Showing 45001 words to 48000 words out of 244445 words

Chapter 16 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16446

kyawunshiba asalima ba burgeta yakeyiba amman wannan kam ta yi declaring nashi as the best dan ya matukar yi masa kyau,wankan nasa ya bi jiki.
Ya murza bak’ar hula kmr zanna bukar itadai bata san ko akwai hula zanna bukar kuma bak’a ba amma yau ga ta anan,sannan hatta cuff links da agogon sa ma duk bak’ake ne ga kamshin mayataccen turarenshi wanda tun lokacin da ya shigo cikin parlourn
shi ya fara yi mata sallama….kallonshi take yi sam
ta gagara d’auke idanunta a kansa,wani irin kyau kwarjini da haiba ta ga ya k’ara…..ahankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata moments d’insu tun daga farkon had’uwarsu a office d’in sir Najeeb har kawo yanzu da yake zaune a kusa da ita a matsayin mijin aurenta…ahankali ta lumshe idanunta a cikin zuciyarta ta shiga godewa ubangiji dan tabbas idan akwai the most lucky mace a duniya to ta yi crowning kanta above her dan ba kowa bace take samun chance ta auri true love d’inta ko first love amma itakam ta samu,sannan kalli kyan Yash kud’i aji ilimi and everything amma ita ya zab’a ita ya so it’a yakeso ya yi rayuwa da……….

“Na yi kyau har haka ne???”
Muryar Yashjub ta dirarwa dodon kunnuwanta
Wanda shima dakyar ya nemo numfashi da nutsuwarshi ya sakawa gangar jikinsa tun lolacin da ya bud’e fuskar tata…..ta yi wani irin kyau wanda tsayawa fad’a ma b’ata baki ne,tabbas Manubiya itace rayuwarsa shiyasa ya kasa daina tasbihi hamdala da hailala ma Allah subahanahu wata’ala da ya mallaka masa ita a yau.
“Yahayyu ya Kayyum ka bamu tsawon rai mai amfani ka sa mu tsufa tare kasa kar Manubiya ta riga ni mutuwa
dan ban san ya zan yi rayuwa idan babu ita a duniyar nan ba”
Ya yi adduar a cikin ransa yana mai k’are mata kallo!.

Ahankali ya ji tace”Ina wuni…”
Bata samu damar d’aura komai ba sakamokon sallama da shigowar Muhsin a tare hannunsa d’auke da lemuka.

Kunya ce ta kama Yashjub…shi da yake Ango ya zo ya shantake gashi har an kawo masa lemo!shiyasa ya cewa
Muhsin d’in “ya maida shi kam
tafiya ma zai yi.”

Muhsin yana fita ya janyota jikinshi yayi hugging dinta wanda hakan yasa duk sukayi shiru,a hankali dai dai cikin kunnenta yace”Allah ya bamu zaman lafiya” daga haka ya cika ta ya yi kissing forehead d’inta yace”thankyou”
tukunna da kyar ya daddage ya yi kokawa da zuciyarsa ya cikata ya mik’e da sauri dan ya san idan ba da saurin ya mik’e ba tou tabbas sai ya k’ara jan lokaci…….Ahankali yace mata “sai Allah ya kaimu anjima”
Daga haka ya sa kai ya fice.
Allah ya so shi babu mutane sosai dan sai da ya fito tukunna wata sabuwar kunya ta lullub’e shi ya ji kamar ya nutse a wajen.


Earlier (11:45am)
Tun k’arfe goma lokacin da aka sallamo Kausar suka dawo gida gabad’ayansu suka gaza sukuni kamar wasu masu zaman makoki haka suka koma,Kausar kam k’arshema d’aki ta mik’e ta shige ta rufe kanta.
Hankalin Mommy bai sake tashi ba sai da ta kira Daddy ya tabbatar mata da an d’aura auren….tashi d’aya ta gaza nutsuwa k’arshe ma kawai sai ta kama hawaye,ba ta yi tunanin za ta shiga damuwa kamar haka ba,duba da yadda suka hak’ura suka tsara dakatar da komai har sai Manubiyan ta shigo tukunna su d’aura a inda suka tsaya.

