Showing 1 words to 3000 words out of 244445 words

Chapter 1 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16415

Bismillahirrahmanirrahim

MANNUBIYA
(Book 2)
Page 01
Na
Humayrah Bulama

Daga k’ungiyar Mikiya Writers Association.


Sai da aka fara kiraye kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an Yassir ya samu wani bacci mai d’an karen dad’i ya kwashesa.

Ba dan ya saka alarm d’in 7:30 ba da ba zai ga fitar Yashjub d’in da ya shiryawa gani ba.
Alarm d’in yana fara k’ara ya farka dan bashi da wani nauyin bacci dama, da sauri ya d’auki wayar sa ya kalla ya kashe alarm d’in kafin ya ajjiye ta tukunna ya fad’a toilet…fitsari ya fara yi kafin yayi brush sannan ya fito ya k’arasa jikin windown d’akin ya tsaya.
Sai da ya yi kusan 2 minute a tsaye tukunna Yashjub ya fito..tabbas Yassir ya ji babu dadi a lokacin da yaga Yashjub ya kira driver ya basa makullin motar yace ya tuk’asa su je,da alamun aiki ne a gabanshi birjik dan suna shiga yaga ya baza takardu da computer ya duk’ufa aiki a nan doguwar kujerar bayan inda ya shiga ya zauna.

D’aga kafad’a Yassir yayi ya d’an tab’e baki a ransa yace’’Atleast ka samu Abokin mutuwa’’
Sai da ya ga fitar su tukunna ya koma cikin d’akin ya d’auki airpod d’in sa ya mak’ala a kunne ya kunna kid’a a wayarshi.Wani d’an labule ya d’aga ata gefe guda chan kusurwar d’akin
kayan motsa jikinsa suka baiyyana
tsaki yayi a ranshi yace
‘’Wajen motsa jiki sai kace d’akin b’era!i can’t wait ayi ayi a gama min ginin chan in tartara in koma gidana nima,
I feel suffocated in here!’’.
Daga haka ya fara motsa jikin nasa
ya d’an jima dan a k’alla yayi 30 minutes yana abu d’aya tukunna ya fad’a toilet don ya samu ya watsa ruwa
ko wacce b’ular gashi dake a jikinshi tana mai tsatstsafo da zufa.A band’akin ma sai da ya kwashe sama da mintuna ashirin tukunna ya fito ya shiga goge goge da shafe shafe da feshe feshe,tukunna ya d’auki wasu had’ad’d’u kuma tsadaddun suite masu masifar kyau ya sanyawa jikinsa.
Tsaff ya shirya ya fito tas da shi,ya kuwa yi kyau,longsleeve d’in sa ce kawai fara amma hatta takalminsa da belt da links duk komai bak’ak’e ne.
A gaban madubi ya tsaya yana taje sumar sa wacce takenan tsaf da ita sannan a cike taff bak’ak’irin babu alamar sank’o
ga wani had’ad’den gyaran fuska da ya sha wanda ya tafi
da tsararren sajen sa da gashin baki had’i da d’an tudun gemunshi,kana ganin sumar tasa kaga ta asalin Bahaushe
amman tsabar kud’i da gyaran da take sha yasanya har wani shek’i sumar takeyi mai tsananin kyau da d’aukar hankali.

Kallon kansa yayi a gaban madubi ya sake,tabbas ya san yana da kyau!son kowa k’in wadda ta rasa, a yadda yake da kyan nan Wallahi mace ko da kud’in ta sai da rabon ta,amman wai dukda haka kalli yadda Kausar take gara sa itama wachchar shegiyar Munirat d’in sai wani kakkaucewa takeyi ta k’i ta bada had’in kai ayi a wuce gurin!wallahi ba dan ya kwallafa rai a kanta ba da tuni ya watsar da lamarin ta….

Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo hayaniya a nan saman,bai gama fahimtar su waye ba ya jiyo muryar Yasmeen tana kuka tana cewa’’Mommy!
Ya Yash ne sukayi accident shine doctor d’in ya kirani,wai
yanzun nan aka kai masa su.’’

Wani kalar murmushi Yassir ya saki daga jin zancen Yasmeen,a take wani farin ciki mara misaltuwa ya lullub’e sa,sai da yayi da gaske tukunna dakyar ya samu ya kawar da farin cikin daya baiyyana akan kyakkyawar fuskarshi ya fita a gigice….

