Showing 225001 words to 228000 words out of 244445 words

Chapter 76 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16424

ta yi anko da Inna kuma kalar ta fi so shine favorite colour d’inta shiyasa ni kuma tun d’azun har yanzu da ta tafi ma ban yarda na cire ba!”tana dariya ta ci gaba da cewa”wuyan Hijab d’ina ma ya yi mini kad’an fa amma haka nake d’aurawa a kan hular ina yin sallah tun d’azu”.
Ta fad’i hakan tana dariya…..daga haka suka nufi d’aki gaba d’ayansu…ita dai Inna abun ya d’aure mata kai saboda har bayan tafiyar Siyama fa hularta tana kanta…amma kawai sai ta tsaya akan watak’il mai sunan Baban ne ya d’auka ya jefa a wani wajen dan haka ta bari akan gobe da safe idan Allah ya tashemu lafiya sai ta duba!!!!.

Manubiya da gwaggo Suwaiba ne kawai suka shiga suka kama ruwa suka yi alwallah dan ita Inna da alwalarta,dardumarta da Hijab d’in kawai ta ajjiye ta kwanta saboda haka kurum ta ji ta wani iri ga kasala!!!
da mugun kyar ma ta iya kaiwa kan gadon,tana kwanciya kuwa wani wahalallen barci marar dad’i ga takura ya yi awon gaba da ita.
Su kansu su Manu sun yi
mamakin baccin da Inna ta yi nan da nan gashi a karkace ma ta kwanta amma sai sukayi tunanin maybe ko gajiya ce,Manu ce ta d’aura mata Kai a kan pillow tana mamakin yadda take fitar da numfashi da kyar daga haka ta rufa mata abun rufa ta d’an rage k’arfin ac dan a tunanin ta sanyin ne ba ta so…daga nan suka d’an tab’a hira ita da gwaggo Suwaiba suka yi addu’o’i suka bi gado suma.



Da asuba!!…kiran sallar farko ne ya farkar da Manubiya da Gwaggo Suwaiba.
Band’aki gwaggwo Suwaiba ta wuce yayinda Manubiya ta d’an zauna a kan gadon ta yi shiruu sai da ta wartsake sosai tukunna ta juya cike da mamakin Inna ta shiga tashinta dan kullum idan suka farka a zaune a kan darduma suke tadda ita.
Sau uku ta kira sunanta tana mai d’an tab’a mata Hannu amma shiruu…cikin tashin hankali ta mik’e ta k’arasa ta kunna wutar d’akin ta koma gareta da sauri ta shiga k’are mata kallo tana kiran sunanta kafin ta zauna a daidai kanta a firgice ta d’an shafa fuskarta ta ajjiye Hannunta daidai saitin hancinta.

A firgice cikin tsananin masifaffen tashin hankali firgice da tsoro ta tashi da ga kusa da ita da mugun sauri ta ta d’an ja baya ta tsaya a kanta tana ci gaba da kallonta jikinta yana wani irin karkarwa!
Daidai nan gwaggwo Suwaiba ta fito daga band’akin…yanayin Manubiyan ne ya sanya ta yi saurin k’arasawa inda take ta ruk’o hannunta itama idanunta suna a kan Inna tace”me ya faru?”
Ta yi mata tambayar jikinta itanma yana karkarwa dan yanyin yadda Innar take a yashe da kuma yanayin Manubiya sun mugun firgigita.

Juyowa Manubiya ta yi ta kalleta dai dai nan hawaye suka samu damar b’alle mata cikin tashin hankali tana magana da kyar tace”ba ta numfashi kuma jikinta ya yi sanyi”
Ta yi mata maganar tana mai nuna mata Innar da yatsa…

Da kyar Gwaggo Suwaiba ta samu ta yi namijin k’ok’ari wajen k’arasawa inda Innar take ta zaune a gefenta ta shiga dubata…..tashi d’aya ta fashe da wani irin rikitaccen kuka ta shiga ambaton “innalillahi wa inna ilaihirrajiun!
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!”.

Luuu!!! haka Manubiya ta tafi ta zube a wajen sumammiya…….

Sama sama take jin muryar ya Musbah shima yana kuka yana
yayyafa mata ruwa yana kiran sunanta!
A hankali ta shiga k’ok’arin bud’e idanunta kanta yana wani mahaukacin sarawa…dishi dishi ta fara gani kafin ta samu idanunta suka ware tarr take kallon fuskar ya Musbah shab’e shab’e da hawaye wanda hakan ya sake tabbatar mata tabbas Inna ta rasu!!!

