Showing 39001 words to 42000 words out of 244445 words
tukunna Manubiya ta d’an sake…..ana fara kiraye kirayen sallar magrib kiran wayar Yash ya shigo wayarta,ta yi mamakin ganin kiransa a daidai lokacin sallah amma sai ta d’auka cikin sanyin murya ta gaidashi,
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”lafiya
Alhamdulillah”
Kafin ya d’aura da cewa”yau na shiga busy ban samu na dame ki da kira ba,”
Murmushi kawai ya ji ta yi a hankali
Shiruu ya yi kamar mai nazartar wani abun kafin yace”wa ya saka min ke kuka??.
Fad’a aka ta yi miki ko?”
Ahankali ta sake yin murmushi kawai. Numfashi ya sauk’e kafin yace”Aikuwa yanzun za’a sake yi mana wani,dan na san nasiha Baba zai yi mana,ya kirani akan yana buk’atar ganin mu a tare,Ina ma unguwar yace bayan magrib zai ganmu.”
Maganar sa ce ta katse jin ana shirin shiga sallah,shiyasa ya yi mata sallama yace ta zama
ready suna idar da sallah Baba zai gansu.
Sallah ta fara yi tukunna su Aisha suka taimaka mata ta chanza kaya zuwa super(exclusive)black colour d’inkin riga da zani,da ash chantily vail mai kyau kauri da tsada!.
D’aurin gaba ta yi irin wanda ake yayi ta rufa mayafin na ta har ka,kana ganinta ka ga amarya dan ta fito rass da ita kamar ka sace ta ka gudu dan tsananin kyau da haiba.
Tana cikin gyara sakun d’an kunnen ta ya Musbah ya lek’o yace ta zo su je ita ake jira.
Sai da ya kaita k’ofar parlourn su Siyama tukunna ya juya…ya so ya shiga ciki shima amma sai ya zab’i ya koma masallaci dan ya samu su rik’e kaka mallan a chan dan tun da ya ga Yash ya zo gaba d’aya hankalinsa ya tashi sun san indai ya shigo cikin gidan to sai ya je inda yake su kuma ba sa so ya je gudun kar ya kwafsa shiyasa da shi da ya Nafi’u suke ta jan sa da zance tunda yanzu yana kula su yana ji da su….dan su samu su yi buying time ma su Baba..
A zaune suke akan carpet su biyu suna magana Yashjub sai wani sussunkuyar da kai yake yi,amman ta na yin sallama bai san lokacin da ya d’ago ya kafeta da idanuwa ba…har ta k’araso ta zauna bai daina kallonta ba sai da tace”ina wuni tukunna ya yi snapping out da kyar ya ce “lafiya”daga haka ya sunkuyar da kanshi k’asa yana jin wani yalwataccen farin ciki yana ratsasa ta koina…..
…Nutsatsiyar nasiha Baba ya yi wa Yashjub da Manubiya tare da fatan alkhairi da sanya Albarka
Daga nan ya bawa Yash d’in amanar Manubiya……
Hatta Yash jikin sa sai da ya yi wani irin sanyi,Manubiya kam tun lokacin da Baba ya fara magana ta fara kuka.
Sosai kukan nata da nasihar Baba suka taru suka kashewa Yash jiki,shiyasa ya gagara d’agowa yana jin kamar shima ya fashe da kukan.
Sai da aka kiran sallar isha tukunna Baba ya sallameta shi kuma suka wuce masallaci shi da Yash.
Tana shiga d’akin nasu Aisha ta dafe kai tace”shikenan an dawo mana da aiki sabo”
Murmushi su inna da Siyama suka yi daga haka suka ci gaba da had’a jakar takeaway d’in da za a raba gobe inshaaAllah a wajen d’aurin aure.
Kamar d’azu yanzun ma
Aisha ce ta yi ta aikin lallashi,especially ma da ta tab’a jikin Manu d’in ta ji zafi rad’au,nan take hankalinta ya sake tashi……
Da kyar kuwa Manubiya ta samu ta yi sallah dan tashi d’aya zazzab’i da ciwon kai suka yi mata rufdugu,shiyasa Aisha ta ja ta zuwa d’akin su yaMusbah ta bata magani ta sha tukunna tace “ta kwanta anan”dan d’akin nasu ya cika da makwaftan da suka lek’o taya su aiki.
