Showing 216001 words to 219000 words out of 244445 words

Chapter 73 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16421

ba!….dan Allah ya janye maganarsa.

Daina ji Yassir ya yi na y’an sakanni…
Ya riga ya san duk inda aka je aka dawo su grenade ne Ummul’abaisin wanan mummunan al’amari da ya faru da shi a yanzu,dama ya san delay d’in da ya yi wajen sakar su dole ya yi facing consequences amma kuma a tunaninsa 3 million d’in da ya bayar ta isa ta yi silencing d’insu.
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ya shiga ambato a cikin ransa dan bai ma san mai zai yi ba ya zai yi ba mai zai ce ba!!!!.
Is this really happening to him kokwadai mafarki yake yi….zai iya cewa tunda yake a rayuwar sa bai tab’a zama helpless cikin matsanancin tashin hankali ba irin wannan!!
Na farko ya san tabbas an san me ya yi na biyu kuma yanzu shi idan ya fita ta ina zai fara?
Ba shi da halin da zai iya ciyar da rai biyu,besides da ma ya gama tsarawa ita kanta yanzu kam sai dai ta ci gaba da ciyar da kanta dan last kud’in hannun sa ne ya yi amfani da su ya je Abuja ya dawo……

Da farko zuciyarsa tunzurasa ta fara yi akan ya yiwa Daddyn bori yace”babu inda zai je sannan yace sharri aka yi masa amma kuma indai videos da voice d’in da mutanen suka turo masa shi suka turawa su Dad tou tabbas bai Isa ya fara cewa sharri baneba..Idan ya yi hakan kamar ya sake tsunduma kansa a wani sabon bala’in ne…so it’ll be better for him ya yi laying low a halin yanzu da halin da yake a ciki.

Cikin fushi Abhi yace”we are morethan disappointed in you Yassir ban tab’a tunanin za a samu b’ata gari a cikin zuri’ar mu ba!dan haka tun kafin mu fara yi maka baki ka b’ace mana daga gani a yanzu yanzu ba sai anjima ba!.”

Dai dai nan Mommy ta sauk’o k’asan.

Wani Irin rikicewa parlourn ya yi da koke koke hatta Yahanasu sai da ta yi hawaye kafin daga bisani ta mik’e ta shige d’akinta.

Dai dai nan Mommy kuma tana k’arasowa cikin parlourn ta tsaya a tsakiyarsu ranta a mugun b’ace hankalinta a masifar tashe jikinta yana wani irin karkarwa tace”Ashe dama gulma da munafuci aka shirya shiyasa na ganku gaba d’aya kun yi family kun zo????”

Bata ga mik’ewar Daddy ba sai k’arasowar da yayi ya d’auketa da wani mahaukacin mari!!
Cikin tsananin fushi hargagi da hargowa yace”dabbancin naki yau har ta kan Mahaifiyata ya biyo Khadija!!!saboda ke mahaukaciya ce wadda ba ta san wa ya yi mata gata ba shine a gaban idanunmu za ki furta wannan kalmar??
Waye ya ke yi miki munafurcin??”
Ya yi mata tambayar kamar yana shirin rufeta da duka!
Tashi d’aya Mommy ta sha jinin jikinta tashin hankalin da take a ciki ya sake hauhawa…Tabbas a yadda ta ga Daddy ya fusata d’innan ta san muddin ta biye masa to fa za ta janyowa kanta matsala….
Shiyasa tashi d’aya ita ta sauk’o a take ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen cikin kuka tace”ka yi hak’uri Daddy dan Allah ka yi hak’uri b’acin rai da tashin hankalin jin abunda kak’e ik’irari ga Yassir ne ya janyo hakan amma ka yi hak’uri da abubuwan da na fad’a ba zan sake ba sannan da n Allah ka yiwa Yassir adalci hak’uri ko me ya aikata a ganina bai chanchanci hakan daga gareka ba!”

Da mugun sauri Yassir ya mik’e ya fice..inshaaAllah tunda har Mommy ta sauk’o ya san za ta san abun yi.

