Showing 90001 words to 93000 words out of 244445 words

Chapter 31 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16467

yi
as far as I know u are the only one for me kuma na san su Daddy ba za su tab’a yi min auren dole ba
So..pls Baby! ki daina b’ata ranki…um?!..”Ya k’arashe maganar ta sa cikin sa hannu ya janyota jikinsa sosai kafin ya d’aura da cewa” ko amarci na ma ban fara ci ba har Amarya ta fara shiga damuwa ta fara fushi da ni,Pls ki daina Plssssss”ya fad’i hakan kamar zai fashe da kuka yana sake sakata a jikinsa.
Shiruu Manubiya ta yi a ranta tace”au bai ma fara cin amarcinba a hakan…”
Tana wannan tunanin ta ji yanayin nasa yana shirin sauyawa dan haka ta d’an yi y’ar dabara ta goce dakyar tace”Ya wuce fa!
Ni ba fushi na yi ba kuma na daina kukan ai”

Cikin sake ruk’ota yana dariya dan ya fahimci zillewa ta ke son yi yace”ba wani nan!fushi kikayi mana bayan k’iri k’iri d’azu aka yi denying d’ina kiss yanzu kuma hug anjima kuma Allah kad’ai ya san mai za a hanani…”
Da ga haka ya janyota ya fara aika mata da sak’onninsa ma su zafi da tsada……
Addua ta fara yi Allah ya kawo mata ceto dan a yadda ya fara sakin layikan nan ta san k’aniyarta za ta ci.
Allah kuwa ya amsa adduar ta dan tashi d’aya wayar sa ta fara k’ara…sai da aka kira har sau biyu bai kula ba jin kiran yak’i k’arewa ne ya sa yace”Ohh God!”kafin dakyar ya samu ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kashewa amman sai idanuwan sa suka hango masa sunan Mommy b’aro b’aro…shi fa sai yanzu ma ya tuna da neman nasu da takeyi wallahi shaf ya manta…sai da ta tsinke ta sake kira tukunna dakyar cikin k’ok’arin daidaita muryarsa ya d’auka ya ce”Mommy gamu nan zuwa”
daga haka ya kashe wayar ya kalli Manu yace”Bamu je ba gashi Mommy har ta fara neman mu,kece kika k’i ki warke da wuri shiyasa mukayi letti”ya fad’i hakan yana dariya k’asa k’asa yana mai sake kissing d’inta tukunna ya mik’e da kyar….
Yasan idan suka zauna a d’aki d’aya suka ce za su shirya ba za su yi sauri ba,gashi ya d’an jiyo fushi a muryar Mommy
hakan ya sanya ya ce mata”ta shirya da wuri bari shima yaje ya shirya”
Daga nan ya koma ya sake kissing nata daga haka ya fice da sauri dan ji yakeyi kamar akwai wani magnet d’in da yake jansa gareta.

Yana fito ta sauk’e ajiyar zuciya had’i da ta’a’uzi dan tashi d’aya taji wani tsananin kishi ya lullub’e ta sakamokon tuno wa da tayi zata had’u da Kausar idan taje gidan.

Cikin nutsuwa tana ta korar shed’an a hankali ta shiga shiryawa…wanka ta fara yi tukunna ta fara d’auko kayan da za ta saka.
A ganin ta gidan surukai za ta je shiyasa ta yanke shawarar saka kayan da suka yi mata a cikin lefe ta san in suka ga ta saka za su ji dad’i kwarai.
Wata dandatsetsiyar atamfar exclusive ta saka kalar royal blue da ratsi ratsin silver da red an zuba mata d’inkin riga da skirt na zamani da sukayi asalin amsarta…ita kanta tasan d’inkin ya fito da ita ras matsalar ta d’aya yadda d’inkin ya matseta rabin k’irjinta a waje sannan skirt d’inma ya kamata ga waist d’in ya fito sosai shima…d’inkin ya fito da surar jikinta gaba d’aya.

dama tun jiya da ta zo zab’ar kaya ta lura da yanayin d’unkunan gaba d’aya sun yi fitting dayawa,gaskiya idan ta samu lokaci zata ce su mayar musu a dan bud’a mata dan ba zai yiu a kashe uban kud’i ba kuma a yi mata d’inkunan da ranta bai so ba….