Yana fitowa ya tarar da su gaba d’aya kowa ka kalla hankalin sa a tashe yake har su Ummi…….already Daddy ya riga ya tafi office shida Yasira,dan haka suka tura musu message kawai daganan gaba d’ayansu suka d’unguma asibitin da Yasmeen ta gaya musu,dan a yadda hankalinsu yake a tashe
babu wanda zai yarda a tafi a barshi,
Baba Larai ce kawai ta tsaya a cewar Mommy in wani ya dawo sai ta je.

Sai da suka kusan Isa asibitin ma tukunna su Yasmeen suka lura babu Kausar,kowa hankalinshi ba a jikinshi yake ba shiyasa ba su neme ta ba.

A b’angaren Kausar d’in kuwa
duk wannan ife ifen da akayi aka gama ba ta sani ba,har suka fita
Jiya through ko rintsawa bata yi ba shiyasa daff da asuba da taga ciwon kai yana shirin halaka ta ta sha maganin bacci mai tsananin k’arfi.


Suna shiga Asibitin dai dai lokacin likitan ya fito kenan daga inda aka shiga da drivern domin taimakon gaggawa.
Gaba d’ayansu rufar masa sukayi
Yasmeen kuwa bata ma tsaya bi takansa ba ta fad’a cikin d’akin da taga ya fito.

Girgiza kai likitan yayi fuska cike da alhini yace’’i’m sorry!
we couldn’t save him!’’

Diff numfashi kowa ya d’auke
suka ma kasa cewa komai

Wani mahaukacin bugawa zuciyar ta tayi jin likitan yana ci gaba da cewa ‘’amma Yashjub is fine!da ikon Allah
da taimakon seat belt
sannan kuma kasancewarshi a seat d’in baya…ya samu iyaka
gocewar k’ashi a hannunshi na hagu.Amman motar da suka daka itama gaba d’aya mutanen ciki duk sun rasu
Haka shima driver d’insa ya rasu sakamokon buguwar da yayi
da kuma glass d’in da ya chakesa a ciki,we tried our possible best amman we couldn’t save him.’’

Ahankali Yassir wanda ya fara ganin dishi dishi ya matsa kusa da likitan ya dafa kafad’arshi ya ce ‘’Doctor Yashjub Is fine am man s h i ko??’’
Ya yi masa tambayar a rarrabe.

Jinjina kai likitan ya yi kafin ya d’aura da cewa’’yana wanchan d’akin anan muka ajjiye sa dan ya samu ya huta an gama gyara hannun nasa da duk wani abunda ya kamata ayi masa.’’

‘’Alhamdulillah gada d’ayansu suka furta cikin tsananin jin dad’i banda Yassir wanda wata kalar zufa ta shiga tsatstsafowa masa kafin a hankali wani hawaye ya biyo ta idonshi guda d’aya,da sauri ya sunkuyar da kansa k’asa ya sa hannu ya goge ya fara murmushi mai kamar dariya kafin a fili yace ‘’Alhamdulillah!’’
sai kuma ya d’ago ya kalli likitan tukunna yace’’can we see him??’’

‘’Yes,sure!’’likitan ya ce kafin ya kira wata nurse yace ‘’ta nuna musu inda Yashjub yake’’.

daganan ya juya ya koma wajen Yasmeen zuciyarsa taff
cike da mamakin yadda gaba d’ayansu suka nuna halin ko Inkula game da rasuwar drivern Yashjub

Yana shiga ya tarar da Yasmeen ta na waya,da alama da familyn drivern take waya.
Tana gamawa ta kallesa tace
‘’Sir!wallahi na tsorata sosai,ashe ma ba abunda ya samu Yash
Alhamdulillah
bara inje in ganshi.’’

Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace’’am sir….family d’in deceased din suna hanya dan na ji yadda hankalinsu ya tashi a wayar nasan anytime from now za mu iya ganinsu anan’’.
Daga haka ta wuce ta fita.


A d’akin da Yashjub yake suka tarar da Daddy da Yassira
dan office d’insu yafi kusa da asibitin shiyasa suka riga su zuwa,suna shiga Yahanasu ta tafi da gudu ta fad’a jikin Yash ta fashe da wani Irin kuka.

