Showing 21001 words to 24000 words out of 244445 words

Chapter 8 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16423

za ta yi inviting nata gidan a yi maka feshi da ruwan addu’a.’’
Ya fad’i hakan yana kallon Daddy yana dariya

Shiruuu duk su ka yi kafin Daddy yace ‘’Allah ya kyauta’’
Dai dai nan wasu mata guda biyu suka tunkaro su,d’ayar ba za ta kai shekaru hamsin ba..bak’a doguwa sanye cikin doguwar rigar abaya ta rufa
mayafinta.
Sai d’ayar matar kuma wacce a k’alla za ta kai shekaru 70 a duniya…fara ce k’all sannan doguwa ce sosai amman bata da jiki,kyakkyawace sosai dukda ta tsufa smman hakan bai b’oye kyawunta ba,tana
sanye da laffaya blue black
Idanunta kuma sanye cikin farin glashi.

Magana suke yi k’asa k’asa itada d’ayar matar kana gani kasan sirri akeyi shiyasa har ba su ma lura da su Daddy waenda suka nufesu ba dan sai da suka k’arasa daff da su tukunna suka lura dasu.

Har k’asa su Daddy suka durk’usa suka gaida ita,da kyar ta iya cewa’’lafiya Alhamdulillah’’
Idanunta suna masu ciccikowa da hawaye tun lokacin da ta kalli Daddy kafin a hankali ta d’an rissina ta d’agosa tsaye.

A hankali take kallon shi tana me shafa gefen fuskarshi kamar wani Yaro tana jin tsananin tausayin sa yana sake ratsata.Murmushi yayi yana mai kallon mahaifiyar tasa kafin ya kama hannun ta wanda ke a gefen fuskarshi ya rik’e a hankali ya ce ‘’ya hanya?’’

‘’Lafiya’’kawai tace still idanunta suna a kansa kafin
daga bisani da kyar ta kauda idanunta ta maida kan Abhi tace ‘’Hankalina bai kwanta ba sam shiyasa nake ta jera addu’o’i tunda muka taho.
Yanzu haka ma a jirgi yi nakeyi
da ikon Allah kuwa sai na ji matar bayana suna magana da ta gefenta,daga conversation d’insu na fahimci maganar tasu shiyasa da aka fito na tsaida ita,shine
take ce min’’Dad d’inta babban malamine kuma da ya zo rasuwa ita ya barwa malintar
shine fa na tsaya na karb’i numberta,to cut it short dai na bata adress za ta zo ta yi feshi
gaba d’aya gidan da ruwan addu’o’i’’

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e
Abhi kuma ya sunkuya da kanshi k’asa saboda a da yana ganin rashin kyautawa da rashin gaskiyar Hajiya Mama amman shima yanzu gaskiya ya d’an fara bin bayanta…

Ahankali Daddy yace’’Mama pls mana matar da ba ki gama saniba itac……’’
Wani kallo Hajiya Mama ta yi mishi wanda yasa shi had’iye ragowar maganganun shi,ba ta sake bi ta kansa ba ta juya ta kalli Abhi tace’’take me to the car’’

‘’Right away’’Abhi yace da sauri daganan suka nufi inda Junior yake tsaye gaba d’ayansu har wad’anda suka
turo akwatunan su Hajiya mama

Suna zuwa Junior shima ya bisu duk suka d’unguma motocin da suka taho da su.


Ana kiran sallah suka isa gidan dai dai Yashjub ya fito kenan zai tafi masallaci,sai da aka murna da oyoyo tukunna su Hajiya Mama suka shige ciki bayan Daddy ya kira gwaggwo yace mata‘’ta nuna musu inda aka gyara musu’’

Junior ma da wucewa zai yi sai da Daddy yayi mishi da gaske tukunna ya yarda ya bi su masallaci
A cewarshi’’ya gaji bacci yake ji.’’
Ana idarwa kuwa ya ce a nuna mishi inda Yassir ba ya nan
dan ya san indai suka had’u to
ba zai yi baccin ba.
Side d’in Yashjub suka nuna mishi daganan Daddy suka nufi sama side d’insa dan akwai maganar da suke so su yi both akan business da kuma family issue.


Sai around 7:00am
Tukunna y’an gidan suka shirya kowa ya fara shirin sauk’a k’asa domin yin breakfast.

