Showing 183001 words to 186000 words out of 244445 words

Chapter 62 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16482

sallar da su Daddy waenda ana idarwa suka tilasta masa ya bisu domin su yi lunch tare.

Daddy ya daina cin abinci a k’asa saboda Mommy dan haka suna shiga suka wuce sama su uku yayinda dinning area na k’asan ya cika da kowa da kowa saboda Ummi ma zuwa yanzu ta d’an ware da taimakon hope da kwantar da hankalin da Hajiya mama suke ta bata,shiyasa take d’an shiga mutane har da ita ake cin abinci.



Ko da Yashjub ya wuce ya bar Kausar ciki ta shiga ta wuce bedroom ta fad’a bathroom domin ta watsa ruwa tana mai jin wani sanyi da farin ciki kamar an yi mata bushara da gidan aljannah…plan A ya kammalu successfully yanzu saura plan B!tunda an yi sati biyu ciki zai iya baiyyana kenan,gashi shima Yash d’in ya fara zuwa gida dama tanaso ayi komai a gaban sa ne dan haka ta shirya akan gobe inshaaAllah dai dai lokacin da ta san yana zuwa za ta yi abunda ta shirya…
Tana wannan tunanin tana jin wani tsantsar farinciki hakanan ta kammala wankan ta ta fito d’aure da towel…

Sai da gabanta ya yanke ya fad’i da ta ga Yassir zaune a kan gado idanunsa da fuskarsa sun yi jazur!!!
Ya tsoratata sannan yanayin sa ma ya tsoratata matuk’a..kamar mai jin tsoro haka nan ta k’arasa a hankali ta nemi guri ta zauna a gefensa tace”me ya faru?”
Ta yi masa tambayar a d’arare…

Sai da ya d’auki sama da minti d’aya tukunna ya juya ya zuba mata manyan idanunsa da suka yi jazur yace”Kausar change of plans..ba za mu tsaya har ki haihu kafin Yashjub ya mutu ba ya zamo dole ya mutu a yau!yanzu.”
Gabanta ne ya yanke ya fad’i hankalinta ya yi masifar tashi tashi d’aya yawun bakin ta ya k’afe…da mugun kyar ta samu ta ce”me ya faru?”
Cikin tashin hankali shima yace”kawai as my partner in everything na ga ya kamata in gaya miki ki sani!ki bari zan yi miki bayani amma not now sai in komai ya kammalu dan a yanzu ba zan iya ba Kausar Ina cikin masifa ba zan iya dogon bayani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai mik’ewa da shirin fita,da sauri itama ta mik’e ta sha gabansa ta tsaya tace”Yassir kar ka yi abunda za ka tona mana asiri ka lalata komai ka tsaya ka nutsu ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka fad’a mini ne ya faru mu san abunyi….dan Allah dan annabi.”
Ta k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.
Saida ya runtse fuskarsa cikin tafin hannunsa ya murtsuka ya fesar da wani zazzafan huci kafin yace”Yaran Grenade sun turawa Yashjub message yanzunnan nima suka turo mini evidence,sun tura masa videos har da wanda nake making agreements da basu kud’i duk sun tura masa ta watsapp komai da kika sani duk wani evidence sun tura,for now na san bai riga ya gani ba dan na duba na ga baya online…..
Kausar kar ki ce mini a’a ko kuma ki ce za ki kawo wata idear ya zama dole Yashjub ya mutu kafin ya ga sak’onnin nan ya bankad’a komai ya saka a kashe ni! Kisan wulak’anci cikin rashin gata.”

Karkarwa jikin Kausar ya d’auka…..ganin yana shirin fita yasa ta sake tare hanya tace”Yassir kar ka je garin kashe sa a kamaka!”
This time around cikin tsananin b’acin rai yace”wai ba kya fahimtata ne???duk baya nin da na yi miki ba kya ji na ne??an riga an tura masa ko na yi yunk’urin kashe sa ko ban yi yunk’urin kashe sa ba zai ga komai kuma kashe ni za a yi?dan haka gara in yi yunk’urin hopefully kuma in samu nasara this time around a samu ya mutu!”

