Showing 81001 words to 84000 words out of 244445 words
sauk’a k’asan da sauri dan ta ji kamar Yashjub d’in zai fito ita kuma har ga Allah a yanzu ko fuskarsa bata k’aunar gani!zuciyarta ta gama aminta da cewa ‘ya san da zancen Kausar amman ya k’i gaya mata’
dan haka tashi d’aya ta yi concluding akan shima yana son Kausar d’in maybe dai akawai wani abu da yake b’oyewa amman dai yanada niyyar auren Kausar duba da yadda ya yi shiruu ya gagara cewa komai.Wani irin mahaukacin tafarfasa zuciyarta takeyi ita kanta ba ta san ta na son Yashjub kuma tana kishin sa irin haka ba sai yanzu da ta ji maganar aure na shi da wata
sannan kuma reaction d’in sa da kame kamen da ya hau yi mata ya tabbatr mata akwai zancen b’oye mata kawai yayi.
Kafin ta k’arasa k’asan har ta fara haki tsabar yadda k’irjinta da zuciyarta suke lugude
ga kuma sauk’an stairs.
A bud’e ta hango k’ofar dan haka ta k’arasa da d’an sauri sakamokon fara hango ahalinta da ta yi dan chan ta hango Muhsin yana fama da roba sai k’ok’arin d’auka yake yi.
Da sauri ta k’arasa ta na fita sukayi karo da su jidda dan haka ta fad’a jikinsu cikin murna da kewar su.
Sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta hana kanta kuka
dan ganin su da tayi ba kad’an ba yasa ta sake zama emotional.
Murmushi kawai suke ta zubawa suna kallon ta tana faman bin su one by one tana huggin d’insu har ya Musbah ya Nafi’u ne kawai batayi hugging ba
Daga nan ta fara jan hannun Jidda tana cewa”su shigo”ba tare da ta kalli kowa ba dan sai yanzu ta tuna yadda ta sauk’o ba tare da ta wanke fuskar ta ba…ta san tabbas idan suka yi mata kyakkyawan kallon kurilla tsaf za su fahimci kuka takeyi sai dai kuma abunda ba ta sani ba shine tan fitowa duk suka lura da hakan.
Ya Musbah ne ya tsaida ita ta hanyar cewa”ki bari ya zo ya shigar damu mana”
Dariya Siyama tayi
kafin tace “Allah ya Musbah ka iya abun dariya,”
Sai kuma ta kalli Manu tace”
Tun d’azu fa shi ya tsayar da mu wai ala dole sai Yashjub ya ce masa ya shiga tukunna zai shiga.”
Ahankali ta juyo tace
“Dan Allah ku shigo mana”.
Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah,amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”.
Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalin sa ya tashi da ganin yanayin Manubiya dan ya tabbatar da kuka ta yi kukan ma bana wasa ba dan gashi hatta kan hancinta yayi ja!……MANNUBIYA
(Book 2)
Page 23
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Ahankali ta juyo tace
“Dan Allah ku shigo mana”.
Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah,amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”.
Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalin sa ya tashi da ganin yanayin Manubiya dan ya tabbatar da kuka ta yi kukan ma ba na wasa ba dan gashi hatta kan hancinta yayi ja!……
Anan parlourn k’asan suka nemi guri suka zazzauan
tukunna su Jidda suka shiga gaida Yashjub cikin girmamawa da mutuntawa.
Da kulawa ya amsa yana tsokanr Muhsin da d’an lukuti
kafin ya amsa gaisuwar Aisha da y’arta daganan suka gaisa cikin mutunta juna shi da su Ya Musbah.
Yunk’urawa Manubiya ta yi tace “bara ta kawo musu ruwa” da sauri Ya Musbah yace “A’a sauri fa mukeyi”
Aisha ce ta kalli Yashjub tace
ga gara nan mun kawo da kayan zak’i,Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya.”
Murmushi Yashjub yayi kafin yace”kun dage dai Aisha,har da wannan wahalar itama?. wannan fa duk bidi’a ne”
Sai kuma ya ce”An gode!haka ake cewa ko?”
Ya yi musu tambayar yana kallonsu.