Mik’ewa ta yi ta zauna ta shiga k’are musu kallo kowa ya hallara har da mai sunan Baba ya Nafi’u da Aisha da Likita yana duba Inna.

Fashewa ta yi da wani irin kuka kanta yana wani kalar mahaukacin sarawa ta samu ta mik’e daga kan sofar dake a d’akin(inda suka d’aurata)
da mugun kyar ta wuce Ya Musbah ta k’arasa inda Likitan yake duba Inna tana shirin yin magana dai dai shi kuma ya d’ago ya kalleta tukunna ya kalli su Baba cikin karyewar zuciya yace”rai ya yi halinsa!sai dai mu yi mata addua!!..i’m so sorry…..”
Gaba d’ayansu har mai sunan Baba da Khairat fashewa suka yi kuka Yayinda ita kuma Manubiya ta nemi nata kukan ta rasa hawayen idanunta suka k’afe k’aff!!! tsabar masifa da tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki wanda ba ta tab’a jin kwatankwacinsa ba tunda Inna ta kawo ta duniya!!tabbas zafi rad’ad’i zugi da d’acin rashin Mahaifiya daban yake!ta yi going through hell a rayuwarta amma ba ta tab’a jin kalar bala’in da ta ke jinta a ciki a halin yanzu ba.!

Ita ba ta fad’i ba ita ba ta zauna ba hakanan ta tsaya musu k’ememe ta k’ame kamar gunki dan haka gwaggo Suwaiba ta ja ta ta kaita kan kujerar da ta taso ta zaunar da ita ta rungumeta tana wani irin kuka kira take”Mannubiya ki yi kuka,dan Allah ki yi kukan nan ko kya rage zugi da zafin zuciya……..”
Dai dai nan Baraka ta shigo d’akin d’ankwalinta rik’e a hannu,haka kurum d’azu suka ga ta fita a rikice yanzu kuma gata ta dawo a hargitse!!!!
Ba ta ita suke ba shiyasa babu wanda ya ko sake kallonta ma har ta Isa ta je ta bintik’e Manubiya daga jikin Gwaggo Suwaiba ta mik’ar da ita cikin tsananin tashin hankali tace”Manu ya ake ciki?”

Girgiza kai Manubiya ta yi cikin rauni ta durk’ushe a wajen tana k’ok’arin janyo kuka amma sam ya k’i zuwa!
Sake mik’ar da ita Baraka ta yi tace”ta mutu kenan yanzu shikenan??”
Cikin fara jin haushinta gwaggo Suwaiba tace”ta rasu zaki ce Baraka ba wai ta mutu ba kuma addu’a za ki yi mata ba hauka ba!”
D’amara Baraka ta yi da d’ankwalin Hannunta tace”ki gaya mini tsakaninki da Allah
A tsakankanin jiya da muka rabu da ku zuwa yau shin ta bi ta kan k’ofar band’akinta ta wuce bi ma’ana ta shiga b’andakin ta kafin ta mutu!???”

Cikin k’unci Ya Musbah yace”Baraka bar nan!!”

Kan sa ta nufa tana zuwa ta tsaya a gabansa tace”Amsa d’aya za ku bani sai in tafi!!
Shin kafin Inna ta mutu ta bi ta kan k’ofar band’akinta? ‘eh’ ko ‘A’a’?
Dan Allah ku bani amsa in san makomata saboda idan ba ta wuce ta shiga band’akinta ba akwai matsala fa!!wallahi akwai matsala!!!!”.
Sai kuma ta nufi Inna tana zuwa ta fara k’ok’arin ruk’ota tana cewa “Allah yau sai kin tashi kin fad’a mini kin bi ta kai ko baki bi ba,ki tashi idan ba ki
bi ba to ki bi yanzu a gabn idanuna in gani…..”
Dai dai na Ya Musbah ya k’araso ya juyo da ita ya d’auketa da wani rikitaccen mari.
Kuka ta fashe da shi tace”ba ta haukace ba ta mutu ni kuma na haukace!!!saboda Allah in banda mugunta irin nata ta ya zata kwanta ta mutu ba tare da ta bi ta kan abunda na zuba mata ba?
salon ta jaza mini bala’i!!!!” sai kuma ta fincike ribbom d’in kanta ta hau barbaza gashin kanta ta fara tsalle tana dira tana cewa”ai ku barshi ba sai kun fad’a mini komai ba ma,yadda na fara ji a jikin nan nawa na san ba ta bi ba ni kuma asirina ya dawo kaina,Innalillahi wa inna ilaihirrajiun mun tafi ba zamu dawo ba,da ni da Inna mun tafi inda ba a dawo wa!! ita ta tafi garin matattu ni kuma na tafi garin mahaukata daga ni har ita ba zamu tab’a dawowa ba!!
Bokan yace mini asirin baya karyewa ba a tab’a iya k’aryawa…”
Daga haka ta juya ta kinkimi takalmin da ta gani a k’ofar band’akin ta rungume ta fice da wani irin mahaukacin
gudu tana kurma uban ihu!!!…

