Showing 186001 words to 189000 words out of 244445 words
sai an gama komai
Junior wuce nace ka je ka d’auko kit ka dawo yanzun nan!!.”
Ta fadi hakan cikin dakawa Junior tsawa.
Juyawa ya yi ya fice a take.
Junior bai dawo ba suna tsaye su Daddy suka sauk’o dan sai da suka tsaya suka d’an yi magana concerning kiran da Hajiya Mama ta yi tukunna suka sauk’o.
Basuyi mamakin ganin gaba daya y’an gidan a k’asan a
tsaye cirko cirko ba!saboda dama tunda Hajiya mama ta kirasu sunsan case ne.
K’arni da wari ne ya daki hancinansu wanda hakan ya sa suka fara waiwaye..ba abunda Yashjub ya tsana irin amai shiyasa idanunsa suna kaiwa kan aman ya fara kwala kiran mai aikinsu..Tana chan ciki shiyasa sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna suka fito tare itada gwaggwo.
Aman ya nuna musu sai a sannan tukunna hankalinsa ya kai kan Kausar wadda ke tsugunne a wajajen ita da Yassira tana hawaye.
Gabansa ne ya ji yayi wani irin mahaukacin bugawa..Adduar sa d’aya Allah ya sa ba Kausar bace ta yi wannan aman!
Ba ya buk’atar Kausar ta yi koda ciwon Kai ne bayan abunda ya faru tsakanin su
Dama yayi tunanin hakan
tun a ranar amma gudun janyowa Kai tashin hankali da masifa ne yasa kawai ya banzatar da tunanin ya kawar da shi ta k’arfi da yaji.
Yana wannan tunanin k’irjinsa yana wani irin bugawa
Junior ya shigo rik’e da first aid box.
Ahankali Daddy da Abhi
suka k’arasa inda suke,suna shirin yiwa Hajiya mama magana tace”Na kiraku saboda wani case daban amma yanzu bari mu fara yin wanda yake a gabanmu emergency!!!……Y’ar ruk’on gidan ka!
Ciki ne da ita a karo na
na tabbatar ita kanta ba ta san adadin ba.
Su Khadijah na san watak’il duk sun san da zaman cikin dan ana cewa a yi mata test
suka gigice.
Wai har ni suka fara k’ok’arin yi wa wayo tsabar raini.
Anyways Junior!!”
Ta fad’i hakan tana kallonsa kafin ta d’aura da cewa”
Ga first aid box!
Ga kausar!!
Ga ciki!!!
Ga jini a jikinta da za a d’auka
a gwada.
Banaso inji kowa yace Uffan!!
har sai an gama test d’innan.
Tunda Yashjub yake a rayuwarsa bai tab’a jin mutum yana tsaye kyam amma ji da ganinsa sun d’auke ba lokacin guda tsabar fargaba sai yau!…da kyar ya samu ya fara gani
amman fa still dishi dishi ya ke gani!.
Shi da kanssa ya yiwa Kausar iyakar fita k’asar waje da yawo
anyhow,har passport d’inta ya kwace da kyar aka samu ya bata
Gashi ta nuna kuma tace
bata son Yassir dukda ya fahimci kamar ba su rabu duka ba amma ya san ba za ta kula shi ba besides in ba ma ta dalilin ciwon nan ba ya san ba sa fita tare
He makes sure of that kuma ba ta zuwa side d’insa
sannan ko su suka kawo Iskanci duniya ya san ba za su
yadda su yi wani abun anan
sama inda d’akinta yake daff da na su Mommy sannan a tsakiyar su Yadira ba…..
Durk’usa Junior ya yi
Abunka da consultant
Idanuwanta tafin hannnunta
da bayan kunnenta sai k’eyarta kawai ya duba ya tabbatar da tana d’auke da ciki.
Sai yanzu ya fahimci komai tun daga kan incidence d’in 2 weeks ago zuwa message d’in da Yassir ya yi masa yanzun daga fitarsa kafin ya shigo..a tak’aice dai Yassir ya dirk’a mata ciki kuma suna so su ce na Yashjub ne tunda A message d’in Yassir cewa ya yi yace cikin 2 weeks ne exact!.
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ya shiga ambata a cikin ransa saboda ya san tsaf Yassir zai yi abunda yace masa zai yi a cikin message d’in muddin ya k’i bin umarnin sa shi kuma ba ya so a had’a Kai da shi a cuci Yashjub.