Jikinta yana wani irin karkarwa tace”Yassir idan kuma suka turawa Daddy fa?shima binsa za ka yi ka kashe sa?ina ji maka tsoro kar ka je garin hanzari tsoro da fargaba kwab’armu ta yi ruwa!ka duba fa ka ga yadda kwata kwata plan d’in mu bai yi aiki a kan Daddy ba dan sam bai ji haushin Yashjub ba sannan ba mu riga mun ce cikin nan na sa bane ba ya ji ya sani!akwai a lot of things a gabanmu da ya kamata mu yi kar ka lalata komai ka saka mana fullstop dan idan aka kamaka komai ya zo k’arshe…misali yanzu ka je garin sauri a kamaka me kake tunani?,komai fa ya lalace mana kenan?”amma idan muka nustu muka yi tunani za mu samu maf…”

Cikin tarar numfashinta yace”idan ba a kama ni ba kuma fa?sannan idan muka yi slow aka kama ni?”

“Yassir a irin wannan situation d’in mutum have to assume the worst!!!
saboda Ana so ka shirya kare kanka ka shirya mafita ka san abun yi idan komai ya rincab’e,ba fa a abu sama ta ka!”.
Abun nan da ya faru ni a wajena da tunanina gyarasa it’s very easy kar ka rikita kanka ta kwab’a komai ka lala ta komai..a gani na dan sun tura masa tsaff za su iya gogewa tunda watsapp ne..Yassir kud’i fa aka basu suka karb’a suka yi maka aiki in the first place!all you have to do shine ka k’ara musu kud’i tashi d’aya za su manta da wani Grenade su bi ta watsapp d’in su goge tun da kace ba ya online ni kuma daga nan har zuwa dare ba zan bashi kwanciyar hankalin da zai hau watsapp d’in ba ma!.ai yana cikin gidan nan dan yanzu ma ta window Ina wanka sai da na hango motarsa a fake so bai tafi ba har yanzu..you just wait and watch..sannan ka nutsu dan Allah!!kashe mutum yana da buk’atar plan da shiri,ko kaza za a yanka sai an wasa wuk’a an tanadi ruwa ballantana mutum d’an adam!ba ka da plan ba ka da komai tashi d’aya kace za ka kashesa a rana d’aya wallahi ba ni da tantama hakan ba mai yiwuwa ba ne ba kuma sai an kamaka!kwanakin baya da ka yi yunk’urin hakan da tsararren plans har biyu ya mutu???sai yanzu a cikin rana d’aya ne kake son miracle ya faru?”.

Shiruu Yassir yayi yana mai fitar da huci kafin chan ya rungumeta cikin huci yace”I love you Kausar na gode da kika wayar mini da kai,tabbas maganar ki gaskiyace…but duk abunda kike planning make it fast saboda inaga masallaci kawai ya tafi daga nan zai wuce…”


“Okay bari in saka kayana”
Kawai tace,daga haka ta nufi closet d’inta ta zaro doguwar riga ta saka ta zare towel d’in ko undies da mai bata buk’ata ba haka nan drawer ta d’auko turaren da tunda cikin ya shigeta ta tsani warinsa ta fesa a palm d’in ta ta runtse da sauri dan tashi d’aya ta ji amai ya taho mata…Tana fara shiri Yassir ma ya fara waya da mutanen,ta san ba shi da enough kud’i yanzu shiyasa k’asa k’asa tace masa”ko nawa suka ce ya yarda za ta cika masa”
Daga haka ta saka Kai ta fice daga d’akin tana jin
mugun mugun haushinsa,a ko da yaushe idan ya yi yunk’urin kashe Yashjub ji take kamar ta kashe sa!.
Addu’ar ta d’aya Allah ya sa mutanen su yarda kar su basu problem ita kuma ko nawa suka ce za ta bayar ba ta so wani matsala ya taso ta koina kafin a yi aurenta da Yash.



