tsaya ku nutsu mu taru mu rufawa juna asiri,ina danne ku kuna biyewa dokin zuciya wallahi za ku kwashi kashinku a hannayen ku fa!kuma idan har hakan ta faru kar wadda ta kalle ni dan babu abunda zan iya yi infact yanzu ba kamar da baceba saboda a da da mutane masu sauk’in sha’ani muke dealing da sab’anin yanzu!ki duba fa ki ga Manubiya a yadda ta shigo cikin gidannnan ta k’arfi da yaji,sannan ita kanta Ummin yanayin aurenta da Daddyn naku komai a lullub’e yake,dan haka ya zama dole ku yi accepting fact ku daina ganinsu as k’anananun alhaki mu had’a k’arfi da k’arfi da wayo da komai tukunna shine za mu ci riba.Ya kamata ace mun dad’e da wuce wajen nan wallahi ku kuke dawo da mu baya,last time duk kun sauk’k’o kun yi yadda ya kamata ammman yanzu kun sake burkicewa dan Allah ku gyara.”
Shiruu duk suka yi kafin chan Mommy tace”Allah ya sa mu dace,sai kuma ta kalli Yassira tace”Yasira,ba na son fad’a tsakanin ki da Yahanasu bana so ki yi mata komai…”
K’ura mata ido Yasira ta yi ba tare da tace komai ba,wanda hakan ya sa Mommy ta matso kusa da ita ta dafa ta tukunna tace”Kamar yadda Baba larai ta fad’a’Ummi!Munirat!Mannubiya!Yahanasu duk kar ki bari hayaniya ta tashin hankali ta shiga tsakanin ki da su wanda har zai janyo idanun
Mahaifinku har ma Yash,ban ce dole sai kin yi zaman lafiya da su ba amman kar ki bari su Daddy su fahimci kuna masu jangolo rigimar,mu yi abunda Baba larai ta ce har zuwa lokacin da Allah zai k’addara rabuwar mu da su a samu su kama gabansu.…sannan yanzu the most important thing shine Daddy!,a yadda ya zuciya d’innan komai ka iya faruwa,dan haka inaso da ni da ku mu yi sauri mu gyara mu dawo da hankalinsa garemu idan ba haka ba akwai babbar matsala dan indai har baya bayanmu to komai ya d’auko hanayar lalacewa kenan.”
Jin jina kai Baba larai ta yi kafin ta ce”Yauwa ko ke fa!hakan ne ya kamata and InshaaAllah nan ba da jimawa ba Daddy zai dawo saiti na san abunda zan yi,amman fa ku ma sai kun taimaka!…”
daga nan ta ci gaba da yi musu lecture….
Shiruu kuwa duk suka yi suna sauraron ta….Yadira ce ta fara lura da yadda Kausar take nan sheme a bakin k’ofa dan haka ta kwala kiran Kausar d’in sai
kuma ta nufi inda take suma duk suka rufar mata…..yau ma sai da Yasmeen ta sha wahala tukunna da ikon Allah aka samu Kausar ta farfad’o.
Babu wanda ba ta bawa tausayi ba dan tana farfad’owa da sunan Yashjub ta fara sai kuma ta fashe da kuka.Dan tun d’azu idan ta rufe idanunta Yash kawai take hangowa tare da Manubiya dan ko ta k’i Allah ta riga ta san by now kam suna manne da juna,wallahi wallahi inda ace za ta iya d’aga k’afafuwanta da sai ta nemi gidan ta je a yau idan ba ta kashe Manubiya ba to ba sunanta Kausar ba.
Baba larai da Yasmeen ne suka d’auketa suka yi sama da ita dan jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi ta ma kasa tsayuwa…Mommy da cewa ta yi a kaita asibiti amman sai Yasmeen tace”ba komai stress ne da tashin hankali idan ta samu rest ta d’an nutsu za ta dawo daidai,ko sun je asibitin ma abunda za’a ce musu kenan.!”
A d’akin Kausar d’in suka ya da zango tukunna Yasmeen ta fita ta je ta had’o allura mai mugun nauyi su Mommy suka danne ta aka yi mata aikuwa ko gama tsiyaya ruwan allurar Yasmeen ba ta yi ba Kausar ta fara lumlumshe ido nan da nan kuwa ta yi bacci.Sai a sannan tukunna suka samu kunnuwansu suka huta dan kuka sosai Kausar d’in take yi tana cewa”ita fa ba zata kwana a cikin gidan nan ba,ba ta da k’arfi a jikinta dan Allah Yassira ta taimaka mata ta fitar da ita daga cikin gidan nan,a nemo mata Manubiya yau sai ta kasheta……”waye waye..harda shirme hakanan ta dinga had’awa tana yi kafin aka samu ruwan allura ya saka ta a silent.
