Showing 54001 words to 57000 words out of 244445 words
ce
Manubiya matar wanki
Ummi kuma matar Daddy ce
masoyiyar mahaifinki ba abar gaba bace a gareki.
Zan so ki gane sannan ki fahimci cewa Mommy using d’inku kawai takeyi amman na san ba za ku fahimci hakan ba
Like I said before
U are not living in reality,there is a lot for you to know”
“Mommyn tawa ce take using d’ina?,tabbas yau na sake tabbatar da ke mahaukaciya ce,bari kiji
Mahaifiyar da ta tsugunna ta haifeni idan tana da hali ko mosquito ba za ta tab’a bari ya cijeni ba.Ni ba mahaukaciya ce Irin kiba na san menene right
nasan menene wrong nobody is using or pushing me…”
Shiruu kawai Yahanasu ta yi tana la’akari da yadda maganganunta suka tab’a Yasira……tashi d’aya mood d’in Yahanasu ya chanza da kyar ta iya hana kanta kuka,ahankali ta kalli Yasira sosai kafin tace “Mommy can do more than
using d’inki Yasira,believe me!”
Wani irin yanayi Yassira ta ji ta shiga daga kallon idanuwan Yahanasu,da sauri da kauda kanta gefe ta yi shiruu na y’an sakanni…da kyar ta fatattaki tausayin Yahanasu da mugun tunanin da take k’ok’arin dasa mata a rai ta juya fuuu ta fita da sauri.
Tabbas sun yi sake kam
d’an hakkin da ka raina….
gashi har tana treatning d’inta
Yahanasunda da idan ta saka mata kara bata Isa ta tsallaka ba amman wai yau itace take fad’a mata maganganu har haka!ba laifin kowa bane laifin
Mommy ne da ta fara taka musu burki a kanta,a tunanin Mommy Yahanasu ba ta Isa yin komai ba to gashi yanzu ta zame musu problem.
…
Ba bu yadda ba su yi ba amman duk ta inda suka zaga gidan a cike yake taff.
Baba larai kamar ta d’aura hannu aka ta fashe da ihu haka tanaji tana gani ta hak’ura da abubuwa da suka zo da su za su yi,ko d’aya cikin kwalayen flask d’in da suka shirya a kan za su saka turaren a ciki suje su jere ya gama su tafi da shi
fasawa sukayi dan zuwa yanzu ba damar yin wannan basajar,dan Yasira ta yi mata signal d’in Yahanasu
sannan ga dangin amarya
sun kunna nasu ba zai yiu su suna dangin ango su zo su hau kunne kunne ba suma,besides ko mahaukaci Idan ya ji warin ya san ba turare bane suka kunna.Yayyafe yayyafen da suka shirya yi shima ko Ina mutane……
Dakyar Yassira ta lallab’a Baba larai had’e da d’an fad’a
tukunna ta hak’ura amman da cewa tayi”sai ta yi a gabansu bata damuba”
Ita dai yassira tsoro takeji da kyar dama ta yadda ta biyo su
bata nuna bane amman maganganun Yahanasu sun ratsata ga kuma abunda Ya’isha tace mata sir Najeeb yace kuma ta san tsaf zai iya bada sheda in Yahansu taje ta fad’i wani abun akansu….ita tsoronta kar su je su sake lalata relationship d’insu da d’an uwansu shiyasa ta yi dagaske suka tarkata suka yi gaba
bayan sun gama kushe gadon Manubiya a gaban su Jidda
Yasmeen harda cewa “Irin gadon matar mai gadin su ne
exactly
Itakam dan Allah anjima a rufe d’akin in an kawo amarya dan wanann abun kunya ne ba kad’an ba”
Yadira ma y’ar k’arama da ita
amman harda ita a masu cewa
“Ita Wallahi da ta ji anata jeere jere ta d’auka za ta zo ta ga wani abun kirki ita wallahi
gadon ma tsoro yake bata…”
Ba wanda yace musu uffan
amman Ummi ta gama shirya gayawa Daddy in ta koma
dukda basa magana
amman for Manubiyas sake zata kulashi ko da ace zai ji haushin tane dan ba za ta
zuba ido su tisa y’ar mutane a gaba ba dan a yadda
taga take taken su indai aka barsu to akwai kallo.
