Showing 30001 words to 33000 words out of 244445 words

Chapter 11 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16477

yin fad’an to da dasauk’i amman fa tana fad’an ne akan wai ‘lokacin da za’a d’aga auren sa ba ‘ayi mata magnar ba ba’a tuntub’eta ba sai ji ta yi kawai an d’aga.Kuma wai Manubiya ba ta kiranta ta gaida ita amma tana ji suna yawan yin waya da Yahanasu har ma da Ummi…idan so yake ta yafesa a cikin y’ay’an ta kawai ya fito ya fad’a dan abunda ya ke yi mata ya isheta,in ba rashin sanin ciwon kai da wulak’anci ba ta ya zai dinga fifita kishiyar ta da y’ar kishiyarta sama da ita a rayuwarsa???….”

Yash ya so ya yi mata bayani ta fahimta sannan ya bata hak’uri amma yadda ta k’i sauraronsa da kuma yadda ya fahimci kamar ma baki take shirin yi masa ne ya sanya shi kawai ya fice ta k’ofar baya ya bar mata parlourn zuciyarsa tana wani irin tafarfasa.

Sam ya rasa dalilin da ya sanya Mommy take bak’in ciki da farin cikinsa.

Bai nufi side d’insa ba direct mota ya nufa ya shiga ya kunna ya fice daga mansion d’in gaba d’aya,ya nufi gidansu Manubiya.
Ya na yin parking a k’ofar gidan ya ji zuciyarsa tana yin sanyi ahankali ahankali,rabonsa da ita tun last month dan wannan karon da yaje uk ya dad’e sosai shyasa yake ji kamar ya yi shekara uku bai ganta ba,suna waya da chatting har ma da video call kullum amman yayi mugun mugun missing d’inta……tana zaune suna hira ita da mai gyaran jikin ta da su Siyama a parlourn su Siyama ta ga kiran sa,murmushi ta yi tana wani Irin blushing kafin ta yi picking,a hankali ta ji yace”surprise!ina waje”
Kad’an ya rage ba ta tsala
Ihun murna ba,da kyar ta iya cewa “ok” tukunna ta katse kiran ta kalli siyama tace”yana waje”ta fad’i hakan fuskarta tana baiyyana tsananin farin cikin da take a ciki.
Dariya Jidda ta yi kafin tace”Allah adda idan aka zo kaiki kika yi mana kuka kowa ya san kukan murna ne,”

Dariya duk suka saka wanda hakan ya sa Manubiya ta d’an nutsu ta bar zumud’in rufa mayafin da take yi kafin ta kalli Jidda ta galla mata harara tukunna ta kalli mai gyaran jikin tace”an gama?”
Murmushi matar ta yi kafin ta mik’e ta shiga harhad’a kayayyakin ta tace “ai ko ba’a gama ba jeki kawai”
Dariya sosai suka yi kafin siyama tace”ki shigo da shi nan bari mu tartare”

“To” kawai tace, da ga haka ta sa kai ta fice.

Tunda ta taho ya kafeta da idanu har sai da yasa ta ji kamar ta nutse dan yau kalar kallon nasa na daban ne….a b’angaren Yash kuwa har wani jiri jiri ya fara ji tsab’ar kasalar da ta rufar masa tashi guda,ya san yana son Manubiya so mai tsanani na tsanakani da Allah amma tunda yake bai tab’a jin kalar sha’awar ta da yake ji a yanzu ba,ya na ji from time to time ba wai ba ya ji ba amman abun na yau ya girmama,dan har wani ciwon ciki ne ya ziyarcesa tashi d’aya,ta yi wani kyau ta yi fresh kamar wata y’ar baby,har wani murmurewa ya ga ta sake yi gwanin ban sha’awa.