Tana sauk’a ta tarar da su gaba d’aya suna cin abinci har da junior Wanda ya zamewa Yadira cingum itama kuma ba laifi ya siye zuciyarta zuwa yanzu musamman ma da ta fahimci yanzu ya shiryu ba kamar da ba gashi shi aka zab’a mata dan haka aka bata shawara kuma itama ta yarda ta amshe sa hannu bibbiyu. Sosai Kausar ta ji dad’in ganin kowa a ranta tace”perfect!”,ba ta ko kalli kowa ba hakanan ta wuce ta nufi kitchen babu wanda ta gaisar har Hajiya Mama shiyasa ita kuma tace”tunda kitchen d’in ba na Ubanta bane ba ta dawo ta zo ta gaida mutane kafin ta shige”.Wani sassanyan murmushi Kausar ta yi dama hakan ta ke so ta faru dan haka kawai ta shige cikin kitchen d’in ba tare da ta ko juyo ba kuma kowa ya san sarai ta ji dan lokacin da Hajiya Maman ma ta fara magana sai da ta ja ta tsaya tana dasa aya kuma ta ci gaba da tafiya ta shige cikin kitchen d’in.
Hatta su Mommy sai da suka sha tsananin mamaki Hajiya Mama kuwa dire cokalin ta ta yi da k’arfi ta mik’e tsaye ta kalli Junior tace”finciko mini Yarinyar chan ka kawo ta nan right away!!.”
Mik’ewa ya yi ya nufi kitchen d’in ransa shima a b’ace saboda da ma a wuya yake da su ita da Yassir ga kuma rashin kunyar da ta yiwa Hajiya mama shiyasa yana shiga ya fincikota kamar yadda Hajiya Mama ta buk’ata da ita da plate d’in hannunta ya fito da ita sai da ya kawota gaban Hajiya Mama tukunna ya cika mata hannu ta hanyar yin cilli da shi….juyawa ta yi ta shiga zabga masa wata uwar harara yayinda shima yake jifanta da wani irin kallo.
Cikin b’acin rai Hajiya Mama tace”ai ni za ki harara ba shi ba..jinin marasa kunya da tarbiyya kawai,idan aka ce ku yi abunda k’uda zai bi ku k’i yi ai ga irinta nan kin fara gani tun a duniya!yadda fuskar ki ta koma izina ce a gare ki kamata ya yi ace kin fara gyara Hali da ke da iyayen naki.”

Shiruu duk aka yi itama Kausar d’in ba ta ce komai ba kuma ba ta bar kallon Junior wanda shima itan yake kallo ba!
Da kyar Mommy ta lallashi kanta ta danne zuciyarta tace”Hajiya mama ki yi h…”
Cikin tsananin b’acin rai da takaici tace “kin san Allah Khadija zan baki kyakkyawan mari wallahi tallahi!!wannan kissar taki ba ta samu guri a cikin kai na ba tun wuri ki daina idan za ki fito mini a Khadijar ki to ki fito idan kuma ba za ki fito ba wallahi kin ji na rantse kika sake tsomo mini baki a cikin issues d’ina sai na make ki!,bak’ar ashana kawai.”

Mik’ewa Ya’isha ta yi kamar za ta tashi sama ta wuce sama ranta a mugun b’ace…cikin takaici Hajiya mama tace”an ce da Uwarta bak’ar ashana ta ji haushi bayan gaskiya aka fad’a tunda kalli attitude d’in da bak’ar ashanar ta koyar da ita,ni fa uwar ubanta ce amma kalli abunda ta yi mini…..”

Shiruu duk akayi kowa ya yi tsit dan haka Hajiya Mama ta juya ga Kausar tace”zaki gaida mutane ko na saka Junior ya koya miki respect yanzunnan??,ke har kin isa ki bawa mutane wannan attitude d’in?kin hana jamaa sukuni kin yi kane kane a gidan mutum amma dukda haka saboda ke d’in ba y’ar halak bace ba shine za ki fara wannan sabon halin?a baki ci a baki sha Allah na tuba in ba dan mu d’in ba ai da sai dai ki shiga duniya inda kika fito…”

Cikin katseta sannan kamar irin kin isheni d’in nan ta juyo ta kalleta ido cikin ido tace”Hajiya Mama Ina wuni”
Da k’arfi…..

Mik’ewa tsaye Ummi ta yi Hajiya mama ma ta yunk’ura amma kafin su yi wani abun tuni Junior ya d’auke ta da mari!”

“Allah ya yi maka albarka imam!”
Hajiya mama ta fad’a kafin ta sake kallon Kausar tace”Shegiyar Yarinyar da ba ta san wa yayi mata gata ba!”.
Difff!!! Haka kowa yayi tsit.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin ta ce”Hajiya Mama ki yi hak’uri ki bar ta da halinta she’s not worth your time”

Wani kallo Kausar ta watsawa Ummi wanda hakan yasa Ummin itama ta kafeta da ido kafin tace”
Ko za ki dakeni ne Kausar??
are you worth her time?”

