Showing 111001 words to 114000 words out of 244445 words

Chapter 38 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16457

ji ga gajiya”.

Jin jina Kai kawai Mommy ta yi daganan ta juya ta fita..tana fita ta hango Yashjub yana sauk’owa tare da Daddy.
Cikin sanyin jiki ta k’arasa suka gaisa da Daddy dama Yashjub d’in take nema ga kuma har da Daddy a kusa da shi dan haka a ranta tace “perfect’’.
Cikin sanyin murya tace
‘’Am ko za ka yiwa Manubiya magana ta fito mu je kuci abinci ,na gama had’a dining a k’asa Inata jiranku tun dazu’’

Murmushi ya yi yace ‘’ok Mommy.
Bara in kira ta tana d’akin Ummi ko?”

Jin jina kai ta yi kawai.

Daga haka ya wuce itama ta nufi k’asa Daddy ma ya wuce k’asan.

Yashjub yana shiga ya tarar da su Yahanasu suna ta faman k’ok’arin zuba mata abinci.
Sai da suka gaisa da Ummi dan d’azu su Mommy ba su bashi dama ba tukunna ya kalli Yahanasu da ta gama zubawa Manu abinci ta mik’a mata ta fara k’ok’arin bud’e d’aya kular.
Bai so zai ce wani abun ba dan ya san Ummi zata ji babu dad’i amman kuma Mommy ta yi masa magana kuma a gaban Daddy sannan ita da kanta aka ce ta yi girkin shiyasa kawai ya dake ya ce “Am Yaha!ko za ku sauk’o da ita da abincin k’asa ko?,basu gaisa ma da Daddy ba”

“Ok”kawai Yahanasun tace
Daga nan shi kuma ya juya ya fita dan baiji dad’i ba
Ummi zata ga kamar ya gwale ta ne.

Yana fita Ummi ta girgiza Kai kawai ta riga ta san ba yin kan sa bane ba.
Daga haka tace musu su sauk’a da abincin.

Ba a dad’e da zama ba su Manubiya ma suka sauk’o wadda zuwa yanzu zazzab’i ya yi mata ruff daurewa kawai take yi ga wani Irin amai da ya taso mata tun d’azu da su Yahanasu suka fara bud’e kuloli har yanzu bai kwanta ba.

Suna k’arasawa ta sunkuya har k’asa ta gaida Daddy da kulawa ya amsa yana tambayar ta ya Cyprus sannan ya suka baro su Hajiya mama ta amsa masa da “Alhamdulillah,suna lafiya Alhamdulillah.”Da kyar saboda wani jirijiri da ta ji yana d’ibar ta ga amai da taji yana shirin taho mata gadan gadan.

Cikin murmushi Daddy yace “MashaaAllah.
Bismillah have lunch with us’’
Ya fad’i hakan yana mai nuni da table d’in dake nan a cike a gaban sa mak’il da abinci.
‘’tam,na gode Daddy”tace,daganan ta mik’e tsaye aikuwa tashi d’aya wani irin gigitaccen jiri ya kwasheta ta tafi luuu za ta zube da sauri Yassir wanda shigowar sa kenan yasa hannu ya tareta had’i da rungumeta tsamtsan a jikinsa tashi d’aya wani yanayi na gigita da fitinar da bai tab’a ji ba ya sauk’ar masa sakamokon tsananin laushi da d’umin jikin ta.
Duk mik’ewa suka yi
A mugun rikice Mommy ta shiga cewa Subahanallah Manubiya lafiyarki?sannu kin ji,Yashjub dama bata da lafiya?”

Cikin tsananin b’acin rai Yash ya finciko ta daga jikin Yassir tsabar tsananin kishi bai san lokacin da ya rufeta da wani irin fad’a ba
‘’Baki da hankali?ba za ki iya rik’e kanki ba?za ki kama ki tafi ki fad’a masa a jiki?yanzu……”

Cikin tarar numfashinsa Ummi wadda ta lura da yadda Manubiya take jin jiki ta k’arasa tace” yi hak’uri Yash
gajiya ce da kuma jiri
a yi mata uzuri ko?
duba ka ga halin da take ciki mana.”

