Showing 6001 words to 9000 words out of 244445 words
ta tsani Yassir tsana ba ta wasa ba
dan ya yi mata kane kane ya tare gaba ya tare baya ya hana ta sakat sannan wannan zargin da ta fara akansa yasa ta sake jin tsanar sa ta nunku a zuciyarta kuma indai har zargin ya tabbata to ba ta jin akwai wanda za ta tsana sama da Yassir a kaff fad’in duniyar nan…
Dakyar ta taushi zuciyarta
ta d’an bud’e idanunta kad’an.
Suna had’a ido da shi ta yi murmushi
ahankali ta d’an mike daga kwancen ta jingina a bakin gadon ta ce’’Baby!’’.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Yassir har sai da ta kai sa ga sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciyar kafin ya sake matsawa kusa da ita ya ruk’o hannunta
ahankali yana kallon cikin idonta trying to fahimci yanayin da za ta shiga
Yace’’ban gan ki a asibiti ba,Y??’’
K’ura masa ido itama ta yi
kafin da kyar ta samu ta iya cewa’’i have better things to do,besides ba kai ne ka yi accident d’in ba
balle in damu kai na.’’
Wani kalar murmushi ta ga ya yi kafin yace’’this means kin san Yashjub ya yi accident
but ba ki damu ma kije ki dubashiba????’’
Wani k’ululun bak’in ciki Kausar ta had’iye tana jin wani kalar takaici ya na sake lullub’e ta…ji take kamar ta yi tsalle ta damk’i wuyansa har sai ta ga ya daina numfashi tukunna ta cikashi.Zuwa yanzu ta gama tabbatar wa Yassir ne ya kwance tayoyin motar Yashjub especially ma da ta tuna
yadda jiya yak’i barinta ta kwana a d’akin shi dama tun jiyan taketa sak’e sak’e a ranta
tana so ta fahimci what he is up to….
‘’Don’t you care about him??’’
Ya sake jeho mata tambayar
still yana kallon cikin idonta
Wato saboda ya na so ya fahimci ko tana son Yashjub shiyasa ya yi wannan haukar kenan??ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba,kafin da kyar ta ce’’like i just said Yassir
I have better things to do.’’Ta fad’a mishi hakan tana
mai kawar da kanta gefe,a ranta tace’’dole ta yi k’ok’ari ta danne kanta ta yi tunani mai kyau da taku mai kyau dan in dai ta bari Yassir ya fahimci wani abun tou daga ita har Yashjub rayuwar su tana cikin hatsari,dan ta lura Yassir ya haukace’’……
Matsowa kusa da ita yayi sosai ya sa hannu ya kamo fuskarta ya juyo da ita saitin tasa daff da shi tukunna yace
‘’Why are u crying ,then?yanda idanunki da fuskanki ya yi it’s obvious kuka kika yi.’’
Lumshe idonta ta yi ta bud’e
tukunna tace’’ba ni da lafiya’’
Murmushi yayi tukunna yace
‘’Kausar!you better not be lying ‘’
Ahankali tace ‘’na ce maka bani da lafiya shiyasa ka ganni haka me ye ne yake damunka haka wai?akwai matsala ne?’’
ta yi mishi tambayar idanunta suna ciccikowa da hawaye.
Zuciya da abinda take so tashi d’aya sai tausayinta ya lullub’e sa,dan haka duk sai jikin sa yayi sanyi yahau inda inda,a hankali ta saki siraran hawayen nata suka shiga sintiri wanda ya sake yin tasiri ba kad’an ba a zuciyar Yassir….dama tun da ya shigo ya ganta hankali kwance ya d’an sak’k’o da kuma ta ce ba ta damu ba sai ya kawar da zarginsa a kan ta dama kawai ya yi mata tambayoyin ne saboda yanaso ya tabbatar ta yanda zai kawar da duk wasu zarginsa a kanta,kuma inshaaAllah daga yau ya kawar inshaaAllah ba zai sake d’aura ayar tambaya a kanta ba.
