Showing 213001 words to 216000 words out of 244445 words

Chapter 72 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16431

yake dan tausar ta shi da su Hajiya mama wanda shima Hajiya Maman ce take tausar sa take tsayar da shi if not da tuni ya san na yi da Mommy…dukda ya san ba shi da wata hujja a kanta amma kawai shi he can’t tolerate her no more,ya tsaneta.


A bangaren Mama itama zuwa yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta saka Yahanasu da Yashjub a idanunta dukda tana tambayar Manubiya ya suke tana jin komai dan har gaisawa
sukeyi ma da Yashjub but tana buk’atar ta saka su a idanunta musamman ma da ta ji har yanzu Yahanasu ba ta yi aure ba!,ta san dole tana da buk’atar ta…..


Bayan watanni uku!!!

An yi auren Siyama da Najeeb gidansu yaana unguwar Badawa,haka shima Junior ya auri Yadira suna zaune a d’aya daga cikin gidajen Daddy dake a Unguwar Darmawa kafin ya kammala abunda ya zo yi ta karb’i transcript d’inta su wuce Uk.
Duk cikin aure biyun nan da aka yi su Manubiya ba su zo ko d’aya ba sun dai turo gudunmawa sun kuma yi addu’a.
Su Hajiya Mama ma da suka zo na su Junior ba su wani dad’e ba suka juya dan ita dama da kyar ma ta yarda ta zo.
Ya’isha tana nan yau lafiya gobe ba lafiya dan yadda ta kad’u ta damu da al’amari sai da ya girgiza su Mommy gashi har yanzu batama da shirin hak’ura da Najeeb.

Kausar ma tana nan tana fama kullum ba lafiya ga ciki ya tsufa..jira kawai take yi su Yashjub su dawo wllahi duk bala’i sai ta san yadda ta yi ta koma masa sai dai ta rasa ranta a hanyar raba sa da Manubiya da kasancewa tare da shi.


Ya Musbah ma ya kammala karatun da ya yi takardar tana fitowa ya fara shirye shirye successfully ya zana waec ya yi jamb yanzu haka neco ya ke yi kuma ya ci jamb d’in dan haka Najeeb ya sake zage damtse wajen nema masa gurbin karatu a fannin Business Administration a jami’ar Bayero uni,Kano.


Gwaggo Suwaiba ma ta zo,yanzu Mijinta shima Allah ya fara nuna masa k’arshensa kuma Itanma ta dage da addu’a sosai dan cikin ikon Allah tana cikin wnnan hali na ha’ula’i Allah ya kawo mata wasu makwabta jajirtattu wajen fanni addu’a har Al’k’urani suke rubuwata da littafai,sama sama suka fara gaisawa su kad’ai suke iya shiga gidan,sai da zama ya yi dad’i labari ya yi labari tukunna suka fahimci ashe ma Matar tana da relationship da Mahaifiyarsu Innar(very distant relative)amma.

Ita ta bata addu’o’i,kuma ta ce ta dage da Azkar da sallolin dare..Aikuwa da taimakon Ubangiji cikin ikonsa yanzu Mijinnata har islamiyya ya barta ta shiga sannan yanzu kam ana iya zuwa wajenta kuma wannan tsangwama ta kyarar duk babu,ba shi ma da lafiya ya kwanta jinya.
Ko da ta tambayesa zata zo ta ga Inna an yi auren su Jidda duk ba ta zo ba! Nan ma sam bai yi yunk’urin hanaawa ba dukda ba ya so amma shi kansa ya san yanzu kam surk’ullensa sun daina tasiri a kanta…hakanan ta taho kano ita da d’aya daga cikin y’ar mak’oftan nasu mai suna Hadiza bafulatanar Yarinya mai shekaru 17 kyakkyawar gaske siririya doguwa fara sol gashi har gadon baya.
Tunda suka zo da Ya Musbah ya kyalla ido ya ga Hadiza itama ta gansa suka kamu da k’aunar juna abun kamar had’in baki.
Satinsu biyu ya ga dai ba zai iya daurewa ba ya amayar da abunda ke zuciyarsa itama kuwa Hadiza ko irin d’an jan ajin nan na mata da kunyar fulani gagara kwatantawa ta yi tashi d’aya tace masa ‘Yes!!’

