Showing 222001 words to 225000 words out of 244445 words
a tab’a iya karyawa!!!”
Jinjina kai Mommy ta yi tace”na ji na fahimta inshaaAllah za a ayi taka tsantsan..ya aikin yake?”
Ta yi masa tambayar tana kallonsa.
Murmushi ya yi kafin yace”rik’e mata numfashi zan yi!…idan kaff likitocin duniya ne za ace su zo su taru a kanta babu wanda ya isa yace tana da rai saboda komai tsayawa zai yi.
Daganan Idan aka yi mata wanka akai mata sutura aka kai ta kabari aka binne muka tabbatar an kai ta ni kuma sai in saki numfashin ya dawo..kinga dai ai bata isa ta fito ba ko?sai dai ta k’arasa a chan!!”
Ya k’arashe maganar tasa yana sakin dariya…
Da sauri Yasira ta mik’e ta fita hankali a tashe ranta a masifar b’ace..Tabbas bayin Allah marasa Imani suna da yawa a duniya..ta ya mutum zai iya aikata haka a d’an Adam musulmi d’an uwansa?.
Wani sanyi da nutsuwa Mommy ta ji daga jin bayaninsa dan bata tab’a jin hukunci mafi dacewa daya dace ace ta yankewa su Manubiya ba kamar wannan!!!
Har za ta yi magana sai kuma ta tuna da su Yusra dan haka ta kallesu tace”ku d’an bamu guri!”
Sai da ta tabbatar sun fice daga cikin gidan gaba d’aya tukunna ta kallesa tace”Ana iya yiwa Namiji ma ko?”
Dariya sosai ya yi kafin yace”Yashjub ko?
Tsaff za ki yi masa shima amma shi gashin kansa za ki kawo.”
“……….Samun gashin kan Yashjub zai d’an yi wuya amma hular Manubiya yanzunnan ka jira a daren nan za ka samu,za ‘a iya kawo ribbom ma?”
Jinjina kai yayi yace”indai ya tab’a gashin kanta ku kawo!!”
Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Mommy gudun ma kar su ci gaba da b’ata lokaci ya sanya ta mik’e da sauri tace masa ya bata awa d’aya da rabi daga haka sukayi sallama ta fita jikinta har yana b’ari ranta fess.
A mota duk ta samesu a zaune Yasira ta had’e rai kamar ba ta tab’a dariya ba!!
Ta san idan ta biye mata b’ata mata lokaci za ta yi dan haka ta sa hannu ta d’auki Jakarta ta kalli Ya’isha tace mata “zo”
Su kuma su Yasira tace”ku wuce gida.”
Yasira za ta yi magana tace”na rantse da girman Allah Yasira zan yi miki Baki!!idan kuma kema Yasmeen da Yadira za ki zama bismillah ki tattara ki koma gidan ubanki kar ki damu da damuwata!Allah zai yi mini gata!”
Sai kuma tafashe da kuka tace”Larai ce fa ta rasu amma kalli Yadira da Yasmeen ko yunk’urin zama inda nake basuyi ba ballanata su taushe ni,tunda Manubiya ta zo cikin rayuwarmu komai ya hargitse ku kanku ya’yana an juya muku lissafi kalli abunda kuke yi mini sannan ki ce wani in hak’ura?”
Cikin zubar hawaye Yasira tace”gaskiya fa nake gaya miki Mommy kuma son da nake yi miki ne ya sanya nake k’ok’arin kub’utar da ke daga hanyar tsira!
Saboda Allah ta Ina kashe Manubiya ya zamto hanyar warwarewar waennan abubuwan da kika lissafa Ina riba a kashe rai??….kece fa baki tsaya kin nutsu kin fuskancemu ba shiyasa kike ganin kamar mun juya miki baya,Yadira fa ciki ne da ita amma baki ma lura ba kina ta abubuwan gabanki tunda ta yi aure ba ki damu ki duba ya take ba!ko d’azun ma amai ta yi shiyasa junior d’in yace su wuce asibiti kuma na san za ta dawo ba wai k’in zama ta yi a wajenki ba,kawai bamuga kin nustu bane balle ki bamu listening ear shiyasa kika ga bama…”
Cikin katseta tace”to duk ba uban ku bane ya rikitani kwana biyun nan!wai Yasira “
Itama cikin katseta tace”Mommy babu laifin kowa ba….”