Su Mommy kuwa a tsaye suka kwana dan tashi d’aya bacci ya k’auracewa idanunsu tsabar tashin hankalin da suke a ciki.
Yadira ce kawai ta d’an runtsa
Mommy kuwa ko zama bata iya yi ba dan abu biyu ne suka had’ar mata,na farko ba wai iya Kausar bace take cikin tashin hankali a wannan rana har ita dan wallahi babban
abunda zai k’arasa kasheta bai
wuce ace Manubiya ta samu ciki ba,dukda Baba larai tace mata “ta kwantar da hankalinta za ta kunce mata jini har zuwa lokacin da za su dawo cikin gida kusa da su da zama a san abunyi”amman sam hankalinta ya gagara kwanciya .
Abu na biyu kuma ‘Ummi da Daddy’!dan tun d’azu take safa da marwa a bakin stairs d’in Daddy amma ba ta ga sauk’k’owar Ummi ba.Tana ganin Daddyn ya zo ya wuce lokacin da suka dawo daga asibiti,a tunaninta magana kawai za su yi da Ummin da saukk’o amman har yanzu an fi awa uku da hawan sa babu Ummi babu motsinta.
……
A kwance cikin sofa Daddy ya sami Ummi a cikin d’akin nasa har ta d’an fara bacci saboda sun d’an dad’e a asibiti tukunna suka dawo,a kusa da ita ya nemi waje ya zauna ya d’an ruk’o hannunta ya na kallon saman goshinta inda Yasira ta daketa wajen har ya d’an yi jaa….farkawarta kenan ta ji ya mik’e dan haka ta shiga bud’e idanunta dai dai ta ga ya nufi fridge da towel a hannunsa yana zuwa ya bud’e ya d’auko ice ya saka a cikin towel d’in ya juyo ya nufota,mik’ewa ta yi ta zauna dai dai ya k’araso tace”ya jikin Yaha?”a hankali ya ce”Alhamdulillah,she’s fine tana d’akinta”tukunna cikin kulawa ya zauna kusa da ita sosai ya fara daddana mata k’ank’arar a inda ya yi jaa yana mai jera mata sannu a d’an rikice….Ummi ba ta san lokacin da ta saki wani sassanyan murmushi ba wanda hakan ya sanya ya tsayar da abunda yakeyi ya shiga kallonta,ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sunkuyar da kansa k’asa yana tunano ire iren abubuwan da aka yi mata a cikin gidan amman ta yi hak’uri ta zauna,bada hak’uri baya daga cikin tsarinsa amman tashi d’aya a yanzu ya yanke shawarar chanja tsari dan tabbas Ummi ta chanchanci ya bata hak’uri ya jinjina mata…a hankali ya d’auke hannunsa daga kan goshinnata ya runtse k’ank’arar dake a cikin towel d’in a hannunsa duk biyu kafin ya kalleta cikin rashin sanin ta Ina ma zai fara yace”am..Ummi,ki yi hak’u!”
Da sauri ta sa hannunta ta toshe masa baki ta shiga girgiza masa kai alamun kar ya bata hak’uri sannan tace”ba komai,ka d’auka a ranka kamar baka tab’a yi min komai ba kamar su Yasira ma ba su tab’a yi min komaiba…”cikin tarar numfashinta yace “taya zan iya?”
Yanzun ma katsesa ta kuma yi tace”dan Allah dan Annabi komai ya wuce,pls ka manta da komai let’s start a fresh.”Ta fad’i hakan tana murmushi sannan ta sake cewa”plssssss”ta had’e hannuwanta waje guda.
Kallonta kawai ya tsaya ya na yi yana mamakin kyakkyawar zuciya irin tata…yana mai jin k’aunarta tana sake shigarsa. A hankali ya ajjiye k’ank’arar a gefe ya sa hannuwansa duk biyu ya rungumota izuwa jikinsa daidai saitin kunnenta yace”thankyou Saddik’a!you are right!let’s just start a fresh ta yadda zan nuna miki da gaske i’m sorryy and I love you so much!”