Dama su Inna sun fahimci take takensu ai kuwa Yarinyar tana gayawa Gwaggo Suwaiba suka hau murna itama kuma Inna Ya Musbah ya gaya mata,ba kad’an ba Inna ta ji dad’in had’in shiyasa Murna ta zame mata biyu,ga farin cikin ganin y’ar uwarta ga kuma farin cikin had’in Hadiza da Ya Musbah da Ubangiji ya had’a!
Hausawa sun ce ba ‘a yabon d’an kuturu sai ya shekara da yatsu amma tabbas ita kam za ta yabi Hadiza saboda Yarinyar tana da hankali ga ilimin addini ga son mutane da girmama na gaba da ita,sannan gwaggwo Suwaiba ma da suka yi watanni goma sha uku tare da su ta bada kyakkyawar shaida a kanta kuma itama ta ji dad’in had’in matuk’a.

Dama su Inna so suka yi a b’oye abun sai an saka rana komai ya kankama tukunna a fito da maganar ba dan komai ba sai dan Baraka amma Allah da ikonsa tun kafin kowa ya ji ma ita Barakar ce ta fara ji kamar wata mai duba…aikuwa nan da nan ta kunno masa wutar bala’i ta koina,ba ta tashi masifar ta sai dare ya yi ya zo bacci nan za ta hanasa bacci sai dai su kwana idanunsu biyu..amma har gobe shi nuna mata ma yake yi bai san a kan me yake take bala’in nata ba!!!shi inama ya ga lokacin yin wata budurwa???
Dukda hakan bai sa Baraka ra hak’ura ba hakanan itama Hadizar ba barinta ta yi ba dan yanzu tun safe har dare a wajen su Inna take wuni dukda fuskarta kullum kamar hadarn Kaji idan ta shiga wajen nasu amma kuma hakanan za ta zauna ta yi ta fad’an maganganu a Hadizan har ma da su Inna ko
a jikinta kuma zuwa yanzu hakanan ta hana Ya Musbahn keb’ewa ko da Innar ne wai duk dan gudun kar ya samu time da momment da Hadiza.
Kamar mai gadin sa haka ta koma ta kafa ta tsare,haka za ta yi ta zaman jiransa yana dawowa daga aiki zata fara hamma har sai sun tafi ko wajen Baba ya je haka za ta yi ta safa da marwa a bakin k’ofar parlourn nasa ta baya har da lab’e har sai ya fito sun wuce tukunna hankalinta zai kwanta.Tsabar bala’in da ta sakawa kanta ko girki ba ta iya zama ta yi ballantana gyaran gida koina ya yi datti gashi ba girki gida duk tsami kuma a da Baraka kam tanata tsafta gwanin ban sha’awa.
Sai dai kullum idan ta gama gadin nasa suka koma b’angaren su yace mata’ta d’an saka turaren wuta ta kimtsa gidan yana kyankyami’ shi kuma ya fita ya je ya siyo musu gurasa da nama…abunda Baraka ba ta sani ba shine idan ya yi fitar siyo gurasa da naman ne yake samun ganin Hadiza,dan sam ba shi ne yake zuwa siyowa ba almajirin su mai wanki da sharar gidan yake bawa shi kuwa ya dawo ciki ya wuce wajen Hadiza inda suke had’uwa kullum wajen wanke wanke ta baya.Yana lura da sa idon da Baraka take yi masa dan ko fitar zai yi sai ta lek’o ta tabbatar ya fita d’in tukunna take komawa ba ta san yana kallonta ba.
A yadda yake son Hadiza ba ya so a samu matsala a aurensu kuma zuwa yanzu ya fahimci Baraka ta hau Buzu,shiyasa ko su Inna da suke ta cewa ya fad’a mata idan auren ya rage saura sati biyu jin su kawai yake yi sai ya samu kansu zai nutsu ya zauna ya yi musu bayani sosai,domin shi kam inshaaAllah sai dai kawai Baraka ta ga Hadiza a d’akinsa matsayin matarsa ko kuma ta ji ana d’aura aure.