Iyaka maganganunta sun isa su faiyyace musu komai!!!shiyasa kawai duk suka bita da ido kowa yana Allah wadai!!!.
Halin da suke a ciki bai sanya kowa ya sake bi ta kan Baraka ba..tana wucewa suka ci gaba da koke kokensu.


Kafin awa d’aya gidan ya cika taff har da matan su Uncle da Mama kowa ya hallara har Najeeb da Siyama su Jidda ma sun ce suna airport.

A nan parlourn Baba mai k’ofa ta baya Gwaggo Suwaiba da Mama suka yiwa Inna wanka amma da ikon Allah ana gama yi mata wankan Gwaggo Suwaiba ta hana a yi mata sutura har kawo yanzu kawai dai sun rufa mata zani sunata yi mata addu’a ita kuma ta k’ura mata idanu tana ta kallonta.
…….
Najeeb da Manubiya sun kira Yash amma bai d’aga ba kuma bai biyo kiran ba shiyasa Najeeb yace bari ya je gidan ya dubosa.

Tun cikin dare Yash ya kasa barci sakamokon mummunan mawuyacin halin da ya dinga ganin Mommy da Ya’isha a ciki a mafarki…shiyasa ya kasa hak’ura duk da yadda Mommy ta ja masa kunne kar ya je inda suke! k’arfe bakwai ta na yi ya fita ya nufi gidan saboda ko rufe idanunsa ya yi kamar Irin a cikin gobara haka yake ganinsu shiysa ma ya yi tunanin ko gobara ce ta kama a gidan gashi duk d’insu babu mai d’aukar wayarsa.


Yasira,da! ta yi fushi tace Wallahi Hatta office d’in ma ta daina zuwa amma sai Mommy da Y’aisha suka yi mata magana jiya da daddare suka ce “ta je ai bazasu zuba masa ido su kyalesa hakanan ba kuma idan ba ta je ba tsaf zai iya d’aura Ummi a kan komai tunda Yash bai gama resumin aiki ba”…dan haka ta shirya saboda dama yau ta san da zuwan manya manyan bak’i.

Tare suka fita ita da Yusra wadda zata ga invigilator d’inta a yau,ta sauk’e Yusran ita kuma ta wuce office……

Sosai yau Mommy take jinta a sama ta dad’e bata samu soundsleep kamar na jiya ba saboda ta riga ta san yau zata ji labarin mutuwar Manubiya….:

Tun a jiyan da suka gama magana da Ya’isha ta yi musu sai da safe ta shige d’aki har suka gama breakfast su Yasira suka fice sam Mommy ba ta ji motsinta ba dan haka ta lek’a d’akin da yake mallakinta..
Da wani irin mahaukacin gudu ta k’arasa cikin d’akin sakamokon hango Ya’isha da ta yi wanwarr a k’asa a yashe…..
Tana zuwa ta d’agota ta d’aurata a kan cinyarta ta shiga kiran sunanta amma ko gezau!!
Duddubata ta hau yi amma sam ba ta ga alamun rai a tartare da Ya’ishan ba ga idanunta sun k’afe suna kallon sama wanda hakan ya sanya tashi d’aya Mommyn ta fashe da wani irin kuka ta rungumeta da k’arfi a jikinta cikin kuka ta shiga cewa “I’m so sorry Ya’isha Innalillahi wa Innailaihirrajiun….”
Sai kuma ta mik’e zumbur ta fita waje
Sai da tabbatar ta kulle ko’ina sannan babu kowa tukunna ta koma ta d’auko makullin mota da Hijabi ta zo ta bud’e boot d’in motar gudun kar a kamata dan motarta babu tint.