Tun d’azu sai yanzu ya samu
murmushi ya d’an sub’uce masa,ahankali ya d’an yi tapping bayanta alamun lallashi,

Cikin kuka ta d’ago ta shiga
duddubashi tana kallon hannun a hankali tace ‘’Allah ya ci gaba da kare ka a duk inda kake’’

Murmushi yayi yace
‘’Ameen,Allah ya kare mu gaba d’aya’’
Daga haka ya d’aga kai ya fara bin su da kallo d’aya bayan d’aya.
Duk matsowa suka yi suka yanyamesa suka shiga yi mishi sannu.
Yayi mamakin rashin ganin Kausar amman kawai sai ya basar a d’ayan b’angare na zuciyar sa kuma yana mai sake tabbatar da zarginshi akanta.


Kowa waje ya samu ya zauna aka shiga jimami kafin Daddy ya kalli Yahanasu yace’’sun gama duba drivern??’’

Shiruu tayi sai daga baya tukunna ahankali ta girgiza Kai tace’’ya rasu’’

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Yashjub da Daddy suka shiga maimaitawa.

Daga haka d’akin ya yi shiruuu.
Dan rasuwar drivern ta girgiza Yashjub ba kad’an ba.Kasa zama suka yi shi da Daddy sai da suka je suka gansa a lokacin har nurses d’in sun rufesa an toshe kumnuwa da hanci,duk dauriyar Yash sai da yayi hawaye yayi masa addu’a tukunna suka koma d’akin da Yash d’in yake bayan sun ce in iyalin sa sunzo ayi musu magana.

Ko da suka koma d’akin ma
haka aka ci gaba da zaman jigum,kafin Yahanasu da Ummi suka ci gaba da jajanta al’amarin.

gyaran murya Daddy yayi kafin
Yace
‘’Tsautsayi irin haka daman yakan faru a irin wannan lokutan na shiga sabon fagen rayuwa’’

Duk nutsuwa sukayi suna sauraron sa yayinda shi kuma
ya ci gaba da ce wa’’ Na so
dama yau in gaya muku
amman tunda gamu duk anan
Alhamdulillah.InshaaAllah
nan da sati biyu in komai ya tafi daidai ba wata matsala
Za’a d’aura auren Yashjub!
Hajiya Mama ma ta riga ta sani anytime from now in ta gaya wa su Abhi za ku iya ganinsu whar da su
Imam.

Khadija ke da Saddik’a in akwai walima da taron da kuke buk’ata za kuyi sai ku yi min magana in samu in sallameku da wuri.’’


Daddy yana dasa aya cikin
tsananin murna
Munirat tace’’Allah ya sanya alkhairi’’
Ta fad’i hakan fuskarta d’auke da faffad’an murmushi.
Sai kuma tayi shiru da sauri ganin babu wanda yace komai sai ita sannan tsabar yadda da fad’a cikin murna yasanya gaba d’aya muryarta ta cika d’akin.

A b’angaren su Yassira kuwa tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wanda bai shiga tashin hankalin a cikin su ba,sun san da maganar ba wai basu sani ba amman kuma fad’a musu d’in da Daddy ya yi a yanzu ya sanya suka sake tabbatar da dahir d’in maganar shiyasa tashin hankalin da suke a ciki ya sake hauhawa.

Murmushi Ummi tayi tace’’
MashaaAllah Yashjub,na yi matuk’ar farin ciki….dukda bamu da ishashshen lokaci
amman inshaaAllah
za mu zage dantse ayi hidima sosai.Na ji dad’i kwarai
Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya yasa matarka ce har abada har a gidan aljannah’’

Murmushi yayi a hankali yace
‘’Ameen Ummi,nagode.’’
Kafin ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zubasu a kan Mommy
daidai ita ma shi take kallo tana nazartar fara’ar da yake ta zubawa.

Diriricewa tayi dan haka sai tahau kame kame
kafin tace’’ni na ma rasa bakin
magana’’

Shiru Daddy Ummi Munirat da Yashjub sukayi suna tsammanin su ji ta d’aura da wani abun amman sai suka ji tayi shiru
dan haka duk sai aka zuba mata ido.

So take tayi magana amman sam ta kasa tama rasa me za ta ce shiyasa kawai sai tahau wasa da bakin mayafinta kamar wata yarinya.

Girgiza kai kawai Daddy yayi ahankali yace
‘’Hmm’’

Cikin son kawar da situation d’in Ummi tace‘’I know this isn’t the right time
amman yakamata ko zuwa anjima in ka d’an huta sai mu
fara maganar had’a lefe
dan nasan maza ba ku iya zab’ar test d’in da mu mata mukeso ba.
Kayi mana magana sai in taya Momin ka tunda bamu da isheshshen lokaci.’’

