Showing 153001 words to 156000 words out of 244445 words

Chapter 52 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16495

ta sanya musu albarka daga k’arshe suka yi sallama suna masu hango silver lining….


A b’angaren Najeeb da Siyama kam a ranar kusan kwana suka yi suna waya…da kyar ta samu ya yi mata sallama suka katse kiran nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita yayinda shi kuma ya duk’ufa Nafila…Tabbas ya manta rabon da ya shiga farin ciki kwatankwacin wannan..shiysa ya kwana sallah yana godewa Ubangiji sannan yana rok’onsa ya tabbatar da aurensa da Siyama!…

Ya Musbah kuwa da ya yi alk’awarin zuwa ko alamar sa babu kuma bai yi waya ba,har cikin dare sai da ya Nafi’u ya gawada kiransa amma bai d’auka ba saboda ya Nafi’u ya lura har da takaicinsa ne suka tarar wa Baba ya birkice musu lokaci guda haka…shi kam zuwa yanzu ya daina jin haushin Ya Musbah instead tausayinsa yake ji kuma inshaaAllah zai taimakesa ya fitar da shi daga kaidin Baraka..shiysa ya shirya zuwa gidan nasa gobe da sassafe dan shi da Yashjub dama sun riga sun san gidan…zai je ya samesa su fara ceto rayuwar Jidda da take shirin fad’awa halaka a gobe daganan zai san abunda zai yi dan abun na Baraka ya zama abun tsoro.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 33
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.


A zaune ta same sa yana aiki a computer…zafi sosai take ji sakamokon zazzab’in da ya fara sauka daga jikinta dan haka ta nufi bathroom domin ta samu ta sake yin wanka bayan wanda ta yi ba da jimawa ba.

Sai da ta sauya kaya tukunna ta fito…kallon ta yake yi yana mamakin yadda ta shiga ta yi wankan ta fito da wayarta rik’e kyam! a hannunta…da sauri ya kawar da zargi a cikin ransa ya mik’a mata hannu alamun ta zo garesa..
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i!…ta san Yashjub ya yi k’ok’ari sai dai ita kuma laulayin ciki ya zo mata har da k’in son kasancewa da shi dan babu abunda ta ji ta tsana kamar yace zai nemi wani abun daga gareta.

Murmushin yak’e ta yi ta nufesa,tana zuwa ya gyara zama ya d’aura ta a kan cinyarsa cikin muryar bege yace”yanzu dai ai jikin da sauk’i ko?”
Sunkuyar da kanta ta d’an yi k’asa kafin ta girgiza kai alamun”a’a”.
Ya ji babu dad’i tabbas dan yana lura da yadda ko hannunta ba ta so ya rik’e a cikin kwana biyun nan..amma sai ya dake still,yace”haba mana!a ji da ni gaskiya ko in yi miki kuka..”
Daga haka bai bata ikon yin magana ba ya fara kissing d’inta cike da shauk’i….
Wani irin kuka ya ji ta fashe masa da shi cikin kukan ta shiga k’ok’arin kwatar kanta.
Dakatawa ya yi ya d’an cikata sannan ya zuba mata rinannun idanunsa yana kallonta kafin da mamaki yace”Abunda na yi yanzun ne ya sanya ki yin kuka har haka?”.
Kasa magana ta yi dan ba ma ta san me za ta ce ba,kafin ta mik’e ta sauri ta zagaya d’aya b’angaren gadon ta kwanta ta juya masa baya still tana sheshek’ar kuka..

Ya fi minti ashirin a haka ya k’ame kawai a yadda ta barsa ya ma kasa motsi kafin da kyar ya samu ya kwanta rigingine yana kalllon sama zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ga wani irin ciwon ciki da ya turnik’e sa tashi d’aya.
Tashin hankalin zarginta da yake shirin dasuwa a cikin zuciyarsa sam bai sa ya yi tunanin ‘watak’il cikin jikinta ne ya zo da laulayin hakan’ ba besides shi bai ma tab’a sanin masu ciki suna gudun mazajensu ba sai ma son kasancewa a tare da su….shiyasa gaba d’aya zuciyarsa ta jagule ransa ya b’aci matuk’a hankalinsa ya tashi,dan ya lura ba ta fara basa wannan attitude d’in ba sai da aka fara kiranta a waya….
Gaba d’aya kwakwalwar sa ta yi zafi haka ma zuciyarsa tunani kala kala yake yi ganin zuciyarsa ta na shirin tarwatsewa ne ya sa kawai ya mik’e ya fad’a bathroom ya kama ruwa ya yo alwallah ya zo ya tada ik’ama…..