Ahankali ya jawota jikinsu ya shiga lallashinta a chan k’asan ransa yace’’Alhamdulillah’’dan ba k’aramin dad’i ya ji ba da ya fahimta kuma ya tabbatar da Kausar d’insa ba ta son wanin sa.Amman fa dukda haka ba wai zai bar Yashjub bane dan ko ba komai ya san in dai Yash ya na da rai to ba bu shi babu walwala saboda har ga Allah jin sa yake yi kamar a tsakiyar kansa,ko yanzun ma da kyar ya ke ta lallashin kansa yake tausar zuciyar sa da take ta faman tunzura shi akan ya je
yace zai kwana ya kula dashi
daganan ya samu ya k’arasa abunda ya soma.
Kawai dai ya san indai hakan
ta faru tou kamar ya baiyyana kanshi ne saboda shi zai fara zama suspect tunda shi ya kwana da shi, shi kuma ya riga ya san ba zai iya danne zuciyarshi daga yi masa kwab d’aya ba dan indai suka kad’ance daga shi sai Yashjub tou tsaf zai iya danna masa pillow a cikin baccin sa.
Shiyasa ya taushi zuciyar sa ya hak’ura ya bari akan gara ya sake sabon plan ta yadda ba za’a kama sa dumu dumu ba..
….
Tun kwana biyu da suka wuce Baba ya fara tantama akan ‘anya kuwa Baraka tana gidan Musbahu duba da yadda kullum yake tare da mai sunan baba tun safe har dare,shiyasa yau yana zuwa ya tambayesa…cikin nutsuwa da fahimtarwa suka yi wa Baba bayanin abunda ya faru akan batun Baraka dalla dalla sannan suka ce’’ ya yi hak’uri akan k’in gaya masan da suka yi dama suna so ya d’an huta sanann abubuwa su d’an yi sanyi tukunna,dan ba sa so hankalinsa ya tashi sosai a lokaci guda.’’
Shiruu kawai ya yi da farko kafin daga baya yace‘Allah ya rufa asiri’’daga haka ya ja bakin sa ya yi shiru yana kallon su Muhsin suna koya wa inna rik’e abu dan jikin nata Alhamdulillah anata samun improvement a cikin kwanakin da basukai sati d’aya ba.
Suna nan zaune gaba d’ayansu zaune,Ya Nafi’u ya kira ya Musbah yace’’yanzu sir Najeeb ya kira sa yake sanar masa’Yashjub ya yi accident yana asibiti driver d’insa ma har ya rasu.’’
Tunda suka ji Ya Musbah ya yi salati dama gaba d’ayan su suka juyo suna kallonsa ai kuwa yana ajjiye wayar suka hau tambayar sa’’me ya faru’’
abunda ya Nafi’u ya gaya masa shima ya fad’a musu idanunsa a kan Manubiya,ai kuwa hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba,ga mamakin su kawai sai suka ga ta fashe musu da kuka.
Murmushi kawai Baba ya yi
yana mai jin wani kalar kwanciyar hankali da nutsuwa su na ratsashi
dama yanayin yanda suke waya akai akai ya fahimci kamar itama tana son Yash d’in
yau kam ya tabbatar,shiyasa ya ji zuciyarsa ta yi k’al!Atleast ya san zai kai Manu gidan wanda itama take tsananin so.
Cikin d’an k’ankanin lokaci suka yanke akan Manubiya ya Musbah Muhsin da Jidda su fara yin gaba su je su dubo shi su yi masa ya jiki,dan haka aka fara shiri dan su samu su je da wuri shi kuma Baba ya ce ‘’in Aisha ta zo kamar yadda Nafi’u ya ce,sai ta zauna da Inna shi kuma sai ya taho da mai sunan baba in ya farka dan tun d’azu da suka shigo ya fara bacci,tare kuma da ya Nafi’un wanda yace yana gama abunda yake yi za su zo
.In ya so sai su dawo gaba d’ayansu a tare’,
ya fad’i hakan yana mai zaro kud’i daga aljihun sa ya mik’awa Jidda yace’’gashi su siyawa Yashjub d’in su ayaba da lemo a hanya’’.
Jikin Manubiya har karkarwa yakeyi,tun kafin a kowa ya shirya ita har ta shirya ta karb’i
address da room number da sir najeeb ya turo a wajen ya Musbah ta zura hijabinta ta d’au jakarta da wayarta ta tsaya musu a bakin k’ofa.