Marin da ta d’auke ta da shi ne ya sanya ta yin shiru…cikin fushi tace”ku wuce gida!!!”
daga haka ta ja hannun Ya’isha suka wuce suka tari napep….
Sun dai san gandu ne Gidan amma sai da Ya’isha ta kira Yadira ta yi mata kwatance tukunna suka d’au hanya….k’asa k’asa gudun kar mai napep d’in ya ji Mommy tace”kina da idear yadda za a yi a samo??”
Jinjina kai Ya’isha ta yi itama k’asa k’asa tace”zuwa zan yi kawai in gaya mata abunda ya faru da Yassir da ke in ce mata nazo ne akan in rok’eta ta yiwa Yash da Hajiya mama magana a samu ku dawo!
Durk’usawa wada ba gajiya bane ba mu dai kawai mu samu abunda muke so…
A ganina hakan shine kad’ai option d’inmu idan ba hakan ba kin san halinsu da rashin yarda na san ba lalle ta sake da ni mu keb’ance in samu in d’auki abunda nake so d’inba.”
Jin jina kai Mommy ta yi tace to ni kenan ba sai na je ba ko?tunda ban jiyo ni a cikin plan d’in naki ba!”
“Eh kawai ku juya idan na gama zan same ku a gidan mutumin ai na gane ba wani nisa ma.”
“To shikenan” Mommy tace daga haka ba ta sake cewa komai ba har suka kaita ta shige ita kuma ta juya……..
A gate ta same su ita da Siyama, ta rakosu har da Najeeb suna ta hira suna dariya….da kyar da mugun kyar Ya’isha ta hana kanta kuka saboda ko waye ya kalli Najeeb da Siyama ya san hankalinsu a kwance yake kuma suna matuk’ar k’aunar juna!
Sunyi wani irin kyau sun yi k’iba sun yi fresh har wani glowing suke yi especially ma Siyaman dan in ba kwakkwaran sani ka yi mata ba ba lalle ka iya gane ta ba sannan idan baka santa ba in har ba bakinta ta bud’e ta yi maka Hausa ba to ba za ka tab’a cewa y’ar Nigeria bace ba…..
Wani k’ululun bak’in ciki tashin hankali da kishi ne ya tokare mata mak’oshi!dama tun d’azu da aka fara maganar tsayar da numfashi Siyaman kawai ta hararo…inshaaAllah ana gama na Manubiya itama za ta san yadda ta yi ta nemo nata yanzu haka ma dan ta lura tafiya za su yi Wallahi da a yau zata had’a har da nata…..
“Ya’isha sannu da zuwa!”
Muryar Manubiya ta katsewa duk su ukun tunani…ko juyawa Najeeb bai yi ba Siyama kuma haka kurum gabanta ya yanke ya d’an fad’i yayinda Ya’ishan ya d’an yi murmushi tace”yauwwa”kawai,daga haka ta yi gaba ba tare da ta san wanne a cikin flat biyun za ta shiga ba,dan ba za ta iya jurar ganin Siyama tsaye jikin Najeeb ba suna wannan rahar ta san tsaf zata iya mutuwa..shi kuma ta lura har wani sake ruk’o hannunta ya yi……
Tana wucewa Najeeb ma yace”bari su tafi”
Hakanan suka rabu Manubiya tana masa tsiya akan ‘gaskiya itadai bata gama ganin k’anwarta ba haka kurum ya zo da wuri!’
shi kuma yanata dariya.
A tsaye ta sameta gabn flats d’in dan haka suka sake gaisawa tukunna suka nufi ciki.
Ba yabo ba fallasa Ya’isha ta gaisa da kowa har Hadiza da Baraka kafin ta nemi ganin Manu in private…a ranta tana addu’ar Allah ya sa komai ya zo mata da sauk’i.
Suna shiga d’akin Manubiya ta cire hijab d’in jikinta ta linke ta ajjiye,sanye take ta wata riga y’ar kanta mai k’aramin hannu pink da hula pink mai d’an karen kyau.