Cikin d’an turo baki tace”ni dai ka daina kallona”
Murmushi ya yi ya bi bakin da ake turo masa da kallo wanda yakenan kamar na y’ar jinjira ma’abociyar tsotso kafin da kyar ya d’an k’ura wa fuskarta ido tukunna yace”gani na yi kin sake zama baby,y’ar babyn Yashjub”
A hankali ta sunkuyar da kanta tana murmushi k’asa k’asa kafin tace” kaima ka k’ara kyau sosai”dan Itanma tunda ta fito ta lura da haske da kyan da ya k’ara….wani irin blushing Yash ya shiga zubawa kamar mai tallar makilin kafin dakyar ya samu ya tsayar da murmushin tukunna ya amsa gaisuwa da ya hanyar da take yi masa.
Daga nan ta yi masa iso zuwa parlourn su Siyama wanda har sun gyara tsaf sun kunnu turaren wuta…..Tabbas Yash da Manu sun yi missing juna dan sai da suka kashe sama da awa uku ba tare da sun ma sani ba,dukda kuwa Yash dauriya ce kawai yake yi dan yau kam shi kanshi mamakin kansa yake yi saboda bai tab’a jin desire irin wannan ba ga kuma ciwon ciki amman kuma ba ya so ya tafi so yake kawai ya yi ta kallonta…da kyar dai yana jin kamar kar ya tafi ya yi mata sallama dan Najeeb yana chan yana ta jiransa. Har mota ta raka sa yana ta zuzuta yadda ta yi kyau dan ba kad’an ba ta tafi da imaninsa…..itan ma santin kyan da ya k’ara take ta yi a cikin zuciyarta,a haka suka rabu kowa yana muradin d’an uwansa.

Bai yi tunanin za su yi dare shi da Najeeb ba dan har sha biyu na dare ba su samu sun kammala abubuwan da suka tisa a gaba ba,
Sai da yaje mota domin d’aukar wasu abubuwa tukunna ya ga wayarsa tana haske dan haka ya yi saurin d’auka ya k’ara a kunnensa
Yana d’agawa ya ji muryar Daddy yace”come home yanzu,Hajiya mama tana nemanka ta d’agawa kowa hankali”

“Okay tam”
Kawai yace daganan Daddy ya katse kiran sai a sannan Yash d’in ya lura da uban jerin misscalls d’in da aka jera masa,ajiyar wayar ya yi ya je ya cewa Najeeb zai tafi sukayi sallama tukunna ya nufi gida.

Yana zuwa
bai tsaya ma yin tunani ba gudun kar ya ji ba zai iya shiga ba dan har ga Allah ba ya son had’uwar sa da Mommy gudun kar ta kuma yi masa abunda ta yi d’azu…wayoyinsa kawai ya d’auka ya zuba a aljihu daga haka ya rufe motar ya nufi cikin gidan.
Tun kafin ya shiga cikin main parlourn ya fara jiyo hayanaiyar Hajiya Mama,tashi d’aya ya fahimci ita da Mommy ne sakamakon yadda ya ji tana
magana cikin fad’a da rashin kara sannan tone d’inta very rude!.
“Ai dama ba ki gaji arzik’i da ‘da’a ba,wallahi yadda na ga ba ki wani damu ba na san kece kika b’ata masa rai ya
bar gidan nan bani da tantama.Dama ta ya za ki so ya yi aure ya tara iyali ba tare da kin riga kin mallakesa ba!..y’a y’a dai Allah ya baki amma wallahi ko Akuya ta fi ki sanin ciwon y’ay’anta,ke kuwa kanki kawai kika sani burinki kawai ke kanki kad’ai sam baki damu da farin cikin su ba.
To bari kiji wallahi tun wuri ki san yadda kika yi ya dawo gida idan ba haka ba kema sai kin bar gidan nan!yau zan nuna miki cewa ba fa surk’ullenki da munafurce munafurcenki ne suka sanya na barki cikin gidan d’a na ba”

Ahankali ya ji Daddy yace “Mama ba fa inda Yash yaje
maybe aiki ne ya rik’e shi..”

Cikin tsawa Maaman tace”shiyasa sometimes nake jin kamar in rufeka da duka!,ai ko ba’a fad’a ba na riga na sani jikina ya bani gashi kuma ba ya d’aukar waya amman sai ce min kake yi aiki ne ya rik’esa wanne irin aiki ne zai hanasa d’aukar waya??”
Ba ta jira jin amsar sa ba tace”kuma Yadira tace min fita yayi ranshi a mugun b’ace,cikin fushi ta juya ta nuna Mommy tace “Kuma na san wanann makirar ita ta janyo fad’a da shi,ba ni da tantama
Ita ta b’ata mishi rai ita za ta yi abunda zai fasa auren dama tun farko ita ta hanashi yin budurwa.Wallahi Khadijah ki ji tsoron had’uwar ki da ubangiji
son zuciyarki yayi yawa,kwata kwata ba ki da tunani da lissafi mai kyau!”