Tana wani irin kuka ta je ta kinkimo Ya’isha da kyar ta sakata a booth hakanan tana ji tana gani ta rufe y’ar tata a booth a ranta tana k’iyasta yadda zata yi da su Yashjub muddin ta samu Ya’isha ta farfad’o dan wannan duk laifinsu ne!!! tunda uwarsa ta shigo rayuwar Daddy har yau ba ta samu kwanciyar hankali ba,gashi yanzu saboda shi da Manubiya ta zo wannan flat house d’in d’an mitsitsi ta zauna sannan kalli a booth ta saka y’arta yo
Idan bata ga bayan su Manu ba ma ai ba ta cika sunanta Khadija ba wallahi…..
Sannan ad’uarta d’aya Allah dai ya sa ba aikin bane ya lalace Allah ya sa dai abun ya kama Manu dan tabbas jiya Ya’isha tace mata bata yi mistake ba to amma kuma mai ya faru!!!?me yasa abun ya tab’a mata y’a!!!!?
Hakanan tana ta sak’e sak’e hankalinta a masifar tashe ta je ta zuge gate d’in tana wani irin kuka…tana gama zugewa ta koma ta fitar da motar ta fito ta mayar da gate d’in ta rufe ta koma ta ja motar ta nufi gidan tsohon jiya ta san shi kad’ai ne zai iya farfad’o mata da Ya’isha………

Sosai tun d’azu Yashjub wanda sam ba ta lura da shi ba ya ke tsaye yana kallonta yana mamakin yadda take kuka sannan yadda ta zuge gate da kanta ta fita da asussubah haka abun mamaki ne tabbas.


Sai da ta Isa k’ofar gidan tsohon tukunna ta tuna ba ma d’auko wayarta ba balle ta kirasa ya bud’e mata dan haka kawai ta fito ta Isa bakin k’ofar gidan nasa ta hau bugu.

Ba ta wani dad’e tana bugawa ba tsohon ya zo ya bud’e mata k’ofar dan dama da ga shi sai
dabbobi ne a gidan

A rikice ta afka ta tura k’ofar ta rufe cikin tsananin tashin hankali tana ganin dishi dishi tace masa”Mun wayi gari
babu Ya’isha,ka taimaka mini ka san yadda ka yi y’ata ta dawo
Ina son y’ata ita kad’ai ce ba ta tab’a yi mini jayayya ba wallahi!
sannan in har su Yasira suka ganta haka sun san ni ce sun san me ya faru tunda a gabnsu aka fara maganar jiya na san wallahi ba za su tab’a yafe mini ba!!! dan girman Allah ka yi wani abun….”

“Biyo ni”
Kawai yace daga haka ya nufi cikin gidan….

Wajen Birin jiya suka je kamar jiyan suna zuwa birin ya matsa musu shi kuma tsohon ya saka hannu ya d’aga dutsen tun kafin ya d’auko babyn robar ya kwab’e fuska ya ce “too ikon Allah mai ya faru kenan?”
Da sauri Mommy ta matso tace”ya akayi?
mai ya faru?
Ba dai aikin ne ya lalace gaba d’aya ba ko??
Ta yi masa tambayar a gigice


Girgiza kai yayi ya sa Hannu ya d’auko Babyn robar tukunna yace”gaskiya kunyi kuskure amma bansan ta Ina ba!sai dai kuma yadda y’ar tsanar ta yi bak’i hakan yana nuni da aiki ya ci ya kama,kuskuren ne ban fahimci ta ina kuka yi ba
Saboda tunda har ya shafi Ya’isha tou tabbas akwai wani abu da kuka yi ba daidai ba.”
Sai kuma ya kalleta yace”ke fa??lafiya kike jin ki dai ko??”

Jinjina masa Kai ta yi da farko sai kuma tace”idanuwana dai suna ta yi mini dishi dishi tun d’azu!!!!”

Jin jina kai ya yi ya sauk’e ajiyar zuciya yace”idanunki ne kenan zasu tab’u,sai kuma ya mayar da gabaki d’aya hankalinsa gareta yace”idan kinaso za a iya karyawa amma in aka karya ba lalle a sake yi mata ya kamata ba sannan babu tabbacin Ya’isha za ta tashi sai dai mu gwada sa’ar mu!”

