Showing 177001 words to 180000 words out of 244445 words

Chapter 60 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16464

Mama da Siyama…


A d’akin suka tarar da Yashjub ga mamakinsu…lokacin Najeeb har ya je ya d’auki Siyama da Hajiya Mama zai maida su gida,ba k’aramin dad’i Hajiya Mama ta ji ba da ta ga Yashjub ya zo haka itama Siyama saboda dama tana ta addu’a Akan Allah ya sa ba fushi ya yi ko ya k’ullaci Manu ba.Ta san dole da zafi shiyasa ta d’aga masa k’afa ya d’an huce gudun kar ta jagula abun hakanan ta yi ta addu’a gashi kuwa yanzu ya zo…..
Shi ya tarar da su Hajiya Mama su Ummi kuwa ba su same su ba iyaka Yashjub d’in suka tarar.

Suna zaune Manubiya a kan gado shi kuma a gefenta ya rik’e hannunta ya sunkuyar da kansa k’asa ita kuma tana video call da Jiddah wadda Manubiya ta ji matuk’ar dad’in ganin yadda k’anwar tata ta yi k’iba ta yi fresh a cikin kwanaki k’alilan alamun Hankalinta a kwance yake.
Yadda su Ummi suka ga walwala da murmushi a kan fuskarta ya sa suka fahimci ba ta ji komai ba.

Gaisawa suka yi da Yash da ga haka ya mik’e ya k’arasa ya shiga had’a mata Breakfast Yayinda ita kuma suka yi sallama daJidda bayan sun gaisa da su Yaha ta ajjiye wayar suka shiga gaisawa da su Ummi.

Yana gamawa ya k’arasa ya ajjiye mata,ya fara k’ok’arin bata tace masa”ai Likita yace akwai allurar da zai yi mata kafin ta ci abinci”

“Okay”kawai yace ya d’an yi mata smiling kafin ya mik’e ya fita domin kiran Doctor d’in.

Yana fita yaha ta zauna a wajen da ya tashi tace”MashaaAllah Jidda ta yi fresh abunta,Al’ameen ya iya kiwo”
Dariya duk suka yi har Ummi kafin Manubiya ta kalli Yahanasu tace”Yaha akwai abunda yake damunsa ne bayaga al’amarin da ya faru da ni? Na ga yanayinsa gaba d’aya ya sauya.”

Shiruu ta yi ta d’an k’ura mata ido kafin tace”za mu yi magana anjima,ki kwantar da hankalinki”
Daga haka ta yi sauri ta mik’e ta fice, ba itace Yashjub ba amma yunk’urin sanar da Manu da ta yi kad’ai a yanzu tashi d’aya k’irjinta ya fara dukan uku uku.
Kusan karo suka yi da shi dan tana fita shi kuma yana shirin yin knocking.
“Ina Doctor?”
“Yace yana zuwa”
Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin tace”Yash Ina ga gara mu bari ta warke garau kafin mu sanar da ita also har ga Allah bana so in yi tarnishin walwalar da na gani a kan fuskarta.”

Jinjina kai ya yi kafin yace”abunda nima nake tunani kenan,da na shigo d’azu she was soo happy to see me ta ma kasa b’oye murnar ta,I don’t think zan iya lalata farin cikin da nake gani a kan fuskarta ba zan iya fad’a ba Wallahi shiyasa kema dama na shirya akan zan ce miki ki yi shiru to Alhamdulillah tunanin mu ya zo d’aya.Mu bari mu koma gida sai a san abunyi dan tabbas kam ba zan b’oye mata har abada ba.”