Wani irin kuka Mommy ta fashe da shi wanda ya sa su Yassira suka k’arasa inda take itada Yasmeen suka rufar mata suka shiga bata hak’uri,fuskokinsu
tamau! alamun sun ji haushin abunda Hajiya maman take yi.
Itakam ko a kwalar rigar ta,haka nan ta ci gaba da tsigale Mommy tass.

A haka Yashjub ya yi sallama ya shigo ya samesu,da da farko so yayi ya juya dan wallahi kansa har ya fara ciwo amman kawai sai ya dake ya shigo.

Dasauri kowa ya d’ago ya na kallonshi Hajiya mama kuma ta nufeshi cikin takun ta na tsoffi da d’an sauri tana zuwa
ta yi hugging d’inshi sai kuma ta d’ago tana kallonshi tace “Karka b’oye min komai,mai ta yi maka?me ta ce maka?matsala take shirin kunno wa ko?so take ka fasa auren na sani.”

Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace “idan akwai wanda zai kunno matsala a aurena ai kece,tunda gashi yanzu ma abunda kike nasan duk kishi ne ya rufe miki ido kike k’ok’arin ki tada husuma tun kafin kishiyar taki ta zo”

Dariya Yadira da Munirat suka yi kafin Ummi ta d’an matsa kusa da su ahankali cikin ladabi tace “Hajiya mama mun gaya miki tun d’azu,babu komai InshaaAllah
Yadira kuma zolayar ki kawai take yi maybe kawai so take ta ja ki da magana”

“Umm um fa Ummi,ba ki san
halin matar chan ba kuma na san duk zolayar Yadira ba za ta
fad’i abunda zan yi wa uwarta fad’a ba ai.Anyways tunda kowa b’oyemin yake yi ba komai.”
Tana gama fad’in haka ta cika Yashjub ta Isa gaban Mommy ta tsaya tace”ko za ki mutu!sai
Yashjub yayi aure da yardar ubangiji,kuma idan kin haifu ki
je kiyi wani abun da zai jawo tangard’a,ko a makirce ko a asirance ko a Isa da mallaka na matsayinki na uwa!a nan za ki gane shayi ruwa ne!”.
Tana gama fad’in haka ta wuce sama ta bar ta anan ita da su Yasmeen da suka kawo iya wuya
Mom da Ummi ne suka bi bayanta daga haka aka fara watsewa daga parlourn.
Sai da Yash ya k’arasa wajen su Daddy da Abhi suka d’an gaisa tukunna ya juya ya nufi side d’insa…har ga Allah yadda Mommy ta durk’ushe tana kuka duk sai ya ji bai ji dad’in abun ba.

Da ruwa mai zafi sosai ya yi wanka ya d’an gwada kiran Manu jin shiru bata d’auka ba ne yasa ya fahimci ta yi barci dan haka ya ajjiye wayoyin sa ya fito ya nufi wajen Mommy bayan ya rufe side d’in nasa dan already Junior ya tartare kayansa ya koma side d’in Yassir tun lokacin da aka gama masa gininsa.

Allah ya so shi kuwa basu rufe ba dan haka ya shige ya haye sama yana mai sake jaddadawa da tirsasawa kansa”dole ya yi creating truce a tsakaninsa da Mommy,dole ya nemi albarkar ta!dole ya lallab’ata!uwa uwa ce!”


