Showing 12001 words to 15000 words out of 244445 words

Chapter 5 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16425

ya zama waiter as long as zai samu ya kalli fuskarta one more time.


Muryar Manubiya ce ta katseshi jin tana cewa‘’Laa,a’a fa,yanzu ma za mu tafi su Baba kawai muke jira’’

Da sauri Yash ya kalleta yace
‘’Nooo!dan Allah ki kirasa ki ce ya zauna a gida ba sai ya zo ba ai na warke.’’Sai kuma ya juya ya kalli Najeeb
Yace’’ka ga abunda ka janyo ko??’’

Murmushi Najeeb yayi kafin yace ‘’Sorry’’tukunna ya kalli Manubiya yace ‘’ki kirasa ki ce ba sai ya zo ba’’.

Da sauri ta d’ago ta kalli Sir Najeeb d’in tace’’Allah in ma nace kar ya zo ma fad’a zai yi min,ya riga ya gama shiryawa akan zai zo d’in.’’

Dafe kai Najeeb ya yi yad’an fesar da iska kafin ya zaro waya yace’’okay,bari ni
in gwada yi masa magana’’
Yana gama fad’in haka ya koma chan gefe kare da waya a kunne.

Shiruu suka yi kafin chan Yashjub yace’’yanzu duk za ku saka ni jin kunya wallahi
Allah yasa ya hak’ura da zuwan’’

Shiruu Manu ta yi kawai ta sunkuyar da kanta k’asa

Turo baki yayi ya b’ata rai tukunna yace’’yanzunnan a
gaban idona kika gama eye contact da Najeeb,ni kuma kin wani sunkuyar da kai k’asa’’.
Tana shirin yin magana
Sir Najeeb ya dawo ya ce
‘’ai suna bakin gate ma’’


‘’Innalillahi!
Najeeb ka kashe ni’’
Yash ya fad’a kafin ya mik’e tsaye kawai ya na zabgawa Najeeb d’in wata uwar harara.

Bai dad’e da mik’ewa ba
su Baba suka k’araso
Shi da mai sunan baba da ya Nafi’u da ya Musbah da Muhsin waenda suka had’u da su a hanya,ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba ganin yadda Yash ya gaida Baba cikin tsananin girmamawa.
Da kulawa Baba
ya amsa yana mai tambayarsa ya jiki daganan ya yi mishi jaje
da adduar Allah ya kare gaba
kafin ya masa gaisuwa.
Daganan suka gaisa da su Musbah suma suka yi masa
kamar yadda Baba ya masa.

Yash ya dad’e bai had’u da Yaron da ya shiga ransa tashi d’aya kamar Muhsin ba,d’an
sukuti Yaron so chubby gashi fari tass kalar ajebo no 1
dan in ka kalli Muhsin ba za ka tab’a cewa a wahala ya taso ba,yanayin round face d’in shi irin na Manubiya ga
Yaron da ladabi dan sai da ya d’an durk’usa tukunna ya gaida shi,tashi d’aya Yash ya fara addu’ar Allah yasa Manu ta Haifa masa irin wannan wai!!ranar bai san ya zai ji ba,zai iya bada komai nasa dan ya samu ya ga wannan rana.

Har kanshi Yash ya d’an shafa yana tsokanarshi da d’an auta
aka yi dariya mai sunan Baba ma yanata tsalle tsallen shi
Yaran sun burge Yashjub kwarai dan yana matuk’ar son yara.


Manubiya ce ta bawa Baba kujera ya zauna ita kuma ta ja su Muhsin suka koma wajen su Jidda,su ya Musbah suka tsaya a tsaye.

Sun d’an jima suna alhini
kafin Baba ya sanar da Yashjub d’in ‘’ai Daddy ma ya kirasa ya ce yana so za su zo ayi tambaya da abubuwan al’ada
sannan yace d’aurin auren nan da kwana goma za ayi inshaaAllah in an gama daidaita komai.
Yace d’an uwanshi kawai yake jira za su taho daga uk yau
Gobe inshaaAllah za su zo tare’’.


