Showing 51001 words to 54000 words out of 244445 words
nufi cikin gidan yana mamakin yadda Yadira da Yusra suka yi masa..wato ko kallo ma bai ishe su ba!tabbas
Yara sun girma kam….
Sir Najeeb yana shiga motar Ummi ta k’araso.
Already su Siyama ko gama gaisawa basu bari sir Najeeb ya yi da su Yassira ba suka matsa da niyyar shiga ciki….Yahanasu ta fito da fara a ta tarbe su kamar za ta goyasu,wanda hakan ba k’aramin sake tunzura su Baba larai ya yi ba…ita Baba larai
Babban tashin hankalinta ma shine
ta yaya za ta aiwatar da mission d’inta
da waennan jama’un a cikin gidan?..
Lissafin da takeyi kenan suka ga gate ya zuge motar Ummi ta danno kai.
Cikin b’acin rai Yassira tace
“Innalillahi!
Tabbas matar nan ta ci a bata sarauniyar y’an naci,
Mace ace ba zuciya kwata kwata,a taho a barki amman sai da kika zo?ko wa ma ya yi mata kwatance oho?!”
“Ba zai wuce angon da kika kira yace ‘mu jira mu taho da y’an d’aukar amarya’ba,kinga
ita da ta fiki ai gashi yayi mata tashi d’aya!”
Yusra ta bata amsa tana mai
wucewa ciki
ranta a mugun b’ace…ta so su Jidda sun biyeta yau da sun ji maganganu wallahi!ta san
ba class d’inta bane su
sannan ta san idan ta yi hakan zatayi acting childish amman
wallahi sai dai a kirata da jinjirar k’auye!ba ta damu ba. Dan tun da ta d’aura idanunta a kansu ta ji ta yi loosing temper da duk wani hankalinta tashi d’aya.
Tunda take a rayuwarta bata tab’a jin tsana irin wadda take yi musu ba…gashi ta san dole ta dinga ganinsu tunda sun riga sun had’a y’ar uwarsu da yayanta,watak’il ma a haifo
musu mai kama dasu
Innalillahi
wallahi za ta iya mutuwa!ya zama dole a san ta yi da Manubiya dan ba ta da guri da muhalli a rayuwar d’an uwanta! ashe dama akan wannan y’ar talakawan ya Yash ya d’agawa kowa hankali kenan!dan ganin da ta yiwa su Jidda ya nuna mata cewa Manubiya talakan tukuff ce,shegu talakawan banza!babu abunda ya fi sake b’ata mata rai kamar ankon atamfar 4500 d’in da suka yi a bikin d’an uwanta!kamar Yash ace wai an yi ankon 4500 a bikin sa wannan lalacewa haka har ina?…..
Kamar zata fashe haka ta afka parlourn,ko bi ta kan masu goge goge bata yi ba ta wuce sama
Wucewa su Yassira suma suka yi suka nufi cikin parlourn
dan haka da sauri Yahanasu tace”mu je ciki muma,idan muka je kowa sai ta kama floor a samu a sassaka turaren wuta ya ratsa ko Ina dan ba lokaci.”
Ko ishashshiyar gaisuwa da introduction Yahanasu bata bari Ummi da Munirat sunyi da su Siyama ba,haka nan ta azalzalesu suka shige ciki.
Aisha ta d’an fahimci wani abun,ga kuma yadda y’an uwan Yashjub d’in suka rabu gida biyu da masu hankali da jahilai,shiyasa suna shiga itama ta cewa Siyama ta tsaya ita da Munirat da Jidda su saka turare a k’asan su yi ta
gyaygyarawa.
Ita da Ummi kuma suka yi sama da masu gado,
Yahanasu kuma ta yi chan sama turakar mai gida…inda
d’aki d’aya ne tak a floor d’in sai tafkeken roof top open terrace.Saman farko kuma
d’akuna biyu ne da parlour d’aya,sai wani parlour mai kamar d’aki wanda Yash ya zuba kayan gym a ciki dan haka suka tattara kayayyakin gym d’in Najeeb ya kira wasu a cikin masu gyara gidan suka kwasa aka kai d’akin Yashjub dan akwai wani guri a cikin glass inda za a iya zuba kayan su kuma suka fara kafa gadon su a nan Najeeb yana cewa “idan Yashjub ya zo Aisha zai nuna”
Itama tace
“Shi za ta ce ya chanza masa tsarin gida!”