Girgiza kai kawai ya Musbah yayi,wanda hakan ya sanya ta d’an lura da zumud’in ta dan haka ta fara kame kame tahau wasa da bakin hannun hijab d’in ta,Jidda ma dariya tayi
kafin ta kalli Baba ta ce’’Baba dan Allah bara in kira Siyama sai mu je tare
Kamar Baban zai hanata
sai kuma ya kawar da wannan tunanin a ganinshi ai babu mahaifiyar Siyama a cikin case din iyakar da aka yi mishi dasu
Iyakar tsakanin shi da su Uncle da Baba Habu ne,shiyasa yace mata ‘’to’’ kawai.
Sai da suka tabbatar su innar basa buk’atar komai tukunna suka yi musu sallama suka fice
suna fita kuwa Baba ya matsa kusa da inna dan dama akwai maganar da yake so ya d’an tattauna da ita akan auren manubiya kafin su ya Nafi’u su k’araso suma su tafi….
Da kyar Manubiya ta lallashi kanta ta hana kanta kuka a cikin adaidaita sahu,a ranta ta shiga aiyyanawa’’kullum shi yake kiranta, da ta ga bai kira ta ba jiya kamata ya yi ace ita ta nemesa,Allah dai yasa bai karyeba Allah yasa bai ji wani mummunan rauni ba
Allah yasa babu abunda ya samu Yashjub…’’
In kuma ta tuno ance driver d’in shi har ya mutu sai ta ji
gaba daya hankalinta ya sake tashi.
Tsararren private hospital ne mai kyau sosai da had’uwa,sai da suka fad’i sunan sa da number d’akin da yake a ciki
a reception d’in tukunna aka raka su har bakin k’ofar d’akin.
Suna tsayawa a bakin k’ofar d’akin su Jidda suka tuna ba su siyo kayan dubiyar ba dan haka suka juya da sauri ba tare da sun cewa kowa komai ba saboda a yadda Ya Musbah yake a fusace kwana biyun nan sun san in suka ce ‘sun manta!’ sam ba zai yi la’akari da ‘har da shi aka yi mantuwar ba’
zai rufe ido ne ya ci k’aniyar su.
Suna juyawa ya lura dan haka ya juya shima ya bi su da sauri bayan ya cewa Manubiya’’ta shiga suna zuwa’’.Muhsin ma bin bayan Ya Musbah ya yi dan a yadda ya ga duk sun fita da sauri ya d’auka wani abun ne…MANNUBIYA
(Book 2)
Page 04
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Ji ta yi kamar itama ta juya dan tashi d’aya ta ji k’irjinta ya fara bugawa,da kyar ta samu ta d’aga hannunta ta d’an yi
knocking a hankali.
Sam bai kawo itace ba dukda kuwa yadda ya ji yanayin sa ya chanza saboda shi dai ya san bai gaya mata ba.
Jin an sake yin knocking a karo na biyu ne ya sanya sa cewa’’Yea come in..’’ya fad’i
hakan a ransa yana tunanin maybe ko sir Najeeb ne ya dawo ko kuma finally Doctor ne ya zo domin ya yi discharging nashi daga wannan prison d’in…
Ahankali ta murd’a handle d’in ta shiga.
Yana kwance a gefen hannun damansa mara ciwon ya d’an
d’ago hannun ya na amfani da shi ta hanyar daddana computer da ke akan
bedside d’in jikin gadon.
Tana shigowa ya d’ago ya kalle ta,bai san lokacin da ya tashi ya zauna ba sai kuma ya mik’e tsaye gaba d’ayansa ya
nufe ta.Da farko ya d’auka gizo take yi masa sai da ya je daff da ita tukunna ya tabbatar ita d’in ce.Ahankali ya sa hannu ya tura k’ofar da ta bari a bud’e tukunna yace’’ya aka yi ki ka sani?’’
Sai a lokacin ta samu ta d’an daidaita numfashi ta kamar za ta fashe da kuka tace’’Mai yasa ba ka gayamin ba??’’