Duk dariya sukayi kafin su fara mik’ewa da niyyar tafiya,da sauri yace”Au wai dama da gaske kuke?tafiya da wurwuri haka kamar ana korar ku?”
Wayar sa ce ta d’auki k’ara dan haka ya yi excusing kansa ya matsa gefe domin amsa kiran Mommy.
Yana wucewa Manubiya ta d’ago kai ta kalli Aisha wadda har yanzu bata zauna sosai ba tace”Wai da gaske tafiya zakuyi haba mana”
Ta fad’i hakan kamar zata fashe da kuka.
Murmushi Aisha ta yi ta na shirin yin magana muryar ya Musbah ya katseta jin yana cewa”Manu, kuka kikayi ne?”
Saida ta sunkuyar ta kanta k’asa na d’an lokaci tukunna ta d’ago ta kalle sa tace “A’a”
Sai kuma hawaye sharr suka b’alle mata a take kamar an kunna famfoo.
Cikin rashin jin dad’i Aisha tace
“Kinga dalilin da ya sa mukeson tafiya kenan!
Yanzu dan Allah in ya dawo ai sai yayi tunanin mu muka ce wani abun ko.Taya zaki sa kuka haka
So kike ki janyo mana bak’in jini?”.
Zuwa yanzu Ya Musbah ya tamke fuska tamau tsabar takaici!duk rashin hak’urin Baraka sai da ta yi wata goma sha d’aya a gidansa tukunna ta fara kuka a ranar sunan mai sunan baba dan ba’a yanka mata rago da tunkiya ba instead an yanka iyaka rago.
Amman shi kalli k’anwar sa ko sati d’aya ba ta yi a gidan miji ba amma har ta fara kuka!ba ma hawaye ba.
A hankali ya mik’e ya k’arasa inda take ya zauna a gefenta
yana jin tsananin tausayin ta yana ratsashi,cikin nutsuwa ya bud’e bakinsa ya fara magana”Manu ko ma menene ya faru ki yi hak’uri kinji ko?ki daina kuka,
haka auren yake sai hak’uri..”
Ajiyar zuciya Ya Nafi’u wanda ya ke shirin tsaida Ya Musbah ya sauk’e dan a tunanninsa tanbayar ta Ya Musbahn zai kuma yi akan ‘mai akayi mata’
amman sai yaga yayi lissafin manya dan haka ya d’an ji
sanyi aranshi saboda shima ba kad’an ba ya ji ba dad’i game da yanayin da suka tadda Manu d’in a ciki.”
Dakyar Ya Musbah ya sake cewa”Mun so mu d’an zauna amman kukan nan naki ya koremu”
Da sauri ta dag’o kanta ta shiga goge hawayenta tana cewa “Allah na daina”
Murmushi yayi yana mai jin inama ace yanada ikon da zai iya goge mata koma wanne irin takaici ne yake addabar zuciyarta haka.Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”Next time idan mun zo sai ki yi k’ok’arin k’in yin kuka ko?idan har ba ki yi ba sai mu zauna,kin ji?”
Ya fad’i hakan cikin d’aga mata gira d’aya.
Dai dai nan Yashjub ya k’araso wajen, tun d’azu ya gama waya da Mommy amman ya kasa komawa wajen su..tun da yake bai tab’a jin kunya da nauyi irin wannan ba,dan tun d’azu tun da ya d’ago ya ga Manubiya tana kuka ya ji wata kalar kunyar ta da nauyin su Ya Musbah sun yi masa kawanya.He’s not supposed to make her cry,ever!.
Yana k’arasowa Ya Musbah ya mik’e ya k’arasa inda yake ya mik’a masa hannu,da kyar
duk su biyun suka k’ak’alo murmushi kafin Ya Musbah yace “Kayan suna varender anan muka jere su ,mun so mu shishshigo da su har kitchen mu d’an zauna to amman wannan shagwab’abb’iyar matar taka ta kore mu…daga
ganin mu ta hau kuka.
Bara mu wuce
Allah ya sanya alkahairi.”