A b’angaren Baraka kuwa har yau ba ta kama Hadiza da Mijinta ba amma ta san something is going on gashi wayarsa koina password ballantana ta yi masa bincike…Bokan ta ne ya fara sanar mata yanzu kuma ya sake d’aga mata hankali ta inda yake ce mata ai maganar aure ma ake yi…dama chan a cikin masifa take sakamokon yadda komai ya k’i tafiya yadda take so Ya Musbah ya k’i ya dawo mata kamar da ta gagara mallakesa kwata kwata sannan so take a raba gidan biyu ko a sayar da gidan a sayi wani su rabu da su Inna amma abu ya ci tura!!!
Gashi gaba d’aya ta rasa soyayyar sa kuma ta gagara dawo da hankalinsa gareta kuma sai yanzu ita kanta ta fahimci masifaffiyar k’aunar da take yiwa mijin nata musamman ma da ta ji zancen maganarsa da wata….shiyasa ta tashi ta tsaya tsayin daka wallahi indai ta haifu Ba’a isa a yi mata kishiya ba kuma Inna da take zugasa ta hana ruwa gudu ta toshe mata duk wata hanya wallahi sai ta haukatar da ita ko kuma ta maida ita kamar farko ta kwantar da ita ta yadda za ta zama da ita da gawa babu maraba!saboda Bokan ta yace mata”Inna ce take yin addu’o’i ba dare ba rana babu ji babu gani shiyasa komai nata ba ya ci komai nata yake tab’arb’arewa.”



Yahanasu ma ta yi sabon saurayi mai suna Egnr Doc Kamal sumaila vice governor d’in Kano state…sun had’u da shi ne ta sanadiyyar tsaya musu da ta yi a matsayin mataimakiyar lawyer su na shar’iar da suka yi ta fafatawa yau kusan shekara d’aya kenan akan mulkinsu da aka yi musu almundahna to yanzu dai Alhamdulillah komai ya daidaita sun hau kan mulki wanda sai a lokacin ne ya fito mata da k’udirinsa!
Ya fi wata d’aya yana binta tana cewa a’a shi ya d’auka ma ko saboda kasancewarsa babban mutum amma bai tab’a aure bane ya sanya tace masa a’a sai da ta fito masa ta basa labarinta tukunna ya fahinceta…cikin ikon Allah shima d’in hakan ce ta yi ta faruwa da shi dan sau hud’u ana samun matsala da aurensa ana fasawa dan haka yace mata ta yi hak’uri tta daure su bawa relationship d’in chance inshaaAllah wannan karon da ga shi har ita za su dace…
Da kyar da taimakon su Manubiya da ta gayawa suka dinga bata shawarwari aka samu ta amincewa Alhaji kamal yanzu dai ya zo sau biyu jiya kuma sunzo shi da Abokinsa sun gaida Daddy.



Hatred tsana da takaicin Mommy ne ummul’aba’isin kwanciyar Daddy rashin lafiya ga kuma damuwa daban daban gashi Yashjub ba ya kusa.
Last week Abhi ya zo ya dubasa sam bai ji dad’in yadda ya ga jikin nasa ba,ba don yana da aiki ba da ba zai koma gida ba.
Hankalinsa duk ba a kwance ba Hakanan ba dan ya so ba ya wuce Uk…tun a jirgi ya kira Yashjub yace”yana son ganinsa a Uk idan ba damuwa.
Ya san suna waya da video call da Daddyn amma ya kamata ya je ya gansa gaskiya.

Bayan kwana uku da dawowar Abhi su Manubiya suka zo ita da Yashjub d’in…ta yi fari k’all ta yi k’iba ta yi fresh ta k’ara kyau amma babu ciki babu alamun sa a tare da ita wanda hatta su Hajiya mama sai da suka d’an ji d’arr!!amma kawai sai suka basar suka ci gaba da murnar ganin juna.

Abhi kam ya ma fi su Hajiya mama damuwa,har ga Allah fa wannan yana daga cikin confidential reason d’insa da ya sa ya so ace Yashjub yanada mata biyu ne ba wai Kausar ba A’a bayan ya sake ta ya so ya auri wata saboda ba zai yiu ace Yash ya k’are rayuwarsa a haka ba duk wannan uban dukiyar ace shege ne kad’ai zai juyata………
“Abhi Ina wuni!”
D’in da Yash d’in ya ce masa ne ya katse masa tunani.