Sai da numfashin Mommy ya yi sama a lokacin da ta fito dan ta na fitowa suka yi ido biyu da mom,ta san kuma indai ta ga mom tou kamar ta ga Hajiya Mama ne.

Murmushi ta k’ak’alo da kyar tukunna ta k’arasa inda mom din take tsaye jikin k’ofa
ahankali tace’’Sameeha
sauk’ar yaushe?’’

Murmushi mom ta yi bayan ta juyo tukunna tace’’Khadija ykk ya gida ba mu dad’e da zuwa ba’’

Dai dai nan Hajiya Mama ta fito daga d’akin inda mom ta rik’e mata k’ofa,tana fitowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ahankali a fili tace ‘’A’uxubillahi
Bismillah’’


Sunkuyar da kai Mommy ta yi
kafin tace ‘’ina kwana mama
sannu da zuwa’’

Banza Hajiya Mama ta yi da ita
dan haka ‘’Mommy ta sauk’e numfashi kafin ta durk’usa sosai har k’asa tukunna tace
‘’Ina kwana mama’’

‘’Ashe dai kinada tarbiyya kad’an’’cewar Hajiya Mama ba tare da ta kalle ta ko ta amsa gaisuwa tata ba.

Dai dai nan Yassira ta fito sanye cikin skirt da suite
sai d’an mini hijab iya kafad’arta,yanayin tsayuwar tasu kawai ta gani ta fahimci har an fara,da farko ba ta yi niyyar zuwa inda suke ba sai
kuma suka had’a ido da Hajiya Mama dan haka kawai sai ta dake ta k’arasa inda suke tana zuwa ta yi hugging Hajiya Mama kafin a hankali tace’’welcome we are glad u make it’’
D’an guntun murmushi tsohuwar ta yi kafin tace’’ya aiki?’’
‘’Alhamdulillah’’Yassira tace
kafin ta cika Hajiya Mama ta kalli mom tace ‘’Sannan ku da zuwa,i’m late muna da bak’i bari in yi sauri in wuce we’ll
catch up later’’
Tana gama fad’in haka ta wuce .

Ganin suna shirin wucewa suma kamar ma sun manta da ita ne yasa Mommyn tace’’bara in yi sauri in d’an had’a muku special,ba ku ce za ku zo yau ba ai da an had’a muku special tun wuri’’
‘’Eh ni na cewa d’an albarkar kar ya gaya miki ai,gudun kar ki hana,ki bar abincinki zan ci na masu aiki’’.
Baki ta bud’e za ta yi magana
su Abhi da suka fito yanzu suka k’araso Abhi yace ‘’Mommy mu je gaba d’aya mana’’

Sai da ta juya za ta yi
mishi magana tukunna ta lura da su Yasmeen….shi kanshi Abhi d’in ta san ya zo amman bata ganshi ba sai yau dan haka tace’’duk sannun ku da zuwa daganan ta juya ta nufi d’akinta dan ba ta jin za ta iya had’iyar ko da ruwa ne a yau kam.

Sai da Daddy ya yiwa su Yasmeen wani irin kallo tukunna suka matsa kusa da Hajiya Mama suka gaida ita
Itada Ya’isha dan Yusra da Yadira ba su tashi ba tunda ba fita za su yi ba
Yusra ta gama finals d’in ta
Yadira kuma sun fara hutu.MANNUBIYA
(Book 2)
Page 09
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ba yabo ba fallasa ta amsa musu daga nan aka sauk’a aka nufi dining table,ko zama
Daddy bai yi ba ya shiga kitchen dan ya san Ummi tana ciki,ai kuwa yana shiga da ita ya fara tozali ita da Munirat da masu aiki…a gaban mutane ne shiyasa Ummi ta d’an gaida Daddy da kulawa ba yabo ba fallasa but still ji takeyi kmr ta je ta shak’e sa dan ita kanta tana mamakin yadda haka kurum tsanarsa ta nunku a cikin zuciyarta kwana biyun nan wani irin mugun haushinshi takeji.
Amsawa ya yi yana mai binta da kallo dan ba kad’an ba ta yi masa kyau yau d’in sosai dad’in dad’awa yana son matarshi kuma yayi missing d’inta ‘’Daddy Ina kwana’’ d’in da Munirat tace masa ne ya dawo da shi cikin kitchen d’in,a hankali ya juya ya kalleta tukunna ya amsa da kulawa kafin ya maida dubanshi ga Ummi yace’’Hajiya Mama sun zo,tare da d’an uwana da matar sa ki fito ku gaisa’’
Tukunna ya shiga amsa gaisuwar masu aikin.