D’agowa ya yi a hankali ya kalli Yassir d’in wanda shima shi d’in yake kallo,bai gama nazartar sign d’in da Yassir d’in yake yi masa ta ido ba ya ji Hajiya Mama tace”ya dai???”
Tabbas Yassir ya ji masifar dad’i da farko da ya ji ance Junior ne zai yi test d’in amma
kuma yanayin sa yanzu sai ya fara bashi tsoro ya shiga tantama a kan anya kuwa zai yi yadda yace masa ya yi???
Numfashi Junior ya fesar
kafin ya kalli Hajiya mama
Yace “Bara inyi confirming..”
“Ciki ne ko?”
Tayi mishi tambayar tana matsowa kusa da su kafin ta
kalli Kausar wadda itan ma Junior take kallo tana yi masa sign ta ce”Wallahi yau sai..”
Cikin katseta Junior yace
“I’m not sure yet,bara mu yi test dai.”
Flat Junior ya ce Kausar ta kwanta ya d’auki wani abu ya d’aura mata a kan mararta sannan ya ld’auko y’ar k’aramar allura ya huda tomb d’inta ya d’auki drop d’in jininta a kan PT.
Sunayen Allah kawai Yashjub yake karantowa dukda sanyin standin Ac guda hud’u da
suke kewaye da makeken parlourn hakan bai hanasa
jik’ewa da gumi ba.
Ahankali Daddy wanda shi kansa ya sha jinin jikinsa ya juya ya kalli Yashjub..Hatta Abhi sai da ya ji tausayin Yash wanda unlike Hajiya Mama shi Daddy ya riga ya gaya komai,sun san ba da sanin sa hakan ta faru ba kuma sun san tsanar da yake yiwa Kausar shiyasa gaba d’aya tausayin sa ya lullub’esu.So suke yi su ce wani abu a samu a fasa wannan gwajin
Amman suna tsoron Hajiya mama kuma ko da ace sun hana d’in in dai akwai ciki kuma na Yashjub ne tou fa dole za a gani kuma za a fahimta sooner or later.
Wayar Junior ce tayi k’ara,bai kula ba saboda ya riga ya san Yassir ne…
Tashi d’aya pT d’in ya nuna Kausar tanada ciki kuma yadda result d’in ya fito da wuri ya nuna hakan ya sa ya fahimci cikin ya dad’e a jikinta.
Abunda ya ke gwadawa a cikin nata yakeso ya samu ya k’arasa dan ya tabbatar kuma yaga ko zai iya kintata adadin kwanakin cikin….
Kamar ance ya d’ago hakanan ya sake d’agowa suna had’a ido da Yassir ya kallesa ya nuna masa aljihunsa inda wayar sa take da sauri.
Sunkuyar da kai Junior yayi yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa ba ya so ya d’aurawa Yashjub laifin da ba nasa ba sannan ba ya so asirinsa ya tuno dan ya san muddin Yassir ya nunawa Daddy da Yadira da su Hajiya Mama video d’in nan Yadira ba za ta tab’a yarda ta auresa ba su Abhi kuma bayanta za su bi ga kuma kunyar da zai kwasa……
Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya zaro wayar sa a aljihu..tashi d’aya gabansa ya yanke ya yi wani irin mahaukacin fad’uwa sakamokon video d’in da ya ga ya turo masa yace”incase idan yana tantama kamar yadda ya turo masa hakanan zai turawa duk wani wanda yake a family d’insu..”
Ko bud’ewa bai yi ba ya riga ya gani ya san shine da sauri ya kashe wayar yana wani irin haki ya mayar aljihu.
“Me kake yi da waya ne haka junior?abun bai yi ba?”
Muryar Hajiya Mama ta katse sa.
Cikin d’an diriricewa ya d’ago ya kalleta yace “time nake dubawa”
Daga haka ya mayar da kallonsa ga abunda ya d’aura a kan cikin nata ya d’an yi shiruu kafin ya sa hannu ya d’auke dan ya kammalu ya mik’e tsaye…
……
Tsayawa ya yi ya k’urawa abun ido kamar mai son fahimtar wani abu nan kuwa ba su san tunani yake yi ba.Ya riga ya fahimci abun ta inda yake indicating cikin jikin Kausar zai iya wuce watanni biyu a jikinta…
Gashi ance yace cikin satinsa biyu if not ya san me zai biyo baya!