A b’angaren Jidda kuwa,zuwa yanzu wallahi ji take kamar ta hana Manubiya tarewa da wannan mutumin,kamar ta wargaza auren ma gabad’aya saboda waenan mutanen,ta san yanzu is too late
shiyasa kawai ta yi shiru ta dinga ajiyar zuciya
tanaji kamr za ta fashe.
Haka ma Siyama,ga takaicin Najeeb ga kuma takaicin dangin mijin Manubiya…anya akwai haske a lamarin nan kuwa!dan ita ko a wasa bata tab’a jin labarin jahilan dangin miji Irin waennan ba.
K’iri k’iri suke yin abunsu ba b’oye b’oye ba kauda kai babu kissa babu kawaici,a yadda
suke ta gaya musu zafafan maganganu babu control
wallahi da waensu aka samu
da sai an dambatu!,kawai dai sun samu masu kauda kai ne da gudun magana shiyasa suka kyalesu.
A haka ma basu ga matsugunnin su ba kenan,shiyasa daga Jidda har Siyama suke ta addu’ar ’Allah yasa banda su za a zo d’aukar amarya.’
Bawai suna jin kunyar gidan na su bane A’a kawai dai ba sa so su zo su yi musu shirme a gaban mutane ne.
Suna wucewa Ummi ta yi musu sallama bayan ta ajjiye ragowar frames d’in da ta so da su tace “za ta je ta d’auki k’awarta,sai sun had’u a wajen d’aukar amarya.
Munirat tashi d’aya tace”ta tafi kawai sa had’u a wajen d’aukar amaryar”
Ummi tana wucewa suma suka fara shirin tafiya
Aisha da Yahanasu za su zauna a gidan har a kawo amarya, Siyama kuma za su wuce gida wajen Manubiya dan an santa ba k’awaye gareta ba so tana buk’atar su.
Jidda ba ta son shiga motar Yassir Siyama ma ta nace itama ba zata shiga motar Najeeb ba.
Allah ya so Siyama Najeeb ya tafi gida yin wanka dan an kusa tafiya d’auko amarya,Yassir ma ya d’an fita shiyasa suka yi wayo suka ce “ba za su iya jira har su dawo ba babu time za a b’ata lokaci,kuma akwai vail d’in manubiya a wajen Siyama kuma yanzu ta kirata tace tanaa buk’ata zata chanja kaya…”
Ba dan Yahanasu ta so ba ta barsu suka tafi su kad’ai amman da har ta d’auki waya za ta kira musu Najeeb.
Sallama suka yi musu daga haka suka fita suka yi tafiyarsu a adaidaita sahu.
Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya
hatta su Jidda sai da suka d’an fahimta.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 18
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Manubiya tana chan d’akin su Siyama dan inna kara ta yi ta ce a tafi da ita chan idan an zo d’aukarta a d’auke ta a chan.Haka nan aka wuce da ita d’akin Anty umma bayan inna Baba ya Nafi’u da ya Musbah sun gama yi mata fad’a sun yi mata sallama had’e da saka albarka..da kyar aka b’anb’are Manubiya daga jikin su Baba tana wani Irin kuka kamar za ta shid’e!
Ba k’aramin mamaki Inna ta ji ba da taga maman Abbakar
da maman Baraka sun zo mata,dan ana fita da Manubiya sai ga su sunzo suna ta washe baki kamar ba su ba,sai da suka zauna a d’akin suka shiga yi mata Allah ya sanya alkhairi tukunna ta tabbatar da gaske wajen ta suka zo dan sam ita bata yi expecting ko iskar su ba…kasancewarta mace mai kawaici yasa kawai ta karb’esu ba yabo ba fallasa,daga haka ta gaya musu inda amaryar take.
Kan Manubiya har ya fara juyawa tsabar turaren wuta,a
neighbors d’insu dama akwai wata mai siyar da kayayyakin gyara,haka aka had’a da wanda Inna ta basu kafin su fito da na matar da na wajen su mama ake ta banka mata,dan dama ita inna kunyar fulani ba lalle ta barta ta cewa Manubiyan tayi ba.