Murmushi tayi itama tace”i love you”tana mai jin son mijinta yana sake shigarta.
……
Sai da gari ya fara haske tukunna Yashjub ya farka daga wahalallen baccin da ya yi awon gaba da shi sakamokon zazzab’in da ya rufar masa lokaci guda!
Juya wa ya yi ya kalli Manu wadda ke kwance lamoo a gefensa idanunta a lumshe,wani kalar farin ciki da annashuwa ne suka lulub’esa yana kallonta yana jin kamar kamar ya had’iye ta gaba d’aya ya huta watak’il zai samu sauk’in abunda yake ji game da ita.Yadda fuskarta ta kumbura saman idanunta sukayi luhu luhu ne ya sanya ya d’an ji wani iri dan ya san ya yi laifi!sam baya so ya zama silar kukanta amman kuma wani ikon Allah ji yake kamar ya k’ara!wallahi he can’t get enough of her..Manubiya ita ce mace ta farko kuma inshaaAllah ta k’arshe da ya fara sani amman tabbas ya san she’s different ba lalle a kuma samun irinta a cikin mata ba idan kuma an samu to ba su fi 1%out of hundred ba wallahi..shi kad’ai ya san me ya ji. Ahankali ya matsa gareta yana mai jin yadda gaba d’aya gab’ob’in jikinsa sukeyi masa ciwo, sosai ya shige jikinta yana addu’ar Allah ya basa ikon lallashintan da yake da niyyar yi ba tare da ya sake yin wani laifin ba,wani sassanyen murmushi ne ya sub’uce masa wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili kafin a hankali ya sa hannu ya yi hugging nata ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nutsatsiyar ajiyar zuciya tashi d’aya ya shiga koro kirari ma Ubangiji a cikin zuciyarsa kafin ya d’aura da addua da sanya albarka a Manubiya
matarsa farin cikin sa cikar
burinsa…. bud’e idanunsa yayi ya na mai kallon fuskarta yace”Baby!”a hankali.
Tun d’azu idanunta biyu dan bacci ba nata baneba,sai dai kuma ba ta jin za ta iya bud’e daidai da kwayar idanunta a halin yanzu…Sau uku yana cewa “baby”jin shiru ya sa ya sake zubawa fuskarta idanu sosai k’irjinsa yana dukan uku uku,ganin tana d’an motsi ne yasanya sa fesar da numfashi a hankali yace
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya sake hugging d’inta ya ruk’umk’umeta kamar wanda akace za’a kwace masa ita……da godiya ya fara kafin
ya d’aura da sanya albarka
sai kuma alk’awarurruka iri iri,har da hawaye sai da Yashjub ya yi yana mai yi mata godiya cike da shauk’i da k’auna bayan wanda ya yi jiya.
Itakam wasu ta fahimta wasu kuma bata fahimta ba tsabar azabar da take a ciki….ta san ruwan zafi zai taimaka mata shiyasa bata da burin da ya wuci da ta jita a cikin ruwan zafin a halin yanzu,dukda ta san za ta sha sabuwar azaba amman ta san hakan kad’ai ne zai taimake ta.
Kamar ya ji abunda yake a ranta kuwa dan shima tashi d’aya tunanin had’a mata ruwan zafi ya zo masa….anan kuwa ake yinta!dan duk k’okarin sa sam sai ya ji ya kasa matsawa daga gareta,yadda ya yi hugging d’inta ya sanya ya sake jinsa a sama ya ji bashi da wani burin daya wuce ya ji sa a duniyar da ya tsinci kansa a ciki jiya,tsabar fitina shi kansa gab’ob’insa da cinyoyinsa ciwo suke yi ga kuma zazzab’in da ya rufar masa amman a haka ya fara k’ok’arin maida su ruwa….Manubiya ba ta san tanada ragowar k’arfin da har sautin muryar ta zai fito ba sai da ta ji ta rushe masa da wani irin gigitaccen kuka mai k’ara!.
Shiruu ya yi yana maida numfashi kafin ya samu da kyar ya cika ta ya mik’e ya nufi bathroom ya na tangad’i dan ya san idan ba tashi ya yi ba bazata tab’a daina yi masa kukan nan da yake jinsa har cikin ransa ba.
Sai da ya shiga bathroom d’in tukunna ya nemi towel ya d’aura sannnan ya soma had’a mata ruwa a makeken bathtub d’in.