Dama tanada abun d’auri na ture kaga tsiya dan haka ta d’auko ta saka a cikin dankwalin nata ta ajjiye kafin ta koma gaban madubin ta d’auka powder ta shafa ta saka eye liner ta d’auko lipstick ta shafawa labb’an ta.
Ita kanta tasan tayi kyau irin sosai d’innan..murmushi ne ya sub’uce mata ta san Yash yana shigowa zai hau mita yace mugunta ta had’a masa dan ta san ba zama za suyi a gidan ba shiyasa ta chab’a wannan uwar kwalliyar.A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya tana jin tsantsar k’aunar mijin nata tana sake shiga jikin ta tana ratsa ko’ina.
Tana tunanin sa tana murmushi ta shiga tufke gashin kanta a ta baya chan k’asa ta kanainaye sa ta saka d’an siririn ribbom black gudun kar ya sunce daga nan ta d’auko dannkwalin data saka abun daurin a cikin ta d’aura sa perfectly.
Saida ta san yadda ta yi ta b’oye uban tulin gashin ta da ya fito ta k’asan d’aurin tukunna ta tafi closet ta bud’e wardrobe ta zaro mayafi jaka da takalmi kafin ta d’auko iyaka y’an kunne zobe da agogo kawai dan ba ta cika son sark’a da awarwaraye ba.Y’an kunnenta,zobe agogo da Mayafinta silver yayinda jaka da takalminta suka kasance red colour.
Tana shirin yafa mayafi ya turo k’ofar ya shigo..dama k’ofar take facing dan a kan gadon nata ta jere jaka da mayafin nata.

Saida numfashin Yashjub yayi sama ya dawo bai san lokacin da a fili yace”MashaaAllah,Ubangiji mai halitta.”ba.
Kamar had’in baki shima sanye yake da kaftan blue nasa da farar hula da farin takalmin da agogo,wanda hakan ya yi kamar anko sukayi.

Ahankali ya taka ya shigo cikin d’akin idanunsa a kanta.
Gaba da’ya Manubiya sai ta diririce sakamokon kallon da ta ga yana mata…so take ta ware mayafin ma ta rufa amman sai ta kasa.
Murmushi yayi kafin ya maida k’ofar ya rufe ahankali ya k’arasa inda take still idanunsa suna a kanta.
Saida ya gama k’are mata kallo tukunna ya sa hannu ya karb’i mayafin sannan ya zagaya ta bayanta ya tsaya tukunna ya ware mayafin gaba d’aya ya rufa mata shi a saman kanta gefe da gefen kuma ya zagaya dashi ya rufe mata gaba d’aya jikinta dashi wanda hakan ya basa damar yin hugging d’in ta
A tare shi da ita suka sauk’e ajiyar zuciya kamar ta saani dama aikuwa ta ji yace
“Wannan dai tsokanata akayi amman kar ki damu zan fanshe idan muka dawo”.
Daga haka ya manna mata wani dogon peck a kumatunta kafin yayi saurin cikata dakyar yana mai sauk’e ajiyar zuciya.Jakarta ya d’auka daganan ya ruk’o hannunta suka fita tare gwanin ban sha’awa. Wani Irin shauk’i da so ne suke jan Yashjub game da ita ji yakeyi kamar ya had’iye ta ya kora da ruwa ko ya samu sauk’in abunda yake ji. Gaba d’aya robobin kayan zak’in garar Manubiya tace su tafi da shi a su Mommy ita za ta raba har su sai ta basu nasu haka akeyi. Sai da ya bud’e mata mota ya sakata a ciki tukunna ya kira masu gadi suka kwasa suka sanya a boot da seat d’in baya sannan ya shiga motar ya ajjiye Jakarta da ya yake rik’e da ita ya zauna tukunna ya kunna mai gadi ya bud’e musu suka fice.

Har suka k’arasa gidan Daddy yana rik’e da hannunta..da hannu d’aya yayi tuk’in sai dai in zai chanja gear ne ya ke d’an cikata yana chanjawa kuwa ya ke sake ruk’ota kamar wani zai kwace masa ita ne.

Haka kurum suna zuwa bakin gate d’in gidan data ga ya danna horn ta ji gaban ta ya yanke ya fad’i sosai..da kuma ta tuna su Yassira da Kausar sai ta ji ranta ya b’aci…..salati ta shiga yi a cikin zuciyarta da ikon Allah sai ta ji fad’uwar gaban da b’acin ran suna raguwa.