Tsananin murna da kunya ne suka sanya Yash kasa cewa komai,ya sunkuyar da kanshi kawai ya kasa had’a ido da Baba.
Sir Najeeb ne ya ce Allah ya nuna mana Allah ya tabbatar da alkhairi yasa za ‘ayi damu’’.
A tare gaba d’ayansu suka ce ‘’Ameen’’har Yashjub daganan Baba yace’’Allah ya ci gaba da kareka Allah ya k’ara sauk’i,na ji dad’in ganin jikin naka haka,da aka ce ka yi hatsari na firgita sosai amma ganin ka haka ya kwantar min da hankali Allah ya k’ara lafiya
Allah ya ji k’an driver d’inka
Ya ci gaba da tsare ka a duk inda kake’’

Cikin tsananin jin dad’i Yash yace’’Ameen ya rabbi na gode sosai Baba’’

Daga haka suka mik’e suka yi masa sallama suka tafi Yash yana ji kamar ya janyo Manubiya ya rik’eta ta ci gaba da zama da shi…..


Ba su dad’e da tafiya ba likita ya shigo,yana shigowa kuwa Yash ya fara masa mita yana cewa
‘shi dai a sallamesa’,dariya likitan ya yi kafin yace ai na riga na sallameka Yasmeen har ta kira su Daddy ma
allura na zo in yi maka ga kuma discharge papers ka yi signing sai ka dinga zuwa follow up kuma akai akai’’
sai a sannan Yash ya yi murmushi a ranshi yace ‘Alhamdulillah’’
Dan kamar a k’an k’aya haka yake jinsa.

Sai da aka yi masa allura likita ya sake duba hannun tukunna Yash ya yi signing papers ya yi wa likitan godiya ya fita.
Bai jima ba ya aiko wata nurse da sabbin magunguna karb’a kawai Yash d’in ya yi ya d’an dudduba kafin ya ajjiye a gefe ya ci gaba da xaman jiran su Daddy.Yana nan zaune boredom ya ishe sa dan haka ya mik’e ya fita domin ya shak’i fresh air kafin a zo d’aukar sa.

Yana fita waje motar Yassir ta danno kai,dama Yashjub ya san maybe Daddy Yassir d’in zai turo dan yanzu a kaff gidan
kusan shine kad’ai yake zaman banza a yanzu,a take tausayin k’anin nasa ya lullub’e shi,sam ba shi da wani abun yi
gashi shekarunshi sun kusan kaiwa talatin amma ba shi da wani source of income mai k’arfi,shares d’in shi na companyn Daddy kawai garesa wanda a ko da yaushe yake adduar Allah ya taushi zuciyar Daddy ya sa ya k’arawa Yassir wani abun.

A ganinshi ya kamata a k’ara mishi dan bai kamata ace yana namiji wanda anytime from now zai fara tara iyali amman shares d’insa ya kasance dai dai da na mata ba,kuma kullum yana zaman banza.Yasan komai laifin Yassir ne tunda ko company d’insa ma da hannunsa ya lalata,baya san zuwa aiki wani lokacin sai 11 zai ci uban kwalliya ya je
ko cikakken awa biyu ba zai yi ba haka zai fita ya shiga gari.
Amman no matter what haka za su dage su ci gaba da taimakon sa dan hannunka ba ya tab’a rub’ewa ka yanke ka yar.
Yana wannan tunanin Yassir ya yi parking a gaban shi ya fito ya zagayo a ranshi yace’’Mutumin da ya kamata in je visiting grave d’insa shine na zo d’auka daga asibitin zan maidashi gida garau!
Anyways I have better plans for you…..’’

Dakyar ya k’ak’alo wani d’an guntun murmushin yak’e
yace’’hi’’

Murmushi shima Yash d’in yayi
Yace ‘’Follow me’’
daganan ya juya.

Binsa ya yi kamr yadda ya buk’ata,suna zuwa cikin d’akin Yashjub ya k’arasa ya d’auko
takardun da suke cikin jakar computer d’in shi da wani a cikin k’aramin envelope ya
dawo nan kan sofa inda Yassir yake wanda ya nemi waje ya zauna kawai yana binshi da ido .