Ahankali ya ke kallonsu shi da Manubiyan kafin ya d’an yi murmushi ya amsa gaisuwar tasu tukunna ya d’aura da cewa “duk kun yi k’iba kun yi kyau abunku tubarkallah!”
Sunkuyar da Kai Manu ta yi cikin tsananin jin kunya yayinda Yashjub ya d’an sosa k’eyarsa yana murmushi….

Ciki su Hajiya Mama suka wuce da Manubiya bayan an gama gaishe gaishe..suna wucewa Abhi ya gyara zama ya kalli Yash yace masa”yaushe za ka je ka dubo mahaifinka??”

Tashi d’aya yanayin fuskar Yash d’in ta chanja idanunsa suka d’an fara kad’awa.
Sai da Abhi ya sake jeho masa tambayar a karo na biyu tukunna da kyar ya samu yace”ba rana!”

“Saboda me??”
Abhi ya tambayesa cikin tarar numfashinsa.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace”Abhi pls dan girman Allah ka bar maganar kawai.”

Jinjina Kai kawai Abhi ya yi kawai daga haka ya d’auki waya ya danna kiran Hajiya mama tana d’auka yace”Mama sai fa kinzo saboda ya k’i gaya mini.”

Runtse idanu Yash ya yi da tafukan hannunsa kafin ya cika ya d’ago ya kallesa yace”Abhi saboda Kausar ne fa dan Allah kawai ka bar…”

“Kausar dai is one of the reasons Yash!,ko har ka manta message d’in da ka turo mini da hannunka??”
Muryar Hajiya mama ta katse sa tana mai k’arasowa inda suke ta zo ta nemi guri ta zauna tana mai fuskantar sa tace”Yash an baka space kamar yadda ka buk’ata Kausar is no longer your wife!dan haka menene dalilinka na k’in komawa Nigeria ko kanada waenda suka fi mu ne da ba za ka gaya mana matsalar ka ba sai su?”

Hawayen da ya zubo masa ya sa hannu ya goge kafin yace”barin maganar nan shine mafi alkhairi ga kowa Hajiya mama bana son yinta…”

Sake gyara zama ta yi da zaman gilashin idanunta ta fuskancesa sosai tace”ni kuma yau na nace sai na ji komai,dan haka the sooner you talk the better dan ka san ba zan tab’a hak’ura ba ko?.!”

Jin jina mata Kai ya yi dan haka tace”perfect..muna sauraronka!”


Sai da Yashjub ya d’auki sama da mintuna goma ya yi shiruu kawai,kafin chan ya zaro wayarsa ya kai musu inda videos d’in Yassir suke ya mik’awa Hajiya mama ya yi sauri ya mik’e ya fita……
….
Sai da hawan jinin Hajiya Mama ya tashi Abhi kansa sai da ya yi Hawaye ba sau d’aya ba….ba su iya b’oyewa Daddy komai ba hakanan suka sanar da shi komai wanda shima sai da suka yi da sun sanin fad’a masa da suka yi ta waya dan sosai ya gigita ya kad’u matuka da al’amarin da kyar Ummi ta taushe sa aka samu ya sha magani ya yi bacci bayan sallar asubah dan throughout ranar ba su runtsa ba.

Da kyar da mugun kyar suka lallab’a Yashjub ya yarda zai zo dan ba k’aramin Takaici ya ji ba da ya ji sunce har sun turawa Daddy shi har ga Allah ba haka ya so ba…sai da Hajiya mama ta zaunar da shi ta yi masa fad’a ta nuna masa illar yin shiru da guduwar da ya yi tukunna ya yarda da kyar ya amince ba dan ya gamsu hundred percent ba.


Sai da suka yi sati d’aya tukunna suka samu zuwa Yashjub Manubiya Abhi da Hajiya mama da Abhi…
Manubiya kanta Hankalinta a masifar tashe yake dan tunda Yash ya sanar da ita komai ta fahimci yau case ne a gidan,shiyasa ta nemi alfarmar ya bari su Ya Musbah su zo
su d’auketa a airport ta yi missing su Inna dayawa bata samu ta yi musu sallama ba,gashi har gwaggo Suwaiba itama ta zo.
Ya fahimci zillewa take son yi kuma shima baya son a yi a gabanta shiyasa ya amince tun kafin su yi boardn ta sanar da su ai kuwa a airport d’in su suka fara gani shi da Ya Nafi’u kafin su Junior suma su ka k’araso.