Yahanasu ta bud’e baki za ta yi magana kenan suka jiyo k’arar fad’uwa sai kuma salatin Ummi…kafin ta fara cewa”Yashjub Yahanasu kuna Ina Ina likitan!!”dai dai ta bud’e k’ofa za ta fito a gigice suka yi kicib’is da su dan haka ta juya ta koma ita a tunaninta ma tare suke da likitan…
A rikice suma duk suka yi kan Manubiya da ta ke zube a k’asa yashe a tsakar d’akin…
Kasa tab’ata Yashjub ya yi tsabar tashin hankalin da tsoro
a mugun rikice ya rarumo gorar ruwa ya shiga yayyafa mata hannunsa yana wani irin karkarwa…ganin ta k’i motsi ne ya sa ya mik’e a gigice ya nufi k’ofar da niyyar sake kiran Likita suka yi karo,ba ma ya iya cewa kawai Manu yake nunawa Doctor d’in hankali a mugun tashe…da hanzari shima Doctor d’in ya k’arasa da taimakon Yahanasu suka kinkimeta suka d’aurata a kan gadon ya shiga bata taimakon gaggawa Yashjub kam ya ma kasa motsi ko magana hawayen ma sun k’afe in banda karkarwa babu abunda ilahirin jikinsa yake yi especially k’afafuwansa
dan har yanzun ba ta farfad’oba!luu haka ya tafi zai fad’i da kyar ya rik’e kansa ya samu ya zauna a kan kujerar bayansa yana ganin bibbiyu.

An kai ruwa rana kafin da kyar aka samu ta farfad’o….ruwa Dr ya sake jona mata ya fita ya je ya kwaso wasu allurai ya yi mata har da ta barci…Sai da bacci ya yi awon gaba da ita tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya juyo ya kallesu yace da Ummi”jiya jiya na gama ja muku kunne akan d’aga mata hankali ko?za fa ku ja wa yarinyar nan stroke da k’arancin shekarunta idan ba ku yi wasa ba!,jininta maimaikon ya sauk’a hawa yake kuma yi ku kiyaye fa!.”

Cikin d’aurewar kai Ummi tace”lafiya fa muke zaune da ita muna magana,na ga ta fara duba wayarta sai kuma na ga ta mik’e daga haka ta tafi ta fad’i a k’asa.”

Numfashi ya fesar kafin yace idan ta farka ku kira ni Allah ya rufa asiri”kawai.
Daga haka ya sa kai ya fice.
Shiruu duk suka yi suka zubawa Manubiya ido kafin Yash ya mik’e da kyar ya k’arasa ya d’auki wayarta a k’asan gado inda ya ga ta fad’a ,matsawa Yahanasu ta yi saboda itaama wayar tata take shirin dubawa….
Yana bud’ewa ya ci karo da sms daga bak’uwar number ta inda aka sanarwa Manubiya abunda ya faru jiya tsakaninsa da Kausar tiryan tiryan tun daga farko har k’arshe….
Jifa ya yi da wayar cikin fushi yace”enough is enough!!!”
Sannan ya fara k’ok’arin fita.
Da sauri Ummi da Yahansu suka tare sa dukda Ummi ba ta ga message d’inba itama zuwa yanzu kwakwalwarta ta bata me ya gani.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka iya tsayar da shi dan ya zuciya matuk’a ransa ya b’aci….
Cikin muryar fushi yace”Ummi ki barni in je in same su komai ma ya ishe ni,Wallahi sai na sauya musu kamanni tunda basu san dai dai ba!”

Cikin rarrashi tace”Yash wa za ka tunkara? Me za ka yi musu?”

Ba tare da sanin inda ya dosa ba ma yace”na san a tsakanin su Yadira so
just let me…..”
Hawayen da suka shiga zubo masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana sai kuma ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa”me na yi musu da zafi haka?me yasa y’an uwana suka tsaneni suka tsani farin ciki na?”
Sai da Ummi ta share hawayen da suka zubo mata tukunna ta k’arasa gefensa kan sofar ta zauna cikin sanyin murya tace”kar ka ce haka Yashjub,ba ka ta tabbaci…”
Cikin katseta yace”Ummi su ne!idan ba su ba wa ya san maganar in ba y’an gidan mu ba?yaushe aka haifi Yaran nan da za su zama mugaye makirai kamar haka?me na tab’a yi musu da za su yi mini haka?”

Shiruu Ummi ta yi dan ta ma rasa bakin magana.Ahankali Yahansu ta matso tace”Kamar yadda Ummi ta fad’a Yash ba lallai su bane ba,ka bi komai a hankali kamar yadda na gaya maka jiya…”ta san ko da ace su d’in ne Mommy ce ta zuga su suka aikata kamar kullum amma kuma ba ta jin a tsakaninsu ta fi tunanin Mommyn ce da kanta ya aikata wannan d’anyen aikin.
Itama cikin katseta ya mik’e yace”Yaha to
waye idan ba su ba?Daddy wanda ya haifeni?ko kece?ko Ummi?ko kuma Mommy?….”
Shiruuu ya yi kafin a hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”damn it!!”
Sai kuma ya koma ya zauna ya yi shiruuu.