Tunda suka shigo gidan ta shiga alajabi da mamakin tsantsar girman gidan,ita
tana ganin gidanta Babba ashe ga mansion anan!
MashaaAllah masu kud’i suna hutawa..tashi d’aya ta fara addu’ar ‘Allah itama ya bata ikon fara aiki ya bata kud’i ta samu ta siyawa su Baba gida ko d’an flat ne suma su ji dad’in rayuwa.


A parking space sukayi poarking kafin ya kashe motar ya d’auki jakarta ya fita da niyyar zagayawa ya bud’e mata,da sauri ta juya ta bud’e ta fito kafin ma ya zagayo.
B’ata rai ya yi sosai kafin
yace”Why?!”
Murmushi kawai ta yi tace “yi hkr”….
Da kyar ya d’an saki fuska ganin ta masa kalar tausayi tukunna suka wuce suka nufi main parlour.

A bakin k’ofar shiga suka ci karo da Yassir wanda ya zo shiga shima..bai dad’e da dawowa daga office bama jakarsa kawai ya ajjiye a side d’insa ya zo da niyyar ganin Kausar dan kwana biyu karantarta kawai yake yi…ya fi
minti d’aya tunda ya hangosu har suka k’araso suka tsaya yana k’are musu kallo yanajin yadda zuciyarsa take wani irin tafarfasa!a ransa yana aiyyana”how can Yashjub be this lucky!ta ya
zai fi sa sa’a ata ko wanne b’angare ata ko wanne fanni
na rayuwa!….”

Da mamaki Yashjub yake kallosa yana la’akari da yadda idanuwansa suke sauya kala dan lokaci guda yaga sun fara rinewa suna chanzaa kala zuwa jajajaja…
Baban abunda ya b’ata masa rai game da Yassir d’in shine yadda ya kafe Manubiya da idanuwa ko kiftawa ba ya yi.

Ashe haka take!wacce iriyar kyakkyawar halitta ce wannan mai tafiya da imanin d’an Adam…tabbas ya zama dole Yashjub ya mutu kwanan nan
ta yadda cikin sauk’i zai had’a Kausar da Manubiya a matsayin matansa ya yi rayuwa mai dad’i.Dan bayan Kausar ba ya jin akwai wata da ya ji yana so ya yi rayuwar aure da ita bayan wannan baiwar Allahn.

“Yasir’’
d’in da Yashjub yace maasa a d’an zafafe ne ya dawo dashi daga duniyar da ya lula.
Wani lumshe idanuwa yayi wanda hakan ya kuma k’ular da Yashjub kafin ya bud’e ya ce
“Welcome”
Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya wadda tashi d’aya ta ji kamar ta rufe sa da duka ganin irin kallon da ya shiga yi mata.Murmushi ya d’an yi yace “antyn mu barka da zuwa bismillah”
Ya fad’i hakan yana nuna mata k’ofa kafin ya d’aura da cewa
‘’Yau dai ya Yash ya bari anga fuskar ki”

Da kyar da mugun kyar Manubiya ta k’ak’alo wani d’an guntun murmushi wanda ya tsaya a iyaka labb’anta ne tukunna ta bi bayan Yash wanda ta ga ya juya kawai ya ruk’o hannunta suka nufi cikin parlourn.
Bayan su kawai Yassir ya bi da kallo yanajin yadda k’irjin sa yake wani irin bugawa…yadda
ya kafe Manubiya da ido yana k’are mata kallo hatta yanayin kwalliyar stones d’in jikin rigar ta sai da ya gani ya haddace ta cikin mayafin ta.

Suna shigewa ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya jin jina kan sa kafin yace “da sake!”