Hakanan suna raha suka shiga had’a gidan.
A tunanin su Aisha sun yi zab’en gado mai kyau da tsada amman sai da suka b’ige da d’an jin kunyar
gadon nasu da suka ga kayan gidan,dan hatta d’akin chan k’asa guda daya na bak’i
Turkish ne a ciki wanda a k’alla sai an zuba miliyan shida tukunna za a sayi gadon.
Kaff gidan Turkish ne,Main parlourn k’asa ne kawai
royal white da royal blue,colour din mai masifar kyau,shima kuma saboda ansan Turkish zai yiwa parlourn kad’an kasancewarsa
tafkeken gaske shiyasa aka zuba royal complete set d’urma d’urman gaske mai tafe da set d’in dining table da madubin sa da komai.
Kitchen d’inta ma royal blue ne da white,wanda had’uwa girma da tsaruwar kitchen d’in
yasanya Siyama da Munirat suka tsaya suna ta zancen kitchen d’in da k’auyanci suna yiwa kansu dariya
Dan tashi d’aya tasu ta zo daya gashi har sun saba……
Gidan ya had’u k’arshen had’uwa,ko ina wajen deco
da saka tv an yi decorating
da wani had’add’en painting
jikinshi kmr marbles,kuma duk
iri d’aya grey da white kalar marbles d’in gidan mai masifar kyau,Pop da chandelier kam ba a magana ga toilets da closets suma abun kallo,gida dai ya had’u iya had’uwa
wani abun ma sai wanda ya gani
….
Shiyasa su Siyama suka dinga jinjina izza da kud’urar ubangiji dan tabbas idan ba Allah ba to babu wanda zai yi haka,wai nan ne gidan Manubiya!
Allah mai girma da iko!.
Murna da farin ciki kam sunyi mata bila adadin dan ta samu duniya sai dai ta tashi ta nemi lahira,sannan ta samu miji mai
tsananin sonta da k’aunarta,ga hutu Allah ya bata matsalar d’aya ce ‘dangin miji’amman baya ga wannan
Manubiya kam ta samu komai…a ce a d’aukota daga gidansu tashi d’aya a kawota wannan gidan haka
mara makusa ko d’aya!
dan tun daga waje!gate!har compound d’in gidan wanda ya ji interlocking concrete da grass carpet da garden
a haka ma basu zagaya baya sunga swimming pool ba
sam babu makusa.
Duk iya kushewar mutum sai dai ya hak’ura in ya shigo wannan gida na Manubiya da Yashjub.
…….
…D’akin bak’i Jidda ta bud’e ta shiga,ita sam ba ta yi tunanin akwai mutum bama sai da ta yi
ido biyu dasu Yasmeen tukunna tashi d’aya tace”Sorry
daga haka ta juya.
Tsaki Ya’isha tayi,dai dai
Jidda ta kama handle d’in k’ofar ta bud’e da niyyar fita ita kuma Yasmeen tace
“Nikam ace wai mutane ko darajar privacy basu saniba
saboda Allah kamar wasu
dabbobi!”Daga haka suma suka nufo k’ofar da niyyar fita da kuma bi ta kan Jiddan idan ba ta ba su hanya da wuri ba.
Duk ba su lura da Najeeb a bakin k’ofar ba sai da Ya’isha ta zo zata wuce tukunna suka yi ido biyu da shi.
Kallon ta yayi sosai kafin ya maida dubansa ga Jidda yace
“Anata nemanki!ki je sama wajensu Ummi za ki taya su da wani abun”
Jin jina kai kawai ta iya yi dan ita kam ta gama shiga shock bayan b’acin rai da kuma mamaki…su da suke a matsayin surukan juna amma kalli yadda suke musu msgana kmr masu shirin shiga filin dambe!.A tunaninta wayayyun mutane masu kud’i da illimi kamar su ba za su yi wannan tumasancin ba.
Shi kansa Sir Najeeb tunanin da yake yi kenan….ya san Ya’isha ba ta da kunya kuma tana da tsiwa amman sam bai yi expecting haka daga garesu gaba d’aya ba.Ya ma rasa me zai ce shine matsalarsu ko yana damunsu!shin kishi ne!ko haushi!ko bak’in ciki!ko rashin sanin ya kamata?.
Shiyasa Jidda tana wucewa
shima ya juya zai wuce ko second look bai yi tunanin sake yi musu ba.