Sai a lokacin ya fahimci yadda ta fara hawaye ta ido d’aya gashi ta dafe kanta ta runtse idanuwanta da k’arfi.
A hankali ya cika mata hannu
kawai ya juya ya nufi cikin parlourn….

Wani kalar farin ciki ne ya lullub’e su su Yassira ganin yadda Yash d’in ya yi mata yayinda Mommy ta fara shiga masifaffan tashin hankali dan yanayin manubiya ya bata tsoro.

Ummi ce ta d’an ruk’ota ta share mata hawayen tace
“Kar ki yi kuka a gaban mutane mana”
Ba tare da kowa ya gani ba
ta d’an sake share mata fuska tace”Mu je ki ci abinci sai mu je sama ki sha magani in ma asibiti zamuje sai aje ko?
ki yi hak’uri”
A hankali Manubiya ta d’aga mata Kai alamun to dan ita mamaki ma ya hanata jin haushin Yash..anya kuwa shine ya yi mata wannan tujarar a gaban jama a har da wani cewa ‘bata da hankali!’

Da kyar dai ta kawar da tunanin suka k’arasa Ummi ta ja mata kujera ta zauna itama ta zauna.
Sai a lokacin tukunna Mommy ma ta zauna tana jan
numfashi da kyar dan ji takeyi gaba d’aya iskar parlourn ta yi mata k’adan
Yanayin Manubiya da kalar cika da fresh d’in da ta ga ta yi dama a gaskiya indai idanuwanta ba gizo sukayi mata ba tou kuwa ciki ta hango d’anye ma kuwa,yanzu kuwa jirin da ya kwasheta ya sake tabbatar mata…amma taya?ta san dama shi Yashjub ba kasafai abu yake kama sa ba ko ya kama sa ma to ba ya dad’ewa a jikinsa wannan gado ya yi a jininsa yake sannan bata tab’a iya juya masa lissafi…to amman ita Manubiya fa??
taya akayi har ta bari wani abun ya shiga tsakanin ta da shi da har ta kai ga samun ciki
Idan ma ta bari d’in to taya ciki zai iya zama a jikin ta bayan ajiyar da akayi
Anya ba gaskiya Yasira ta fad’a ba kuwa da tace ‘aikin Baba larai ya daina ci yanzu!’
Tunda gashi dai
tun farkon had’uwarsa da Yarinyar nan aka gagara rabasu aka gagara lalata maganar auren
suka gagara su hana d’aurin auren suka gagara cireta a ransa da rayuwarsa
yanzu gashi ciki yana neman b’ullowa kuma sun gagara cusa Kausar cikin gidan Yashjub.
Dan haka
Indai har Yarinyar nan ba waliyyiya baceba tou tabbas da gaske aiyyukan Baba larai sun daina ci.”
Mommy ta aiyyana hakan a cikin ranta.

Yasira ce ta zuzzuba mata duk abubuwan da suka dafa a plates ta tura mata gabanta tana mata wani kalar murmushi kafin tace “bismillah”
Ahankali Manubiya tace “thankyou”sannan ta sa hannu ta d’an sake jan abincin gabanta.

Da kulawa Daddy yace
“In duk abincin ba su yi miki ba akwai cooks ki fad’i abunda kike ra’ayi sai a dafa miki.

Ahankali Yassira tace
“Idan ma na waje kike so sai a siyo miki”

Dakyar Manubiya tace
‘’A’a zan ci wannan d’in ,nagode sosai ‘’

Tana mai jin dad’in yadda Daddy yake yi mata had’e da mamakin Yassira.

Sai da ta juya ta kalli
Inda Yashjub yake zaune a chan cikin parlour ya yi kicin kicin da rai tukunna ta juyo
ahankali ta d’auki lomar abincin da Yahansu ta zuba mata ta kai Baki…..ba don kar ta fito da shi waje su ji ba dad’i ba tou da tuni ta fiddo sa dan tashi d’aya ta ji wani irin amai ya yunk’uro mata dan haka ta yi sauri ta had’iye ta d’auka ruwa ta kora ta shiga k’ok’arin danne aman da yake ta so ya fito, a ranta kuma tana mamakin ‘wacce irin fever ce haka wadda bata tab’a yin irin ta ba mai amai’ dan har ga Allah kwata kwata lissafin ta bai kawo mata ciki ba.
Cike da k’arfin hali ta d’aura spoon d’in ta a plate d’in da Yassira ta turo mata gaban ta
gudun kar Mommy ta ji ba dad’i idan ba ta ci nasu ba…a hankali ta deb’o ta yi bismillah a cikin ranta ta nufi bakin ta da shi wanda hakan ya sa tun
daga kan Mommy har izuwa kan Yadira gaba d’ayansu suka tsaya da cin nasu abincin sukayi mata ‘k’uuurrr!’ da ido suna jira kawai su ga ta kai bakinta.