Murmushi ta yi tana mai jin wani tsananin farin ciki yana lullub’eta dan suna waya da hajiya mama kuma suna shiri sosai shiyasa ko gama abunda take yi ba tai ba haka ta cika ta kira gwaggwo ta bata daga nan ita ta fita ita da Munirat da murna kwance akan fuskarta.

Daddy ya ji dad’in yadda Ummin ta yi farin ciki da zuwan mahaifiyar tasa,ya san Hajiya Mama ba sa shiri kwata kwata da Mommy kamar ba y’ar aminiyarta a farko ba haka take rufe ido ta tsigale ta tass!sannan ya ji abunda ta yi mata yanzu amma dukda haka yadda Mommy ta nuna tashin hankalinta har ta kai ta gagara sauk’owa a yi breakfast da ita hakan ba kad’an ba ya sosa masa rai dan ya san daga ita har su Yasmeen da suka k’i zama duk saboda
Hajiya maman ne,amma zai ci ubansu in ya samu lokacinsu dan uwa ba ta fi uwa ba.

Faram faram kamar su Ummi da Hajiya Mama za su cinye juna haka aka shiga gaisawa ana murnar had’uwa har ma
da Sameeha dan Itanma suna waya suna chatting da Ummin,kamar yadda suka yiwa Ummi haka suka yi wa Munirat Itama ta ji dad’i kuwa
matuk’a dan atleast ta san ba duka aka taru aka zama d’aya ba kuma yanzu ta tabbatar Ummin ta za ta d’an rage zafi tunda ga oga kwata kwata ta gani da idanunta ba wai a waya ba
ta na sonta kuma tana ji da ita.

Su kad’ai sai Daddy da Abhi ne aka yi break fast d’in yau dan ko Ya’isha ma k’in zama ta yi tace za ta makara depending project d’inta na masters da take yi.

Tana fita Hajiya Mama ta kalli Daddy tace ‘’Saboda shegiya!
da kai da matarka kun janyo wa y’ay’anku karatu a Nigeria’’

Kallon Ummi tayi sai kuma ta kalli Daddy kafin ta ci gaba da cewa’’ai ni ban san irin power da wannan shegiyar Yarinyar take da ita a cikin gidan nan ba ,Saddik’a saboda fa ni da Daddy mun ce ‘idan kausar ta fita k’asar waje karatu za ta sake lalacewa a barta ta yi
karatu anan gida Nigeria’shine
ita uwar Yaran tace’tunda Kausar ba ta fita waje ba to babu wanda zai sake yin karatu a waje’.Duk dan kar ran y’ar gwal d’in ya b’aci!akan
ranta ya b’aci gara na ya’yan ta ya b’aci kuma shima Imam din ya zuba mata ido ya k’i tab’uka komai akai shiyasa ka kaf cikinsu Yassira ce kawai ta zo ta yi karatunta
Itanma dan ta riga Kausar d’in farawa ne da wata d’aya shiyasa aka barta ta kammala Oxford sai Yash da Yassir da Yahanasu tunda su sun riga ta yi’’
Hajiya Mama ta faiyyace hakan cikin d’an b’acin rai.

Shiruu Ummi ta yi ta rasa abin cewa dan haka kawai sai ta sunkuyar da kanta.

Cikin b’acin rai still Hajiya Mama tace ‘’Kuma ai gaskiya aka fad’a tun kafin fa ta tafi makarantar k’asar wajen ta yi ciki ta haihu d’an ba rai,lokacin tana gama secondary school.
Me kike tunanin zai faru inda an barta ta je wata k’asar..?’’