Zuwa yanzu tabbas bai san abun yi ba.
“Junior ka yi shiru ka k’ank’ame abubuwa ba ka fad’i sakamako ba.”
Muryar Hajiya mama ta katse masa lissafi.
Ahankali ya d’ago ya kalli kowa
kafin yace
“She’s pregnant!”
“Yauwwwa!!ai dama na sani”
Hajiya mama ta fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai yayinda gaba d’aya parlourn akace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
kamar an yi rasuwa
Har su gwaggwo dasuka lab’e a bakin corridor d’insu chan gefe.
Wani irin karkarwa jikin Yashjub ya fara yi..
Tunda ya shigo ya ma kasa k’arasawa cikin parlourn ganin yana shirin zubewa ya sa ya ja kujerar dining ya zauna ya dafe kansa.
Yana sake karanto sunayen Ubangiji.
A ranshi yana “Ya Allah ka san yadda na ke k’in Yarinyar nan
ka san yadda na tsani zina Ya Allah ka sa ba zan haifi shege ba Ya Allah ka kawo mini sauk’i da mafita.
Ya Allah Ina son Manubiya ban san ta ina zan fara yi mata bayani in fara bata hak’uri wannan karon ba..Ya Allah ka sa wannan cikin ba nawa bane ba.”
Dan har yanzu bai cire hope ba
Tunda ta tabbata ciki ne da kausar to yanzu yake son sanin sanin adadin kwanakin cikin…
Kamar Daddy ya san meye a ransa hakanan shi da Abhi suka matso kusa da Junior Abhi ya d’an juyo da shi a hankali gaban Daddy yana fad’uwa dan bai san ta ina zai fara had’a jini da Kausar ba..yana murna Yassir ya tsallake rijiya da baya yanzu kuma ace innocent Yashjub d’insa ne a ruwa…tausayinsa ya ke ji matuk’a dan tun d’azu ya lura da halin da ya shiga…
Ahankali ya kalli Junior yace
“Zaka iya aunawa?,kwanakin?”
Dan a yanzu bashi da wani burin da ya wuce ya ji ance cikin nan ya fi sati biyu…
Sai da Junior ya juya ya kalli Yassir wanda ya ke yi masa wani kalar murmushi,Dan tunda ya tura masa last message da video ya lura tarkonsa ya kama kurciya..
Had’e fuska Junior ya yi ransa a b’ace hankalinsa a tashe ya kalli su Daddy yace”Eh amfanin abun nan da na d’aura mata ma a cikin nata kenan,new invention ne….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 37
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Gyaran muryar da Yassir ya yi ne ya sanya Junior ya yi shiru ya juya ya kallesa….signal ya yi masa kawai ya nuna masa Yadira da ido daga haka ya sunkuyar da kansa bai sake yin komai ba.
Wani irin kallon fusata da takaici Junior yake jifansa da shi ya had’e rai da fuska kafin da kyar ya janye idanunsa daga kan Yassir d’in ya juyo ya kalli su Daddy yace”bai bayarda exact weeks ba amman a yadda na fahimta da k’irgen da na yi banajin ya fi 12 days gaskiya…”
Ajiyar zuciya Kausar da Yassir suka sauk’e a b’oye yayinda Daddy ya d’an tafi Luu zai fad’i
Abhi yayi saurin ruk’o sa.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ummi tace sai kuma hawaye
domin itama tun d’azu da ta lura da yanayin Yashjub wani mugun mugun tausayinsa ya lullub’eta,yanzu kuwa ana fad’a yadda ya mik’e ya nufosu yana tangad’i dole ko waye ya ji tausayinsa….ta san ciwon ka zamo responsible akan abunda baka da masaniya a kai baka kuma da ikon chanjawa…
Yana zuwa a hankali ya shiga tsakanin Daddy da Junior ya rik’e kafad’unsa yace “Junior tsakanin ka da Allah,cikin nan 2 weeks ne??”
Shiruu Junior yayi yana ji kamar ya kurma uban ihu…..wani irin tausayin Yashjub da tsanar su Kausar had’i da bak’in cikin mai tafe da tashin hankali ne suka rufar masa a lokaci guda.