Da mamaki Daddy ya saki Baki kawai yana kallon su…lura da hakan da Baaba larai ta yi ne yasa ta yi sauri ta zunguri Mommy cike da takaici,da sauri Mommy ta juya ta kalle ta Baba larai tana shirin nuna mata yadda Daddy yake kallonsu suka ji Manubiya ta tura kujerar ta baya da sauri ta mik’e…
Ko gama juyawa ba ta yi ba amai ya kece shaaa……..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 27
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Da wani irin sauri Yashjub ya taso ya k’araso inda suke yana zuwa ya rik’eta da niyyar shigar da ita ko da d’akin Yahanasu ne amman hakan bai yiu ba
Tashi d’aya ta shiga kwarara masa aman a jikin sa ba ji ba gani…ganin yadda jikin ta yake karkarwa ne ya sanya ya riketa sosai had’eda d’an tallafota,ahankali ahankali yana d’an bubbuga mata baya.

Sai da ta amayar da gaba d’aya abun dake a cikin ta tukunna ta d’an fara dawowa haiyyacin ta…dukda yadda take cikin jin zafin abunda ya gama yi mata d’azu,sai ta tsinci kanta da jin tausayin sa da kuma rashin jin dad’i ganin yadda gaba d’aya ta b’ata masa jiki.

Still layi ya ga tana yi
besides wannan uban aman da ta shek’a dama dole ta zama bata da k’arfi dan haka ya durk’usa bai damu da wai a gaban su Daddy yake ba ya kinkimeta ya nufi d’akin Yahansu da ita.

Da sauri Kausar ta goge hawayen da suka silalo mata sai kuma ta juya ta nufi sama da gudu.Kallon ta kawai Yassir ya yi saida ta b’ace wa ganin sa tukunna ya juya ya kalli su Yashjub da suke shiga d’akin Yahanasu kusan a tare da shi da su Ummi da Munirat da Yahanasun.


Sai da ya kaita cikin shower glass tukunna ya dire ta.
Sai a sannan itama ta bud’e idanunta.
Gaba d’aya fanfunan dake a jikin shower d’in ya ware musu
wanda hakan yasa ta sauk’e wata k’ak’k’arfar ajiyar zuciya.
Ganin yana shirin fara zuge mata zip d’in rigar tata ne ya sa da sauri ta ce”Dan Allah A’a su Yahanasu fa suna waje!
Idan muka gama wankan ta ya za mu fita??”
Murmushi kawai ya yi yana kallon ta yace”Kar ki damu kafin mu gama mu fita na san za su fita su
ba za su zauna a d’akin ba.”
Ya fad’i hakan yana sake k’ok’arin ruk’ota yana mai jin wani so da k’auna da kuma tausayin ta suna ratsashi
Add’ua kawai yake yi Allah Ubangiji ya sa tunanin sa ya zamo gaskiya.

Turo baki ta yi ta d’an ja baya da dukkan ragowar k’arfin da take ji kafin tace
‘’A’a ni dai,kuma Allah ka daina d’aukata a gaban su Daddy dan ni yanzu ban san ma ta Ina zan fara kallon su ba”

Shiruu kawai ya yi yana kallon ta yana wani irin murmushi
kafin a hanakali ya matsa yace
“Sorry!ki yi hak’uri about
earlier but dan Allah kar ki sake
Har yanzu zuciyata zafi take yi.”

Ta fahimci mai yake nufi dan haka ta had’e rai tace
‘’A tunanin ka na fad’a jikin sa da gangan ne?‘’

Shiruu yai yana kallon ta dan shi sai yanzu ma ya yi wannan lissafin…a hankali ya fesar da iska ya matso ya yi cupping face nata a cikin tafukan hannunsa sannan yace
‘’Mu bar maganar pls na ji na yi laifi misunderstanding ne I shouldn’t have shouted at you that too in public ki yi hak’uri ki yafe wa Babyn ki um…..”
Ya yi maganar yana mai lankwasar da kai.