Wani abune ya tokare k’irjin Manubiya ganin yadda duk cikinsu babu wanda ya damu ma ya tambaye ta me akayi mata sannan kuma bama za su tsaya ma ta gansu sosai su yi hira ta d’an ji sanyi ba,har zasu tafi..ga kuma kishin Kausar da zuwa yanzu haka kurum ta ji ya sake turnik’e ta
dan haka kawai sai ta mik’e da kyar ta je ta yi hugging su Siyama tace “na gode”
daga haka ta wuce sama da sauri mai kamar d’an gudu dan
bataso ta sake sakin wani kukan a gaban su kar su ce sun fasa dawowa next time d’in ma gaba d’aya.
Tun kafin ta kai ga k’arasawa d’akin nata ta saki kuka.
Yashjub ne ya rakasu har mota yana ta musu sannu da godiya da basu sak’on gaisuwa a Baba da Inna,dauriya ce kawai yake yi dan gaba d’aya jin sa yake wani iri duk ba da’di.Sai da ya ga fitarsu tukunna ya kira masu gadi yace su shigar da komai ciki.
Kasa tsayawa ya yi har su gama,hakanan ya barsu anan k’asan ya nufi d’akin Manubiya ransa duk a jagule…ya lura bayan cin fuskar da su Yassira suka yi wa Manubiya da kuma zancen Kausar tabbas akwai shagwab’a da tab’ara a lamarin ta,ya san sai ya yi lallashin da gaske tukunna za ta sak’k’o…gashi Mommy ta kira sa tace “ya zo shi da Manubiya yanzun nan!…..”
Kamar d’azu yanzun ma a zaune ya same ta a bakin gado
tana kuka.
A hankali ya k’arasa inda take ya durk’usa a gaban ta….shi fa bai iya lallashi ba wallahi bai ma san ta Ina zai fara ba!.
Tun lokacin da ya durk’usa a gaban ta gaba d’aya sai ta ji ba dad’i!no mattar what komin takaicin da take ji bai kamata ta bar sa ya d’urkusa haka da sunan bata hak’uri ba dan ta san hak’urin zai bayar.
A hankali cikin sharar hawaye tace”Ka tashi,ba kuka nake yi ba”
Murmushi yayi kafin ya ruk’o k’afafunta ahankali yace “Dan Allah ki yi hak’uri…”
Da sauri ta zamo daga kan gadon ta fara k’okarin kwace k’afar ta tana cewa”Ni dai dan Allah ka daina!babu kyau.”
Y’ar guntuwar dariya ya yi yana kallonta yace
‘’babu kyau miji ya bawa matar sa hak’uri?’’
Cikin tarar numfashinsa tace
‘’A’a babu kyau ka durk’usa kamar haka,dan Allah ka daina kana sakawa Ina jin ba dad’i”
Ta fad’i hakan tana mai goge ragowar hawayen da sukayi saura a fuskar tata.
Cikin kwabe fuska tare da kwaikwayar muryar ta yace
“To ke ba ki san babu kyau ki yi ta kuka kina d’aga min hankali ba?sannan kalli fa a yadda su Siyama suka tafi na san duk hankalin su a tashe yake za ayi tunanin ko har na fara cutar da ke ne tunda daga ni sai ke a gidan.Ni addua ta d’aya ma kar su gayawa su Baba”.
Shiruu ta yi tana sauraron sa
ganin haka yasa ya matso kusa da ita sosai ya tallafo fuskarta a tafin hannun sa yace “Hawayen ki tsada gare su,dan Allah dan Allah Baby ki daina saurin zubar min da su
kalla idanunki gaba d’aya kin wahalar min da kanki ba tare da kin tsaya kin ji kan zancen ba ma.”
Shiruu ta yi kawai ta kasa cewa komai,haka shima yayi shiru ya zubawa kyakkyawar fuskar ta ido…kad’an kad’an ta ji yana matso da fuskar ta ta garesa yana d’an murza gefen kumatunta,ta san inda ya nufa shiysa ta yi saurin mik’ewa ta juya masa baya tana kallon gadon tana mai gyara d’aurin dankwalinta.
Lumshe ido ya yi ya bud’e kafin ya mik’e tsaye ya na kallonta,lokaci d’aya ya saka hannu ya yi hugging nata tsantsan ta baya a hankali ya d’aura kansa a kan dokin wuyanta yana mai shak’ar k’amshin jikinta mai sanyaya zuciya had’i da dimauta sa a ko da yaushe.