Ba ta dad’e da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita dan har da maganin bacci Aisha ta had’a mata da shi ai kuwa kasancewarta a gajiye kwana biyu ya sanya nan da nan baccin ya d’auke ta.
Ko da Yash ya kira Aisha ce ta d’auka,yana ji Aishar tace ta yi bacci ya ce “Alhamdulillah”dama aikin lallashi ya so ya yi kafin ya wuce but tunda har an lallab’ata ta yi bacci shikenan dan haka ya yi wa Aisha sallama da godiya daga haka ya kashe wayar ya wuce bayan yayi sallama da su Baba da kaka mallan………
Washegari.
A d’akin ya Musbah Aisha Manubiya da khairat suka kwana dan tunda Manu ta kwanta sai kiran sallar asubah ne ya farkar da ita,Aisha bata so ta tasheta shiyasa ta cewa su ya Nafi’u su tafi da shi da su Muhsin da ya Musbah yau d’akin su is occupied
Tana farka wa ta hango Aisha a kan daddum tana nafila,dan haka itama ta mik’e ta fad’a toilet ta kama ruwa ta yi alwallah ta d’auraye bakinta da iyaka makilin d’in da yake available ta fito tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo dan ba ta saba kwana da manyan kaya ba.
Har ta fito Aisha ba ta Ida ba…darduma itama ta nema ta shimfid’a a gefen Aisha itama ta tada ik’ama domin gabatar da nafila….ta na idarwa aka kira asslatu dan haka ta mik’e ta gabatar da sallar asubah….
Sai da suka kammala Azkar tukunna suka gaisa ita da Aisha, ta bata wayar ta..miscalls d’in Yash ta gani na jiya kafin Aisha ta d’auka sai wanda ya kirata around sha biyu na dare da kuma yanzu da asubah.
Sai da ta fara cire wayar a silent tukunna ta kira sa…ringing uku ta yi ta kashe dan ta san ko ta bari ya kai k’arshe ba d’auka zai yi ba.
Ko gama haske wayar ba ta yi ba ya biyo kiran,sai da ta d’an d’auki lokaci dai dai wayar tana shirin tsinkewa tukunna ta amsa. Murmushi ya yi kafin yace”sai an ja min aji tukunna za’a d’auka?kar ki damu gobe by this time na san babu maganar jan aji ko kunya a tsakanin mu dan tuni zan yi fata fata da su.”
Da sauri cikin san kawar da zancen tace”Ina wuni”
Ta fad’i hakan a ranta tana mamakin Yash,a da kamar ba ya magana amma ta lura tun lokacin da aurensu ya matso ya zama mai surutu,ko wacce Irin magana in ta zo bakinsa juye mata yake yi,gaba d’aya ya daina jin kunyar ta.”
Ta na cikin wannan tunanin ta ji yace”lafiya Alhamdulillah,matar Yash in the next 5 hours!7 minutes!37seconds inshaaAllah.”
A take ta ji gabanta ya yanke ya fad’i,tana son Yash amman ta rasa dalilin wannan fargaba da tsoron da suka lullub’eta tun shekran jiya suka k’i barinta,tun shekaran jiya hankalinta yake a tashe….
A hankali ta ji yace”baby!kin yi shiruu,ko ba a yau zan cire kunyar b…”
Cikin katseshi ta ce”na’aam!”
Sai kuma tace”inna tana kirana,bari inje?”
Dariya sosai ya yi dan ya fahimci zillewa take son yi,kylaleta kawai ya yi ba dan wayonta ba….cikin sanyin murya yace”ki gaida ita….”
Ahankali tace “sai anjima”
Yana wani irin blushing yace”Allah ya kaimu”
Daga haka Manubiya ta yi saurin kashe wayar ta d’aura a kan k’irjinta tana haki akai akai,dariyar da Aisha ta kwashe da ita ne ya dawo da hankalinta cikin d’akin sam ita ta ma manta da Aisha a d’akin wallahi….
Sosai Aisha take dariya kafin ta mik’e tsaye ta je ta ta tofawa y’arta da take ta bacci add’ua tukunna ta juyo ta kalli Manubiya cike da zolaya tace”Yarinya ba ki ga komai,ba ki ji komai ba.”