Sai da ta ji shigewarsa bathroom tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya ta yi addu’o’i ta shiga karatun Al’Qurani a cikin ranta da haka wani bacci mai d’an karen dad’i ya yi awon gaba da ita…..


Sai da ya tashe ta sallar Asubah tukunna ya juya ya fice ya nufi masallaci…ta lura da yadda ransa yake a d’an b’ace dan haka ta shirya idan ya dawo za ta yi masa bayani ta basa hak’uri ta san zai fahimceta.

Tana idar da azkar Yahanasu ta kira ta tace”tun jiya cikin dare ta so ta kirata,da kyar ta iya bari asubah ta yi…kamar yadda su Yash suka samu identity d’in mutum biyu su kuma sun samu na mutum biyar har an fara nemansu maybe Allah bai yi su Yash d’in za su ga wannan footage d’in ba,yanzu tana ganin su gayawa Yash d’in ne su k’ara musu haske su had’a k’arfi da k’arfi ko kuma su yi nasu a daban?”
Ajiyar zuciyaManubiya ta sauk’e ta yi hamdala a fili tana mai jin dad’in good news d’in tukunna tace”Yaha mu yi namu a daban kawai,inaso in taimaka nima,Ina kwad’ayin ganin farin cikin da zai wanzu a fuskar Ya Yash a ranar da muka kama culprit d’in inaga ya ga muma mun yi participating mun taimaka.
Na ji suma suna maganar da sir Najeeb and a ta b’angaren nasu akwai haske,if to say they are stuck ne to da sai mu k’ara musu haske, dan haka kawai muma mu yi namu idan mun riga su yin nasara Alhamdulillah idan sun rugamu hakan ma Alhamdulillah kawai ni inaso in taimaka in yi participating ne.”
Murmushi Yahansu ta yi kafin tace”shikenan Manu,duk yadda kika ce”
“Ok akwai kud’in da na ajjiye zan baki na case d’in yaushe za ki karb’a cash ne”
Murmushi Yaha ta yi tace”ai kawai ki barshi…”
Da sauri Manu tace”Ina so in yi participating ta ko ina ne fa Yaha,pls kar ki ce A’a”
“Ok”kawai Yahansu tace kafin tace”yana Ina?”.
Dai dai nan Yash ya k’araso bakin k’ofar d’akin.
Tarr ya ji muryar Manubiya tana cewa”ya fita sallah ai,shiyasa ma na samu damar yin wayar,jiya ma na ga misscall na san watak’il a kan maganar ne shiyasa ban d’auka ba saboda muna tare da shi…”
Da sauri ya juya ya bar wajen dan ba ma ya so kunnuwansa su sake jiyo masa wani bala’i da tashin hankalin..har dishi dishi yake gani da kyar ya k’arasa kan sofa na corridor ya zauna
yana wani irin haki kamar wanda ya yi y’ar tsere…


Manubiya ta san akwai gwaggwo mai aiki kuma har ta fara jiyo k’amshin girki amma hakan bai hanata mik’ewa ta d’an kimtsa domin ta je ta had’awa Mijinta breakfast ba dukda kuwa morning sickness d’in da ya fara rufar mata mai zafiii.