Suna zaune a d’akinta itada Baba larai Yassira ta shigo ta same su
Numfashi Yassirar ta fesar kafin ta k’araso ta zauna a kusa da ita tukunna tace “Mommy idan Ina ganin ki a haka za ki sa inje inyi shirme a wajen d’auko yarinyar nan,ku ne kuka ce mu kwantar da hankalinmu amman ganinki a haka gaba d’aya ya na nema ya dawo min da komai sabo.”
“Ta ya kuke so mu yi welcoming d’inta with open arms bayan gashi muna ganin yadda ta zama reason din kukan ki!”

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin ta kalli Yassira tace”dan Allah kar ku dawo mana da hannun agogo baya mun riga mun gama magana,yanzu ki bar jan lokaci mu samu mu je mu yi abunda za mu yi a gidan kafin ta tare, na riga na gaya muku idan har ta tare ba’ayi ba to gaskiya akwai matsala!
ki yi sauri ki je ki cewa Yahanasu ta baki makullai da frames d’in da suka siyo ita da ummi a kasuwa za ku had’a ku kai gidan tare da flasks d’in da kuka siya kuma…..na ji d’azu ummin tana ce mata ya kamata a kai a kafa kafin zuwan amaryar,so ki yi sauri ki karb’o…

Saida Yasirar ta fesar da wani bahagon numfashi tukunna tace”okay Baaba”daga haka ta sa kai ta fice.

Sai a sannan Mommy tace”ni kam da kun yi abun nan tun a jiya…
“Ai dole sai a ranar da za ta tare tukunna za’ayi,karki damu ba za a samu matsala ba…..”
Baba larai ta bata amsa.

Ahankali cikin mutuwar jiki tace”kin tabbatar zuwan nata ba zai yi affecting surrukana ba ko?
Sai da Baba larai ta sauk’e numfashi tukunna tace”na gaya miki ai…ita Manubiya tana tafe ne da fad’uwar ki a bayanta,muddin ta zo ta zauna ta yi rayuwa a cikinmu to komai naki sai ya tab’arb’are a hankali a hankali za kiyi ta shiga bala’i kala kala kuma babu ranar farin ciki….amma inshaaAllah da izinin Allah mu kuma ba zamu bata ikon dad’ewa a cikin gidan nan ba ballantana har matsala tafara tasowa…kuma dukda haka still Ina ta add’ua inshaaAllah babu abunda zai taso har ta zo ta tafi.
Zuwan nata ma dan bamu da yadda za mu yi tunda akwai rabon zaman a tsakaninsu..kinga ai yadda akayi ta shan fama amman duk ya tafi a banza,but inshaaAllah na yi miki alk’awari ba za ta yi dogon zango a cikin gidan nan ba.
Ina fatan kin fahimceni???”

Jin jina kai Mommy ta yi kafin ta ce”na fahimceki,”
Sai kuma ta share kwallarta ta d’ago ta kalle ta kafin tace”ki yi min alfarma guda d’aya ku je ku d’auko ta banda ni sannan duk runtsi kar ki bari a wani kawota nan a ce ta gaida ni,dan muddin na yi ido biyu da Yarinyar nan yau tou tabbas zan iya mutuwa….”
Shiruu ta yi kafin ta fashe da wani irin kuka tace”larai na tsani Yarinyar nan ban tab’a tsanar mutum kamar yadda na tsane ta ba!,a cikin watanni da basu wuce hud’u ba gaba d’aya ta rabani da peace of mind d’ina,……”
Cikin share hawayen da suka wanke mata fuska sosai tace” dan Allah Larai this time around ki dage sosai,sannan a yi duk abunda ya kamata dan ba zan karb’i excuse daga gareki ba zuciyata ba zata iya tolerating Yarinyar nan na tsawon lokaci ba. Besides idan har ta dad’e na san kin fi kowa sanin abunda zai faru da mu….”

Murmushi Baba larai ta yi kafin tace”ki kwantar da hankalinki,inshaaAllah ba za ta yi dogon zango ba…”

Dai dai nan Ya’isha Yadira da Yusra suka shigo suka nemi guri suka zauna,suma suna jiran dawowar Yasira da Yasmeen a samu a kama hanya da wuri dan yanzun suka had’u da ita tace makullai za ta karb’o a wajen Yahanasu sai su wuce,shine Yasmeen ta bita su kuma suka yo nan.