Ahankali ya ji Ya’isha tace “Ya
Najeeb!”
Kamar ba zai juyo ba sai
kuma ya juya yace”Naam
Ya’isha!”
Wuceshi Yasmeen ta zo ta yi ta bar musu space shi da Ya’ishan.
Ganin ta yi shiru tak’i yin magana kuma sai wani irin kallo take yi masa ne ya sa yace “Inada abubuwan yi fa Ya’isha akwai matsala ne??”
Ya yi mata tambayar yana d’an juyawa yana kallon masu aiki dake a cikin parlourn dan har sun kusan kammalawa.
Ba k’aramin b’aci kuwa ranta ya sake yi ba shiyasa itama ta fito bakin k’ofar ta tsaya daff da shi sannan tace”A ganinka bai kamata mu yi magana anan ba ko?shiyasa kake k’ok’arin zille wa gudun kar ta ganmu tare??”
Dama ya san sai tayi maganar Siyama shi kuwa har ga Allah bai shiryawa maganar yanzu ba dan ya san tsaf zai iya breaking up da ita right away shi kuma ba ya so yayi breaking up da ita ba a right manner ba….
Sai da ta sake cewa”Bakace komaiba”tukunna ya juyo yace
“Tou me kike so in ce miki??
Ya’isha Meyene problem d’in ku da mutanen nan?daga ke har su Yasmeen har ga Allah I’m very disappointed in you guys!Kuma na tabbatar kin san me zai faru idan Yash yaji haukar da kukeyi ko?
Dama ashe kishi tsakanin matar wa da siblings d’inshi
Is real?dan ni dai ban tab’a gani ba sai a kanku to be honest
sannan kishin naku ma is way too local,haba mana!.
Ki gayawa su Yasmeen
kar su sake wani shirme kema kuma ki nutsu
Amarya za a kawo idan ba haka ba wallahi zan fad’a ma Yash.”
Yana gama fad’in haka ya fara k’ok’arin juyawa sakamokon hango Munirat da Siyama dayayi sun tunkarosu da kaskon turaren wuta…..ya san
abunda yakeyi is so selfish amman Yaisha ita ta janyo komai in da ace tana bashi time d’inta da maybe a lokacin da ya ga Siyama months ago da ba lalle ya saka hope d’in samunta ba,zai iya lallashin zuciyarshi ya hak’ura da ita
duk da ya san zai sha wahala.
Amman Ya’isha ita ta banzatar da shi shi kuma ya kamu ya fad’a yayi dakon soyayyar Siyama for almost 4 months,sannan yanzu da ya sake ganinta a yadda yakeji wallahi ko goya sa Ya’isha takeyi ba za ta samu gurbi a zuciyar sa ba dan Siyama ta mamaye ko Ina shiyasa shi kansa ya ke d’an jin tausayin Ya’ishan dan har ga
Allah ba ta da matsayin da zata hana sa zama selfish bata da matsayin da zata sa yak’i rabuwa da ita kuma bata da matsayin da zata hanasa bin zab’in zuciyarsa……
Ba k’aramin mamaki ya shiga ba da yaji Ya’ishan ta ruk’o hannunshi dan haka ya juyo a mugun firgice
Ita kanta su Siyaman ta hango
shiyasa ta yin hakan,hannun
ya kalla kafin ya d’ago ranshi a mugun b’ace yana shirin fara magana yaga fuskarta shab’e shab’e da hawaye.
Da mamaki yace”Ke!lafiyarki kuwa?”
Cikin kuka tace”na san saboda sister d’inta kake ta wahalar da ni haba Ya Najeeb
taya kake tunanin ba zan ji
haushinsu in kuma tsanesu gaba d’aya ba?kalli fa yadda ka ganni a situation d’in da ka ganni amman sam baka damu ba instead treatning d’ina ma kake yi akan zaka gaya wa Yash mun tab’a dangin matar sa.Shekara nawa muna tare
tashi d’aya ka juyamin baya ya kake so inyi?shin ba ka tsoron hakki?idan ka yaudareni fa Allah ba zai barka ba.
A tunanina a matsayin k’anwa nake a wajen ka bayan masoyiya,ta yaya za ka min haka tashi d’aya sannan kuma kace ni da y’an uwana ba zamu ji haushin sa ba?”