Cikin kuka Ya’isha ta tari numfashin Daddy tace “Daddy ka yi hak’uri akan komai,dan Allah.
Sannan ka duba yadda fa ka ke yiwa Mommy!!!ka sanyata ta durk’usa haka a gaban kowa!!
a gani na kamar yadda ranka ya b’aci muma namu fa zai b’aci idan ka tab’a mana mahaifiya!”
Cikin tsawa junior yace mata”bar nan kafin na yi ball da ke!!
Manya suna magana kina saka musu baki that too ‘rude tone’!!”
Harara ta zabga masa wanda hakan ya sanya ya mik’e ya nufota gadan gadan,cikin bashi kwarin guiwa Hajiya mama tace”kana zuwa ka rufeta da duka kar ka raga mata!!”
Ganin yadda ya taho kuma ta san tsaf zai aikata ne ya sanya ta mik’e ta bar wajen da gudu ta haye sama tana sharar hawaye.”
Tsaki Hajiya Mama ta yi tace”marar kunyar banza”
Sai kuma ta kalli ragowar tace”duk wadda na sake jin muryarta a cikin ku za ta sha mamaki.”

Yayinda Daddy ya had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinsa da kyar ya juya kawai ya k’arasa ya d’auki wayarsa ya fara k’ok’arin playing video d’in da sauri Abhi yace”ka yi hak’uri ba sai kowa ya ji ya gani ba”
Cikin fushi Daddy yace”tabbas Abhi ya kamata kowa ya ji ya gani sabida idan ba haka ba wannan makirar matar sai ta k’unsa k’iyayyata a zuk’atan dukkannin jama’ar gidan nan dan cewa za ta yi Yassir bai yi mini komai ba hakanan na koresa,kalli fa kukan kissa da kisisinar da take yi bayan itace silar komai!
Muguwar zuciyar ta da gurb’atacciyar tarbiyyar ta su suka janyo komai dan haka kawai ka bari kowa ya ji ya gani.”
Daga haka ya wuce ya k’arasa inda take ya cilla mata wayar yace”bud’e ki kalla ,kalla ki ga abunda rashin tarbiyyar da kika yiwa y’ay’ana ya janyo mana!!ki duba kiga abunda Yassir ya aikata a d’an uwansa…..”
Tarin da ya sark’afe sa ne ya sanya ya gagara ci gaba da magana…
Da sauri Abhi da Hajiya mama suka k’arasa inda yake suka ruk’osa suka kaisa kan kujera suka zaunar Junior ya yi saurin matso masa ruwa daga dispenser ya kawo….
Shiruu parlourn ya d’auka in banda sheshshek’ar kukan Mommy da na su Yassira ba ka jin komai!!.

Mommy ce take kallon video d’in amma iyaka voice d’in Yassir da bayanansa sun fahimtar da kowa na wajen abunda ke faruwa!!!

A tare Yasmeen da Yadira suka mik’e suka bar wajen suna wani irin kuka kamar ransu zai fita dan ba ma su san abun cewa ba.

Da kyar aka samu Daddy ya dawo dai dai,tarin ya d’an lafa…cikin gajiya da komai ya d’ago ya kalli Hajiya mama yace”ki gafarceni Hajiya mama ba zan iya ci gaba da zama da matar nan k’ark’ashin inuwa d’aya ba!”
Gaba d’aya a tare Yasira
Yusra da Mommy k’irjinsu ya yi wani irin mahaukacin bugawa..Ummi kuwa ta san me Daddy zai yi dan ya dad’e da gaya mata matsayin Mommy a cikin gidan dan haka ta mik’e da sauri ta wuce sama…..

Har ga Allah Junior ya ji dad’in abunda ya faru da Yassir amma kuma sam bai ji dad’in abunda yake da shirin faruwa da Mommy ba shiyasa ya ce”Daddy koma me Mommy ta yi ka yi hak’uri…”
Cikin tarar numfashinsa yace”Junior ba ka san me ta yi ba!!!”
A hankali yace”Daddy ta ci albarkacin y’ay’anta!!!”