Ya yi mamakin samun su da ya yi a d’akin Mommyn su dukansu har Baaba Larai da
Yadira kamar wasu masu yin meeting.
Sake gaidashi suka yi gaba d’ayansu daga haka suka fara mik’ewa suna yiwa Mommyn sai da safe suna ficewa one by one dan yana gama amsa gaisuwar ta su ya koma gefe ya ya chake ya tsuke fuska…sai da Baaba Larai ta zo fita tukunna ya kamo hannunta yace “Banda ke Baaba”
Kallonshi ta yi ta kalli Mommy kafin tace “to d’an albarka”daga haka ta koma kusa da Mommyn ta zauna anan gefen gado.
Shiruu d’akin yayi kafin ahankali Yashjub ya fara takawa zuwa inda suke zaune,yana zuwa ya durk’usa a gaban Mommy.
Ba k’aramin shock suka shiga ba dan ko da wasa ba su tab’a kawo hakan ba,yaushe ne ma Yash ya durk’usa mata irin haka ba lalle ta iya tunawa ba


Suna wannan tunanin suka ji a hankali ya fara magana yana cewa “Mommy akwai abubuwa da yawa da kuma misunderstandings a tsakanin mu,ke mahaifiyata ce shiyasa no matter how na so in rik’e ki a raina hakan ba zai yiu ba dan ya zame min dole in yafe miki
sannan kuma in nemi gafarar ki amman pls Baaba ki zama shaida sannan ki nuna mata mahimmancin mu especially ma ni
a wajenta.Akwai abubuwan da kikayi min da yawa shiyasa in na tuno raina yake b’aci,idan
nine wani abun ya faru da ke hankalina a tashe har sai na ga anyi miki adalci amman ke sam bakya dubani a ko da yaushe..
Anyways komai ya wuce yanzu albarkarki da yafiyarki nake nema.
Sannan akan abunda kika yimin magana d’azu shima ki yi hak’uri zan yi k’ok’ari in gyara kema
kuma dan Allah ki gyara Mommy.”

Ahankali ta sa hannunta duka biyu ta d’ago shi ta zaunar dashi a gefen ta.
Shiruu ne ya biyo baya kafin ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana “Yashjub ba wai ban damu da kai bane
A ‘a
Ina duba circumstances ne,
na san kana jin haushina akan Yassir.Yashjub!ba ka riga ka haihu ba shiyasa bazaka tab’a sanin yadda na ji a lokacin da naga Yassir kmr gawa ba….inaso ka fahimceni ka fahimci ba wai na fi son shi akan ka bane ya sanya na fad’i maka abunda na fad’a ba a wachchar ranar,na fad’a na sake fad’a gaba d’ayanku ya’yana daidai kuke a cikin zuciyata,na san ko kai ne ka tarar da d’anka a halin da na ga Yassir a wachchar ranar na tabbatar sai ka yi kuma ka fad’i abunda yafi wanda ni nayi na kuma fad’a.Amman duk da haka kayi hak’uri ba zan sake ba inshaaAllah b’acin rai ne”

Ahankali Yash ya rik’o
hannunta ya girgiza mata kai yace “ba komai Mommy ba sai kin bani hak’uri ba”