Tabbas Yashjub bai yi deserving haka daga garesa ba amma kuma ya zame masa dole shima ya tsayawa kansa……
Ahankali ya ji Yashjub d’in yace
“Ba haka bane ba ko?
Cikin ya fi 1 month ma I’m sure of it.”
Da kyar Junior ya bud’e bakinsa yace “Am
Yashjub…cikin nan bai wuce 12 weeks ba I’m sure of it dan na gwada yadda ya kamata kuma wannan abun ba ya k’arya sabon shig….”
Wata wawuyar shak’a
Yashjub ya kaiwa Junior cikin tsananin b’acin rai yace
“Ya za ka ce abun nan baya k’arya?k’arfen nasara ne f!
k’arya yake yi bashi da tabbas,ba gaskiya ya fad’a ba!!”.
Sai kuma ya juya ya kalli Daddy yace
“Daddy,I’m not responsible
i….”
Shiruuu ya yi ganin yadda gaba d’aya mutanen parlourn suka tsura masa ido…a hankali
ya lumshe idanunsa yana jin
duniyar tana juya masa kafin da kyar ya d’aga k’afarsa kawai ya juya ya fice da mugun sauri…bai tsaya a koina ba sai side d’insa na da dan bai shirya fuskantar Manubiya a haka ba.Yana shiga ya zube a kan kujerar parlourn ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro.
Yashjub yana fita, Hajiya Mama wadda tunda aka fara maganar kwanakin cikin da taga yadda Yashjub ya yi ta shiga tsananin tashin hankali! tace”kun dai san
Ina da buk’atar a yi mini bayanin komai ko???
Dan kaina ya d’aure tamau tun d’azu kuma zuciyata ta k’i yarda da lissafin da kwakwalwata ta yi
considering
reaction d’in Yashjub.”
Tayi maganar tana kallon su Daddy.
Ahankali Mommy wadda ta fara crocodile tears ta matso kusa da ita tace”kar ki ga
laifin Kausar kuma kar ki ga laifin Yashjub”
Cikin katseta da tsawa Hajiya mama tace”A’a!!!!
A’a sam ba na son jin wannnan maganar!
Bana son jin maganar k’azamiya Kausar da kamulalle Yashjub a waje d’aya,ba na so!
Tun wuri ma ku nemo wani sharrin ba wannan ba!
Ku fad’a mini gaskiya in je in samesa in yi masa bayani dan na san yadda ya yi d’innan da kuma abunda kike shirin fad’a mini dole akwai abuunda kukayi wanda ya sa yake zargin wannan shegen cikin nasa ne!”
Ahankali Daddy wanda yake ji kamar ya fashe da kuka yace
“Hajiya mama mu je sama in yi miki bayani”
This time around zabura Hajiya mama ta yi tace”Au kaima??sharrine fa!kar ka yarda da makirci sharri da asiri…ba batun wata Kausar da Yashjub
ba ma naso in ji wannan batun
kawai ku gaya mini gaskiya
Inje in fad’a masa a samu ya bar d’aga hankalin sa a aikin banza..”
Ahankali Abhi ma ya matso yace “Hajiya Mama muje
mu yi miki bayani wannan duk b’ata lokaci ne!
Ki tsaya ki ji komai dan Allah….”
Shiruuu ta yi kafin ta juya ta shiga watsawa Kausar wani kallon tsana!…..Hajiya mama ji take inama ace babu zunubi wallahi yau da sai ta kashe Kausar
A nutse za ta shiga kitchen ta d’auko wuk’a ta b’oye a cikin rigarta ba za ta bari kowa ya gani ba sai ta zo daff da ita tukunna za ta zaro ta lulluma mata….
“Mu je Mama”
Muryar Daddy ta katse mata tunanin da take yi.
Juyawa kawai ta yi ta nufi sama
Sai a sannan su Mommy suka d’aga Kausar suka nufi saman da ita.
Yahanasu da Ummi kuma suka bi bayan Yashjub…sun jima suna knocking kafin ya bud’e yace musu”ba komai kar su damu yana buk’atar hutu!”
Yahanasu za ta sake yin magana yace”plss”kawai.
Dan haka Ummi tace mata “su je su barshi ya huta d’in.”
Daga haka ta ja Hannunta suka wuce suna masu jin tsananin tausayin Yashjub d’in.