Tausayinta ne ya d’an kama shi ganin yadda take kuka wiwi…tabbas ya kamata ya rabu da Ya’isha as soon a possible ya kamata ya yi setting nata free tun kafin a samu more damage….”
Yana cikin wannan tunanin ya ji kansa ya wani irin sarawa sakamokon rungumar da ta yi masa.
Cikin kuka tace
“Allah ban shirya barwa kowa kai ba”.
Bai tsaya wata wata ba ya zarota da dukkan k’arfinsa cikin fushi yace”ba ki da hankali ne?wanne irin shirme ne wannan?..”
Ya fad’i hakan yana juyawa ya ga ko Siyama ta gansu,bai ga kowa ba amman tabbas ya san ta gansu….ji ya yi kamar ya rufe Ya’isha da duka!ko hannunshi bata tab’a rik’ewa ba sai yau kuma yau d’in ma har da runguma tsabar iskanci.
Ganin in ya ci gaba da tsayuwa a gaban ta zai iya mammaketa ne ya sa kawai ya juya da sauri,ko a parlourn bai yarda ya ci gaba da zama ba tashi d’aya ya fice ya na fita ya nufi motar sa ya shige ya zauna ya kunna ac.Bashi da tantama Siyama ta gansu tabbas shiyasa ta yi sauri ta gudu,shikenan ya san tun kafin
aje ko Ina har ta fara yi masa kallon d’an iska kuma mayaudari.
Suna shiga kitchen Siyama ta cika hannun Munirat tukunna ta dafe k’irjinta ta na mamakin
zafin kishin Najeeb da taji,yau ne fa kawai suka d’an samu momment amman kalli yadda zuciyarta take tafarfasa na ganin shi da wata da tayi.
Dariya Munirat ta yi kafin tace”Tab!amman ba ki riga kin shiga university ba ko?kina ina couple suke kissing juna in public!dan kinga d’an wannan shine duk kika koma haka sai kace wadda taga wani abu serious….”
Cikin katseta
Siyama tace”couple?Mijinta ne?”
“Nop,amman saurayinta ne
kuma shi zata aura na ji Mommyn su tana fada rannan
kmr sun kai almost 7 years tare
tun tana secondary school…but gaskiya ni kaina ta bani mamaki saboda ban tab’a ganin wani d’an gidan da bad behavior haka ba
Apart from Kausar da Yassir,ban yi tunanin suna irin haka ba suma shi kansa Najeeb d’in he looks decent..anyways sha su ta shafa!.
Kina gayamin Manubiya a buk take?maybe ma mun taba haduwa fa”
Sai yanzu Munirat ta lura da yadda sam hankalin Siyama baya a kanta.
Dan haka ta d’an yi snapping fingers d’inta tace”Hey!”
Firgigit Siyama tayi
dakyar ta d’an daidaita b’acin ranta tukunna ta kalleta tace”Yassir! wanda suka kawo mu shi da Ya Najeeb ko?,dama daga ganinshi wanann d’an iska ne”sai kuma ta yi sauri tace”Au sorry brother dinki ne ko?”
Shiruuu Munirat tayi daga jin zancen Yassir…zuwa yanzu ta gama tsara yadda za ta yi su shirya dan tana mugun son Yassir gaskiya…..
“Munirat kin yi shiru”
Muryar Siyama ta katse mata tunani.
Numfashi Munirat ta fesar kafin tace”A’a ba brother d’ina bane,mu bar maganarsa kawai”
“Ok”Siyama ta ce kafin ta d’aura da cewa dama na ga kamar he is intrested in my sister shiyasa na ke so in d’an yi confirming halinsa kafin komai.
Dasauri Munirat tace”Really?
wanann farar ko?”
“Yeah” kawai Siyama tace
daga haka ta chanja topic d’in
ba tare da ta tsaya ta lura da fuska da kuma reaction din Muniran ba..
A parlour Su Baba larai suka zauna Yassira kuma ta wuce sama wajen Yahanasu,ba abunda ya basu mamaki ya kuma basu takaici kamar yadda su Aisha suka rarrabu
it’s like sun fahimci wani abun kuma sun lura Yahanasu ce ta nace ayi hakan…….
Tana zaune akan couch d’in
private balcony na d’akin tana tunani ta ji an bud’e k’ofa dan haka ta mik’e da sauri
ta shigo cikin dakin.