Kasa ci gaba da zama a d’akin Ummi ta yi dan ba ta san ta Ina za ta fara ba..ba ta so tana shigar musu Irin wannan case d’in.
Shiyasa ta kalli Yahanasu ta ce”bari in je Allah ya rufa asiri,Yash k’addara kowa da kalar tasa ka yi k’ok’ari ka cinye jarabawarka.”
Daga haka ta d’au Jakarta ta fice…ba ta da tantama wannan aikin Mommy ne.

Tana fita yace”ki je kema,idan ta tashi zan ji da ita,I can face her…”

Cikin tausayawa tace”Yash ka yi hak’uri”

Wani kalar murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kafin yace”Yaha hak’urin nake yi a ko da yaushe amma wani abun dole aga weakness d’ina!…tunda nake a rayuwata ban tab’a jin labarin uwa irin Mommy ba,I’m not sure yet Akan abubuwan da ta yi mini sannan ta saka su Yasira suka yi mini amma Yahansu tashin hankalin da nake a ciki ba kad’an bane ba saboda Ina jin tsoron ranar da zargina zai tabbata Yaha ban san ya zan yi ba.
Ina jin tsoro in ji sunada hannu a case d’in estate d’ina!
Ina jin tsoro in ji sune suka yi chatting da Abbakar suka bawa Manubiya magani….shiysa nake ta k’ok’arin gocewa amma message d’in nan da aka turo tabbas na san su ne wannan kam ba ni da tantama kuma hakan ya sanya na sake yarda sune suke yi mini abubuwan da na kasa fahimtar ribar su idan sun tarwatsa ni!”
Ya fad’i hakan yana mai sakin kukan da yake ta k’ok’arin dannewa,rungumesa Yahanasu ta yi itama a take wani irin kuka ya kufce mata…Tabbas ta san zafin da Yashjub ya ke ji a yanzu da ya fahimci Mahaifiyarsa ba ta son sa sannan ba ta damu da shi ba ba ta damu da farin cikin sa ba saboda she went through the same thing kuma har gobe tana rayuwa ne a cikin pain d’in….
Sun jima suna kuka babu mai rarrashin wani kafin da kyar Yaha tashiga lallashinsa tana basa baki…cikin sheshek’ar kuka tace”Yash har gara kai!
InshaaAllah na san akwai ranar da za ta zo maka wadda za ka fahimci Mahaifiyarka ta na son ka ba son kashe ka take yi ba tana son dukkanin abunda kake so infact tana son ka fiye da komai da kowa a duniyar nan!
Unlike me! da zan rayu and have to live with the fact that mahaifiya ta ba ta sona ba ta k’aunata ba ta damu da ni ba ta yi using d’ina to get what she wan…”
Cikin katseta Yashjub yace”Yahanasu ki daina cewa haka!babu kyau kin san fa ta rasu kar ki k’ara mata nauyi…kwakwalwata ba za ta iya tuno mini ita ba amma a ko da yaushe hajiya mama tana sanar da ni ita d’in mutumiyar kirki ce,kar ki ce za ki shiga abunda ya faru tsakaninta da Daddy har ta kaisa ga cewa TV ‘kar mu sake ko da ambatar sunanta ne!’ wannan tsakaninsu ne kuma kinga har yau ba mu san menene ba balle mu shiga!
kawai ke dai har ma da ni kamata ya yi mu bi ta da addu’a da fatan samun aljannah…dan Allah Yaha kar in sake ji kin yi wannan furucin game da mahaifiyar ki!.Mommy kuma tunda Allah ki ka ce nasan gagara misali ne….dan haka nima zan yi addu’ar abunda kika fad’a d’in ya tabbata zan yi addu’ar Allah ya sa duk zargi ne kawai muke yi ba gaskiya ba.”

Kallonsa take yi tashi d’aya wani Irin yanayi na tausayi k’unci da rashin jin dad’i suka lullub’eta.Ba ta san lokacin da ta afka jikinsa ta fashe da wani sabon kuka ba.!