Ahankali Abhi yace’’Maaamaaa’’
Ya d’an jaaa maganar.
Sai a lokacin Hajiya Mama ta lura da yadda gaba d’aya ita kanta Ummin she’s not comfortable da zancen dan haka ta yi shiruu kawai tana mai sake tabbatar da innocence d’in Ummin a ranta tace’’tabbas ban ga ta zama ba dan matar nan ba ta san komai ba
sannan ba ta san wacece mommy ba,ya kamata a yi wani abun tun kafin ta cutar ta ita
that is
idan ta kasa cireta a gidan kenan…’’

Shiruu dining d’in ya yi ba ka jin k’arar komai sai cokula sai
kuma albarkar da Hajiya Mama taketa sakawa Ummi dan ta ji dad’in girkin da ta tarar Ummin ta yi da kanta kuma ya yi mata dad’i sosai.

Ummi kuwa baki har kunne dan ba kad’an ba take jin dad’in addu’o’in da Hajiya Mama take ta zuba mata.
Sosai Daddy ya ji dad’in yadda Ummi da Hajiya Mama suka fahimci juna suke shiri da kuma yadda Ummin take girmama Hajiya Mama
shiyasa ya yanke shawarar zai sake tuntub’ar ta maybe zuwa yanzu ya san ta huce..shi dai ba zai bata hak’uri ba no matter what dukda zuwa yanzu shi kansa ya san ya garu!Ummi ba yaji ta yi ba tana cikin gidan shi amman fushin ta gareshi ya fara illata shi matuk’a…..


Ganinta a tsakiyar manya yasa gaba d’aya ta ke ta jinta unconfortable shiyasa ta yi sauri ta kammala daga haka ta mik’e tace musu’’ta k’oshi’’ta yi musu sai anjima kafin ta
nufi sama.

Clashing suka yi da Yassir wanda yake sauk’owa k’asan sanye da suite har da brieficase ya yi masifar yin kyau kana ganinsa kasan office zai tafi.
Sarai ya lura da ita amman sai ya d’auke kai kawai ya wuce wanda hakan kuwa ba k’aramin gigita Munirat yayi ba
dan ba ta yi tunanin zai iya yi mata haka ba..tun jiya take jiran kiranshi bai kira ta ba sannan yanzu kalli abunda ya yi mata duk dan shekaran jiya ya ce ‘’su had’u a gidan Abokinsa’’ta k’i yarda ta yi fushi tace ‘’ita ya ma daina yi mata irin maganar nan bata so’’dga haka ta kashe wayar to ashe shima ya d’au zafi da gaske tunda gashi ya d’auke mata d’iff…anya kuwa ba za ta sauk’ar da kai tun wuri ba su shirya ta nuni masa komai ba komai ba dan tana jin tsoro kar ta je ta taro match d’in da ba za ta iya ba dan wllahi ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba….

Ya yi mamakin ganin Hajiya Mama dan haka ya yi saurin k’arasawa suka gaisa ba yabo ba fallasa kafin ya tambayesu Junior,ya kuwa ji dad’i kwarai da ya ji Junior ya zo,bai wani damu ba da aka ce mishi Na’ima ba za ta zo ba dan bai damu da Yarinyar ba
muguwar gidahumace
kamar ba a uk aka haifeta ta girma ba ga shegiyar rowa sannan tun ranar da ta fito mishi a mutum ta gaya mishi Yash take so ko chatting d’in kirki ba sa yi
shi manta wa ma yakeyi da ita in ba a family group ya ga ta yi magana ba.

Kad’an ya d’an chakali abinchin kafin ya mik’e ya yi musu sallama yace ‘’bara ya je office’’kai kana ganin Daddy ka san yana cikin tsananin farin ciki sai murmushi yake ta zubawa sakamokon ganin Yassir da ya yi a shirye caff!zai tafi office kuma da wurwuri haka,a ranshi ya godewa Allah ya shiga addu’a Allah ya sa fad’an da aka yiwa Yassir ya shige sa kenan Allah ya sa ya shiryu kenan har abada’’. Kasa hak’ura Daddy ya yi sai da ya mik’e har bakin k’ofa ya je ya shafa kan sa ya yi masa addu’o’i tare da fatan nasara tukunna ya koma ya zauna yana ta zuba murmushi.
Tunda Yassir yake a rayuwar sa bai tab’a jin guilty conscious irin na yau ba,ya san saboda ya ga zai je aiki ne ya sa yaketa wannan murnar alhalin a asalin gaskiya shi ba aiki ne zai kaisa ba..wani Abokin sa ne ya had’a sa da wata yarinya yarinyar ta had’u matuk’a mahaifinsu ya rasu kuma itace babba shine take neman aiki,shiyasa aka had’ata da shi shi kuma yace su had’u yau yaga ko za su daidaita……

‘’Tunanin mai kake yi??’’muryar Daddy ta katse masa tunani,murmushi kawai ya yi bayan ya kallesa daga haka ya yi waving d’insu ya sa kai ya fice.