Haka suka d’aura ta akan kujerar tsugunno itakam kanta in banda ciwo ba abunda yake yi mata.
Har zuwa wannan lokacin ba matar Baba Habu ba matan Uncle babu y’ay’ansu kamar
ba biki akeyi ba.
Adaidaita sahun su Siyama tana yin parking
motocin Abokan ango suka k’araso suma wajen guda goma.Ba k’aramin dad’i Siyama ta ji ba da taga babu motar Najeeb a ciki,abunda ba ta sani ba kuwa ashe mota ya chanza…d’azu da Yahanasu ta yi shirin kiransa ashe ya shiga ita bata sani ba,daga jin yadda Siyaman take bada excuse tashi d’aya ya fahimci dodging d’insa take yi,shiyasa ya chanjo mota mai tint yana tunani da addu’ar shigarta motar dan yana buk’atar su fahimci juna a yau ya wanke bak’in fentin da tayi masa.
Ana ajjiyesu ya hange ta kuwa,murmushi ya yi yana jin wani sanyi yana ratsashi,
ya san ya yi mata laifi
kuma Ya isha ta b’ata mishi sunanshi a idon Siyama
amman kuma abunda tayi
wanda yake nuni da kamar kishinsa ne takeyi hakan ba k’aramin dad’i ya yi masa ba….
Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya
hatta su Jidda sai da suka d’an fahimta,gudun kar su ji ba dad’i ne ya sanya ta yi sauri ta ware dan ita kawai mamaki ta d’an yi ba wai kyama ko wani abun ba dan ta san da talaka da mai kud’i duk Allah ne ya yi su.
Kudin yana cikin jakar jidda shiyasa ta tsaya sallamar mai napep d’in su Siyama kuma suka ce bari suyi sauri suje su sanar dasu a fara shirye shirye.
Tana gama bada kud’in ta juyo kenan kawai ta ga mutun a tsaye a daff da ita.Ba ta d’ago ta kalli fuskarsa ba
amman tabbas ta fahimci shine sannan ga k’amshin turarensa da ta sanshi da shi
shekara da shekaru!
She’s not suppose to be feeling this way!kamata ya yi ace babu wani sauran son sa da k’aunar sa da ya rage dede da kwayar zarrah a cikin zuciyarta sai dai kuma tashi d’aya ta ji komai ya dawo mata sabo kamar ma bai tab’a yi mata laifi a rayuwa ba haka takeji a halin yanzu,ba ta da wani burin da ya wuce ta d’ago ta kalli kyakkyawar fuskarsa ma’abociyar murmushi wadda ta bada gudun mawa matuk’a
wajen sace zuciyar ta!
ta yi misssing d’insa sosai sannan ta tabbatar wa da kanta har yanzu tana son abunta amman kuma ba zata iya ignoring abunda ya yi da kuma wahalar da y’an uwanta suka sha duk a ta dalilinsa ba.!
Dan haka da sauri ta yunk’ura za ta matsa shi ma ya yi sauri
ya sake shiga gabanta ya tsaya har sai da goshinta yad’an bugi k’irjin sa!.
She’s trying real hard amman tabbas ta ga alamun
Al’ameen ya rantse sai yayi breaking d’inta….ba ta san
lokacin da hawaye suka fara sintiri a kan kyakkyawar fuskarta ba tana jin wani irin yanayin shauk’i k’auna tausayi mai tafe da rashin jin dad’in hakan da ta ke ji game da shi.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya sauk’e kafin yace
“Ba ki ma yi missing d’ina ba ko?takura miki ma nayi ko?
Jidda kin tsanesu har haka
ko kalllona ma bakya son yi?”
Ya k’arashe maganar tasa a hankali sannan kamar mai shirin fashewa da kuka!.
Sai da ta yi kokawa da zuciyarta tukunna ta samu ta d’aga mishi kanta alamar ‘EH’.
Shiruuu yayi kamar baya wajen
shiyas ta d’an d’ago ta kalle sa,ba ta yi zaton ganin hawaye a idonshi guda d’aya ba amman sai ta yi sauri ta saka a ranta crocodile tears ne sannan ta yi saurin mayar da kanta k’asa….