Suna zuwa suka tarar da Yahanasu tana waya tana shiryawa da sauri da sauri…tana ganinsu dama ta san ba alkhairi ne ya kawo su ba dan haka ta yi sallama da wanda suke wayar ta ajjiye wayar ta kalli Yasira tace“Yassira har kun shirya?ai sai yamma tukunna za’a d’auko amaryar”

Sai da Yasirar ta nemi waje ta zauna tukunna tace”Am,Ina buk’atar keys ne za mu kai gifts d’in da muka siyawa ango
da amarya gidan,idan kinada abunda za’a tafi da shi ki kawo sai mu yi miki gaba da shi dan mu yanzunan za mu tafi.”

Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin tace”keys ba sa hannu na….inada sak’o but na bawa friends d’insa yanzunnan suka wuce da shi suma wai za su kai gifts ne daga nan su biya su masa sallama saboda flight d’insu ya kusan d’agawa….”

Cikin tarar numfashinta Yasmeen tace”no wahala…ki ba mu adress d’in gidan kawai sai mu wuce.”
Ta fad’i hakan tana mai k’arasa shigowa cikin d’akin dan ita a bakin k’ofa ta chake ta tsaya tun d’azu.

Murmushi Yahanasu ta yi tukunna ta ce”Yasmeen nima ba sanin adress d’in gidan na yi ba,shiyasa ma kika ji nace miki na bawa friends d’insa sak’o na sun tafi da shi dan naji sun ce su sunsan gidan wai sunje d’azu da safe….”
Tana gama fad’in haka ta d’auki makullin motarta sannan ta k’arasa inda Yasira take ta damk’a mata key d’in d’akin nata tace”idan kun fita ki rufemin pls,Ina sauri ne.”
Daga haka ta sa kai ta fice
da sauri dan ko hauka takeyi
ba za ta bari su Isa gidan nan ba tare da an riga an kai Manubiya ba….


Tana fita Yasmeen tace”idan nace muku ku barni in ci uwar matar nan kuce ba haka ba,yanzu kalli!gaba d’aya ta raina mutane,gani take yi itama ta kawo mutun…”

Shiruuu Yassira tayi tana lissafi kafin ta mik’e da sauri tana shirin bin bayanta ta jiyo tashin mota,sannan ta ji an wangale gate an fice da gudu. Ko ba’a fad’a mata ba tasan tashin motar Yahanasu ne shiyasa cikin b’acin rai ta yi wulli da makullin akan gado ta fice
ranta a b’ace.


A yadda suka fita suka bar su Mommy a haka suka dawo suka tarar da su…suna shiga ko zama ba su yi ba
Baba larai tace”ya aka yi?ta baku?”

Ajiyar zuciya Yassira ta sauk’e
tukunna ta matsa kusa da ita tace”ta fice,da sauri!bayan ta ce mana keys ba sa hannunta sannan wai bata san kwatancen gidan Yash ba tsabar ta raina uwarta!”
Sai da ta sake sauk’e numfashi tukunna tace”Inaga ta yi suspecting wani abun….a ganina gara kawai mu hak’ura,kinsan halinta mahaukaciya ce Ina tsoron kar ta je ta gayawa Yashjub ko Daddy wani abun mu je ta taso mana da case.

“Ta fad’a d’in”
Mommy ta fad’i hakan tana mai k’arasowa inda suke sannan ta sake cewa”dan Allah ta fad’a!sai me?.
Ki kira Yashjub d’in yanzu ya yi miki kwatance,ku bi bayanta na san gidan ta nufa..idan kukaje ko a gaban ta ne ku yi abunda kukaje yi,ita ta sani ta dad’e ba ta fad’a ba.”

Shiruuu Baba larai ta yi,sai da ta gama lissafi sannan ta kalli Yassira tace “ki kira Yashjub d’in,wannan shine kad’ai chance d’in mu,dan in dai har muka bari Manubiya ta shiga gidan a haka sakayau ba komai to munada gagarumar matsala.

Shiruuu Yassira ta yi ta k’i cewa ko yin komai sai da Yasmeen ta ce mata “ko ni in kira sa ne?”tukunna ta fita waje domin yin wayar,
mintuna biyu ta d’auka a waje kafin ta dawo….duk tsura mata ido sukayi suna jiran amsa.
Sai da ta zauna akan gado ta dan dafe kanta tukunna ta d’ago tace”Mommy dan Allah mu bar wannan idea d’in”
Sai kuma ta kallesu duka kafin tace “ba zan b’oye muku ba gaskiya ni tsoro nakeji….na san babu yadda za ayi ya Yash ya bar gidan sa babu cctv…haka kurum a hangomu muna yayyafe yayyafe da hayak’i da abubuwa.
Inda ace cewa akayi idan mukayi ba za ta tare ba tou da zan biye muku ayi
komai ta fanjama fanjam,amman ba zan d’au wannan risk d’in all because of
wani foundation da mukeso mu gina ba,haka kurum muna zaman zaman mu kar ku janyo mu saka kanmu a case gaba d’aya.
Ni kam count me out gaskiya!.