Dukda uwar suite d’in da ya ci kuwa yana fara magana Yarinyar ta fahimci inda ya dosa ta kuma
fahimci ba aiki ake son ba ta ba dan haka ta mik’e tsulum ta fice ta bar sa cikin tsananin mamakin ta,dan ko irin sallamar nan ba ta yi masa ba hakanan ta mik’e ba um ba um um ta fice ta bar masa office d’insa…..ko minti uku bai k’ara ba shima ya fice daga company d’in ransa a mugun b’ace yana mmakin yadda sam ya daina cin galaba a kan y’an mata anyhow kamar wanda aka yiwa asiri,duk wani abu mai kyau na gidan Daddy Yashjub ya d’auke harma da farin jinin y’an mata……

Ko da ya dawo gida direct side d’in Yash ya nufa wajen Junior aikuwa kafin awa d’aya ya ware war suka ta hira abunsu
dan kusan Junior shine best friend d’in Yassir,halin su kusan d’aya ne dan indai aka zo batun mata to kowannen su sai a hankali sai dai unlike Yassir shi Junior ya san class d’insa sannan shi he’s very hardworking yanzu haka Doctor ne shi looking forward into becoming a consultant.

Junior ya yi mamaki da ya ce mishi ‘’ya zo su je su gaida antynsu matar Yashjub but sai ya ji Yassir yace ‘’shi bai ma tab’a ganinta ba’’amma kuma
Junior d’in da ya tuna waye Yashjub sai ya ga hakan a wajenshi ba komai bane dan haka ya kawar da zancen su ka fad’a wata hirar.
….
Mommy tana shiga cikin d’akinta ta fashe da wani irin kuka mai hawaye wiwi kamar wata yarinya,ta kasa tsaye ta kasa zaune sai faman safa da marwa take yi tana hawaye
tunda ta shigo cikin d’akin.A haka Baaba Larai ta turo k’ofar d’akin ta shigo dan d’azu tana parlourn Kausar wadda itama damuwa ta sauk’ar wa da zazzab’i ta fara jiyo
Hajiya Mama da Mommy shiyasa ta bari sai da suka wuce tukunna ta biyo ta ga halin da y’ar uwartata take a ciki.Da mugun sauri ta rufe k’ofar ta k’arasa kusa da ita ta rik’eta tace’’subhanallah Mommy….’’

Ingijetan da Mommy ta yi ne yasanya ta kasa ci gaba da magana,cikin tsananin fushi Mommy ta fara magana tana hawaye tana cewa’’kar ki soma tab’ani,ki bar ni kawai in mutu Larai tunda kin kasa min maganin matsalata,abu d’aya tak zuwa biyu amma ya gagareki which makes me think anya ma kuwa kina min aikin nan tsakani da Allah?.In ba ki ci in ba ki sha in baki sutura da wajen zama amma ace wai ki kasa mi……’’
Yadda Mommy ta ga Baaba Larai ta kafeta da manyan idanunwanta da suka yi jazir suka cicciko da kwallah ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana dan haka kawai sai ta juya mata baya ta sake rushewa da wani irin kuka.

Baaba Larai ta so yin fushi da Mommy itama ta so mayar mata da martani daga nan in yaso su yi kacha kacha amman kuma sai ta kasa,saboda ta san zafin failure d’in da suke ta fuskanta ne ya tunzura ta ga aikata hakan,dan ko ita kanta daurewa kawai takeyi amman abun ya fara bata tsoro kuma ta fara gajiya,ba wai iyaka kai kud’in Yash da suka kasa hanawa ba hatta su Hajiya Mama sai da suka so su hana su zuwa amma kalli tsulum kawai sai ganin su sukayi…..

Tana cikin wannan tunanin Mommy ta juyo tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login