Cikin d’aura hannayenta a kan nasa tana k’ok’arin kwatar fuskarta tace
‘’ Kai d’in Babba da kai ai ba Baby bane sai dai in kwace mini suna kake son yi
Kalli fa yadda ka fini tsayi”

Murmushi ya yi yana mai farin cikin yadda ta huce nan da nan a hankali yana kallon kyakkyawar fuskarta ta cikin ruwa da yake rushing a ta koina na jikin su yace
‘’Ok,let’s see waye ne Babyn……’’



Kamar yadda ya fad’a ko da suka fito da ga wankan ba kowa a d’akin sai akwatunan su.

Murmushi kawai ya yi ya bud’e ya d’auki towel ya cire vail dinta daya rufa ya d’aura kafin Ita ma ya d’aukar mata towel ya nufi toilet d’in.
Kamar za ta fashe da kuka haka ta fito,ita kam bata san da wanne ido za ta ke kallon y’an gidan ba…d’azu ya d’auke ta yanzu kuma ya sa su Yahansu sun fita sun bar musu d’akin….

Jiri take ji sosai shiyasa ta nemi waje ta zauna a kan gado tana ganin uku uku.
Da kyar da taimakon sa ta shirya cikin wata English dress har k’asa mai dogon hannu,sama sama ya yi mata drying gashinta ya saka mata hula da ga nan ya durk’usa a gaban ta yace
‘’za mu je asibiti ne ko a kira doctor gida?’’

A hankali tace
‘’Ba na jin dad’i jiri nake yi kuma inaso in kwanta”

“Ok” kawai yace
Daga nan ya mik’e ya k’arasa ya d’auko wayar sa ya danna kiran family doctor d’insu…
Suna gama wayar ya koma inda take ya saka ta a jikinsa kafin yace
‘’Me kike so?me kike sha’awar ci in je in nemo miki??”

Girgiza kai kawai ta yi tana jin zuciyar ta tana tashi
dan sunan abinci kawai da ya ambato gaba d’aya sai ta ji kamar za ta yi amai.
Sake rungumota ya yi tsan tsan kafin yace
‘’Ki fad’i ko menene zan nemo, ba zai yiu ki zauna a haka ba.”

Ahankali tace
‘’Allah ba na son cin komai ni dai’’
Yana shirin yin magana wayar sa ta d’auki k’ara..ganin sunan Yahanasu ne yasa ya d’auka ya kara a kunnen sa….

Earlier
Su Yashjub suna wucewa
su Mommy ma suka nufi sama ba tare da b’ata lokaci ba,parlourn ya rage saura Daddy da Yassir wanda ya ke jin zuciyar sa tana wani irin tafarfasa
Tabbas zargin sa a kan Kausar ya tabbata kenan son Yashjub take yi idan ba haka ba meye na kuka?sannan ta wani wuce sama da gudu!
Shi kuma Yashjub wai shin shi ya fi kowa sa’a a duniya ne
ga mata nan kyakykyawa Allah ya basa ga d’aukaka da success ga farin ciki sannan yanzu kuma har zai haihu dan in ba da kyar ba ya san Manubiya ciki gareta…yanzu idan ta yi ciki yana ji yana gani haka za ta haihu ba tare da ya same ta ba??! sai dai ya sameta as mama kenan fa..inaa ba zai yiu ba!
bayaga haka ba zai tab’a yarda Yashjub ya sake samun wani farin cikin apart from wanda ya ke a ciki kafin ya mutu ba….
Runtse idanunsa ya yi da k’arfi sakamokon sarawar da kansa ya shiga yi.
Mik’ewar da Daddy ya yi ne ya dawo da tunanin sa cikin parlourn a hankali ya bud’e idanunsa da suka rine sukai jazur!bai gama dawowa daidai ba Daddyn ya wuce sama ranshi fes yana murna da adduar Allah ya kawo masa first jika d’insa d’an gidan Yashjub lafiya tabbas za‘a ga gata!.