Murmushi ya yi tukunna yace
‘’Sorry’’
Ahankali ta kalli hannun kafin ta d’ago tace masa ’’ mai ya sami hannun?’’dukda yadda ta ji dad’in ganinsa garau a kan k’afafunsa sai da ta shiga tashin hankali daga ganin yadda aka d’aure hannun nasa.
Yashjub kuwa yadda ta nuna damuwarta garesa abun ba k’aramin dad’i yayi masa ba Shiyasa ma ya gagara bata amsa hakanan kawai ya tsaya ya kafeta da idanu yanata zuba mata wani kalar sihirtaccen murmushi.
Kallon sa ta yi taga yadda yake kallonta yana murmushi shiyasa gaba d’aya sai ta jita a takure dan haka sai ta hau wasa da y’an yatsun hannunta.
Y’ar siririyar dariya Yashjub yayi kafin yace ‘’mu je ki zauna mana’’ daga haka ya d’an matsa ya bata hanya yana mai jin wani farin cikin da ya dad’e bai tsinci kansa a ciki ba.
Ji ta yi kamar ta ce masa a’a bara su Jidda su shigo tukunna ko kuma ma kawai su yi sallama ta juya tunda ai ta ga jikin nasa,ita sai yanzu ma lissafinta yake bata yadda ta burkice da kuma yadda ta shigo tsulum ba tare da ta yi kawaicin jiran su Ya Musbah su dawo ba,kamata ya yi ace ta jira su ko kuma d’azun kafin duk su tafi da ko hannun Muhsin ne ta dan rik’e ta hana sa bin ya Musbah sun shigo tare shikenan yanzu ta san za su ga rashin kararta in ba dakyar ba ma sun riga sun gano sirrin zuciyarta shikenan ta tonawa kanta asiri da kanta…gaba d’aya hankalinta gaba yayi ne d’azun shiyasa kwata kwata bata yi waennan tunanin ba….
So take ta juya kawai ta tafi
amman kuma still tana so ta ga yanayin jikinnasa sannan ta ji ya akayi hakan ta faru
tana so ta duba sa sosai..shiyasa duk yadda ta so sam sai ta kasa tafiya.
D’agowa ta yi ta d’an saci kallonsa still itan yake kallo yana murmushi shiyasa ta d’an d’auke idanunta kafin ta wuce ciki ta isa kan kujerar mai jinya ta zauna.
Dariya ya yi kafin ya juya shima ya k’arasa bakin gadon ya zauna sannan yace ‘’Tabbas likita ya na shigowa zai sallameni,yadda kika zauna anan kujerar za ki yi jinya ta ai na san ko minti uku ba zan k’ara ba zan warke.’’
Sake yin k’asa ta yi da kanta kawai tana sauraronsa…ita ba abun ta tashi ta koma chan gefe kan sofa d’in da ke cikin d’akin ba dan tunaninta a lokacin da ta kalli sofar ‘kar ta je ta zauna tunda guda d’aya ce shima Yash d’in yace zai zauna akai’ shiyasa ta yo nan tou gashi nan d’in ma ba ta tsira ba,ba ta tab’a jinta un comfortable sosai dashi ba kamar yau dan a kusa da ita sosai ya zauna.
A b’angaren Yash kuwa so yake ma ta d’an d’ago amma ta k’i k’arshema gani ya yi ta d’an muskuta ta ja baya ita da kujerar tata sannan ta sake sunkuyar da kanta.
‘’Inaa yarinya ba za mu yi haka dake ba wallahi’’ Yash ya fad’i hakan a cikin zuciyar shi kafin a fili yace’’Auch’’
Da d’an k’arfi.
Da sauri ta mik’e tsaye ta d’an matsa inda yake kafin tace’’menene,me ya faru?hannun dai?’’
Ta jero masa tambayoyin a gigice saboda yadda ta ga
yana yi kmr irin azabar nan yake sha.
Kamar zai yi kuka yace’’zafi sosai har cikin zuciyata’’.
LlAi kuwa babu shiri ta yunk’ura tace’’ Bara in kira Doctor’’da fad’i hakan tana shirin juyawa.