Murmushi Yashjub yayi kafin finally ya d’auke idanuwanshi akan Mommy ya mayar kan Ummi tukunna yace’’am..actually Ummi
Yahanasu ce za ta had’a
na ma tambayeta already…’’

Cikin katse shi Yasmeen tace’’ oooh,wato Yahanasu ta riga ta san maganar auren naka ahead of us,ko Yaha??’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai kallon Yahanasu da alamun tambaya.

Wani kallo Yash ya d’ago ya watsa mata wanda yasa ta kawar da kanta gefe

Yahanasu tana shirin yin magana Ya’isha ta sake cewa
‘’Yaha ba ki amsa tambayar Yasmeen ba’’

Sai kuma ta kalli Yash tace‘’I mean no disrespect bu
a ganina
you have like 6 classic sisters
then y choose Yahanasu wadda batasan komai ba?
No offense
but duk mun san bata da wayewar mu bata son shiga mutane ita haka nature d’in ta yake.
Wannan shine biki na farko da za a yi a family d’in nan so I think bai kamata mu bawa kanmu kunya ta ko wacce hanya ba,sam bai kamata a bar Yaha ta je ta ta had’o abun da bai kamata ba salon ta ja mana jin kunya tunda na san itama yarinyar definitely y’ar manya ce.

Anyways I’m already hurt by the fact that’sai da ka fara gaya mata har kuka fara had’a lefe tukunna mu muka sani’
therefore I can’t stay here
bara kawai in wuce tun kafin in je in fad’i wata maganar da za ace na yi rashin kunya!!’’


Shiruu kawai Yashjub yayi ya zubawa Ya’isha ido…ranar da Najeeb ya fito mishi a mutum yace’’Ya’isha batada kunya kullum rashin kunyarta k’aruwa takeyi’’
dukda yasan tsiwa nature d’in ta ne amma sai da ya ji haushin Najeeb.
Yau kam tabbas ya tabbatar
he can’t believe yadda take magana da kuma attitude d’in ta sam ba respect.

Muryar Ummi ce ta katse mishi tunani jin cikin kwantar da murya tana cewa’’Ya’isha waya ce miki ta san maganar kafin ki sani?ai cewa yayi ita yakeso ta had’a kawai bai riga yace ya bata ba,besides ko ta sani ma ai itace Babba kuma naga kmr yafi shak’uwa da ita’’.

Cikin katseta Ya’ishan ta d’aga mata hannu tace’’Ummi Plss’’sannan ta juya ta kalli Yashjub tace’’Allah ya sanya alkhairi
Allah ya baku zaman lafiya
Allah ya baka lafiya’’
Daga haka ta juya ta fita fuuu
kamar zata tashi sama

Tsayawa kawai Yashjub yayi yana kallon inda ta bi ta fita a ransa ya raya’’wato dai yanzu ita bata tsoro ko shakkar kowa’’

Yassir dama neman hanyar fecewa yake yi,dan haka da sauri ya samu ya juya shima ya fice hankalinsa a mugun tashe.


Ajiyar zuciya Yasmeen ta sauk’e kafin itama ta mik’e tace’’nima bara inbi bayan Ya’isha mu tafi tare.’’

Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace’’Ummi plss next time kar ki sake cewa wani wai Yash ya fi shak’uwa da Yahanasu or something like that!saboda
ba haka family d’in nan yake ba,babu banbanci a tsakanin sibling d’in gidan Daddy we re all one and the same
Iyakar fad’an hakan ma da kikayi ya soosa min rai’’
Ahankali ta kalli Yashjub sannan tace’’i hope u can imagine yadda zan ji idan aka yi treating d’ina haka and less important.
Allah ya k’ara sauk’i
Allah ya sanya alkhairi’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fita.

Dafe kai Ummi ta yi tana danasanin kulasa Yasmeen da ta yi yau bayan ta yiwa kanta alk’awarin fita a harkar su har abada
Maybe kawai dan tana cikin farin ciki ne shiyasa ta manta ta biye su
Har ga Allah taji dad’in maganar auren Yashjub,ta san ko wacece yarinyar to tabbbas tana da hankali da tarbiyya dan a yadda Yashjub yake ba zai d’auko musu ballagaza ba da izinin Allah, tun a bakin Daddy take jin labarin Yashjub
da kuma ya dawo ya fara aiki dasu nan ta tabbatar tabbas Yash mutum ne asalin jajirtaccen me hankali wayo nutsuwa neman na kanshi me mutunci kamala da sanin ya kamata………….