Girgiza Kai kawai Daddy ya yi yace”not anymore!!!
Daga haka ya kalli Mommy yace”shekaru 32 kina zaluntata Khadija..na san nima wasu lokutan na kan sab’a miki ta hanyar nuna soyayyar wata fiye da taki ko kuma nuna halin ko in kula da nake yi a kanki amma Khadija wannan ma duk laifin ki ne!saboda kin san ba na sonki ba na k’aunarki amma haka kika tilasta mini zama da ke…tsakanina da ke wata shari’ar sai a lahira dan wallahi ko da zunubin tarbiyyar Yarana da kika lalata a ka barki ya isheki!!
Duk wata cutarwa da kika yi mini da su Ubangiji zai saka mana!!
A alamarin Khadija
Sam ban kama ki da komai ba Tabbas kin yi k’ok’ari wajen kare kanki amma na san komai laifinki ne kuma shima zaki had’u da Ubangiji zai yi mana hisabi mu uku ya bi mata hakkinta wanda a ko da yaushe idan na tuna hankalina tashi yake yi matuk’a amma dole na san sai na fuskanci Ubagiji da wannan tarin zunubin da kika yaudareni kika sanya na aikata …..
Kukan da ya kufce masa ne ya sanya ya gagara cewa komai kafin da kyar ya samu ya ci gaba da cewa”zamu had’u da ke a lahira!!!but for now Khadija bana k’aunar in sake jin ko da labarin ki ne dan haka ki bi Yassir ku b’ace mini da ga gani har gaban abada ba na so in sake jin ko da muryoyinku ne!!!!!”

Tabbas wannan itace rana mafi muni a rayuwar Mommy…wani irin kuka take yi tana janyo numfashinta da mugun kyar….duhu duhu kawai take gani!!
tabbas ta san Idan ta biyewa Daddy tsaff zai sake ta a take a yanzu shiyasa ta yanke shawarar tafiya kamar yadda ya buk’ata tun kafin ta b’intike igiyoyin aurenta ta tonawa kanta asiri ta tarwatsa kanta….gara ta samu ta je ta yi sabon shiri a samu ya biyota ya rarrasheta ya d’aukota da kansa ya dawo da ita gidan, daga nan kuma ta san abun yi saboda ta riga ta san ba kowa bace silar wannan bala’in da take a ciki face Manubiya,dan haka dama ta gama tsarawa tunda ta k’i fita daga rayuwar Yashjub gara kawai su mutu tare cikin gaggawa……tun kafin su zamo ajalinta…..

Tana cikin wannan tunanin kamar a mafarki ta ji muryar Daddy yana cewa”kwanaki da kika tarwatsa auren Yassir da Kausar na sake ki!!
Da na fahimci abunda kika koyawa y’ay’ana kika turasu suka je suka aikata a gidan Yashjub shima a take a wannan lokacin na sake sakinki!!!
Kuma na san baki manta da sakin farko ba.. dan haka yanzu ni da ke babu maganar aure har abada!.”

…..Da farko duhu Mommy ta gani ya mamaye ganinta,sai kuma ta daina ji gaba d’aya kafin ta ji k’afafunta da hannunwanta da duk wani sassa na jikinta kamar ma babushi!!finally kuma ta tafi luuuuu ta zube a wajen sumammiya.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 42
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.


Gaba d’aya Yaran kanta suka nufa har Junior,babu kalar ruwan da ba su yayyafa mata ba amma ko gezau!
Dan haka Yasira ta kalli Junior hankali a masifar tace”Junior taya ni mu d’auketa mu kai ta sama sai in kira Dr…”

Ko gama rufe bakinta ba ta yi ba Daddy yace”amma ba ku ji abunda na fad’a ba ne?!!
Wanne saman za a kai ta?”

Cikin tsananin mamaki Yasira ta d’an cika Mommyn ta d’ago tana kallonsa idanunta jazir tace”Daddy suma fa ta yi?a hakan still baka hak’ura ba so kake ta fitar maka daga gida?
Atleast ka tsaya a samu ta dawo cikin haiyyacinta mana sai a yi komai dan girman Allah.”

Hajiya Mama ta so ta saka musu baki tun d’azu amma kuma sai ta ga wannan decision d’in Daddy ne to make, ita dai ta basa shawara dan haka kawai sai ta ja bakin ta ta yi shiru.

Cikin d’aci Daddy yace”Yasira ban bawa kowa ikon ya hau mini da ita sama ba sannan iyaka minti biyar na bayar a fitar mini da ita daga cikin gidana!”.