Da sauri ya mik’e ya tare ta ta hanyar tsayawa a gabanta tukunna yace’’in kikayi murmushi ma kad’ai ya wadatar zai daina,dama kyaliyar da kika yi min ne yasanya ya fara wani irin azababben zugi’’
Shiruu ta yi da farko sai kuma ta d’ago ta kalleshi,murmushi ta ga yana yi mata suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya,
b’ata rai ta yi sai kuma ta
maida kanta kasa a ranta tace
‘’lalle wannan mutumin da alama garau yake kawai tab’ara ce yake ji da ita’’.
Murmushi yayi kafin yad’an matso kusa da ita ahankali ya d’an lek’a fuskarta ya langab’ar da kai kafin yace’’ kuma wai a haka ank’i ace mun ana sona’’
Ji ta yi kamar ta nitse cikin k’asa dan haka ta juya da sauri ta bashi baya tana jin yadda yanayin bugun zuciyarta ya sauya lokaci guda.
A hankali ya d’an sake taku d’aya izuwa gareta ya tsaya a daidai bayanta yace’’Manu plsss,jan ajin nan ya fara cutar da ni,ki fad’a min wani abun mai dad’i mana ko so kike inyi miki kuka tukunna???’’
Shiru tayi kawai ta kasa cewa komai dan zuwa yanzu bugun da k’irjinta yake yi ba na wasa bane ba ma ta jin kalmar ‘A’
za ta iya fitowa daga gareta.
Jin da ya yi ta yi shiru yasa yadan sake matsawa kad’an ahankali daidai saitin kunnenta yace ‘’dan Allah ki ce kina so na…plss Baby!….’’
Inaa….she can’t take this anymore shiyasa da sauri ta d’an yi gaba kad’an kafin ta juyo da niyyar fita ta yi hakan ne gudun karma ta juyo tashi d’aya taje ta fad’a jikinsa,amman ta na juyowa sai ta ga ba hanya dan gefenta fridge ne d’ayan gefen gado bayanta kujera gabanta kuma shi…
Da sauri ta sunkuyar da kanta dan wani irin kallo ta ga yana yi mata,ba ta gama dawowa daidai ba ta ga kamar ma tunkarota yakeyi dan haka ta yi sauri ta d’ago tace’’Allah ya k’ara sauk’i,Allah ya ji k’an driver d’in ka ya sa ya huta,z z an wuce ggi d a….’’ta fad’i hakan cikin in inaa
Tsayawa yayi chak kafin yace’’Saboda na ce kice kina sona shine za ki gudu??haba mana Baby aure fa za mu yi amman har yanzu ban san matsayin na ba kuma daga na yi magana sai a fara gudu na…’’
Juyar da kanta tayi gefe
tukunna ta girgiza masa kai alamun ‘’A’a’’ kawai.
‘’Good!saboda gaskiya yau ba za ki fita daga d’akin nan ba
sai na san matsayina a cikin zuciyarki.Inaso mu wuce
wannan stage d’in na kauda kai!kasa kallona!jin kunyata da kike yi mu shiga next stage
saboda in samu in dinga expressing miki how much I feel dan sun cikamin zuciya da gangar jiki dayawa.So I’m all ears.’’
Shiruu ta yi shima haka
duk suna anan tsaye ba wanda ya sake cewa komai
Manubiya ji ta yi inama ba ta zo ba,gashi kwata kwata ya k’i ya daina kallonta dede da second d’aya,gashi ya titsiyeta,shiyasa ta ji kamar ta fashe masa da kuka…….
Sun fi minti goma a haka
sam tama k’i ta yarda ta kalli direction d’in shi balle ta fad’i abunda yake son ji d’in.
Ahankali ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kawai sai kuma ya koma ya nemi waje ya zauna akan gadon jinyar nasa.’’Na gode ki gaida su Inna
InshaaAllah zan zo in gaida ita da zarar na fita a nan.’’ Ya fad’i hakan cikin kumbura fuska.
Duk kuma sai ta ji ba dad’i,har za ta wuce ta fita sai kuma ta tsaya kamar wadda ba ta son yin magana tace’’Tun d’azu nake ta tambayar ka ya jiki baka ce komai ba,ya aka yi
hakan ta faru? Ya kuma hak’urin driver