A tsaye ya tsaya ya mik’a masa takardun,sai da yace’’ungo mana’’
Tukunna Yassir ya janye idanuwanshi a cikin na Yashjub ya maida kan takardun ya sa hannu ya karb’a ya fara duddubawa.
Tashi d’aya ya fahimci na mene ne sai kuma d’ayan takardun mota ne motar da ya dad’e yana ta yiwa Yash d’in nacin ya siya masa…
Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya gama duddubawa kafin
ya ajjiye takardun a gefenshi ya d’ago ya kalleshi yace ‘’What’s the catch??’’

Although Yashjub dama bai yi expecting Yassir ya huce da wuri ba amman
sam bai ji dad’in yadda ya yi ba dan ko d’igon murna bai gani a fuskar Yassir ba.
Kud’in da ya kashe ya siyi motar ba wani abu bane a wajenshi amma wahalar da yasha wajen registering da had’a mishi company d’in nan
ba kad’an bace.Ganin ransa yana shirin b’aci ne yasa yayi saurin cewa ‘’Auxubillahi’’a cikin ranshi
sannan ya fesar da iska ya
mayar da hankalinshi ga Yassir wanda ya tsareshi da dara daran idanuwanshi tun d’azu,cikin sigar lallashi yace
‘’I was wrong Yassir sorry,amman fa still stay away from that girl saboda yanzu haka Daddy ya na zargin ita take kai kanta gareka ne,kar ka
shiga tsakaninsu abun ba zai yi kyau ba,idan kuma ka san son ta kakeyi tsakani da Allah
to ka yi magana a aura maka ita
Munada yarinya mai shekaru 17 a gida inda ace ita taga abunda ni nagani ranar a kai da Munirat mai kake tunani?..
anyways ya riga ya wuce ka yi
laifi pls ka gyara nima kuma na yi laifi
I’m sorry.
Company d’in na yi maka ne saboda inaso inga kaima ka tsaya da k’afafunka,dukda kana b’oyewa but na riga na san abunda yake faruwa a
building d’inka,pls Yassir
Put all your hard work into this new one yakamata ka farka ka fara abunda zai fishsheka.
Sannan motar na siya maka ne
As
Peace offering
ka yi hak’uri akan abunda na yi maka that very day ya kamata ace na fahimci ka riga ka girma.’’
Ya k’arashe maganar yana murmushi

Dakyar Yassir ya samu ya k’ak’alo murmushi shima ya mike tsaye
Hugging Yashjub ya yi kafin yace’’na gode’’

Tapping shoulder d’in shi Yashjub d’in yayi tukunna yace’’We’re good right??’’

‘’Of course we are’’
Yassir d’in ya ce daganan ya cika sa ya sake cewa ‘’na gode’’
Murmushi duk sukayi daga haka suka had’a y’an kayan Yashjub
Yassir ne yakira wata cleaner ta tayashi kai wa mota
Yashjub kuma ya je ya rufe duk wasu bills daganan suka kama hanyar gida.

A motar ma Yashjub hira yayi ta jan Yassir da shi,yana basa
ideas da yadda zai janyo mutane da yadda abubuwa suke da yadda zai fi mishi sauk’in samun income.

A fuska kam ba laifi
Yassir yayi iyakar bakin k’ok’arin shi dan sam bai bari Yashjub ya yi tunanin komai daga gareshi ba amman fa a zuciyarsa ji yake kamar ya mutu…..saboda bashi da shi
shi talaka ne shitakai har Yashjub ya ci mishi mutunci
kuma yake k’ok’arin bribing d’in shi da mota mai tsada.
Sannan shine ma zai nuna mishi yadda zai yi business da ragowar abubuwa wato kenan shi an maida shi ma bai san komai ba.
Shi ya kamata ya zama shi yake rabon kud’i da abubuwan alfarma amman kullum akasin haka ake samu,kullum sai dai Yashjub ya basa ya bawa wasu.
This has to end!!!!!
Dukda Daddy shine sila
amman yafijin haushin Yash
tunda shike da kud’in yanzu
Ya tabbatar inda ace Daddy
bai ci mishi fuska ya fifita Yash tun farko sama da shi ba to da tuni haka ba ta faru ba!da tuni shima yanzu yanada successful company da estates kamr Yash………


Yasmeen tana isa gida direct wajen Mommy ta nufa,tsabar
rashin tunani da tsananin son kai su fa ala dole sai dai a tarwatsa maganar auren gaba d’aya kuma a yi musu farrak’u.