Suna kai ta d’aki Mommy tace
“Kowa ya fita!ta na son za ta yi magana da Kausar.”
Suna fita Kausar d’in ta mik’e tace”Ina buk’atar zan watsa ruwa,jikina ya b’aci da amai.”
Cikin fushi Mommy ta ruk’o ta tace”ba fa ki isa ba
Kausar!!!
Wallahi sai kin gaya mini gaskiyar lamari..although na riga na sani but inaso in ji da ga bakinki”.
Kallonta Kausar d’in ta yi na y’an dakik’u kafin ta fesar da numfashi tace”Days ago bakya ko kulani fushi kike yi da ni!
So banga dalilinki na titsiyeni akan sai kin ji ta bakina ba!.
Ai Ina ce haushina kike ji?
Kin gama rayawa kanki abunda zuciyarki ta aiyyana miki a kaina,ko ba haka ba?
To me kuma ya faru yanzu
da kike son jin ta bakina? kawai inaga gara ki ci gaba da believing abunda zuciyarki ta baki.”
Kausar ta dire aya
cikin tsare ta da idanuwa kafin ta ci gaba da cewa”Besides ai gashi kin ma ce kin riga kin sani so meyasa kike so ki ji a bakina?ko dai Baki sanin ba?”
Cikin fushi Mommy tace
“Kausar na san ki ciki da waje
na san komai!ba ri ki ji in gaya miki abunda ya faru abunda
kuma kika shirya kike so ya tabbata!
…Na san
Magani ko kuma wani abun kika shakawa Yashjub
a ranar da aka ganku tare ke da shi.A wannan ranar abunda ban fahimta ba shine dalilinki na yin hakan gashi na san mun riga mun gama magana a kan zamu san yadda za a yi ki aureshi.
Yanzu kuwa na fahimta
Dama burinki ki samu ciiki
saboda ki aureshi kenan ko?
Bima’ana dai idan na fahimceki da kyau
baki gama trusting d’ina ni da Baba larai ba!shiysa kikaje kikayi gaban kanki
Shiyasa kike ta faman b’oye mini ki ka k’i gaya min komai….
Hakane ko ba haka ba??”.
Ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e
kafin ta matso kusa da Mommy sosai tace”Mommy
Taabbas na san Yashjub a buge yake a wannan ranar
Maybe daga office ko wani wajen ko asibiti
wata ta so taci galaba a kanshi
Allah bai yi ba ya dawo gida da wuri abun ya fad’a kaina…dan ni dai da hannuna ban shak’awa ko na sakawa Yashjub komai ba.!
Na san kin daina yarda da ni kuma kin daina trusting d’ina
amman tabbas idan kika yarda da abunda nake fad’a miki yanzu to za ki ji dad’i za kuma ki samu salama saboda hakan ne gaskiya
Ban bawa Yashjub komai ba
ban zuba masa komai ba
sannan ba plan d’ina bane in samu ciki da shi wannan tsarin Ubangiji ne.
Ko a gaban waye hakan zan fad’a tunda hakan ne gaskiya
Ruwan ki ki yarda
Ruwanki karki yarda..ba damuwa ta baceba
kawai dai Ina takaicin cewa
kin daina yarda da ni sannan kin daina so na.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta shige toilet da sauri a ranta tace”komin lalacewa na san Yashjub d’anki ne…ba zan bayarda k’ofa a kowa ba banda Yassir har sai na ganni a d’akin Yashjub zaune a matsayin Amaryarsa.
Yadda Yashjub ya gigice d’innan tsaf za ki tausaya masa shi kuma na san in dai ya ji wani abun to ba zai yi takin step d’in da nake shirin d’auka next! serious ba…
Mommy ta dad’e tsaye a dakin
tana tunani amma kwakwalwarta ta kasa yin lissafin abu mai kyau…da kyar dai ta ja k’afafuwanta ta fita bayan ta yanke shawarar yarda da abunda Kausar d’in ta fad’a mata.
Shiruuu!!!haka gidan ya koma kamar na zaman makoki…daga jigum sai tagumi….sai da Daddy da Abhi suka gama ji da Hajiya mama tukunna Daddy ya kira Junior yace a kuma yin wani test d’in.
Yana fitowa daga wajen Daddy ya nufi d’akin Kausar domin ya d’auki jininta ya wuce office d’insu…
Knocking