Tana fitowa ta hangesa zaune a corridor kan sofa ya dafe kai da hannu bibbiyu.K’arasawa ta yi da hanzari da d’an mamaki ta zauna a kusa da shi kafin tace”Ina kwana”sai kuma ta d’aura hannunta a kan nasa tace”Ya Yash”.
A hankali ya bata iko ta zame hannuwan nasa da yake k’ok’arin yi daga kansa kafin ya juyo ya zuba mata ido kawai ba tare da ya ce komai ba.
Sai da gabanta ya fad’i sakamokon yadda ta ga idanuwansa sun yi jazir…tashi d’aya tausayinsa ya rufe ta sannan gaba d’aya ta shiga jin babu dad’i dan ta san itace silar wannan yanayin da yake a ciki…ta san ba ya iya d’aukar kwanaki masu tsawo ba tare da ya rab’e ta ba.
Haushin kanta ma ta soma ji dan haka cikin inda inda tace”Ya Yash dan Allah ka yi hak’uri,ka san ba ni da lafiya shiyasa…”
“It’s fine”d’in da ya ce mata cikin katseta ne ya sa ta yi shiru.
Tashi d’aya ta ga ya mik’e,yace “idan breakfast ya kammalu ki kawo mini,bari in d’an kwanta kaina yana mini ciwo,idan na tashi zan ci”
Daga haka ya wuce ya shige cikin d’akin.



Sukuku! haka ta had’a masa abinci jikinta da ranta duk babu dad’i ga kuma zazzab’i,babu yadda Yasira da gwaggwo ba su yi da ita a kan ta kawo su taya ta ba amma tace musu”ba komai,za ta iya”dan haka Yasira ta yi mata sai anjima ta wuce office Gwaggo kuma ta ci gaba da had’a na su.

Abinci kala uku ta yi
masa da coffee ta d’auka ta nufi saman ta je ta ajjiye a cikin d’akin,ta so ta zauna a tare da shi amma tana zuwa sai ta ga yana bacci gashi d’azu ta yace mata kansa na ciwo shiyasa ba ta tashe sa ba ta ajjiye a dining table d’in d’akin ta yi wanka a hankali yadda ba zai ji ba ta fito ta rufo masa k’ofar d’akin.
Tana fita ya bud’e ido ya bi k’ofar da kallo…”a yadda ta ga yanayin sa in da ace ta damu da shi ai da ta tsaya a tare da shi”
Ya aiyyana hakan a cikin ransa.


A d’akin da Siyama take ta tarar da su Yusra suna hira itama Siyaman ta na d’an biyesu ba laifi…
Sai da Manu ta zauna tukunna suka gaida ita kafin Yadira ta mik’e tace”bari ta je ta d’ebo mata abinci”
Ba yadda ba ta yi da ita akan ta barshi ba amma ta k’i ta fice ta tafi deb’owa.
Tana fita Yusra tace”jiya ma kuwa muna rabuwa Mommy ta kira tana so ta ji ya jikinki ba ta so ta kiraki direct kuma gudun kar ta tasheki dan ba ta sani ba watak’il ko kun yi bacci,bari in kirata yanzu sai ku yi magana”.

Murmushi Manubiya ta yi kafin tace”barshi ni in kirata da layi na”
Murmushi Yusra itama ta yi tace”anya kuwa kina da sabon layinta?barshi dai in kira”
Daga haka ta kara wayar a kunnenta bayan ta yi dialing…

Bugu biyu a na uku Mommy ta amsa sai da suka gama gaisawa tukunna tace”ga Adda Manu d’in ta sauk’o jikin nata Alhamdulillah amma ga ta dai ki ji muryarta.”
Tashi d’aya Mommy ta fahimci they are up to something dan haka ta ce “ok ba ta wayar”
Kawai.

Yusra tana mik’awa Manubiya wayar ta tsink’e.

“Ki yi magana mana kin yi shiru”Yusran tace.
“Ai naga kamar ya tsink’e ne”
Cewar Manubiya.
“Oh God!I forgot fa!wayar tawa ban yi recharging ba!akwai kud’i a wayar ki?Yadira ta fita kuma ban san password d’inta ba….”
Yusra ta fad’i hakan ta na mai mik’ewa ta k’arasa kan Manubiya ta tsaya tana jira ta bata wayar.
Siyama har za ta ce ga tata nan a kira dan kamar ta fahimci akwai wani abun,sai kuma ta tuna babu kud’i a wayarta dan haka ta fara k’ok’arin cin bashi da sauri dan a samu a kira Mommyn da wayartata amma sai ta ji Manu tana cewa”Eh akwai gashi”kafin Siyama tace wani abun har ta danna password d’inta ta bud’e ta mik’awa Yusran wayartata ita kuma ta sa hannu ta karb’a tana cewa”Bara in saka miki sabuwar number tata in yi saving,ai ta dad’e ta daina amfani da wachchar.
Zuciyar Manubiya d’aya dan ba ta yi tunanin akwai abunda Yusran za ta iya yi daga karb’ar wayarta da making call ba..cikin jinjina kai tace”tabbas kam dan ko na kirata wani zubin ta shiga ba ta d’auka ba wani zubin kuma ba ta shiga.
“Yeah a salon aka sace ita kuma ba ta samu ta yi welcome back ba har yanzu”
Ta fad’i hakan tana kwafe number da ta ga anyi ta kiran Manubiyan da ita a jiya ba ta d’auka ba dan gashi ta ga 090 kamar yadda Yadira ta fad’a dan haka ba ta da tantama itace ta gayen.