Sosai Ya’isha ta ji dad’in ganin hular dan haka ta shiga tunanin ta Ina za ta fara!ya za ayi ta samu!…
Da kyar ta iya yiwa Manubiya bayanin yadda suka shirya ita da Mommy d’azu a Napep tana yi tana hawaye itama Manubiyan sai da ta yi hawaye tace mata ta kwantar da hankalinta inshaaAllah zata saka Baki a al’amarin Mommy kar ta damu itama Mommy ai uwa ce a gareta…sam bata ce zata yi komai a case d’in Yassir ba dan babu ruwanta a case d’in Yassir.
Sosai ta girgiza da ta ji ance Baba Larai ta rasu
A take ta gayawa su Inna aka kira su Mommy itama Ya’ishan aka yi mata gaisuwa sannan suka fara shirye shiryen zuwa amma sai Ya’ishan tace”ba komai su bari sai gobe”dan ta san Mommy ba ta gidan yanzu.
Hakanan shima Yash da ta kirasa ta tanbayesa yace ta bari sai gobe a ransa yana mamakin mai ya kai Ya’isha gidan su Manu!!.
Kiraye kirayen sallar Magrib aka soma dan haka duk aka tashi aka shiga alwallah ana gabatar da salla,a d’aki Ya’isha ta yi alwallah ta fito waje domin yin sallah,zuwa yanzu hanakalinta ya fara tashi dan tun d’azu Manubiya ba ta cire hula ba bare ribbom..
Sai da ta ji kamar ta doka tsalle sakamokon pink d’in hular Manu da ta hango a kan hannun kujera itakuma ta d’aura k’aton jilbab d’inta na d’azu a kanta ya rufe ko’ina tana sallah ita da Inna a gefenta.
Ba ta yi wata wata ba ta k’arasa dan parlourn babu kowa tana zuwa ta zauna a kan kujerar ta d’au hular ta danna a jaka jikinta har yana karkarwa.
Ko sallar ba ta yi ba, suna idarwa ta cewa Manubiya za ta tafi da aka tambayeta ta yi sallah tace “eh”
Ba yadda basu yi da ita akan ta tsaya ta ci abinci ba nan ma ta ce”ba komai,ta koshi”
Hakanan Manubiya ta yi mata rakiya suna fita ta samu Napep,har ga Allah sosai tausayinsu ya lullub’e manu wai yau Ya’isha ce ta zo neman alfarma a wajenta tabbas daman idan mutum ya yi hak’uri komai ya yi farko zai yi k’arshe….
Fad’an kalar murnar da Mommy ta yi da Ya’isha ta kai hular b’ata baki ne..hakanan ta yi ta sanya mata albarka…
A gabansu tsohon ya d’auko wata k’atuwar babyn roba ya sanya mata hular Manubiya a kanta bayan ya yanka kaza a kan hular jinin ya gama zuba a kai! daganan ya nemo allurai ya caccake zuciya da kan y’ar tsanar ko Ina uku uku guda d’aya kuma ya chaka a mak’ogwaronta….…haka dai ya yi ta abubuwa abun tsoro akan y’ar tsanar ya fi minti talatin,yana aiki a kan y’ar tsanar nan kafin ya nad’e ta ya tambayesu cikakkun sunayen Manubiya suka sanar maasa ya ambata sau uku tuukunna ya mik’e ya ce musu “mu je”….
Hakanan suka zagaya bayan gidansa inda yake kiwon kayan daji kala kala har da macijizai suna zuwa ya nufi wani k’aton biri kamar gunki,suna zuwa birin ya tashi daga kan dutsen da yake tsohon ya d’aga dutsen ya saka Babyn robar a k’asan dutsen ya mayar ya ajjiye birin ya koma kai ya zauna..
With full confidence ya ce musu “an gama!!.. kar ma su biya sa sai sun tabbatar an kai Manubiya kabarinta…….
Hakanan suka nufi gida ransu fess…ko da suka je su Yasira suka nemi d’aga musu hankali ce musu suka yi ba su yi abun ba Ya’isha har da rantsuwa dan haka suka yarda da su.