Yanzun da na fita na kira shi har sau uku bai d’auka ba a na
hud’un kuma yace”mu bari kawai ba sai mun kai flasks d’in yanzu ba,mu saka a motocin mu idan muka d’aukota anjima sai mu yi zuwa d’aya….k’arshe ma kashe wayar ya yi yace min yana zuwa.”
Na san kuma maybe zai yiwa Yahanasu maganar ita kuma
Allah kad’ai yasan me za ta ce masa ta yadda na san tashi d’aya zai
fahimci gidan kawai muke so mu je.”

Cikin fushi da fad’a Ya’isha tace “ya fahimta mana sai me?
Gidan d’an uwan mu ne fa!…kina wasa in ban kwashe kayana na koma chan da zama ba ki chanja min suna!”

Cikin sako wani sabon issue Yasmeen ta kalli Mommy tace “Ya’isha ta yi magana anan fa Mommy,mu muna nan su suna chan abun fa ba zai yiu ba,ya kamata ace ko
Yadira ta je gidan ta zauna da su.“
Mikewa tsaye Yassira tayi kafin tace”wai ba ki da lisssafi ne?me yasa bakwason bin komai a hankali?ya ana neman toshe wannan kina nemn b’ullo da sabon abunda zai d’agawa kowa hankali??….ki yi shiru da wannan zancen dan Allah ki bari ayi komai at once.”
Cikin son su fahimce ta tace”idan har zan bada shawara a bi,to kar wanda ya janyo fad’a ko case da Yash..dan haka mu hak’ura for now,dan Allah a bar batun zuwa gidan yanzu a nemi wani alternative d’in.
Haba mana!!!ku ko ta Kausar ma bakwayi?sannan idan fa muka bi komai a sannu muka samu Kausar ta shiga gidan na tabbatar Manubiya ba ta Isa ta k’ara ko da sati a cikin gidan ba ai kunsan wacece Kausar!kunsan ita kad’ai ta ishi yarinyar riga da wando wallahi!ba zata barta ba,kunga wannan ma ai wani alternative d’in ne…amman gaba d’aya kun k’i ku nutsu ku bi komai a sannu kun dage sai kun bankad’a komai a idanun kowa an gani…..”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin.”

Tana fita Baba larai ta sauk’e ajiyar zuciya…..tabbas ta
san Yassira tana da gaskiya,sai dai kuma indai ba abunda ta shirya akayi kafin Manubiya ta shiga cikin gidan nan ba to kwata kwata bata
hango rabuwa tsakaninta da Yashjub ba!.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace” Larai manta da zancen Yassira ba zata fahimta ba,Yarinyar nan ba alkairi bace ba,rayuwarta a matsayin matar Yash hatsari ne garemu dan haka kar ki biyewa Yasira kar mu yi taking any issue concerning Yarinyar nan likely…”.

Ajiyar zuciya Yusra ta sauk’e kafin tace”Mommy bana son Yarinyar nan tun farko.”
Cikin tarar numfashin ta Yadira tace “tunda aka fara zancenta babu zaman lafiya a cikin gidan nan,gashi sai sake raba kanmu takeyi muda ya Yash..”
“Bata Isa ba kuwa,Allah ya fi ta”
Cewar Baba larai kafin ta kalli Ya’isha tace”ki kira Najeeb,ki tambayeshi location d’in gidan
If possible kar ki bari ya san zuwa zamu yi.
……………
Already an sallami masu hotuna shiyasa suna fita suka kama gabansu.
Aisha suka tsaya jira wadda ta shiga gida domin ta sanar da su inna sun wuce.
A gefen Jidda Yassir ya d’an
tsaya kafin yace “Bismillah ku jira ta a mota mana akwai rana”.
Kasa bashi amsa ta yi sakamokon tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki yanzunnan,da kyar ta d’an juya ta kalleshi a hankali ta ce”to gamunan zuwa”.
Bakinta kawai ya bi da kallo kafin da kyar yace”ok”daga haka ya wuce ya nufi motarshi ya shiga ya zauna.