Cikin tsananin mutuwar jiki ya ce “ki yi hak’uri ban gaya miki asalin maganata da Kausar ba
dalili kuwa shine a time d’in da na ji maganar sam ban dauk’i abun serious ba shiyasa kikaga ban saka shi a fannin da yake important na rayuwata ba.Dukkannin abunda na gaya miki kika sani game da ni tou shine important duk abunda kika ga ban gaya miki ba tou bashi da amfani shiyasa amma naga kamar rashin gaya miki maganar Kausar d’in yana neman janyo wani labule a tsakanin mu wanda ba zan bada k’ofar hakan ba.”
A hankali ya juyo da ita yana facing d’inta rik’e da k’ugunta ya fara zaiyyano mata yadda ranar ya ji Kausar tana gayawa Mommy ‘tana sonshi’
sannan ya d’aura da cewa”Wallahi Wallahi apart from Kausar d’in da Mommy sai kuma Yahanasu da ya gayawa sam shi bai ma san wani a ciikin su Yassira ya san zancen ba,bai san maganar ta je kunnuwansu ba ta yadda har suke tunanin zai aureta,shi a mazaunin shirme da rashin tunani ma ya d’auki maganar tata shiyasa bai bawa abun importance ba.Amman yana so ta yi masa alfarma d’aya!’ta manta da komai da kowa
ta yi trusting d’insa akan abunda zai fad’a mata yanzu
‘Tun yana Yaro shi tsarin mace d’aya garesa kuma Kausar is the last parson da zai iya aura
saboda kwata kwata jinin sa bai d’auke ta ba tun yarinta,
ko da ace su biyu ne kad’ai suka rage a duniya ba ya jin zai iya rayuwa da Kausar a matsayin matarsa’….’’
A hankali Manu ta sunkuyar da kanta tana jin wani sanyi da nutsuwa yana lullub’eta dan tabbas maganganun sa sun rufe kusan kaso arba’in na damuwarta zuwa yanzu ta fahimci ba b’oye mata yayi ba.
Dukda tana fargaba da kuma kishin yadda Kausar d’in take son Mijinta amman still ta d’an ji sauk’i da ya fito ya gaya mata komai,sannan she has chosen to trust him akan lamarin,kamar yadda ya buk’ata.
Cikin son sake kwantar mata da hankali ya d’ago da fuskarta yana mai kallon kwayar idanunta yace”Mannubiya ce kad’ai a cikin zuciyar Yashjub!Ba ki san yadda kika tare gaba da baya ba shiyasa kike wannan tunanin amma inda ace kinsan yadda kikayi bake bake a cikin zuciyata da ko ni da kaina in nace miki zan k’ara aure ko zan kula wata na san ba za ki tab’a yarda ba
I love you only you no one else!
So idan ma akwai wani tunanin zan auri wata ko zan kula wata a ranki gara ma tun wuri ki cire
saboda wahalar min da zuciyar ki kawai kike yi
as far as I know u are the only one for me kuma na san su Daddy ba za su tab’a yi min auren dole ba
So..pls Baby! ki daina b’ata ranki…um?!..”Ya k’arashe maganar ta sa cikin sa hannu ya janyota jikinsa sosai kafin ya d’aura da cewa” ko amarci na ma ban fara ci ba har Amarya ta fara shiga damuwa ta fara fushi da ni,Pls ki daina Plssssss”ya fad’i hakan kamar zai fashe da kuka yana sake sakata a jikinsa.
Shiruu Manubiya ta yi a ranta tace”au bai ma fara cin amarcinba a hakan…”
Tana wannan tunanin ta ji yanayin nasa yana shirin sauyawa dan haka ta d’an yi y’ar dabara ta goce dakyar tace”Ya wuce fa!
Ni ba fushi na yi ba kuma na daina kukan ai”
Cikin sake ruk’ota yana dariya dan ya fahimci zillewa ta ke son yi yace”ba wani nan!fushi kikayi mana bayan k’iri k’iri d’azu aka yi denying d’ina kiss yanzu kuma hug anjima kuma Allah kad’ai ya san mai za a hanani…”
Da ga haka ya janyota ya fara aika mata da sak’onninsa ma su zafi da tsada……
Addua ta fara yi Allah ya kawo mata ceto dan a yadda ya fara sakin layikan nan ta san k’aniyarta za ta ci.