daga haka ya sa kai shima ya nufi cikin parlourn
A main parlourn gidan suka samu Mommy Baba larai Ya’isha da Kausar a zaune suna magana da alama mai mahimmanci ce,sallamarsu su ce ta sanya sukayi sauri duk suka d’ago suka zuba musu ido….tashi d’aya yanayin fuskar Ya’isha ya sauya ganin Yashjub d’in ne ma ya ruk’o wa Manubiya jaka.
Da sauri ita kuma Kausar ta mik’e ta wuce sama
Yayinda baba larai ta mik’e ta fara cewa “Lale marhababiki Amarya surukar mu
Yashjub bismillah mana k’araso!ku shigo ciki ya ka barta nan bakin k’ofa a tsaye”
Ta fad’i hakan tana nufar su tana Isa ta kamo hannun Manubiya ta zare a cikin na Yashjub ta ja ta suka nufi cikin parlourn.
Dakyar Manubiya ta iya janye idanuwanta a kan Baba larai
sarai ta shaida ta itace suka ce sai ta d’urk’usa sannan duk wani mai hankali yana kallon fuskarta tashi d’aya zai shaida ba farin ciki takeyi da auren ba,amma kalli yau itace kamar zata cinye ta! tabbas waennan shaid’anu ne wato idan a gaban Yashjub ne ba za su nuna mata k’iyayya ba kenna dan ta lura da Yasira ma d’azu saida ta bari babu Yashjub a wajen tukunna ta gaggaya mata maganganu.
A gefen Mommy daff da ita Baba larai ta zaunar da Manubiya kafin tace”bari in je in kawo muku ruwa,sannu Amarya lalle marhaba”
Ta fad’i hakan tana wucewa da sauri har da d’an yin tuntub’e. Yashjub ne ya d’an tsani da ita ya sanar da ita batun kayan zak’’i dan haka ta karb’i makullin motarsa tace bari ta nuna su gwaggo su kwasa su saka a kitchen.

A hankali Ya’isha ta mik’e kamar ba itace ta baro gidan d’azu tana fushi ba ta k’arasa wajen Yash tace “kawo jakar ni in rik’e mata”
Ta fad’i hakan tana mai amsar jakar.

Tashi d’aya kawai sai ya ji kunyar Mommy ta kama sa dan haka ya cika mata jakar ya k’arasa inda Mommyn take ya zauna a gefen ta dai dai nan su Yassira ma suka fara sauk’owa da alamar Kausar ce ta gaya musu Yash d’in ya zo,tare suka sauk’o gaba d’ayansu har da Daddy da alamun tare suke da shi a saman,shi Yashjub ma bai yi tunanin Daddyn yana nan ba ya d’auka yana office duba da yadda shi baya nan Yasira ma ya ga yau ba ta je ba.

A hankali Manubiya wadda tun d’azu ta ke jin nauyin zama a kusa da Mommy ta d’an sullub’o daga kan kujerar tace “Mommy Ina wuni”

Saida Mommy ta yi namijin k’ok’ari dagasken gaske tukunna ta iya dafa kanta a hankali tace “lafiya y’ar albarka ya bak’unta”
“Alhamdulillah”tace a ranta tanajin wani sanyi dan yadda Mommyn ta yi mata ta ji dad’i sosai ta fahimci itan tana sonta ba kamar su Yassira ba..ta san dama zuwa d’auko ta da kai lefe ba hurumin Mommy bane amma da aka d’aukota tace “a wuce da ita ba sai ta zo ta gaida ita ba!” da kuma yadda take kiranta a waya amma ba ta amsawa ya sa ta d’an ji tsoro ta shiga damuwa da tunani..

Muryar Daddy ce ta katseta jin yana cewa”Manubiya mik’e ki zauna a kan kujera mana,tashi
kinji”

Murmushi ta yi sai da Yashjub wanda shima yaketa zuba murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’in yadda iyayen nasa suka nuna kulawar su ga matar tasa,tukunna a hankali ya d’an sunkuya ya kalli Manu yace “mik’e ki zauna mana
Daddy yana magana”
Tukunna ta mik’e ta zauna a kusa da Mommy inda take tun farko tanajin wani nauyi da girmanta yana ratsa ta,dai dai nan su Daddy suka k’araso suka zazzauna,shima saida ta durk’usa har k’asa tukunna ta gaidashi ya amsa da kulawa.
Da sauri yace”Ummi bata sauk’o ba Yassira jeki ki kirata”
sai kuma ya zaro waya yace “Bari in kirata”ya fad’i hakan yana dialing number Ummi,ba ta dad’e tana ringing ba ta d’auka.
Tana d’auka yace “ki zo munyi bak’i”daga haka ya katse kiran yana mai tambayar Manubiya “ya bak’un ta”
Cike da girmamawa da kunya suke amsa shi.
Suna a haka Munirat suka sauk’o ita da Ummi.
Da sauri Munirat ta k’arasa ta je ta zauna a kusa da Manubiya tana “oyoyo antyn mu ashe kune Ina wuni”
sai kuma ta kalli Yash ta gaidashi.
Kamar yadda Manubiya ta yiwa Mommy da Daddy haka ta zamo ta gaida Ummi itama,
ta kuwa ji dad’i dan haka ta shiga tambayar ta ya sabon waje ya su Innarta…. mik’ewa Yash ya yi yace”Bara mu lek’a Yahanasu,ya jikin nata?.”
Da sauri Mommy tace”da sauk’i!.Munirat ta kai Manubiya wajen Yahanasu kai kuma ka zauna munada magana da kai!”
Shiruu ya d’anyi da sam bai ji dad’i ba ya san Manubiya zataga kamar an ware ta ne…
Yana cikin wannan tunanin suka mik’e ita da Munirat suka nufi d’akin Yahansu jiki ba kwari.