Sai da ta gama kwafewa ta adana a wayarta tukunna ta yi copying sabuwar number Mommyn daga wayartata ta loda a wayar Manubiya ta danna call ta mik’a mata tana murmushi.
“Lucky morning!na ga password na kwafe number.”
Yusra ta fad’i hakan a cikin ranta.Kafin ta juya ta wuce ta koma wajen zamanta ta zauna.

Da kulawa suka gaisa da Mommy har da Baba larai,suka tambayeta ya jikinta tace “Alhamdulillah”daga haka suka yi sallama dai dai nan Yadira ta shigo mata da abinci.Babu yadda ba su yi da ita ba amma ta k’i ci Siyama ma ta ji dad’in k’in cin da tayi dan itace ma ta fara yi mata signal da ido saboda yadda suka dage ya sa suka fahimci in ba da kyar ba sun mata abu a cikin abincin ne…shiyasa ta k’i yarda ta ci iyakaci ta d’auki ruwanta na bohole da ta d’ura a gora jiya wanda taga har ya yi k’ank’ara k’ank’ara ta bud’e ta yi bismillah ta kai baki..kalar ruwan bai chanja mata ba hakama taste d’in shiyasa hankali kwance ta sha sosai ta ajjiye tana sauk’e ajiyar zuciya…
Murmushi Yusra ta yi a ranta tace”in kin san wata ai ba ki san wata ba!”.

Ba su fi minti ashirin da zama ba Inna ta kira Manubiya ta sanar mata halin da ake ciki tace”nan da 11 za a d’aura aure”
Daga Manubiya har Siyama duk kuka suka saka…gashi sunata kiran Jidda ta ma k’i d’agawa.
Sama Manubiya ta je ta sanar da Yash halin da ake ciki dan haka ya mik’e yace bara ya shirya sai su tafi”
shima duk hankalinsa a tashe.Ba yadda ba ta yi da shi ya tsaya ya karya ba amma ya k’i yarda yace”su je da wuri kawai ba su da ishashshen lokaci,ya san idan ya yiwa Baba magana inshaaAllah zai d’aga k’afa”
A gaggauce ya yi wanka ya shirya cikin wata had’add’iyar b’akar jallabiya daga nan suka d’auki hanyar gandun albasa gaba d’ayansu har Yusra da Yadira.

A mota Yusra ta yi chatting Yassira ta tura mata har da number Abbakar…Ya’isha Yasirar ta kira ta tsara mata komai yadda za ta yi kafin tace”idan ya k’i yarda ta kira ta za ta san abun yi”.

A b’akin gate d’in gidan suka tarar da Baba Ya Nafi’u da kaka mallan da wasu mutane su uku.Da mamaki su Ya’isha suka shiga kallon juna ita da Yusra dan basu san sun chanja gida ba kuma za su iya dafa Al’Qurani akan cewa Yashjub ne ya basu gidan!tabb!aikuwa yanzu ba sai anjima ba za su gayawa su Mommy dama sun san irin haka ce za ta yi ta faruwa,gashi kuwa har an fara.
Suna wannan tunanin suka k’arasa suka gaida su Baba daga haka ya Nafi’u ya ce bari ya bud’e musu gate su shiga da motar amma sai Yash yace ya barshi bari ya bar motar tasa a waje kawai.
Shi ya bud’ewa su Manu k’aramar k’ofa suka shige ciki daganan suka juya wajen su Baba da shi da Yash.