Itadai Siyama za ta iya cewa tunda take a rayuwarta bata tab’a had’uwa da wanda tashi d’aya ta tsaneshi kamar Yassir ba,gashi dai kyakkyawa d’an gayu amman sam bai mata ba,ta lura da yanayin kallon da yake wa mutane kana gani za ka san ba na Allah bane sab’anin na sir Najeeb…kana gani ka san ya fisa hankali.
Shiyasa yana Siyaman ta kalli Jidda tace”sai dai fa ke ki shiga motarsa dan na san in na shiga kafin mu k’arasa tsaf zan iya tsinka masa mari in gaggaya mishi magana! na tsani Namiji mai kallon iskanci….”Jin ba ta ce mata komai bane yasanya ta kalleta sosai kafin tace”Jidda!”
Firgigit taga Jiddan ta yi ta d’an juyo ta kalleta sai kuma taga ta sake juyawa ta maida idanunta ga balcony d’in gidansu Al’ameen,a ranta tana mamakin “anyi shi ta gani kuwa ko dai gizo ya ke yi mata..yaushe ya dawo…ko nemanta bai yi ba”da sauri ta kawar da tunanin…still a zuciyarta tace”ko ma ya nemeni ni kam dama ba kulasa zanyi ba”

Da mamaki Siyama take kallonta kafin ta kalli inda ta ga ta tsurawa ido tukunna tace”Jidda!ki shafawa kanki lafiya ki rufawa kanki asiri…”

Kasa cewa komai Jidda ta yi tana mai jin yadda kwallah take k’ok’arin zubo mata dan haka tayi sauri tace”ki zo mu je kawai,Aisha in ta fito sa tafi ta wanchan”
Tayi maganar tana mai yi gaba abunta….Tabbas ta san ko da ace tanason ta b’oye sannan ta share al’amarin to ba lalle ta iya ba!dan ba kad’an ba ta ji tsananin ciwon abunda Al’ameen yayi mata,har fa aiki yayarta ta yi a gidansu duk ata sanadiyyarsu amman shine ko sak’on ‘hi’ bata samu daga garesa ba bayan ya dawo kuma ta san ya ji komai.
Tana k’arasawa ta bud’e gaban motar ta shiga ta zauna ta runtse idanunta…k’ok’ari
kawai takeyi ta ga ta hana kanta kuka.


Tun d’azu ta lura da yanayinshi da yadda yaketa faman shishige mata,shiyasa
yanzun ma tak’i yarda ta tsaya opposite d’inshi ko kuma kusa da shi,ba ta son shiga motar Yassir har ga Allah d’ayar motar kuma ta sir Najeeb d’in ce shiyasa ta tsaya tana wasuwasi akan ta bi bayan Jidda ne ko kuma
ta tsaya Aisha ta zo su wuce tare a motar Najeeb d’in…..ba ta gama tunani ba ta ga ya tunkaro ta. Tashi d’aya ta diririce ta kuma fara data sanin k’in bin Jidda da tayi….har ga Allah nervous take zama idan ya matso kusan ta.
Yana k’arasowa daidai Aisha tana fitowa rik’e da robar capulas wadda ke d’auke da turaren wuta har da kasko da ashanarta.

A hankali Siyama ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya
wadda har sai da duk su biyun sukaji,dariya ya d’an yi kafin ya ce da Aishar”kin barmu a rana”
Kallonshi kawai Aisha ta yi a ranta tace “ikon Allah”ita yake yiwa magana amman idanunshi na akan Siyama,shiyasa kawai sai ta yi murmushi tukunna tace”ku yi hak’uri”.
Siyama ce tace mata”ga Jidda chan,bari in je mu tafi tare,ke
kwa taho”.
Dasauri Aisha tace”a’a bari ni in je mu tafi tare da su,ku kwa taho ku biyu.”
Tana gama fad’in haka ta yi gaba,dan ita harga Allah had’in nasu ya burgeta gashi Najeeb d’in nutsattse dashi daga gani…..ko bai fad’a ba ta san yana ciki ne da Siyama shiyasa ta basu space ta barsu su biyu ita kuma ta nufi motar da akace mata Jidda tana ciki mai uban tint
Ita kanta Jiddan sai da ta shiga ma tukunna ta lura da tint d’in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login