……If not because Yassir ba ya gidan ya tafi Abuja ya ce ya je yin business ne to da tuni Daddy ya dad’e da d’aukar mataki a kan sa…da farko masifa ya shiga da tashin hankali mai tafe da tausayin Yassir d’in yanzu kuwa haushi da tsanar sa yake ji he don’t think zai ma iya kallon fuskarsa.Ba ya son jin ko da sunan sa ne….

Kaff gidan zuwa yanzu kowa ya san Daddy yana cikin b’acin rai on top of na farko da kuma rashin lafiyar sa shiyasa kowa ya sha jinin jikinsa harda Mommy wadda ta fara shirye shiryen yi masa bori saboda kwata kwata ya daina raba musu kwana ita da Ummi,dukda ko da chan d’in ma tana zuwa yake korarta amma dai ai ya fi mutunci da daraja a kan yanzu da ya had’ewa Ummi kwanakin gaba d’aya kaff.

Jirginsu Yashjub ya sauk’a da safe around 6:00am na su Yassir kuma ya sauk’a around 6:40am Shiyasa ya zamana sun shigo cikin gidan kusan a tare dan su Yashjub suna gama shiga shima ya shigo.

Side d’insa ya fara nufa ya je ya yi freshening up
Daga haka ya fito a gurguje dan ya yi misssing Kausar over!!
Dukda wajen sabuwar budurwarsa da suka had’u a instagram ya je ya gwangwaje abunsa amma da kewar Kausar yake kwana yake tashi,har ga Allah shi kansa bai san wanne kalar so yake yiwa Kausar ba.

Ita kuwa Kausar tana chan ta shiga damuwa dan mutanen sun ce mata ba za su tona Yassir ba he kept his promise ya dad’e da taimakawa oganninsu sun gudu.


Ba k’aramin tashin hankali Yassir ya shiga ba da ya fara jiyo kamar muryar Yash suna magana shi da Ummi a baki bakin k’ofar.

Aikuwa yana shigowa da shi ya fara cin karo ya juya baya yana magana shi da Ummi….
Tashi d’aya hankalinsa ya tashi ransa ya yi masifar b’aci zuciyarsa ta fara tafarfasa wani irin sabon haushi tsana da k’iyyayyar Yash d’in suka yi masa k’awanya..

“K’araso ciki Yassir!!”
Muryar Abhi ta katse masa tunani,a dake!.

Kasa juyawa Yashjub yayi sakamokon wani irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki.

Yassir d’in kamar ba zai kula sa ba sai kuma ya d’an matsoshi yace”sauk’ar yaushe?”
Bai jira jin amsar sa ba yace”welcome”
Daga haka ya wuce ciki dan he can’t stand him.

Parlourn taff cike daga Mommy sai Kausar wadda take ta uban bacci ba ma ta san sun dawo bane kawai babu.

Shiruu kowa ya yi har su Yadira da basu san me ke faruwa ba!

Yayinda su Daddy suka tsura masa idanu kawai.

Cikin nutsuwa Yassir d’in ya k’araso ya nemi guri ya zauna ya fara kallonsu one by one dan zuwa yanzu kam ya san something is definitely wrong.

Gyaran murya Abhi ya yi kafin ya kalli su Yasmeen yace “ku d’an bamu guri”

Girgiza kai Daddy yayi yace”ka barsu Abhi,Ina buk’atar shaidu.”
Bai jira d’aukar lokaci ba ya kallesu one by one yace”ina so duk ku zama shaidata!
Daga yau har gaban abada babu ni babu Yassir!!!”
Sai kuma ya kalli Yassir d’in yace”mintuna arb’ain na baka ka tartara ya naka ya naka ka bar mini cikin gidana!!!!”.

Da mugun sauri Yashjub ya juya ya fita Yayinda su Yusra suka kaure da kuka suka shiga rok’ar Daddy suna basa hak’urin ya taimaka ya bar Yassir ko me ya yi bai yi deserving haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login