Sun jima a haka kafin da kyar suka samu suka lallashi junansu ta sake jaddada masa”ya bi komai a hankali kamar yadda suka gaya masa kar ya d’au mataki a kan kowa ba tare da kwakkwaran shaida ba.”


Awannnin Manubiya biyu tana barci kafin suka ga ta fara motsi…duk su biyun tashi d’aya k’irjinsu ya buga kafin Yash ya dake ya mik’e ya k’arasa ya zauna a setin kanta bakin gadon yacewa Yahansu ta je ta kira Likitan.

Tana gama bud’e idanunta Doctor ya shigo…yana nan inda yake aka gama dubata Dr d’in ya fita.

Yana fita tun kafin su yi magana ta kalli Yahanasu tace”d’azu kin ce za mu yi magana.Dan Allah Yahanasu kar ki ce mini akan maganar message d’in da aka turo mini ne dan Allah Yaha ku ce abunda aka rubuta a jiki k’arya ne.”

Yahanasu tana shirin yin magana Yash ya ce “gaskiya ne.”
A hankali ta saki wani irin kuka mai cin rai….mik’ewa Yahanasu ta yi ta fice zuciyarta sam babu dad’i.
Sai da Yash ya sauk’e wata nannauyar ajiyar xuciya ya had’iye wani abu mai d’aci da ya mak’ale masa a mak’oshi tukunna tiryan tiryan ya fara zaiyyano duk wani abu da zai iya tunawa wanda ya faru a jiyan bai b’oye mata komai ba…

D’ari bisa d’ari ta yarda da shi sai dai kishi takaici da bak’in cikin da suka tarar mata ne suka sanya take jin zuciyarta kamar za ta hantsilo ta fito waje har wani Jan numfashi take yi yana kufce mata.

Dai dai nan Mommy ta ja ta tsaya a bakin k’ofar ita da Ya’isha waenda zuwansu kenan.

Kamar zai fashe da kuka yace”mun so mu d’an jinkirta saboda yanayin jikinki daga baya sai mu gaya miki amma kuma sai aka turo miki message.Ga gaskiya nan na faiyyace miki ita Baby da message d’in nan da aka turo miki da kuma abunda ya faru da ni ya kamata ace kin fahimci so ake yi a raba mu dan Allah dan Allah Annabi kar ki bada k’ofa ki yarda da ni plss dan Allah….”


Tabbas wannan abu ne mai nauyi na tashin hankali da ya sameta dan za ta iya cewa bata tab’a shiga rikici da k’unci kamar yau ba amma kuma ya zama dole ta bawa mijinta support sannan kamar yadda ya fad’a tabbas so ake yi a raba su,dan haka ita kuma duk rintsi duk wuya ba za ta bud’e k’ofa a shiga a raba su ba…..da izinin Allah.
Wani irin zafi da rikitaccen tashin hankali ta ke jinta a ciki amma ya zame mata dole ta danne kanta ta taushi zuciyarta ta tsaya musu…dan haka cikin sharar hawaye ta sa hannu ta rungumo sa itama kamar yadda ya yi mata tace”I trust you! kuma babu wanda ya Isa ya rabamu ba zan bada k’ofa ba…duk runsti duk wuya ba za mu karaya ba.Abunda ya faru jiya babban al’amari ne amma na dad’e Ina neman tukuicin da zan k’ara maka na k’aunarka tsakaninka da Allah a gareni ban samu ba..
Ya Yash a matsayina na matarka Ina so ka saka a ranka kamar babu abunda ya faru tsakaninka da Kausar ka goge hakan a kwakwalwar ka nima na goge!ina so mu manta da duk wani takaici da bak’in ciki na daren jiya….indai saboda ni ne kake damuwa da fargabar mai zan yi tunani ko mai zan ce a kan case d’in to inaso ka san cewa Manubiya ta goge komai ba ta rik’e a rai ba bata saka a gaba ba babu komai a gabanta sai burin farantawa mijinta dan haka ka cire damuwa ka cire bak’in ciki mu ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki…inshaaAllah da ni da kai har abada ba za a ji kanmu ba.”