Murmushi ta yi ta d’an shafa fuskarshi kafin tace”I love all of you amman kuma in ka lura mahaifinku ya fi fifita ka sama da kowa idan nima na yi hakan
to tabbas mu da kanmu zamu taru mu lalata tsakanin ku ne especially ma kai da
Yassir wanda yake ganin kamata ya yi ace kunada equal right da kai da shi,shiyasa dole wani abun zan ke kauda kai ba wai dan ban damu da kai ba sai dan son ganin an zauna lafiya.
Sannan maganar Kausar dan itama na san kana ganin kmar Ina fifitata sama da ku ko?”
Bata jira jira jin amsar sa ba ta d’aura da cewa”Kamar yadda ka kauda duk wani abun da kake tunanin na yi maka ka zo
ka bani hak’uri sannan kake neman yafiya da albarka ta a matsayina na mahaifiyarka
To
nima albarkar tawa mahaifiyar nake nema dukda kuwa ba ta
raye saboda inaso inga na cika mata burinta dan kafin mahifiyarmu ta rasu sai da ta damk’a min amanar maman Kausar tana kuka tana rok’ona in zame mata uwa da uba mu had’e kawunanmu,to haka itama maman Kausar a lokacin da ta zo rasuwa tana kuka haka ta bani amanar Kausar,
ta yaya
kake tunanin zan zubar da wannan amanar??
Kuma bayaga haka ma
Allah ya d’aura min tausayi da k’aunar Kausar sannan ka duba kaga Yarinyar nan ko uban da ya haifeta bata saniba wasu lokutan a gaban idonta Mama da Daddynku
suke kiranta da ‘shegiya!’na san ba mu Isa chanza wannan fact d’in ba amma kara ai tana da dad’i
kuma abun yana damunta sosai sannan gashi ba uwa ba uba ka gayamin idan banyi making nata ta yi feeling at home sannan whole ba wa zai yi?ina za ta saka kanta?
Ba wai nafison Kausar a kanka ba ne kai kanka ka san hakan bazai tab’a yiwuwa ba tunda
kai a cikina ka fito
kawai dai
Ina k’ok’arin inga ban biyewa son zuciyata na cutar da kowanne a cikin ku ba,kuma
kamar yanda kake fushi da ni akan na fi son wasu akanka
ko kuma kake ganin kmr ban damu dakai ba to haka nima nake fushi dakai shiyasa kaga kawai Ina rabuwa dakai wasu lokutan dan sai inga kamr baka damu da ni sosai ba d’azun ma k’ureni ka yi kuma ai kai kanka ka san gaskiya na fad’a Yash baka shawara dani,ban gama jin d’uminka ba aka d’auke min kai kuma ban Isa in ce wani abun ba sannan kai d’in da nake counting on you gaba d’aya ka k’i ka sake da ni da y’an uwanka gashi har za ka yi aure ka sake yin nesa da mu shikenan na san burina na ganin mun had’e kai
Ni da Kai da y’an uwanka ba zai tab’a yiwuwa ba kenan??”
Kasa ci gaba da magana tayi
sakamokon kukan da ya taho mata…
Ahankali ya janyota ya saka ta a jikin shi ya shiga rarrashinta
kafin cikin kwantar da murya yace “Mommy sam ba haka bane ata b’angare na,su Yassira mata ne
Yassir kuma kinga yanayinshi
In ban tsaya na yi haka akansu ba akwai matsala sannan Mommy ba wai ban saki jiki dake bane kasa fahimtata kikayi…amman inshaaAllah zan gyara.
Ina da fatan za ki daina fushi da ni sannan ki saka min albarkar ki.”


Ahankali Baba Larai tace”Ku dai gyara tsakanin ku,family
is above everything kuma new member za ka kawo Yashjub
duk abunda ta ga kana yi wa family d’inka to itanma haka za ta yi musu”…Cikin son fahimtar da shi su biyun suka shiga nuna mishi importance d’in family kama daga y’an uwanshi har iyayensa.
Tabbas kuwa maganganun su sun ratsa jikinshi matuk’a…

Daganan suka fara maganar auren nashi…ya saki jiki dasu sosai bai b’oye musu komai ba
ya ji dad’in yadda Mommy ta ce”komai komai ya wuce”sannan ta nuna farin cikin ta a auren ta kuma gaggaya mishi abubuwan da da shi ba su ma shirya da shi da Yahanasu ba.

Tabbas duk lalacewar uwa
Uwa ce kuma tanada matuk’ar amfani ata ko wanne b’agare
na rayuwar y’ay’anta dan shi sai yanzun ma da suke maganar tukunna yake jin wasu aladun da kuma abubuwan da ya kamata ayi waenda da duk ba za ayi ba.
Bai bar wajen ba har number Manubiya sai da ya bawa mommy,hakanan suka rabu ran Yashjub fess…Mommy ta sake sosai
sannan ta amince kuma ta sanya albarka a auren d’ari bisa d’ari.

Yana murmushi haka ya fito daga d’akin,da fari ko sanda ya shigo cikin gidan ko kallonta baya son yi amman gashi da ya danne zuciyar shi ya zo suka fuskanci juna ya ji sanyi a ranshi. Addu’ar sa itace”Allah ubangiji ya bashi ikon had’a kan Manubiya da su gaba d’aya,Allah ya sa komai ya zo mishi da sauk’i dan no matter yadda mutum yake jinshi though indai case ya had’a da mata dayawa kuma ya zamana shine a tsakiya to fa
abun ba sauk’i.


Yashjub yana fita Mommy ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta kalli Baba Larai tace “yanzu menene next???”

Shiruu Baba Larai tayi kafin ta furzar da ajjiyar zuciya tukunna tace”ki yi hak’uri mu ajjiye komai mu hak’ura a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login