Showing 285001 words to 288000 words out of 299981 words

Chapter 96 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17662

zancewa mutumin da yai watsi dani a cikin duniya tun ina yar karama na bai san cina ba bai san shana ba,
Baidamu da yana da wata ya a rayuwan shi ba ya watsar dani da dan yan shi, ya manta da kowa nashi sai sabbin abokan rayuwan da ya samu,
Haba Aisha inji Baba kowani dan adam da kika gani fa ajizi ne ga Allah don duk kaddaran da zai samu bawa a rubuce yake mai a rayuwan shi,
Wanan tafiyan da yayi kaddararen al,amari gare shi ba makawa sai yayi shi don a rubuce yake mai shi cikin littafin shi,
Ashe ba godiya ya kamata yau kiwa Allah ba da ya kadara akwai robon kara saduwa a tsakanin ku,
Don haka maza ki tarbi mahaifinki kada ki sakawa kanki tsanar shi har ki dawo kina da kin sani daga baya don haka ba halin mumuminai bane,
Bai tafi ya barki don bai kaunarki ba Aisha yatafi ne akan kaddaran Ubangijin shi,
Kukan da nakeyi harda dayan mutumin yana bani hakkuri cikin harshe da nuna hannun shi,
Fita daga zauren baba yayi ya barni zaune da mahaifina shima mutumin sai ya mike yafita zuwa gurin driver su,
Inda nake zaune Abba ya taso yazo ya zauna ya dan dafani yana cewa haba Aisha nasan cewa ban kyauta maki ba na tafi na barki a cikin wahalan rayuwa ke da mahaifiyar ki,
Sai dai ki sani hakan ba,wai yana nuna na manta da ke bane a,rayuwana ko abinci zanci sai kun fado min arai ina tunanen ko yanzu a wani irin hali kuke ciki a inda kuke ko kuma kina inane yanzu,
Sai yai shiru jin da nayi baiyi magana,ba yasani dago kaina hawayene naga suna zubo mashi daga idanuwan shi,
Hada ido mukayi yace cikin kuka Aisha ki yafe min don Allah don nasan ban kyauta,wa rayuwan ki ba don nasan kin fuskanci kalubalun rayuwa iri iri a tare dake,
Tausayi yabani nace Abba na yafe maka don nice yakamata na,roke ka don sai nake ganin laifin Ummina ne yashafeni a gareka,
Yace cikin girgiza kai ko daya ni Uwarki batai min komai ba don yar uwatace halal malal, don may zan kufule ta a raina,. Haka dai Allah ya tsaro muna rayuwan mu,
A hankali nafara fada mashi irin abubuwan da na fuskanta da bai nan da kudaden dasu Baba na yan uwan shi suka bani a bayan shi da kuma taimakon da kulawan da nasamu a gurin shi,
Yace to Alhamdullahi dama abinda na matsu naji kenan kafin na isa gare su naji wani irin kulawa kika,samu a gudin su,
Don nasan yadda zan isa gare su dalilin da yasa banje gurin su ba sai na iso inda kike naji komai daga bakin ki,
Yace Aisha na dago kai yanzu mijinki nake son gani amma kafin ya iso ina so ki fada min duk matsalokin sai na san irin taimakon da zan maki ke kuma,
Nace Abba ni banda matsalar komai don Hamza yana kokarin shi dani yace nagani kuma nasani don gashi har yakai mahaifiyarki da mijin ta saudiya sun sauke farali hakan ma kawai ya isar min da nasan yana kokari a kanki,
To amma yanzu da kika bar gidan ki ka dawo nan kina ganin hakan shine alheri a gareki don ni ban son na saka bakina a wanan zancen don malam Mudi yai min duk yadda akeyi kinga idan nazo nasa baki a matsalarki nai mashi butulci sosai,
Ban yi magana ba sai gasu Jidd mama ta kawo su don suka mahaifina suna shigowa sukayo kaina da murnan su suka fada a jikina suna cewa mama, mama mu ba zamu koma gidan batare da ke ba,
Ban yi magana ba sai nuna masu Abba da nayi inacewa a gaida babana nima, gashi,
Juyawa sukayi sina kallon shi sai Jidda ce tace wanan ai ba babanki bane Baban gona,
Yai murmushi yace masu ni ba Baban gona bane baban mama ne ni Jidda tace ba kai bane baban mama ba fa ban gona ne Baban ta,
Nan ya dan fara jan ta da dan hira a hankali har suka dan fara sake jiki dashi suna bashi amsa cikin nuna jin dadi
Sun gaisa da mama nake fada mashi yadda suke da Hamza ya kaea gaishe ta a cikin mutunci ,
Sun dan yi hira tana tambayan shi iyalinshi yake fada mata duk suna lafiya suna gaisu ma,
Sai an kwana biyune zai zo da su suga gid shi ya fara zuwa ya nemi yafiyan yan uwa tukun,.