Tana gama fad’in haka ta sa kai ta fice abinta
Da sauri Manubiya ta cusa kanta a cikin cinyoyinta tana mai jin kunya!fargaba da wani irin yanayin da ba ta tab’a tsintar kanta a ciki ba.
Har Yash ya kashe wayar ya ajjiye a gefe bai daina blushing ba,ya jima a zaune yanata tunane tunane da zumud’i kafin ya mik’e ya fad’a bathroom.
A side d’in Yashjub da ga shi sai Abokansa biyu da suka zo jiya..…gidan kamar ba biki ake yi ba!bakowa,dan side d’in su Mommy ma ba kowa hatta y’ay’an uncle d’inta ma ba su zo ba sakamokon fad’an da suka yi da ita kacha kacha recently.Yayar Munirat ma ta so zuwa amman sai ta had’u da laulayi mai tsanani shiyasa ta hak’ura akan bayan bikin in ta samu sai ta zo ta ga amarya ta yi Allah ya sanya alkhairi.
K’arfe 7:25am Yashjub ya fito daga wanka k’arfe 8:00dai dai ya shirya tsaf ya kafa hula ya d’auki makullin mota da wayoyinsa ya zuba a aljihu rik’e da babbar rigarsa ya nufi k’asa sai tashin k’amshi yake yi.
A zaune ya tarar da Abokansa suna breakfast akan dining table ko wanka ma ba su yi ba,tsadadden agogon da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa ya kalla kafin yace”ku yi sauri fa kar ku sa mu makara.”
Dariya d’ayan yayi kafin yace”ango ka sha k’amshi”
“Bai sha ba tukun!wai Yash da gaske yanzu kake so mu tafi?8:00fa yanzun,ba sai 11:00 ne d’aurin auren ba?”cewar d’ayan
Cikin takunsa ya k’araso ya zo ya chake musu yace”na san 11:00 ne mana amman ai ya kamata mu tafi da wuri pls ku taso in ba haka ba Wallahi zan yi gaba in barku”
Dariya suka yi suka fara tsokanarshi da’mai zumud’i’suna yi suna k’ak’arin fahimtar da shi akan ya d’an jira amma inaa!sam Yash ya k’i hak’ura,hakanan suna ji suna gani ya azalzalesu suka yi wanka suka shirya8:30am suka fice daga sid’e d’insa,suka je suka gaida Daddy ya yi masa addu’a ya sa masa albarka haka ma Mommy da Ummi…daga haka suka fice daga gidan shi kam ko breakfast d’in ma bai yi ba.
Tun k’arfe 8:00am unguwar su Manubiya ta san yau akwai gagarumin d’aurin aure sakamokon motocin polisawa da sojoji da suka fara yi musu sallama,kafin 10:00am kuwa taff layin ya cika da jama’a,duk saurin Yash sai 10:00 am d’in tukunna shima ya samu ya k’arasa unguwar dan suna fita suka had’u da Najeeb da electrician d’in da zai yi wani wiring a gidan dan haka suka d’unguma gaba d’ayansu,da farko Yash so ya yi ya yace musu ‘su su je su tsaya a kan electrician d’in!shi kuma ya wuce’,sai kuma ya ga idan ya yi haka kamar yayi rashin kara ne ga kuma su Najeeb d’in da suke ta cewa “wallahi idan ya je tun yanzu dariya za’a yi masa,”shiyasa kawai ya hak’ura ya bi su ba dan ya so ba.
10:30am dai dai Daddy da Abhi suka k’araso da tawagar manyan mutane Abokanansu,ba iyaka layin ba hatta titi sai da ya cika da manya manyan motoci na alfarma…….
11:00am dai dai dubban mutane suka shaida d’aurin auren Yashjub Iman kura
Da amaryarsa
Manubiya Musa akan sadaki naira dubu d’ari uku lakadan ba ajalan ba.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 15
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Mai kwalliyar da Aisha ta d’auko tana gama pinning mayafin Manubiya a jikin d’ankwalin ta suka ji loudspeaker ana sanar da d’aurin auren Yashjub Imam Kura da Manubiya Musa wanda aka gama d’aurawa yanzun akan sadaki dubu d’ari uku lakadan ba ajalan ba…sai kuma hayaniyar maza ta fara tashi…..