A b’angaren Kausar ma tana chan tana ta shirinta…akwai wata k’awarta y’ar babban jami’in tsaro mai fad’a a ji a Nigeria da kewaye da ta ga hoton baba larai itama tazo yi mata gaisuwa,
Ta yi mamakin ganin ta da ciki tsoho dan haka ta tambayeta ba’asi itakuma Kausar d’in tace”Yashjub ta aura amma har yau kishiya ta hanata tarewa”
Dan haka k’awar tata tace ta kwantar da hankalinta za ta taimaketa.. yanzu haka
Ita kanta tanada sojojin da idan ta saka suka k’ulle mutum Wallahi ba Yashjub ba ko
waye bai Isa ya fito da shi ba,yanzu abunda za a yi ta bari idan ta haihu ranar suna za su k’ullawa Manubiya sharrin sata inshaaAllah indai sojojinta suka tafi da ita ba a Isa a karb’ota ba sai ta dad’e sosai in lokacin sakinta ya yi suka ga dama sai su sakota kafin nan ita kuma Kausar d’in inshaaAllah ta gama samun Yashjub ta saka shi a corner har abada…”.
Sosai Kausar ta ji dad’in plan d’in dan haka ta bari akan sai ta haihu d’in sai ta had’a har da abunda suka shirya ita da Abbakar za su yi d’azu a yita duk a lokaci d’aya ta yadda ko bibiyarta ma Yash d’in ba zai yi ba kuma dama still akwai abunda ta shirya zata yi wa Manubiya a kan Yaron nan ma ta san dole abun ya sake zama effective…
InshaaAllah kafin ta fito ita kuma ta san yadda ta yi ta ko wacce hanya ta aure Yashjub,tunda har ga d’a a tsakani kuma babu Manubiya ta san aurensa ba zai yi mata wahala ba inshaaAllah.
Sosai ta ji dad’I hakanan suka rabu ita da k’awar tata tana ta murna ranta fess kamar an yi mata bushara da gidan Aljannah.
A b’angaren Yassir shima yanzu ya sake hawa ya koma gidan jiya..saboda da farko ya ji tsoro matuk’a amma yanzu da ya d’inke da Abokinsa ya gaya masa komai ya samu goyon baya d’ari bisa d’ari daga wajen Abokin sai zuciyarsa ta sake bushewa especially ma daya tabbatr video d’in a iyaka family yake yawo bai je ga hukuma ba tashi d’aya tsoronsa ya kau!
Kuma ya ji Mommy tana cewa sharri aka yi masa dan haka zai fake da sharrin aka yi masa ya dage har sai su Daddy sun yarda ya samu su shirya.. da ga nan zai yi mai kankat dan Abokin nasa yace”InshaaAllah zai tsaya masa zai taimaka masa su ga bayan Yashjub kuma ba za su sake tura wani ya kashesa ba!saboda kar a sake samun matsalak kamar lokutan farko! Next time kawai sakawa za su yi a d’auko musu shi su kashe sa da hannunsu.
But first ya samu ya fara wanke kansa ya shirya da su Daddy daga nan sai su k’addamar da shirinsu saboda yanzu wani abun yana samun Yash shi za a zarga.”
A ranar da daddare Ya’isha tana tafiya daga gidan su Manu itama Baraka ta je ta karb’o garin maganinta wanda za ta barbard’a ta haukatar da Inna dan yanzu tace ba za ma ta sakata jinya ba haukatata za ta yi dan sai ta fi wulak’anta idan ta haukace akan jinya.
Sam ba ta da mu da sharad’in bokan ba da yace mata”idan ta b’arbad’a abun Inna ba ta bi ta kai ba to itace za ta haukace”
Tashi d’aya tace masa “ta amince!”
Hakanan ta zube masa mak’udan kud’ad’e ta amso ta taho saboda ta san a inda za ta zuba ta yadda dole innar sai ta bi ta kai, ai abun ma ya zo mata da sauk’i tunda yace”kowa zai iya bi kawai dai ta tabbata itama Innar ta bi ta kai.Kuma awa ashirin da hud’u abun zai yi bai lalace ba saboda yana da k’arfi.”
Dan haka ta gama tsarawa a bakin k’ofar ban d’akinta za ta zuba ta san ko cikin dare ko da safe ko da rana dole ta shiga ta yi uzuri ta yi alwallah!ai Inna ta tafka babban kuskure da ta bata access da bedroom d’inta…hakanan tana ta sak’e sak’e a ranta ta iso gida jakarta kawai ta ajjiye, ta nufi cikin gidan…a nan ta samesu duk d’insu gaba d’aya har Baba ana hira,inna kuma tana zaune a kan darduma tana lazimi dan har ta yi shirin barci.