…..ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace’’Yash!da gaske suke Yahanasu ta san maganar auren nan kafin su??’’

Lumshe ido yayi ya bud’e kafin yace’’Daddy plss mana….’’

Cikin d’an fushi Daddy yace ‘’tambayar ka nakeyi ka bani amsata kawai!’’

Ahankali Yashjub ya jinjina kai yace’’eh’’

Shiruuu Daddy yayi kafin chan ya kawar da kanshi gefe kawai.


Ahankali Mommy ta matsa inda Yash d’in yake ta dafa kanshi tace’’Allah ya cigaba da kare ka a duk inda kake Allah ya baka sauk’i’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice,hatta Yadira bata ci gaba da zama a d’akin ba dan Mommy tana fita suma duk suka bi bayanta suka fice.
Yassira ce kawai ta tsaya sai Ummi da Munirat da Daddy da Yahanasu.

Ahankali
Yassira ta matso kusa da su tace’’Ya Yash,aure zaka yi,new member zaka kawo mana! tayaya kake tunanin za ta yi respecting d’in mu as your sisters idan kai da kanka ka nuna mata akwai banbanci a tsakaninmu?.
Atleast in mu mata baka gaya mana ba ya kamata ka gayawa Yassir tunda shima Namiji ne kmr kai ya kamata ka fara jan shi a jikin ka.
Mata in-laws d’in gida in aka auro su su suke tarwatsa kan family musamman in suka ga akwai hanya mafi sauk’i da za su bi
Nasan za ka ce wannan k’aramin abu ne amma mu a wajen mu and yadda yanayin rayuwa yake sam wannan ba k’aramin abu baneba.
Kamata yayi in aka fara auratayya mu had’e kawununamu mu yi sticking together kar mu bawa kowa damar shiga tsakaninmu
amman a yadda ka fara nuna wa tun yanzu Yahanasu ce favorite d’in ka ita ka fi so kaf cikimu
To fa idan matar taka ta zo Yahanasu kad’ai za ta ja a jikinta mu kuma ba za ta bamu muhimmanci ba
wanda hakan ba k’aramin issue zai janyo ba.

Dan Allah ka yi considering maganata in kuma na b’ata maka rai ka yi hak’uri amma
dan Allah ko ba komai ka yi k’ok’ari ka gyara tsakaninka da Mommy da Yassir
kafin matar nan ta zo ta fahimci wani abun.
Ka duba fa kaga duk kowa yaji haushi ya fice
Mommy fa ko Allah ya sanya alkhairi bata ce ba ka san maanar hakan kuwa?wallahi no matter what dole sai da albarka ta.
Dan Allah kar ka bari matarka ta fahimci kanada issue da su,na ji na yarda mu ci albarkacinta
ka jawo Yassir jikinka ka dinga nunawa Mommy itace ta haifeka
Plss Ya Yash dan Allah.’’

Ahankali ta juya ta kalli Daddy tace’’Daddy ka sa baki’’.
Daga haka ta juya ta fita itama.


Ganin duk sun fita kuma kamar Daddy yanaso yayi magana da su Yash d’in ne yasa Ummi ta mik’e tace’’akwai abunda kake sha’awar ci?ko in dafa maka komai ma??’’

Murmushi yayi yace
‘’Anything Ummi,tnx’’

Allah ya k’ara sauk’i suka yi mishi daga haka suka juya suka fita itada Munirat.


Suna fita Daddy ya mik’e daga inda yake ya k’araso ya zauna akan kujerar da ta ke kusa da gadon inda Yash yake kishingid’e Yahanasu kuma a zaune.


Shiruu duk suka yi kafin Daddy ya kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa’’Yashjub abunda Yassira ta fad’a gaskiya ne’’

Lumshe ido Yash yayi kafin ya bud’e ahankali yace’’haba
Daddy,kana jin maganar tasu fa kasan kawai shirmen mata ne’’

‘’Koma akwai shirmen mata to gaskiya ta fi yawa a ciki’’
Daddy ya bashi amsa cikin katseshi kafin ya d’aura da cewa’’ba ka kyauta ba!
From today onwards banason ka bada chance d’in da wata zata gane akwai banbanci tsakanin y’an uwanka,inaso ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login