Kuka ta fashe dashi ta zube anan kan katifar,yayinda su Aisha kuma suka shiga jero hamdala,matan da suke shigowa cikin gidan yanzun kuma suka shiga rangad’a gud’a…..nan da nan a cikin mintunan da ba su kai ashirin ba d’akin nasu har ma da gidan gaba d’aya ya cika taff da jama’a ba masaka tsinke masu hoto da amarya na yi masu Allah sanya alkhairi da hayaniya suna yi,…..itakam Manubiya gaba d’aya fuskarta ta kumbura kwalliyar ma har ta fara d’an gogewa.
Suna cikin haka gwaggo suwaiba ta kira waya,da inna suka fara gaisawa ta yi mata Allah ya sanya alkhairi sannan ta sake bata hak’urin rashin zuwanta (dan k’iri k’iri jatau ya hanata zuwa)tukunna ta nemi magana ta Manu…..fad’a da nasiha ta yi mata sannan ta sanya mata albarka daga haka suka yi sallama.
Duk yadda Manu ta so daurewa sam sai ta kasa dan haka ta saki hawayen da take ta rik’ewa,tana yi tana sheshshek’a da jan hanci…..su kansu su Aisha zuwa yanzu jikinsu ya fara yin sanyi
dan sai yanzu suka sake tabbatarwa da cewa “Manubiya tafiya za ta yi ta barsu”ga kuma fargaba da sanyin jikin da kan lullub’e kowa kama daga kan Amarya zuwa kam y’an uwanta
tashi d’aya duk sai ya lullub’esu gaba d’ayansu.
Jidda ce ta fara fashewa da kuka ganin haka yasa itama Siyama ta saki nata kukan da take ta k’ok’arin dannewa,murmushi kawai inna da mama suka yi suka ci gaba da harhad’a abubuwan da sukeyi ba tare da sun yi yunk’urin lallashinsu ba dan sun san muddin suka doshi inda suke tau tabbas suma kukan za su yi. Especially ma Mama wadda hankalinta yake a matuk’ar tashe sannan kanta ya d’aure katamau tun lokacin da ta ji an ambaci ‘imam kura’ ta san maybe coincidence ne amman dukda haka sai da ta shiga cikin tsananin fargaba.
Dakyar Aisha ta daure ta k’arasa inda Manubiyan take da niyyar lallashinta amman tana zuwa itama kawai sai ta fara hawaye.
Dai dai nan anty umma ta shigo tana cewa”Siyama ku zo ku tayani fara zuba abinci kuna mimmik’awa jama’a ga mutane chan suna ta shigowa har a b’angaren su Uncle,sannan ku kira su Musbahu a samu a fitar da takeaway d’innan kafin jama’a su watse…...”
Salati ta saka ganin yadda suke shirin mayar da d’akin kamar na zaman makoki,k’arasa shigowa cikin d’akin ta yi ta ajjiye k’atuwar kular hannunta tukunna ta k’arasa inda suke suka shiga lallashin Manu ita da ragowar matan da ke cikin d’akin.
Da kyar aka samu suka yi shiru kuwa tukunna ahankali cikin mutuwar jiki Aishar tace “Bari inje mu fara mik’a abincin”
Mik’e wa su Jidda suka yi suma suka bi bayan Aisha……
Duk wannan girkin da hayaniyar d’aurin auren da ake ta yi babu wanda ya lek’a ya taya su inna girki sai anty umma sannan kaff gidan ya Yusuf ne kawai ya lek’a wajen d’aurin auren sai kaka mallan wanda ya daddannawa Baba Habu zagi da ya so ya hanashi zuwa….sune ba sa kula Baba kuma fa ya bisu ya basu hak’uri ya fi sau nawa, shekaran jiya ya bi su ya basu invitation amman sunce”wai sau d’aya ya gaiyyacesu sannan bai sako su a cikin al’amarin sosai ba,sannan lokacin da aka kawo kud’i a gaban sa Nafi’u ya so yiwa Baba Habu rashin kunya amman bai ce komai ba sai da ga baya ya biyosa zai basa hak’uri tsabar ya raina musu wayo.”