Kuka ta fashe dashi tace”kamar ya zaka ce mini Ya’isha ba za ta tashi ba!!idan fa Yarinyar nan ba ta tashi ba wallahi na san duk su Yasira sai sun fahimci komai kuma ba za su tab’a yafe mini ba k’arshentamasu tona mini asiri…”
Cikin tarar numfashin yace”ai
dama sai da na gaya miki aikin yana buk’atar taka tsantsan yanada hatsari….”
Cikin yi mata nuni da babyn robar yace”dan ci kam aiki ya ci…amma kuma halin da Ya’isha ta shiga yana nuni da aiki ya riga ya fara tab’arb’arewa kenan…..kuma zamu iya warwaresa….ta you Ya’isha ta tashi ta you kuma ta tafi kenan amma tabbas Manubiya za ta tashi ita wannan a rubuce yake…..”
Cikin tarar numfashinsa tace”to mu bari mana sai an kaita sai mu warware a tare!”
Girgiza Kai yayi yace”sam ba haka abun yake ba..kuma ni yanzu mintuna uku ne ma
suka ragemini zaki ga y’ar tsanar nan ta kama da wuta (idan har ta kama da wuta to baza a iya warware wa ba)saboda abun ya fita daga hannuna,daga nan!!
dan haka ki yanke hukunci da wurwuri kin riga kin lalata komai da ke da y’ar ki aiki ba ya hannuna kuma….”

Shiruu ta yi kafin tace”idanuwan nawa da na fara ganin dishi dishi a haka zan dauwwama?”

Shiruu ya d’anyi kafin yace”akwai taimakon da zan baki,inshaaAllah za a dace”
Cikin sake jeho masa wata tambayar tace”tashin Ya’isha k’ila wak’ala ne ko?”
Jinjina kai ya yi yace”Bari ki ji ba zan b’oye miki ba Ya’isha ba ma na jin tanada rai dan haka ba zan iya yin komai a kai ba saboda kun damalmala komai ne,gashi kuma bamusan ma ta ina matsalar take…ga dai aiki ya yi yana ci…to shafarta da abun ya yi ne matsalar shiyasa abun zai fi k’arfina!”


A hankali Mommy ta lumshe idanuwanta hawaye suka zubo cikin d’acin zuciya tace”ka bar shi kar ka karya!!!”
Ta ji tsananin zafin mutuwar Ya’isha tabbas amma da ta tuna abunda ya ke faruwa da Manubiya a halin yanzu sai ta d’an ji sanyi ko banza ta san kwalliya ta biya kud’in sabulu!!!!….

Ba ta dad’e da gama rufe bakinta ba Babyn robar ta kama da wuta tana jin tsohon yana cewa “yanzu shi kansa kam bai san ranar da numfashin Manu zai dawo mata ba aiki ba a hannunsa yake ba sun riga sun damalmala komai!!”

Itadai Mommy ta ji sanyi a ranta tunda ba a warware ba ta san duk bala’i ko nan da shekara nawa ne Manubiya ba ta Isa ta fito ba!.


Da shi da ita suka yanke shawarar gara su binne Ya’isha maganar ta tsaya a iyaka su biyu dan idan wani ya sani tofa a kwai matsala
Inyaso
Mommyn sai ta ce ta aike ta k’auye kafin su san abun yi,shi kuma inshaaAllah zai rufewa duk wani wanda zai d’aga mata hankali wajen tambayar ‘Ina Ya’isha’ Baki.

Hakanan suka je wani k’ungurmi daji ya hak’a rami yana shirin d’auko Ya’isha ya sakata a ramin aka kirasa.
Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne dan haka yace ta yi masa hak’uri dole
zai tafi ta k’arasa sakata ta rufe ramin ta koma gida,hakanan ya wuce ya barta a wajen jikinsa yana karkarwa dan babban mutum ne ya kirasa ya san a k’allan a lalace yau sai ya samu sama da miliyan biyu…..

Tsoro da fargabar dajin gata tare da gawa ne suka sanya Mommy saka Ya’isha cikin ramin anyhow,ko gama rufewa ma ba ta yi ba hakanan ta yi sauri tabar wajen jikinta ya na karkarwa tana kuka.

Bata wani jima da komawa gidan ba su Yasira suka dawo…
Jikinsu daga ita har Yusra duk a sanyaye suka gaisa tana mai bin Mommyn da wani irin kallo daga ita har Yusran kafin chan ta d’an yi waige waige tace mata “Ina Ya’isha?” hakanan
Mommy ta had’e fuska tace musu”ta turata k’auye!tunda sun hana a tsayar da numfashi ta turata k’auye zata yo musu mai sauk’i…”
Shiruu Yasira ta yi kawai Tana kallonta…sam ba ta son ta zargi Mommy amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login