So take ta ce ya matsa ta wuce amman ta kasa saboda asalin gaskiya sam bata k’aunar matsawa daga gareshin.
Ajiyar zuciya ya sauk’e
tare da fesar da numfashin da har sai da ta ji calm scent d’in numfashinsa kafin yace”Na san dole za ki ji haushina dole
za ki yi fushi da ni amman ba ki san yadda na ji da kika ce ko ganina bakya son yi ba,a tunani na mun wuce haka!.
Amman ba komai laifina ne
na d’auki blame d’in saboda Jidda bakya laifi a wajena kin riga kin sani.Alfarma d’aya nake nema a wajen ki
dan Allah dan Annabi kiyi min adalci ki taimaka ki bani lokaci
In yi miki clearifying komai
dan Allah pls”
Ya k’arashe maganar tasa yana mai had’e hannayen sa biyu waje d’aya alamun rok’o ba tare da ya damu da a waje su ke ba.
D’agowa ta yi ta kallesa da idanuwanta da suka cicciko da hawaye kafin tace
”Ya Al Ameen!
ni da kai
ba zai yiu ba!.
Baka san halin da ahalina suka shiga ba duk a ta dalilin biyewa son zuciya da nacin mu,idan
akwai alfarmar da zan rok’a a duniya a halin yanzu daga gareka shine ka fita a harka ta ka hak’ura dani ka rabu dani har abada dan girman Allah”
Da sauri yace”Jidda kin san ba zan iya ba”
D’an matsawa gareta ya yi wanda hakan yasanya ta ja baya da sauri,kamar zai fashe da kuka ya share fuskarsa da duk hannunwansa biyu sannan
ya d’an ja hanci kafin yace”Pls just one more chance!I’ll make everything right I promise
sannan zan yi miki clearifying komai,na san
kina jin haushi na ne akan rashin nemanki da na yi tun bayan tafiya ta,Inada reason Jidda kuma na san idan kika ji za ki yi min uzuri”
Sunkuyar da kanta ta yi sosai ta share hawayenta daga haka ta zagayesa dan ba ta ga amfanin tsayuwar tasu ba,ita kunya ma takeji wani a cikin y’an gidan su ya ganta da Al’ameen.
Tana wuce sa ta ji ya rik’o vail d’inta,da sauri ta juyo da niyyar ce masa ya cikata amman sai ta gagara sakamakon ido biyu da suka yi da Ya Musbah.
Tashi d’aya ta rikice wanda hakan yasa Al’ameen d’in waigawa shima,shi kansa sai da ya d’an ji kunyar Musbahu dan haka ya d’an lumshe ido ya bud’e kafin ya k’arasa juyawa gaba d’ayanshi.Ganin yadda Ya Musbahn ya k’i kallon either of them instead kawai ya tsurawa hannun Al’ameen wanda ke rik’e da mayafin Jiddan ne ya sanya Al Ameen d’in cikata a hankali,daga haka ya d’an fesar da numfashi ya kallesa sosai tukunna ya mik’a masa hannu alamun su yi musabaha.
Ba tare da ya kallesa ko hannunsa ba ya cewa Jidda
“Wuce ki shiga gida!”
Kamar jira takeyi
kuwa hakanan ta wuce wuff
har tana d’an tuntub’e.
Bata san ya sukayi ba amman ko da ta je gaff da shiga gidan ta juyo ta tsinci Ya Musbah ne yana magana da Al’ameen d’in kuma daga gani ba maganar dad’i bace dan ran Ya Musbah a mugun b’ace yake yi masa
maganar har yatsa taga yana nunawa Al’ameen d’in.
Tana shiga d’akin su ta fara nufa,ba kowa daga Inna sai Mama sai wata y’ar tsohuwa(iya ramma).Inna tana had’a y’an ragowar kayayyakin Manubiya da suka yi saura tana hawaye Mama tana zauna a gefenta suna rarrashinta ita da iya ramma.
Anan ta zauna ta shiga taya Inna suna yi suna hawaye duk su biyun sun k’i ma su ji rarrrashin da ake ta yi musu.