Tana zuwa ta zayyane wa Mommy yadda Yash ya
shanyata a bakin k’ofa tanata uban bugu bayan ya bud’e kuma ya disga ta ya hanata shiga inda yake bayan ya san Manubiya tana ciki kuma tana ji tana ganin komai sannan da k’annen Manubiyan suka zo ya mutunta su ya amsa gaisuwar su da kulawa ita kuma aka barta a tsaye a bakin k’ofa su suka shige ciki

Kamar zata fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda yarinyar take kallon mutane kuwa ‘akan hanci’mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba……MANNUBIYA
(Book 2)
Page 06
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Kamar zata fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda yarinyar take kallon mutane kuwa’akan hanci’mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba,k’annenta ne kawai suka gaishe ni amman ita d’auke kai ta yi ta sake tamke fuska’’

Yusra da suke tunanin yarinya ce itanma yau kam ta bi bayansu dan a lokacin da Yasmeen ta shigo tana d’akin Mommyn a tare ta gansu tana taya ta gyaran wardrobe,sosai itama Yusra ta taya Yasmeen zuga Mommy,dama chan ba son auren suke yi ba,yanzu kuwa ganin Manubiya da kuma abunda Yasmeen d’in take ik’irarin an yi mata shi ya sake tunzura su Yasmeen d’in,a cewarsu ’’sam ba zai yiu su bari Yash ya auro wata chan daban ba gashi tun yanzu k’annenta sun fi su daraja da mutunci a idanun Yash ba ma ita ba,dama irin abunda suke gujewa kenan ga shi an fara tun yanzu in ba haka ba ta ya zai shanya
Yasmeen a waje ya hanata shiga sannan ya dinga wani ririta k’annen so called fiancé d’in sa
Sam bai ma nuna musu wacece Yasmeen d’in ba
ballantana su girmamata.
A gaskiya ba zai yiu su bari Manubiya ta rayu da Yash ba
tunda ya fara haka to akwai babbar matsala a gaba gara kawai a tarwatsa wannan auren a had’a shi da Kausar tunda itace tasu,ta haka ne kuma za su zama d’aya kansu ya had’u da d’an uwansu.’’

Ita Yasmeen wani sabon abunda ya sake d’aga mata
hankalin ma shine ‘yarinyar y’ar gidan talakawa ce’
Saboda yanayin abayoyin Jidda da Siyama da hijabin jikin Manubiyan kad’ai ya isa ya sanya mutum ya fahimci talakawa ne,shikenan ta san akanta zai k’are ita da dangin ta dan yadda yake uban rawar k’afar nan ta san bud’e musu bakin aljihu zai yi ya yi ta b’arin kud’i su tatike komai komai ya koma wajenta,ita kuma ita da su Mommy a ajjiyesu a gefe dan ta lura yarinyar batada kunya sam kuma bata da mutunci tashi d’aya zata raba shi da su.
Haka nan dai kamar za su ari harshe suka yi ta mita su biyu
dan sam Mommy ta ma kasa magana saboda ita duk ba wannan ne abunda ya fi d’aga mata hankalinba dan ta san ta riga ta gama tsarawa indai ta haifu cikin uwarta da ubanta
to Manubiya ba ta isa ta auri Yash ta shigo cikin family d’in ta ba wallahi dan ko hauka take yi ba zata tab’a bari Yash ya auri yarinyar da take tafe da downfall d’in ta ba dan Baba Larai tace ‘’indai har Manubiya ta kasance a tare da Yash to duk wasu sirrinkanta na sama da shekaru talatin da y’an kai sai sun bankad’a a fili kowa ya ji ya gani kuma sai ta shiga masifar da bata tab’a tunani ba’’,sannan bayaga haka indai tana raye to Yashjub bai Isa ya auri wata mace idan ba Kausar ba saboda tasan duk fad’in duniyar nan Kausar d’in ce kawai za ta iya yi mata yadda take so.