Allah kuwa ya amsa adduar ta dan tashi d’aya wayar sa ta fara k’ara…sai da aka kira har sau biyu bai kula ba jin kiran yak’i k’arewa ne ya sa yace”Ohh God!”kafin dakyar ya samu ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kashewa amman sai idanuwan sa suka hango masa sunan Mommy b’aro b’aro…shi fa sai yanzu ma ya tuna da neman nasu da takeyi wallahi shaf ya manta…sai da ta tsinke ta sake kira tukunna dakyar cikin k’ok’arin daidaita muryarsa ya d’auka ya ce”Mommy gamu nan zuwa”
daga haka ya kashe wayar ya kalli Manu yace”Bamu je ba gashi Mommy har ta fara neman mu,kece kika k’i ki warke da wuri shiyasa mukayi letti”ya fad’i hakan yana dariya k’asa k’asa yana mai sake kissing d’inta tukunna ya mik’e da kyar….
Yasan idan suka zauna a d’aki d’aya suka ce za su shirya ba za su yi sauri ba,gashi ya d’an jiyo fushi a muryar Mommy
hakan ya sanya ya ce mata”ta shirya da wuri bari shima yaje ya shirya”
Daga nan ya koma ya sake kissing nata daga haka ya fice da sauri dan ji yakeyi kamar akwai wani magnet d’in da yake jansa gareta.
Yana fito ta sauk’e ajiyar zuciya had’i da ta’a’uzi dan tashi d’aya taji wani tsananin kishi ya lullub’e ta sakamokon tuno wa da tayi zata had’u da Kausar idan taje gidan.
Cikin nutsuwa tana ta korar shed’an a hankali ta shiga shiryawa…wanka ta fara yi tukunna ta fara d’auko kayan da za ta saka.
A ganin ta gidan surukai za ta je shiyasa ta yanke shawarar saka kayan da suka yi mata a cikin lefe ta san in suka ga ta saka za su ji dad’i kwarai.
Wata dandatsetsiyar atamfar exclusive ta saka kalar royal blue da ratsi ratsin silver da red an zuba mata d’inkin riga da skirt na zamani da sukayi asalin amsarta…ita kanta tasan d’inkin ya fito da ita ras matsalar ta d’aya yadda d’inkin ya matseta rabin k’irjinta a waje sannan skirt d’inma ya kamata ga waist d’in ya fito sosai shima…d’inkin ya fito da surar jikinta gaba d’aya.
dama tun jiya da ta zo zab’ar kaya ta lura da yanayin d’unkunan gaba d’aya sun yi fitting dayawa,gaskiya idan ta samu lokaci zata ce su mayar musu a dan bud’a mata dan ba zai yiu a kashe uban kud’i ba kuma a yi mata d’inkunan da ranta bai so ba….
Dama tanada abun d’auri na ture kaga tsiya dan haka ta d’auko ta saka a cikin dankwalin nata ta ajjiye kafin ta koma gaban madubin ta d’auka powder ta shafa ta saka eye liner ta d’auko lipstick ta shafawa labb’an ta.
Ita kanta tasan tayi kyau irin sosai d’innan..murmushi ne ya sub’uce mata ta san Yash yana shigowa zai hau mita yace mugunta ta had’a masa dan ta san ba zama za suyi a gidan ba shiyasa ta chab’a wannan uwar kwalliyar.A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya tana jin tsantsar k’aunar mijin nata tana sake shiga jikin ta tana ratsa ko’ina.
Tana tunanin sa tana murmushi ta shiga tufke gashin kanta a ta baya chan k’asa ta kanainaye sa ta saka d’an siririn ribbom black gudun kar ya sunce daga nan ta d’auko dannkwalin data saka abun daurin a cikin ta d’aura sa perfectly.
Saida ta san yadda ta yi ta b’oye uban tulin gashin ta da ya fito ta k’asan d’aurin tukunna