Sosai zuciyar Yasira ta hau tafarfasa ta fusata sosai dan a ganinta no matter what ko dan darajarsu bai kamata ace ya kori Mommy ba on top of that kalli halin da take a ciki amma ya dage kawai shi a fitar masa da ita daga cikin gida kamar wata annoba!!
Idan ta gaskiya za a bi ai ba ita ta sanya Yassir ya yiwa Yashjub abunda ya yi ba!…..
Cikin sharar hawaye ta mik’e zuciyarta a iyaka wuya tace”Daddy muddin fa Mommy
ta fita muma binta za mu yi tabbas!!!
Cikin matsowa kusa da shi tace”are you still willing to loose us too??akan dai ka tsaya a yi magana a yi sulhu??”

Shiruu ya yi kamar ba zai ce komai ba (dama wannan shine abunda shi da Hajiya mama suke gudu!!!)
kafin chan ya d’ago ya kalleta yace mata”time d’in da na baku ku fitar da ita ya kusan cika…Yasira nan gidan ku ne feel free ki zab’i wajen Mahaifiyarki sannan ki dawo nan a duk lokacin da kika ga dama no body will stop you.
Iyaka abunda na sani na kuma tsaya akai shine a yau a yanzu sai Khadija ta bar cikin gidana ta bar rayuwata har abada!!!!.”

Wani irin kuka Yasira ta fashe da shi ta juya ta fita daga parlourn gaba d’aya rai a b’ace hankali a masifar tashe…….


Tana fita Daddy ma ya sa hannu ya share hawayen sa ya wuce sama da sauri…..
Hajiya mama ta bisa…..A tsaye ta same sa yanata faman safa da marwa yana ganinta ya k’arasa gareta ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka yace”ki yi hak’uri na gagara ci gaba da tolerating Khadija gashi kuwa abunda kike gudu shi zai faru da ni ‘za ta rabani da y’ay’ana Maamaa’!”.

Cikin tsananin jin tausayinsa Hajiya mama ta shiga rarrashinsa tana cewa”kar ka damu ba komai…dukda ba haka na so ace ka yanke hukuncin da wuri cikin fushi ba amma ba komai inshaaAllah komai zai yi dai dai,mai gaskiya shi ke da riba a ko da yaushe inshaaAllah za su dawo gareka za su gane gaskiya mu dai namu addu’a!!”.
…..
Har sama su Yadira suka bisa suka d’urkusa suka rik’e k’afafuwansa suna kuka akan ya yi hak’uri ko ba aure a tsakanin sa da Mommy ya barta ta ci gaba da zama a gidan ko a k’asa ne ya bata d’aki amma furr!!Daddy ya k’i yarda ya k’i amincewa k’arshema a gaban su ya kira y’an sanda ya ce su zo gidansa!
Yana gaama wayar ya kallesu yace”Wallahi idan Mommy da Yassir ba su fice masa daga gida ba har suka bari y’an sandan nan suka zo to sai ya sa an tafi da su cell!”.

Kuka sosai Yaran suke yi suna magiya amma Daddy ya sam ya k’i sauraronsu,Hatta Ummi wadda suka zo suka tarar da ita tare da shi a d’akin sai da Yadira ta rik’e hannunta tana kuka tana cewa”dan Allah ta saka baki ta tayasu bashi hak’uri.”
Hakanan Ummin ta fara bawa Daddyn hak’uri itama dan sosai zuciyarta ta tab’u da al’amarin gwanin ban tausayi,ta san Mommy ba ta kirki amma ko dan Yasmeen da Yadira da ta tabbatar sun shiryu sosai tun kwanakin baya yanzu kuma suke irin wannan kukan ya kamata a tausaya musu……

Sai dai fa duk wannan abun da suke yi ko a kwalar rigar Daddy fad’a musu yake yi yana sake maimaitawa “wallahi idan har suka bari y’an sanda suka zo to
sai sun tafi da su Mommy.!”

Suna cikin wannan halin Ya’isha ta kira su tace”idan za su bi su su sauk’o,ita da Yasira suna k’asa suna jiransu!”
Dan ita dama tun lokacin da Yasira ta kira ta ta sanar mata ko yunk’urin lallab’a Daddyn ma ba ta yi ba kuma wallahi ta gama sakawa a ranta sai ya nemesu ruwa a jallo!!!.