Manya manyan flat house ne guda biyu iri d’aya gate d’insu d’aya ko wanne yana d’auke da 4 bedroom da 2 parlours da kitchen da dining area,ga babban tsakar gidan da ya ji interlock wanda atleast sai a gina irin gidajen uku a cikinsa.Har da d’akin mai gadi a kusa da gate d’in.
Ba kad’an ba gidan ya burge su Manubiya tashin hankalin da suke a ciki ne ya sa ba su tsaya santin gidan ba suka afka b’angaren da suka ga k’ofarsa a bud’e.

A chan waje kuwa sai da Yash ya tsaya tukunna ya fahimci limaman masallacin area d’in ne Baba yake tare da su…
Sai da suka gama suka yi sallama suka wuce tukunna Yash ya yunk’ura da kwarin guiwa zai lallab’a Baba amma instead sai Baban ya rigasa ya shiga had’a sa da Allah yana neman alfarmar indai ya d’aukesa a matsayin uba kuma yana ganin girmansa to kawai ya bar maganar ya yi wa su Jidda addu’ar samun zaman lafiya.
Sai da Baba ya tabbata ya d’aure Yash da jijiyoyin jikinsa tukunna ya barshi jiki a sanyaye…..



Tun daga nesa da ya taho ya Nafi’u ya fara murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’i a cikin ransa matuk’a
Dama d’azu da sassafe da ya je ya yi masa magana a take ya yi masa alk’awarin inshaaAllah zai zo,kuma dama tun a d’azun ya lura wannan karon ya Musbah ya ji fad’an da ya yi masa sosai shiyasa tun a lokacin ya ji sanyi da dad’i a ransa dukda kuwa uwar ramar da ya ga
Abokin nasa ya yi.

Sai da ya gama parking mashin d’insa tukunna Baba ya lura da shi ya gane sa…..k’uraaa masa ido ya yi gaba d’aya tashi d’aya tausayinsa ya lullub’esa dan kana ganinsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa.A hankali Baba yake jin duk wani takaicin Ya Musbah da ya k’unsa yana warwarewa sakamokon fahimtar da ya yi tabbas ba yin kansa bane kuma shi kansa ba ya jin dad’in abunda yake yi d’in dan gashi gaishe da shi yake yi amma sam ya kasa kallon cikin idanunsa kamar ma kuka yake son yi.
Ahankali ya had’iye wani k’ululun abu da ya tokare masa mak’oshi yace”Alhamdulillah Musbahu”still yana kallonsa yana karantarsa.

Sai da ya sake yin k’asa da kansa kafin yace”ya k’arfin jiki ya fad’i hakan a hankali.
“Alhamdulillah”Baba yace daga haka ya maida dubansa ga Ya Nafi’u yace”Nafi’u na tura maka kud’in,ka je ka siyo gadon,kaka mallan kai yake jira tun d’azu ku kai gidan.”

A hankali Ya Musbah yace”Baba ba za a hak’ura da maganar nan ba,ka yi hak’uri dan Allah ka….”

Cikin fushi Baba yace”kai har yaushe ka zo ka ji halin da ake ciki da har za ka tsomo mini baki a cikin al’amurana?Kar fa ka kaini bango Musbahu kulaka da ka ga na yi ba shi yake nufin na manta abubuwan da ka tafka ba!”
Da sauri kaka mallan ma ya tsomo baki,dama d’azu ma saboda Yash ne ya yi magana shiyasa bai tanka ba dan haka yanzu ya samu bakin magana harda cewa “a cikin duhu aka kama Jidda da Al’ameen amma shine saboda rashin sanin ciwon kai still suke da bakin k’orafi ga Yusuf wanda ya ji ya gani ya rufe ido zai aureta a hakan.”
“Yashjub mu je ciki”
Baba ya ce,daga haka ya juya,har Yash zai bisa sai wayar sa ta d’au k’ara ganin sunan Daddy yasa yace”Daddy yana kirana bari in je in dawo kafin d’aurin auren.”
“To”kawai Baba yace daga haka ya shige cikin gidan dan yana so ya yi wanka ya shirya da wuri gashi har 9:00 ta yi.

Su Ya Musbah sun san shawo
kan Baba ba abu mai sauk’i bane dan ransa ba a b’ace ba ma idan ya turje babu mai sa shi ya bari ballantana yanzu da yake a fusace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login