Mutane sai zuwa suke suna gaida shi yana kuma masu abin arzki take labari ya yadu a uguwa, lokaci guda,
Mama Rahana tazo sun dauki lokaci suna hira yaushe rabo a tsakanin su,
Sai yamma kis suka bar mu yace a sokoto yake son su kwana da safe zai karasa gida gurin yan uwan shi,
Kudi masu yawa ya barmin yana cewa sai ya dawo zai ganni mu karasa maganan mu dashi,
Ya tafi cikin farin ciki a ranshi inda suka,gama ganawa da hamza ya kama hanya sai Burkusuma,

****** ********* ******
Da dare ya isa garin don haka ba kowane yasan da shigowan shi garin ba,
K9fan gidan su ya tsaya da motan shi inda yafito lokacin Baba Liman yana zaune yana karatu a zauren shi kamar kullun,
Sallaman da yaji yasa shi dago kan shi sai ido biyu yayi da dan uwan shi duk da dare ne bai hana shi gane Abban ba a lokacin, yace, BELLO kaine ko mafarki nakeyi haka ne wai,
Murmushi Abba yayi yace nine yaya ba mafarki kakeyi ba nine a gaban ka,
Rugumay Abba yayi a jikin shi yake cewa Allah na gode maka da ka nuna min wanan ranan dana dade ina jira a rayuwa na,
Jan shi yayi zuwa cikin gida yana fadin ina mutanen gidan nan ku fito yau ga BELLO ALLAH ya dawo muna dashi lafiya cikin mu,
Babba da yaro na gidan sai faman tururuwan fitowa sukeyi don ganin abinda baba Liman ke fadi in gaskiya ne,
Kuka murna da shewa shi kawai ke tashi a gidan don murna da farin ciki a zuka tan su,
Duk da dare bai hana mutane na kusa da nisa fitowa daga gida jen su ba don ganin shi duk wanda yazo tun awaje da sunga motocin Abba da security din da yazo dasu sai mamaki ya kama su, su shiga cikin gida don ganin shi ranan zakace ba dare ba ne a lokacin,
Sai da mutane suka dan tsagaita shigowa don Baba Liman yace a bari har da,safe kowa ya tafi gidan shi, don dare yayi sosai a lokacin,
Kwana raye sukayi da yan uwa yana basu labarin bayan rabuwan su inda yace, lokacin da nabar gida da farko kasar Niger na shiga na kai wata uku a damagaran sai na hadu da wasu turawan faransa da nake wa aikin kula da dawakai da rakuma,
Da zasu tafine suka taya min idan zan bisu zusa kasan su banki ba sai nai kasadan bin su can din,
Shekara na Ukku a tare dasu sai maigidan nawa ya yarda da zamana dashi,
Shike turani fatauci a nan kasa shen Afrika ina mashi business din motoci da sauran abubuwa bayan karatun da yasani na ci gaba na zamani,
Sannu Sannu har aka sanni a kasashen da nake zuwa nima idan zamu shigo sai na fara nawa san,an shigo da wayoyi da computers, da sauran kayan naororin wuta,
Ganin nawa business din yafara karbuwa sosai yasa shi bani kudi masu yawa wanda ban taba zaton zan taba samun irin su ba a duniya,
Ba adade ba Allah yai mai rasuwa shine na kwaso nadawo kasan Ivory cost da zama inda nan ne ake shigo muna da kayan mu daga waje,
Sai Allah yasa min albarka shine har ya kaini ga haka na samu nawa nakai wanan matsayin,
Nayi aure a can na auri wata yarinya da,namu yazo daya yanzun haka muna da yara biyu da ita matar tawa ,
Zan kawo su suga gida idan hankali ya kwanta dama nazo ne nafara ganin gida don Fatima da muka hadu a,saudiya ta fada min nabarku har yanzu a cikin damuwan rashin ganina da bakuyi ba,