Yassira ce ta matso tace”dakata Ummi ba ma son shishshigi,Allah mun gode maka kaff cikin mu babu wadda ta tab’a guduwa yawon karuwanci…wannan family matter ne dan haka ki ja bakin kki kiyi shiru ki bar Hajiya mama ita za mu iya d’aga mata k’afa….
Kausar is our sister ba za mu zuba miki ido ki taka ta haka ba.”
Yasira ta kora mata warning ta na huci,kasancewar sun d’an samu misunderstanding da Kausar ba shi zai sa ta tsaya ta zuba ido a wulak’antata ba.


Wani wawan Mari Hajiya mama ta yarfawa Yassira cikin
fushi tace”na san uwarki bata baki tarbiyya ba amma ban yi tunanin kin zubar da wadda imam ya baki ba…”
Sai kuma ta juya ta kalli Ummi tace “Ai dama na sani wallahi muddin shegiyar y’ar nan tana cikin gidan nan tou babu batun tarbiyya….”
A hankali a hankali Kausar take shak’ar turaren hannunta ba tare da kowa ya lura ba amma kuma amai ya k’i zuwa..gashi tana gani kamar har taron ya kusan watsewa.
Dai dai nan Yassir wanda sauk’owarsa kenan ya k’araso wajen da hanzari ganinsu carko carko ya kalli Yassira wadda har yanzu take dafe da k’unci tana kallon Hajiya mama yace
“Me ya faru?”

Cikin fushi tace”ka tambayeta!
Na tabbata ko mai zan ce maka cewa za ta yi ba dai dai bane ba,ka san she’s always right.”
Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta haye sama

Kasa ma magana Hajiya mama ta yi tsabar shock kawai
ta tsaya sake da Baki.
Sai kuma ta juya kan Kausar a fusace tace”Wallahi b’oyayyen Ubanki ma bai Isa shiga tsakani na nida jikokina ba!
Imam ja mini ita ka fitar a cikin gidan nan
It’s an order…”


Dasauri Yassir ya shiga tsakanin Imam da Kausar yace”Hold on!” Cikin fushi kafin ya kalli Hajiya mama yace”Nobody is throwing nobody out!
Hajiya mama abunda kike yi fa is too much…tare kika ga mun taso da Kausar tun Yarinta har kawo yanzu,so it will be better for you ki bar ik’irarin korar ta a cikin gidan nan dan za ki janyowa kanki matsala ne!”
Ya fad’i hakan yana me kafeta da manyan idanuwan sa da suke nuna seroiusness d’in maganar da ya gama fad’a.

Cikin tsananin fushi
Hajiya mama tace
“Ok!!!..bari in kira ubanka
wanda na Haifa shi kuma ya haifeka daga nan sai inga shi wa zai zab’a
Ni ko Kausar.
Dan yau ko ni ko ita a cikin gidan nan.”
Tana gama fad’in haka tace
wa Yahansu ta bata wayarta.


Cikin nustuwa Yahanasu ta d’auki wayar ta mik’a
mata a ranta tana adduar Allah Ubangiji ya sa a kori Kausar yau!
Tun ranar da ta shiryawa Yash wannan tarkon ta gama cire duk wani hope na shiryuwa a kan Kausar.
Da wannan tunanin ta mik’awa Hajiya mana wayarta
Ita kuma ta karb’a ta gyara zaman gilashin idanunta ta lalumo number Daddy ta danna call ta d’ago ta kallesu tace”Yassir da Yassira sun janyo mata yau sai ta tafi.”
Dai dai nan Daddy ya amsa kiran cikin bada order tace”ka zo kai da d’an uwanka har da Yashjub duk Ina buk’atar ganinku a k’asa yanzu.”
Daga haka ta kashe wayar.

Tana kashewa su Yasmeen Yadira da Yusra suka matso suka yanyameta suna lallashinta amman fur ta k’i sauraron kowa ta nace ta kafe Itafa Kausar yau sai ta bar gidan d’anta.