Tana shiga suka fara tambayarta ya jikin maman Abbakar d’in tace da sauk’i,daga nan ta fara rarraba ido lucky for her Manubiya tace mata”ya yi barci yana d’akin Inna,in kun zo tafiya sai in d’auko miki shi.”
Ita ba ma shi take nema ba amma daga jin hakan ko gama rufe Baki ba ta bari Manubiya ba ta yi ba ta yi wuff ta mik’e ta afka d’akin tana mai cewa”ai
yanzu za mu tafi ma bari in d’auko sa!”
Tana shiga ta tura k’ofar ta mayar ta rufe,sai da ta zuzzuba tukunna ta mayar cikin bra d’inta ta d’auki mai sunan Baban ta fito ta yi musu sallama ta tafi yau ko jiran ya Musbah ma
Bata tsaya ba…shima kuwa ya zauna sai da ya gama zancensa da Hadiza tukunna ya koma kuma da ya je ya balbaleta da masifa dan bai
san da zancen zuwanta dubo maman Abbakar da daddare ba sam ba ta tambayesa ba,sannan yace”idan Inna tana cikin d’akinta to za ta iya shiga in har kuwa ba kowa a cikin d’akin kar ta sake afka mata d’aki kamar yadda ta yi d’azu tun da d’akin ba na sa’arta bane ba!”
Saboda shi har ga Allah haka kurum bai yarda da shigar tata da ta yi ba da yanayinta na yau gaba d’aya bai yarda da shi ba.
Ga mamakinsa har k’asa ta durk’usa tace”ya yi hak’uri ba zata k’ara ba!”
Ita kuwa a ranta cewa tayi “kar ka damu,zuwa gobe mai karekan ba za ta sake samun dama ba!daganan wallahi ko
kara idan na ajjiye baka isa ka shallaketa ba.!!”.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 43
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Ya Musbah yana tafiya su Inna ma suka fara k’ok’arin shiga domin suma su samu su kwanta barci, dan Baba shi kam ya jima da wucewa d’akinsa tun lokacin da suka gama yiwa Yash da Daddy gaisuwa,ya wuce abunsa…
Hijab d’inta ta cire ta linke ta ajjiye a kan dardumar tukunna ta d’auka ta had’a ta yi folding d’insu tare ta tsaya tana kallon Hannun kujerar inda ta ajjiye hularta tun d’azu da Magrib da zata yi sallah amma da ikon Allah har yanzu ba ta ganta ba.
Manubiya ta kalla ta kalli hular kanta wadda gwaggwo Suwaiba ta basu tsarabarta su biyu iri d’aya tace”Manu hular ki ce a kanki ko?
Ni Ina tawa??”
Murmushi Manubiya ta yi tace”
Dama na sani!”sai kuma ta d’aura da cewa”ai dama kinsan Siyama tace itama kalar take so..ba ta son kalar tata ita da Jidda!
bani da tantama itace ta d’auke takin a tunaninta tawa ce na ajjiye shine ta d’auke ta tafi da ita!”.
Shiru Inna ta yi kafin tace”Anya kuwa?
Kuma inda ace ita ta d’auka ai da na san za ta ajjiye tatan..
kuma ai kafin Magrib Siyama ta tafi,ni kuma sai da na zo yin sallar Magrib d’infa tukunna na cire!.”
Cikin tarar numfashinta gwaggo Suwaiba tace”To,watak’ilan mai sunan Baba ne ya d’auka ya saka a wani wajen
,yanzu mu je mu yi barci idan Allah ya kaimu gobe da safe sai a duba!
Idan ma ba a samu ba sai in je kasuwa in siyo yadi kalarsa ai ba za a rasa ba duk ku hud’un sai in had’a Hadiza ta kai tela ya d’inke a yi muku iri d’aya,kinga an huta ai ko?”
Dariya Manubiya ta yi kafin tace”Allah ni fa Ina tunanin Siyama ce ta d’auke! ta yi tunanin tawa ce saboda fa tun da ta ga tamu(ni da Inna) tace ita za