Shiyasa ta tsaya tsayin daka ko menene ya kamata to zata yi muddin za ta samu ta hana auren Yash da Yarinyar nan dan ba ta da guri a family d’inta,sai dai kuma idanunta da suka rufe akan raba aure kawai ya kaita ga kasa yin tunani mai zurfi dan kamata ya yi ace ta raba sa da ita har abada tun a karon farko ba wai iyaka aure ba tunda ko babu aure indai suna tare to akwai matsala gashi kuma yanzu Yasmeen ta zo mata da wani zancen na sabon tashin hankali dan ba k’aramin tashi Hankalinta ya yi ba da ta ji
Yasmeen tace’’Yash ya shanyata a waje for more than 30 minutes tana ta knocking sunk’i su bud’e mata da shi da Yarinyar’’
A yadda Yash yake da kud’in nan ta san ba ko wacce irin mace ba ce zai nuna yana buk’ata ta k’i amincewa da shi,ballantana Yarinyar da ta riga ta san ita zai aura nan da kwanakin da basufi goma ba.
Karfa ta je tanata k’ok’arin hana d’aurin Aure aje Yarinya
ta samu ciki kafin ma ta shigo gidan,dan indai ta riga ta samu ciki to komai ya zo musu k’arshe,dan ta zame wa Yash k’arfen k’afa kenan.

‘’Mommy!’’d’in da Yasmeen tace mata ne ya katse mata tunani,firgigit ta yi ta kallesu gaba d’aya su biyun ransu a b’ace hankalinsu a tashe
Yasmeen ta bud’e baki za ta yi magana kenan Mommy ta katseta ta hanyar ce mata ‘’Tashi ki je ki kiramin Baaba Larai,Yusra kema bita ku
turomin ita’’

Wani sanyi Yasmeen ta ji a ranta dan haka ta mik’e ta fice da sauri Yusra ma ta bi bayanta,kamar bayan mintuna
biyar da fitar su Yasmeen Baaba Larai ta shigo,a yadda
su Yasmeen suka fita suka barta a haka ta shigo ta sameta.
Kusa da ita ta nemi waje ta zauna kafin ta ce’’yi hkr,sun sameni ina girki ne,Ummi na tarar za ta yi masa girki wai an sallameshi Yassir ya tafi d’auko shi shine na samu na k’arba da kyar kuwa ta barmun kinsan halinta’’.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace ‘’Kin kammala abunda kika fara ne?’’

‘’Eh!ai shiyasa ma na karb’i girkin’’
Baba Larai ta bata amsa a cikin ranta tana addu’ar ‘’Allah ya taimakesu su samu nasara a kan Yashjub dan abun nasa kamar gado ya yi ko me aka yi masa ko anci sa’a ya kamasa to fa ba ya tasiri kuma baya dad’ewa yake karyewa.’’

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace ‘’Sannu y’ar uwata’’

Sai da Baaba Larai ta gama nazartarta tukunna tace’’mai ya faru kuma?’’
Ta yi mata tambayar tana gyara zama

Sai da Mommy ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace’’Gobe za’a kai kaya ayi tambaya a yi komai Daddy sai shirye shirye yake har yanzu banga alamun fasawa ba,anya Baaba ana yin komai yadda ya kamata kuwa?naga kamar rura wutar ma ake yi.’’

Ahankali Baaba Larai tace’’da izinin Allah za mu yi nasara,inshaaAllah ba za’a d’aura ba,ke dai kawai ki zuba min ido kamar yadda na gaya miki’’

Numfashi Mommy ta fesar kafin tace‘’sai maganata ta biyu,mun yi tunanin yara fa Baaba,mun gaza mu yi lissafi mai kyau,ba mu auna cewa tsaf shaid’an zai iya tunzura Yashjub aje Yarinyar ta samu ciki ba ko da kuwa ba ayi auren ba
kinga kuwa in akwai ciki bamu isa hana aure ba ko da ace ma mun hana d’in to munyi ta banza ne.Na san Yashjub ba shi da neman mata amma akwai shed’an ita kuma yarinyar a nata b’angaren na san a yadda Yashjub yake da kud’i kyau da kwarjini ba ko wacce mace bace za ta k’i amincewa da shi dan in akayi rashin sa’a akaje ba nutsatstsiya bace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login