Gashi sai tujara take zubawa Kausar d’in harma da Mommy da Baba larai shiyasa cikin fushi Kausar ta matso tace”na ji ya Isa haka zan fita zan tafi,tujarar ta Isa haka.”
Ta k’arashe maganar cikin tsawa!

Zaro ido Hajiya mama ta yi
batasan lokacin da ta yi kan Kausar ta kifa mata marin da ya sa ta tafi za ta fad’i ba
Da sauri cikin fushi Yassir ya yi kanta amma bai yi nasarar rik’eta ba dan sai da ta fad’ kuma fad’uwar ma ruf da ciki shiyasa tsabar takaici b’acin rai da firgicin ganin yadda Kausar d’in ta fad’i a kan cikinta bai san lokacin da ya d’aga
hannu zai kifawa Hajiya mama mari ba!.

Da mugun sauri Junior ya rik’e sa cikin tsananin b’acin rai yace”Are u crazy
Seriously?
Marinta za ka yi?”


Dunk’ule hannu Yassir ya yi jajayen idanunsa
cikin na Hajiya mama
wadda ta shiga tsananin tashin hanali ba na wasa ba.

Da style Kausar ta sake saka hannunta a karo na biyar a kan Hancinta ta shak’i turaren da tun d’azu yake ta taso mata da amai yak’i fitowa aikuwa tashi d’aya wannan karon ya taho
gadan gadan ta shiga shek’awa ba na wasa ba dan sai da ta zauna a wajen tsabar yadda ya taho da k’arfi.




Gaba d’ayan su kanta suka yi kowa hankali a tashe!
Har ta gama babu wanda ya iya cewa uffan!


A hankali Yassir ya durk’usa ya ce”taso mu je sama sannu”
K’asa k’asa yadda babu wanda ya Isa ya ji tace”Yassir ka daina haka mana,kar ka lalata komai.”

Shiruuu yayi,ya d’anyi tunani kafin ya mik’e tsaye ya kalleta
ya kalli aman ya yi shiruuu kawai.
Ahankali Yassira ta matso tace
“Dama ba ki da lafiya??”
Ta yi mata tambayar tana yi
mata wani irin kallon k’urilla wanda duk sai yanzu suka lura da yadda Kausar d’in ta sake kod’ewa ta yi dauu!!.


Da kyar ta iya cewa”lafiya ta k’alau..haka kurum nima na ji aman ya taho mini!”
Maybe na ci wani abun
ne mara dad’i shine ya b’ata mini ciki.”


“Eh kam tabbas…ya b’ata miki ciki indeed!”
Hajiya mama tace kafin ta kalli Junior tace
“Hurry!maza d’auko kit d’inka yanzunnan.”
Sai kuma ta kalli Kausar tace”wallahi ba ki isa kwashe albarkar gidan d’ana a karo na biyu ba!”

Da hanzari Mommy ta matso a d’an rikice tace”Hajiya mama
kar ki damu!
Kince ta fita shikenan za ta fita ba sai su Daddy sun shiga an yi ta case ba.
InshaaAllah zan siya mata gida zan san yadda zan yi da yardar Allah.
Muje Kausar.”
Ta fad’i hakan tana mai kama hannun Kausar.


“Ka ji makira ko!!!
Wato kin riga kin san da batun cikin shiyasa za ki janyeta ku tafi ko?
Tou na chanja shawara!za ta tafi amma sai an aunata an tabbatar yadda zan fi samun hujja akanta… na tabbatar
shi kansa wannan Yaron bai san da cikin da dalilinshiba
duba da yanayin yadda ya shiga shock tashi d’aya.”

Yasmeen ce ta matso tace
“Bara muje in aunata sai a kawo miki result d’in.”

Cikin fushi Hajiya mama tace
“Daga kan Khadijah zuwa kan ya’yan da ta Haifa da Larai duk wanda ya sake mini magana kafin Junior ya d’auko Abu ya gwada Kausar sai ranshi ya yi
mugun mugun b’aci wallahi!
Kun d’auke ni wawiya ko?
A tunanin ku zan yarda da ku ne a kan batun wannan Yarinyar?.
Yau sai asirinta ya sake tonuwa
kowa sai ya fahimta kuma ya gasgata shegen cikin da ta sake kwasowa a karo na ba adadi!!
Karya kawai!!!
kuma kar inga kowa ya bar nan har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login