Ido biyu sukayi da Yassira dan haka tace “Ashe kece”
“Are u expecting someone else
besides me?kema kika shigo ballantana ni?,a tunani na da lissafina na fiki iko da d’akin nan da gidan nan ma gaba daya” Yassira ta fad’i hakan tana mai k’arewa d’akin kallo.
Numfashi Yahanasu ta fesar kafin ta matsa kusa da ita ta tsaya tukunna tace”Finally kin fito da real face d’inki kenan ko?
hakan yafi ai dan kin san ni I hate pretends,and FYI da ni da ke duk iko d’aya muke dashi da d’akin nan
u are just living in delusion!”
Shiruuu Yassira ta d’an yi kafin
ta matsa kusa da ita itama
tace’me nene problem d’in ki?
me kikeso kiyi proving?
a tunanin ki ni da hannuna zan cutar da d’an uwana ne ko me kike zato?dan tsaf na fahimceki na kuma gano abunda kikeyi wanda har ya kai ga kina k’ok’arin saka doubt namu a idanun waennan k’azaman mutanen!
so kike ki nuna musu wani abu akan mu ko me?.
Nasan ba uwa d’aya ce ta haifemu ba amman still ke y’ar uwa tace kuma na san matsayinki a wajen na shiyasa kika ga Ina binki a sannu
amman fa Yahansu karki kaini bango kar ki bari mu fara yak’i dake a cikin gidan Imam kura wallahi baza ki ji dad’i ba.
Dan na lura kwana biyun nan
wani gigi kike ji kina overstepping boundaries d’inki,tsabar rainin hankali in tanbayeki kwatancen gida ki ce baki sani ba sannan kuma ko kunya ma bakiji ba mun had’u da ke kinsan mun gane k’arya kika yi mana amman shine zaki zo da wani sabon shirme?
I think it’s about time da ya
kamata ace kin koma place d’inki dan na lura freedom bai kamace ki ba
Murmushin takaici Yahanasu ta yi kafin tace”Very well good said,yayi kyau!gara da kika fito k’iri k’iri kika gayamin komai na ji dad’i sai dai inaso ki san cewa nima fa na san kaina kuma zan iya tsare jikina da ayoyin Ubangiji dan haka
ko me kike tunanin yi a banza ne”
Da fushi sosai Yassira tace
“me kike nufi?wa ma ya
damu dake balle ya miki wani abun besides me kika maida mutane?”
Dariya sosai Yahanasun tayi sannan tace “dad’ina da ke Yassira har gobe ba ki iya magana ba annan rashin iya sakaya maganar ki har yau bai chanza ba.Nasan kinsan me nake nufi dan haka mu rufe chapter kawai.
I just want u to know that ba zan tab’a bari ku zalinci Manubiya ba..and kamar yadda kikai suspecting to be frank ban yarda daku bane
shiyasa nayi duk abunda nayi
kuma karki sha wasa in aka kawo Manubiya in zaunar da ita in gaya mata su waye ku
gudun karkuyi mata shigo shigo ba zurfi,an yi min ban ji dad’i ba shiyasa ba zan bada k’ofa ayiwa wani ba
hatta su Ummi lokaci kawai nake jira sannan akwai abunda nake dubawa but still akwai ranar da zanyiwa kowa zazzagar kwanyo,har a gaban Daddy dan wallahi ba wai ke kad’ai ba hatta Mommy ba
tsoron ta nakeji yanzu ba kuma za ki tabbatar da hakan soon”
Cikin fushi Yassira ta d’aga hannu zata kifa mata mari,da sauri Yahanasun ta rik’e hannun tace “Wannan era d’in ya riga ya wuce Yassira na wuce haka daga gareki
har abada wallahi,sannan Ina so ki san kunyi mistake!
tara abokanan adawa da yawa shi yake janyo mutum k’asa wanwar,kinga ga ni ga Ummi sannan ga Manubiya
kuma dukkan mu babu yadda kuka isa kuyi damu wallahi,ban san wanne dukan za ku fara
karewa ba dan tabbas kun d’aukarwa kanku dala babu ganmo….
Kin d’aukar wa kanki aiki mai tsananin wahala,kin jefa kanki a masifa sannan kin biyewa son zuciyar da ba inda zai kaiki sai garin dana sani”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya tace “I just wish za ki san kuma za ki ga abunda na sani da kin gane wacece Mommy da kin daina biye mata.Gaba dayanmu mu
uku ba abun tsana bane a wajen ki,ni y’ar uwarki