Lumshe ido Yashjub ya yi har suke shige bai bud’e ba..
Muryar Daddy ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula jin yana cewa”Yash,mai ya faru yau ka koro k’annen ka daga zuwan su na farko?”

Da sauri ya bud’e idanuwansa ya kallesa sai kuma yayi kan Yassira a zuciye.
Da sauri Mommy ta mik’e ta tsaya a gaban Yasirar tace”ai ni za ka daka ba ita ba!tunda nice nan na gayawa Daddyn naku ba ita ba!”

Ummi ba ta san kan labarin ba
ba kuma ta san abunda ya faru ba amman tashi d’aya ta fahimci laifin su Yassira ne…baya ga haka saboda Allah ta ya Daddy zai biyewa Mommy a zuwan Yashjub da Manubiya na farko gida a fara da case!
Su da ya kamata ace sun saka su a gaba sun yi musu fad’a da nasiha sannan sun yi k’ok’ari wajen basu chance su fahimci juna amman kalli yadda tun farko aka sallami Manubiya akace a rakata d’akin Yahanasu saboda Allah wanne irin rashin lissafi ne wannan?,ya suke tunanin Yarinyar za ta ji saboda Allah…..
Ta san inhar ta zauna to tabbas za a yi fad’a da ita
shiyasa ta mik’e tace
‘’Am Daddy bara in d’an baku guri dan Allah”tana gama fad’in haka ta wuce sama bata yadda ta kuma had’a ido da Daddyn ba….sai da ta had’a da sauk’ar AlK’urani da addu’o’i tukunna ta daina jin matsananciyar tsanar sa,haka kurum ta samu sun shirya shima ya daina fushi da ita da kyar !
ba ta ga dalilin da zai sa ta zauna a wajen da zata fad’i abunda zai ji haushi su yi fad’a su sake komawa ruwa ba.


“Ta fi Nono fari”Mommy tace a cikin zuciyar ta kafin ta maida hankalin ta ga Yashjub wanda ya ke cewa Yassira da ta b’oye a bayan ta “k’ara ta kika kawo?
ke ba ki fad’i abunda kuka yi ba?”
Cikin tarar numfashin sa Daddy yace
‘’Mai sukayi?’’

Tun kafin Yash yayi magana
Ya’isha tace
‘’Wallahi Daddy bamuyi komai ba,dama tun da mukaje ta tare hanya ta hanamu wucewa sai da ya zo tukunna ta matsa.
Ina ga yanayin fuskar ta ya kalla dan tanata faman kumbure kumbure shine ya kira Yasira ya ce ta kwashemu mu tafi’’

Wani irin takaici ne ya lullub’e Yashjub wanda ya sa ya ji kamar ya finciko Ya’isha daga kusa da Daddy ya feffella mata mari…ya godewa Allah da ba a kusa da shi take ba dan ya san yau da sai ya illatata!
Ganin Yaran suna neman haukatasa ne yasa ya koma ya zauna ya dafe kansa da ya fara sara masa.

Gyaran murya Daddy ya yi kafin yace”Yashjub!!tun wanchan ranar a asibiti na fad’a maka kar ka bada k’ofar da matar ka za ta raina y’an uwanka!and again a washegarin ranar da ka yi aure ma sai da na rok’ek’a da kaina akan kar ka bada k’ofar da kawunan ku zai rabu a ta dalilinta amman naga that’s exactly what you are trying to do. Sam!ban ga dalilin da zai sanya dan ka yi aure ka tsame y’an uwanka a jikin ka ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login