Jidda ba ta yi mintina uku da zama ba…suna gama zuge akwatin wayar Mama ta hau k’ara,cikin mutuwar jiki ta k’arasa ta d’auki wayar a hankali ta kara a kunnenta dan duk su Inna sun gama kashe mata jiki…
“Subahanallah”
Suka ji Mama ta ambata kafin tace”ki yi hak’uri ki daina kuka gani nan zuwa.”
Tana ajjiye wayar Inna ta mik’e ta na share hawayenta kafin ta shiga tambayar ta “mai ya faru?”
A gaggauce tace mata”Ammi ce ta kirani wai in zo mu kai Al’ameen asibiti yanzunna haka kurum yana shiga gida ya yanke jiki ya fad’i…dama ni tun da ya dawo wallahi na lura kamar ba shi da lafiya kullum wani iri nake ganin sa.”
Cikin rashin jin dad’i ta k’arasa ta rike hannun Inna kafin tace”ki yi hak’uri inna,na so in zauna na raka Manubiya d’akinta,amman Alhaji baya nan dole suna buk’atata!”
Da sauri Inna tace”kar ki damu ki je ba komai hakan ma wallahi na gode kwarai Mama,Allah ya basa lafiya”
Ahankali ta jinjina kai tukunnan ta yi musu sallama ta wuce,sai da ta fita tukunna Inna ta lura da yadda Jidda ta cusa kanta a cikin cinyoyinta jikinta har wani irin vibration yake tana wani irin silent kuka kamar ranta zai fita,ajiyar zuciya ta sauk’e dan dama sai da ta saka haka a ranta daga jin bayanin Mama….a hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna tukunna ta sa hannu ta d’ago fuskarta wadda ta yi dagaje dagaje da hawaye da gumi har ma da majina,sai da ta share mata fuskartata tukunna ahankali sosai tace”kin had’u da shi ne yanzu?”
Cikin kuka Jidda take kallonta tana so ta yi magana amman sam sai ta gagara shiyasa kawai sai ta afka jikin Inna ta sake fashewa da wani Irin kuka abun tausayi.
Ajiyar zuciya wannan tsohuwar ta sauk’e kafin ta k’araso kusa da su ta ci gaba da lallashinsu dan ita ba ta ji abunda innar ta ce da Jiddan yanzu ba……Sun jima sosai matar tana lallashinsu kafin da kyar aka samu Jidda yi shiru ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.
A haka Siyama ta shigo ta same su itama idanunta sun yi jaa alamun ta taya Manubiya kuka,sai da ta k’arasa kusa da su ta zauna jikinta duk a sanyaye tukunna tace”Umma tace wai ace miki iyayen ango sun zo,a je a ce musu su shigo ne?
Dum!!
Haka duk su biyu suka ji k’irjin su ya buga.
A hankali Inna ta kalli Jidda tace mata”su je ita da Siyama su shiga da su parlourn su Siyaman. “
Ba su dad’e da fita ba itama suka fita ita da wannan Iya ramma wadda ta tilasta mata dole suka wuce parlourn su Siyama tare…..
Su Jidda suna fita da Baba larai suka fara cin karo tsaye
a bakin motar Yassira tana zazzare ido tana k’arewa gidan kallo fuskar nan a yatsine.
“Ya salam”
Jidda ta ambata a cikin zuciyarta kafin ta d’auke kai
ta k’arasa wajen Yahanasu
wadda ta gani suna fitowa daga mota itada wata,kusa da
motar Yahanasu motar Ummi ce itama su biyu dan haka Jidda ta d’an saki fuskarta….Su Ummi dama tun ranar farko ba su raina gidansu Manubiya ba,to haka yau suma k’awayensu da suka zo tare da su….. talaka da mai kud’i duk Allah ne yake yinsu,kuma Ubangiji yana iya maida talaka mai kud’i cikin dare d’aya vis versa sannan
kowa da kalar tasa baiwar,kuma babu wanda yafi wani a wajen ubangiji sai wanda yafi bauta masa ya fi tsoronsa,shiyasa su kam basuga kuma basuji komai ba,all that matters shine Yash yana son Matarshi kuma tana da tarbiyya hankali da nutsuwa.
Sab’anin su Yassira da hankalinsu ya sake tashi
ransu ya sake b’aci….”tabbas
dama a yadda Yash yake