Ina fatan zaku yafe min akan irin halun tashin hankali da damuwar da na barku a cikin shi,
Sai da,na,fara zuwa gurin su Fatima din don mijin Aisha cikin rashin sani abokin kasuwanci nane a can,
Aishan tafada min irin alherin da kulawan da kuke mata a bayana banda abinda zance sai dai na gode maku da irin wanan kokarin da kukai min a bayana don nasan koda mutuwa nayi ina da yan uwan da nabari masu halarci da alheri a rayuwan su,
Sai washe gari kofan gidan ya kara cika da jama,a yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke suna taya shi murna,
Sai yamma lis ya koma garin sokoto don ya samu masauki da mutanen shi,

Hamza yana zuwa gidan shi yaga duk gidan ya koma mashi bakikirin bai ko jin dadin gidan gabs daya a ranshi,
Kofan dakina ya dan tsurawa idanu zuwa wani dan lokaci sai ya nisa da kyat yaja kafan shi zuwa dakin shi,
Gado ya fada ko takalman kafan shi bai cire ba sai tunane yake barkatai,
Yasan da ina gidan yadawo haka da gajiya da yanzu dani da yara muna nan muna mashi oyoyo da taro mai daraja,
Amma yau gashi shi kadai a cikin gidan ba motsin kowa a gidan sai yaji gidan ya koma mai kaman makabarta,
A hankali ya bude idanuwan shi da suke a rufe ya furzo iska mai zafi yana fadin haba Umma may nai maki haka kika yanke min farin ciki a rayuwana,
Rayuwan mu ya tuna da irin gwagwalmayan da akasha a lokacin da Lima ta daure shi da asirin ta,
Duk irin kokari da halarcin da Aisha tayi bata guje mashi ba amma Umma bata gani,
Yasan da itace akai wa yar ta haka da tuni ta raba wanan auren ko tuntuni,
Sadiya kuma da ta tilasta mashi ya aure ta itama tazo da nata kalan iskancin har tayi tagama ba,a ji shi da Aisha ba sai,
Zuwan Biba duk Umma batai saduda ba takara kawo mai wani sabon rikici mai muni,
Abin kunya wai ace uwar shi ce tai wanan kalaman haka akan zurian shi shi ko kadan baiga laifin iyayyen Aisha da ita ba gurin dauka mataki haka,
Amna gaskiya indai shine zaice ya saki Aisha gaskiya ba,a bakin shi ba kan sai dai in duniya zata hade ne amma bai sakin Aisha gaskiya,
Saki saki fa yace ina ai gara na mutu da ace na saki Aisha a rayuwana in na saketa na zauna dawa a gidana,
Dunkulewa yayi guri guda kaman mai jin sanyi yana tausayin kan shi da iyalin shi da Umma ta jefa a wani hali,
Yasan duk inda Aisha take itama tana can tana zaman hakkuri ne saboda yasan tana son shi da zuciya daya har cikin ran ta,,
Amma ga Umma nason ta kawo masu shamaki a tsakanin su ta raba abinda Allah ya hada a halarci,
Ya kai wani lokaci a haka kwance cijin matsanacin tunane sai dai ya kasa kai ga mafita har lokacin,
Da kyat ya tashi yai sallah shafai da wuturi yana kokarin komawa barci bayan ya dauki lokaci yana addu,a sai kuma yaji cikin shi na son cin dan wani abu,
Kitchen din gidan ya shiga komai tsab a kitchen din nawa sai dai yarasa mai zai dafa yaci komawa yayi falo ya dauki wayan shi ya kira Ibrahim din shi ,
Kira daya gana biyu ya dauki wayan yana cewa ko ka dawo ne yaya ?