Ko da ya fito a yadda ya barta a haka ya sameta sai dai ta d’an sassauta sautin kukan nata,ko bargon da ya sauk’a ya bar mata a iya guiwar ta saboda saurin ganin ya bar cikin d’akin ba ta samu ikon ja ta rufe jikinta da shi ba.
Tsayawa kawai yayi yana kallonta a ransa yace”Allah mai halitta!how can some one be this beautiful!and this perfect!!so awesome.”
Ta san yana kanta a tsaye kuma yana k’are mata kallo gashi ta kasa motsi shiyasa kawai ta k’ara sautin kukan na ta.Shi kam yana chan zuwa yanzu idanunsa sun sauk’a akan d’an jinin da ya biyo ta gefen cinyoyinta d’an kad’an ba mai yawa ba,dama ko bai ga hakan ba ya riga ya sani amman ganin da ya yi sai ya sake sanya shi cikin wani irin farin ciki yana mai jin sa a saman gajimare yana yawo ga kuma tsananin nutsuwa da nishad’in da ya samu shiyasa kawai ya fara jinsa kamar wani
sabuwar halitta!.Ya ma rasa wanne irin gift zai bawa Manubiya as token of appreciation dan tabbas bai isa ya ce zai bata gift dai dai da abunda ta basa ba…. ba kad’an ba ganinta a hakan ya sauya shi amman sai ya daure yana jin tausayi da begenta suna ratsashi,ahankali ya lumshe idanunsa da suka d’an fara chanja launi ya bud’e su kafin ya k’arasa inda take ya d’urkusa ya shiga share mata hawayenta yana cewa”ni kaina haushin kaina nakeji,kar ki damu anjima zan baki bulala ki zaneni!”yana gama fad’in haka ya d’auketa suka nufi bathroom d’in bai ajjiyeta a koina ba sai cikin ruwan d’umin da ya gama had’a mata.
Ita kanta batasan ta na da raki ba sai yau amman kuma ba za ta kira hakan da raki ba dan wallahi ko macen soja ce ta ji kalar azabar da take kwasa yau ta tabbata itama sai ta koka. Da kyar ta tsaya ya yi
mata ruwa biyu ya ta ya ta tai wankan tsarki yai mata wankan sabulu daga haka ya sake sakar mata warm water ya juya ya fita
don ya samu ya chanja zanin gado.
Yaye mara kyan ya yi ya shimfid’a sabo tukunna ya d’auki mara kyan ya nufi toilet d’in da shi ya je ya saka a washing machine ya d’auraye ya busar ya saka a closet d’in dan ya d’an sha iska tukunna ya koma cikin bathroom d’in wajenta.
A kwance cikin ruwan ya sameta kamar d’azu ta lumshe idanunta,ita kanta tana jin dad’in yadda ruwan zafin yayi mata tana jin yadda jikinta yake d’an sakewa ciwon yana raguwa….kamar d’azu yanzun ma d’aukarta ya yi bayan ya d’aura mata towel sai faman shagwab’a takeyi shi kam kamar ya maida ita ciki haka yake ji sai wani lallab’a ta yake kamar ya samu kwai,a haka suka fito ya sanya mata babban hijabi ya kwantar da ita a kan gadon tukunna ya koma ciki dan
shima ya samu ya yi nasa wankan bayan ya ce mata “ta yi sallah anan inda take babu
damuwa.”
Sai da ta d’an zauna da kyar tukunna ta samu ta yi sallar,ta na idarwa ta kwanta
atake bacci mai masifar nauyi ya yi awon gaba da ita….ko da ya fito ya ga tana baccin bai tasheta ba,Sallah shima yayi
daganan ya je ya soyo musu omelet ya had’o da ruwan zafi da kayan shayi da dambun nama ya zo ya ajjiye a d’akin tukunna ya wuce sama d’akin shi ya shirya tsaf cikin wata dakakkiyar sky blue d’in shadda da farar hula!ya yi kyau matuk’a kyawunsa ya sake fitowa gashi har wani glowing yakeyi ya fito ango abunsa ras…idan ka gansa dole ka sake waigawa ka kalla.
Tana cikin baccin ta ji ana shafa fuskarta,turo baki ta yi
kad’an kafin ta d’an bud’e idanunta….kyakkaywar fuskarsa ce ta fara yi