A b’angaren Yassir kuwa yana chan side d’insa yana jiran azo a ce masa ai Mommy ta wankesa komai ya wuce amma kawai sai ganin Yasira ya yi a hargitse tace masa”Mommy ta suma Ashe Daddy yanata sakinta ita ba ma ta sani ba yanzu babu aure a tsakaninsu sannan su Yasmeen suna chan suna ta lallab’ata Daddy amma ya k’i yarda su ci gaba da zama a gidan ya ma kira y’an sanda ya ce “a zo a tafi da su(shi da Mommy)”
Dan haka kawai ya taho su tafi gidan Mommy dake a tudun a Yola Ya’isha ta kwaso keys a samu a kira Likita Mommy ta farfad’o dan Yasmeen ta kasa yin komai kuka kawai take yi,idan ta farfad’o suka nutsu sai su san abun yi!.”

Da farko dafe kai Yassir ya yi da mugun k’arfi da hannunsa duka biyyn kafin ya cika ya fara fatali yana fashe fashe har hannuwansa sai da ya farfasa!

Hausahinsa Yasira take ji d’azu amma har ga Allah zuwa yanzu duk sai ya bata tausayi dan haka ta matsa ta rungume sa wanda hakan ya sa ya fashe a wani Irin kuka ya sakar mata dukkannin nauyinsa suka zube suka durk’ushe a wajen duk su biyun suna kuka!!
Cikin wani irin kuka yace”Yasira ba laifina bane ba,Daddy ya fi fifita Yashjub ya bashi duk dukiyar family d’innan bayan kamata ya yi ace ni da shi munada equal right….”
Muryarsa ce ta sark’afe sakamokon kukan da ya ci k’arfinsa ya sake sakinsa sa da mugun k’arfi…
Tabbas zuwa yanzu kam Yasira itama ta yarda idan Yassir yanada mugun mugun laifi tou Daddy ne silar komai shiyasa tausayinsu ita da y’an uwan nata da Mommy ya sake lullub’eta ta kuma rushewa da wani kukan….

Sun jima a haka suna kuka kafin dakyar Yasira ta d’ago fuskarta tace”Yassir a situation d’innan da kake a ciki kar ka bari ka shiga case da hukuma,kamar yadda ya fad’a ka tashi mu bar masa gida!
Tabbas abunda ka yi ba ka kyauata ba Yassir amma kar ka damu kana da mu!kana da y’an uwa tunda na fahimci pushing d’inka aka yi…ka taso mu tafi mu je mu fara ji da Mommy a samu ta farfad’o sai a san abunyi…..”
Kamar wani k’armin Yaro hakanan ya shiga d’aga mata kai dan a mugun tsorace yake bai saba shiga masifa da tashin hanakali irin wannan ba…

Important abubuwa ya kwasa daga nan ya rufo side d’in nasa suka nufi motocinsu.

Dai dai nan Yusra ta sauk’o itama da akwatinta dan Yasmeen tace a nan ita za ta zauna,already Ya’isha da Junior sun saka Mommy a motar Ya’ishan shiyasa tana ganin su ta kunna motar amma sai fitowar Kausar data gani a gigice ya sanya ta kashe motar ta fito.
…..
Da kyar suka yi convincing Kausar ta hak’ura da binsu a cewarsu ta zauna a nan ta zame musu ido a nan d’in kafin su dawo sannan ta samu ta haihu a nan d’in sai ya fi tunda ga Yash nan ya dawo inshaaAllah za su san abun yi Akan duk wata matsala tasu ta kwantar da hankalinta komai zai gyaru!za su dinga waya suna communicating,kar ma ta soma binsu yanzu gudun kar Daddy ya samu damar korarta itama…..

Sun ci kuka sosai Yassir ma ce mata ya yi kawai za su yi waya daga haka suka shige motocin su suka fice daga gidan Yasmeen kuma da ba ta bisu ba ta kamo hannun Kausar d’in suka koma ciki dan ta yi nauyi sosai…duk su biyun suna kuka wiwi haka nan suka nufi cikin gidan…
Su Yadira kuma direct gidansu suka wuce dan kukan da yake yi sosai ya d’agawa Junior hankali Shiyasa ya hanata binsu ma saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login