Murya a kasalance ya amsa mashi da,eh don Allah ka sayo min kaza abincin kowa mai zafi sosai da drinks na kwali mai sanyi,
Ba a dauki lokaci ba Ibrahim ya shigo gidan ya samay shi zaune saman kujera yana saye da wani riga mai hannu guntu da wandon rigar tree quarter,
Kallo daya yai mashi ya gane cewa yana cikin damuwa tausayin dan uwan shi ne ya kamashi lokaci guda,
Gaisawa sukayi ya aje mashi abincin daya kawo mashi yake cewa ashe ka iso ko,
Yace eh tun kafin magariba ai ina garin nadan tsaya ne yin wani abu,
Ibrahim yace gashi kuma kun sha banban da mahaifin Aisha don yazo yau amma yatafi garin su akace,
Yai dan guntun murmushi yace ai muna tare dashi dama na tafi shigo da wasu motocine da ya turo har da na ita Aisha cikin motocin,
Ikon Allah Aisha ya sayawa mota ya tambaya cikin fara,ar shi yace don yasai mata mota may akayi bafa karamin mutum bane yadda kake tsanmani ba ita kadai ba inajin harda wasu yan uwan shi don mota biyar ya turo ashigo mai dasu sune costume suka kama su,
Sun dauki lokaci suna hira duk Ibrahim yanayi ne don ya kawar mai da damuwan shi,
Ibrahim yace amma dai kunyi magana akan zancen Aishan da shi kuwa,
Dan tsuki Hanza yaja yace ba abinda zai iya don ba a wurin shi take ba don haka bai sa kan shi a zancen ba,
Yaya zancen naka auren Hamza ya tambaye shi sai Ibrahim yace ku ake jira kuje sai a saka rana da lokaci,
Ok zanyi kokarin na shirya zuwan su Baba kafin na koma don yanzu zancen gidan da nake son sama muna a kaduna ne yake gabana,
Hamza yace amma bazaka zauna gida ba a gurin Umma dai ko don ina gudun abinda ya faru da ni yafaru a kan ka don abin na Umma a jinin ta yake,
Don sai nake rasa may Aisha taiwa Umma ne haka a,rayuwa karshe dai ban gano komai ba sai naga kamar bata son taga mace ta rabe ni ne kawai,
Don kaga ba wai da Aisha kawai Umma take adawa ba har Sadiya da Biba da na zauna dasu akwai matsala a tsakani,
Ibrahim yace ni na dade da sanin haka,wallahi yaya ina dai tsoron nai magana ne inja zagi gurin ta,
To mau yakawo wanan hakane wai don gaskiya na rasa may Aisha take mata ta tsaneta haka sai nagane don kawai taki rabuwa dani ne kawai,
To Allah ya kyauta don shine matsalar kawai, in bashi ba ni dai banga wani matsala daga gurin Aisha ba wallahi,
Sun dauki lokaci suna tataunawa har sai da dare yayi yai mashi sallama yatafi cikin tausaya mashi,,

Da labarin zuwan mahaifina ya riski Umma da farko tace karyane sai da su Sa,a suke ce mata kamana da mahaifina har kamar ta baci wallahi, don kamar an tsaga kara ne,
Nan suke bata labarin irin shigar sa da kuma motar da yazo da ita,
Bata kara gaskan tawa ba sai da taga kudin da Abbana yaba su Jidda a gurin mama yakai dubu dari sabbi dal dasu,
Ido ga kudi sai ta rude ta na cewa ikon Allah ashe kuwa ba karamin mutum bane dai don wa zai iya ba mutum kudi haka masu yawa,
Nan tafaracyan sake sake a ranta yadda itama zata kwanta a ci arziki da ita batare da wata matsala ba,
Ta so mama ta bata kudin amma sai mama tace sai Hamza yazo an gwada mashi kudin tukun ,
A ran ta tace lalai tayi sakaci sosai don da bata sake ba taja jikokinta a jikin ta da dole kudin nan a hannun ta zasu zo,
Tace na samu kudin nan haka ai sai kawai na sayowa autana kayan dakin da bamu saya ba dasu,
Amma ai sai na samu ko yayane sai kuma tafara jin haushin mama wai itace ma da shegen shishigi tsiya wallahi duk ta shigewa wanan yar Agwi din mai kama da uban ta,
Muna nan da,safe sai ga Sa,a datu wai Umma tace tazo ta dauki tagwaye tana son ganin su,
Ummina da su mama saude sukace ace suna barci baza a samu kawo su ba sai dai ayi hakkuri,
Maimakon ta fita,sai ta dan tsaya taji Atika tana cewa baza a kaisu ba ta shafa masu mugun abu su ga yara sun gi bulbul a lalata masu rayuwan su,
Tana zuwa ta samu Umma da mama sai tace masu Umma sai da nace maki ba zan tafi ba kika matsa min gashi kinji abinda suka ce,
Nan Umma ta hau fada tana cewa ko dai anki ko ansi dole ace jikokina ne su don ba,a taba raba anta da jini,
Yanzu anga ci yazo shine Atika take nuna ita ta kwarai ne ko ina nan take wanko kafan ta ta,shigo gidan nan da gulma akan Fatima da yar ta,
Yanzu tasan tana son su zanje na samay ta a yi tsiyan da take son ayi yau,
Mama tace wallahi yaya na raba ki ana kokarin ganin an shirya a tsakani kina son zuwa tayar da wani balli kuma,
Dama aikowa yasan akanki Aisha tabar gidan mijin ta bawai basu son junan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login