Daddy yana wucewa su Ummi ma suka fito
Direct sama suka nufa yayinda Munirat ta d’an tsaya dube dube tana ganin wucewar su ta zauna kusa da Yassir.
Da sauri ya mik’e ya kalleta da kyar ya yi mata murmushi yace
‘’Daddy cewa yai in bisa sama, we will talk later.”
Daga haka ya wuce ya barta zaune a wajen ita kad’ai.
Tsabar tsananin tashin hankali mai tafe da dana sani Munirat ba ta san lokacin da ta fashe da wani Irin kuka ba….

Direct sama side d’in Kausar su Mommy suka nufa…Yasira da Ya’isha ne suka shige cikin d’akin wajen Kausar d’in suka shiga bata Baki…dukda ba kuka take yi ba amman ajiyar zuciyar da take sauk’ewa ya ishi ya fahimtar da kai tsananin tashin hankalin da take a ciki.

A parlourn Mommy Baba larai Yadira Yusra da Yasmeen suka tsaya dan har ga Allah su Yasmeen bama sa so su had’u da Kausar tsabar tsananin tausayinta da suke ji.
Mommy kam tashin hankali
ne ma ya hanata k'arasawa ciki…itama ta kanta take yi.

Cikin rashin jin dad’i Baba larai ta ja Mommy gefe tace
‘’Khadija sam kin chanja
gaba d’aya,bari ki ji wallahi ke kike dawo da aiki baya
Ban san mai ya faru mai ya sa yanzu kike kasa danne kanki ba.
Tun da suka tafi na ce miki ki dinga jan Yarinyar nan a jiki a san halin da take ciki a chan amma kin kasa,kamata ya yi ki dinga kiranta akai akai amma na sha ganin misscalls d’inta ma a wayarki ba ki d’auka ba.
Idan fa an yi abu ba wai zuba ido za ‘a yi a nad’e hannu a jira aiki ya ci ba kai ma sai ka bada gudummawar wayo da kissa tukunna sannan kuma ka shiga jikin mutun ta yadda za ka fahimci abun ya yi ko akasin haka,amma sam kin kasa!gaba d’aya Ummi da Manubiya sun chanja ki..yanzu ko d’azu da Ummi ta hana Manubiya cin girkin ki ta kwaso ta sama na san kin fahimci zarginki take yi ko?
Sannan itama Manubiyan kalar kallon da take yi muku da taga kuna nan nan da ita a iyaka yau kawai ai kinsan na mamaki ne ko?.
Ko da ace su Yadira sun yi fushi da su ko fad’a ko wani abun makamancin haka it’s okay amman ke kina yi tashi d’aya komai zai tab’arb’are na gaya miki na gaya miki amma kun kasa ganewa gaba d’aya kun bari zuciyar ku tana controlling d’in ku
Gashi yanzu in ba da kyar ba Wallahi ciki gareta kuma ban san tayaya akayi hakan ta faru ba.
Kun k’i yarda ku shiga jikin ta balle ku san kalar tsari da addu’o’in da take yi a samu a san abunyi.Yanzu na tabbatar inda ace kina waya da ita akai akai kuna video call kuna hira da ita sosai da tuni a cikin watanni ukun nan za mu fahimci abunda mukayi bai yi ba kinga da sai a sake sabon shiri da wuri amma sam kun k’i ku bani had’in kai kinga kuwa ai dole a yi ta ganin ba daidai ba…

Da kyar Mommy ta shak’i iska ta fesar kafin ta sa hannu ta yafito Yasmeen.
Yasmeen tana k’arasowa ba tare da shakku!thinking twice ko tunanin wani abu ba
Mommy tace”Ki rubutawa Ya’isha allura yanzu kafin mu sauk’a k’asa..muna sauk’a za mu je ki gwada Manubiya ,idan kika gwada ta kika ga alamun ciki gareta kar ki bari a yi test kowa ya gani a tabbatar kawai ki ce musu ba ta da ciki!,na san ai ba za su fahimta ba,sai ki yi mata allurar da Ya’isha za ta siyo miki ba tare da kowa ya gane ba!
A had’o allurar da ta ciwon jiki da ta hana amai.
Kin fahimci allurar da nake nufi???”

Ahankali cikin tsananin mutuwar jiki da rashin jin dad’in abunda Mommyn take shirin saka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login