Kuka sosai Yash ya ke yi ya k’ank’ameta a jikinsa yana godewa Ubangiji da ya basa mar’atussaliha….ya ma rasa bakin magana in banda sake ruk’umk’umeta babu abunda ya ke yi yana ji kamar ya maida ita cikin cikinsa.

Shiruu Mommy ta yi har sai da Ya’isha tace”hmmm..mu shiga Mommy za ta ci ubanta ne!.”
Tukunna suka d’an gyara daga tsayuwar lab’en da suka yi suka fara knocking.

Gaba d’aya Mommy kanta ya d’au zafi tabbas Manubiya fa sai sun sake tsayuwa a kanta sun k’ara k’arfi fiye da tunani dan tabbas Yarinyar nan ba ta wuce tunani su gashi shegen naci gareta…ita da ta zo ta d’anyi b’arin zance akan case d’in a samu ta ji ta yadda za ta d’aga hankali har sai ta ji komai daga nan su yi baram baram da Yashjub ta tafi sai gashi an samu wani d’an albarka ya tura mana message ma gaba d’aya amma dukda haka ji abunda take cewa!..tana da tabbacin Kausar ce ta turo message d’in! tabbas dama tundaga jiya ta fahimci Kausar is up to something,ta d’an ji zafin yadda ta tsame su daga plans d’inta ta fara yin gaban kanta ita kad’ai amma kuma da wata wainar gara wata!da Manubiya gara ta bi bayan Kausar sau million ma dan haka a nan za ta tsaya!a yadda ta ji furucin Manu na yanzu ta riga ta gama deciding abunda za ta yi….ba dare ba rana ita da Baba larai za su duk’ufa daga yau! Wallahi indai ta haifu cikin uwarta da ubanta sai ta juyawa Daddy lissafi ya aura wa Kausar Yashjub daga nan sai ta ga k’arshen soyayya sai ta ga k’arshen naci za ta ga yadda Manu za ta yi idan Yash ya k’ara aure za ta ga k’arshen maratussalaha da Manubiya ta ke playing….



Yadda yashjub ya karb’esu ita da Ya’isha sai da suka sha jinin jikinsu…ga Daddy ya juya musu baya yanzu kuma Yashjub tabbas Manubiya ta tabbata mugun tsuro a cikin family d’insu amma ba komai inshaaAllah komai ya kusan zuwa k’arshe.
An riga an yi abunda suka zo yi
shiyasa kawai suka yi musu sallama suka fito jiki duk ba kwari ba kad’an ba attitude d’in Yash ya tab’asu Mommy ta d’an tsorata akan kar fa kwab’arta ta yi ruwa dan muddin Yash da Daddy suka zargesu suka juya musu baya suka fara gano su to fa akwai Babbar matsala dan haka dole ta tashi ta tsaya tun wuri ta gyara abunda ya fara lalacewa a tsakaninta da su Yashjub ,Yashjub ya auri Kausar Manubiya kuma ta kama gabanta…..
Gashi ta nemi fad’a kacha kacha da Daddy amma ba komai za ta gyara inshaaAllah….


Bayan sati biyu….
Babban abunda ya fi d’agawa Ummi har ma da su Yahansu hankali shine guduwar da Munirat ta yi…haka kurum kwanaki tara da suka wuce ta rubuta wasik’a akan ‘kar a nemeta ta tafi ba za ta dawo ba’ har yau babu inda ba a duba ba babu Munirat babu mai kama da ita,Ummi sai da ta yi sati d’aya a asibiti tukunna aka sallamota tsabar masifa…su Yasira kuwa an samu abunda ake so k’iri k’iri a gabanta suke yi mata dariyar mugunta suke cewa karuwanci Munirat ta tafi…

Mommy ta so su shirya da Daddy amma abunda ya yi mata sai da ya sakata a al’ajabi dan korar kare ya yi mata da ta je d’akinsa kuma har yau ko kallo ba ya shiga tsakaninsu in kuwa ya kalleta to harara ce! ko abinci ya daina ci a dining d’in k’asa duk dan saboda ita.Wannan al’amari ba k’aramin d’aga mata hankali ya yi ba har y’ar rama sai da ta yi gashi Yash da Manu shiruu ba a jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login