Shiyasa yanzun ma ba su je ba kuma ba su turo matayensu hidimar mata ba,kaka mallan ma sun so su hanasa zuwa amman ya k’i hanuwa dan shi tun sassafe ma ya shirya ya sanya farar shaddarsa ta sallah ya nufi masallaci bayan ya yiwa baba habu kaca kaca…da shi kuwa aka dinga tarar bak’i…..babu wanda ya lura da su ba wanda ya san da su amman haka suka dinga faman shishshigi a wajen da shi da Yusuf!shi Yusuf connection yake nema Kaka mallan kuwa maula tuk’uru ya dinga yi a wajen dan ko marok’in wajen bai kai ya shi a iya maula da tara abun duniya a wannan rana ba.
Ba wanda ya fi tsanar sa a kaff wajen kamar Yassir dan ji yake yi kmr ya d’auke shi yaje ya jefa a rami kowa ya huta,ya tsani tsohon nan haka kurum bai mishi ba tun farkon had’uwar su. Ya tsani layin…gaba d’aya kunyar Abokansa guda biyu
da suka zo d’aurin auren tare yake yi,shiyasa fa dama shi bai gaiyyaci kowa ba! waennan d’inma dan Yashjub d’in ya sansu ne shiyasa ya gaiyyacesu da kansa su kuma suka zo,tun da suka shigo layin suke ta jero masa tambayoyi “me ya kawo Yashjub nan?
a nan kuma matar tashi take?”waye waye…..
Tou kuma yanzu ga kakan ta
wanda idanunsa suka rufe har Yashjub d’in ya je ya cewa” ya bashi kud’in da za a rabawa almajirai anjima ayi musu sauk’a” ……
Anan cikin gida kuwa
Su anty amarya suna nan a d’aki har yanzu ba wanda ya lek’o ko murna ko taya aiki,sun so su d’an lek’a su yi murna amma sai mazajensu suka sake hanasu,hatta su Salaha rufe su a d’aki maman su tayi hakanan Yaran suka hak’ura ba dan sun so ba….sai dai kuma ko minti talatin ba ta yi da rufe k’ofar ba aka zo aka fara bubbuga mata tana bud’ewa ta ga mak’oftan da take shiri da su ne suka shigo wunin biki hakanan suka shige suka zazzauna mata,kafin minti d’aya parlourn nata ya cika har ma da na su Baba Habu suma duk sai da aka shiga, ba yadda suka iya dan duk wanda ya fi shiri da su a neighbors idan ya zo wajen su ya ke zuwa ya zauna bayan ya je ya ga amarya….
Su siyama ma haka suka dinga kai abincin suna ajjiyewa da fara’a a fuskokinsu kamar ba su san me ma suka yi ba,shiyasa gaba d’aya kunya ta kama su ga shi dai ko Allah sanya alkhairi ba su je sunyi ba amman wunin biki ya kankama a parlourn su.
…..
Anan waje kuwa sun sha hotuna abunsu…haka aka yi komai aka kammala da ikon Allah cikin kwanciyar hankali da tsananin farin ciki. Sai da su Daddy suka wuce Abokan Yash ma duk suka wuwwuce dan bai cewa kowa zai shiga ya ga amarya ba saboda tsabar kishi, tukunna shi da Najeeb suka k’arasa wajen ya Musbah wanda suke tsaye da shi da ya Nafi’u suka mik’a musu hannu suka yi musabaha suka yiwa juna Allah ya sanya alkhairi kafin Najeeb yace”Am,muna so za mu ga amaryar
za a d’an yi
hoto,sannan za mu gaida su inna”
Ahankali ya Musbah wanda gaba d’aya yake jinsa upsidedown ya jinjina musu kai kafin yace”Bara in sanar da su
Innar”
Daga haka ya wuce ciki….
Su Siyama suna gamawa,suka yi sauri suka shiga wanka dan Aisha su take jira suje su kwashi kaya su kai gidan amrya,suna fitowa suka shiga shiri da hanzari…ba komai a fuskokinsu sai Vaseline ankon
su da suka yi na atamfa shi
suka saka dan har Aisha
Itama shi ta saka da mama,
A shape aka yi wa Siyama Jidda kuma riga da skirt
Atamfar kalar light blue ne da white shiyasa ta karb’i jikinsu ta sake fito da ainihin kyawun hasken fatar su…Tsayin su kusan d’aya ne sai dai Jidda ta d’an fi Siyama jiki kad’an.
White vail Siyama ta rufa