Showing 282001 words to 285000 words out of 299981 words

Chapter 95 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17631

haka ,
Gaskiya anzo karshe don ni inda miyon bakina zata koma badai gidan nan ba,
Bafa ban son ta bane na kyale duk wani cin fuska da ake mata ina son abina nima don haks taje ta rike dan ta ita kuma Allah ya bata wani ba shi ke nan ba, amma gaskiya bata komawa gidan nan ,
Mama taita ba Ummi hakkuri karshe ma dakin ta bar mata alamar bazata ma ji hakkurin ta ba,
Haka mama tai muna sallama da fuwan ya dan tsagaita kadan takoma gida dakin Umma take tai mata tas tace yau dai kin kai ga yadda kike son don sun karbi yar su suma kuma sunce badai gidan nan ba, kuma,
Magana masu zafi da tsuma zuciya ta fadawa Umma din sai da tai kuka sosai tace ni wanan yarinyar tagama dani hausatu,
Wallahi sheri taimin akan may zanki jini na tace ai duniya duk sun san baki kaunan su yaya kin taba jan yaro ko daya a jikin ki harda sanan yarinyar da aka sakawa sunan ki babu duwanki da ala,amarinta,
Haba yaya yaran nan ma ai sunyi kokari wallahi in badon iyayyen nata suna da kawaici ba aida tun tuni sun raba wanan auren ko,
Hankalin Umma yai matukar tashi sosai wanan ne karo na farko da tai matukar na dama da wanan bakin akidan da take gwadawa a kaina,

****** ********* ******
Waahegari tin da safe ya tashi bayan yai sallah bai kara kwantawa ba yana zaune a falo shi kadai sai faman tunane yake barkatai a ran shi,
Duk abin duniya ya damay shi ya kulla wanan ya kwance Jidda ce tafara tashi daga barci, Allah ya taimake shi yaran suna hutu a lokacin,
Tana fito ta fada jikin shi tana cewa Daddy ina maman mu ta tafi ne da twins din ta a kaimu gurin maman mu daddy please zan je gurin maman mu ne ni,
Bugun kofan da ake da karfi yasa shi tashi a fusace ya fita don a zaton shi su Biba ne yai masu rashin mutunci,
Sai ganin mama yayi da Umma da Ibrahim jayewa yayi yabar masu kofan suka shige,
Suna zama Jidda takara cewa, daddy please ka kaini gurin mamana sun tafi ita da anty Madina sun bar mu da twins din ta,
Gaisawa suka farayi mama na cewa zonan kin ji mutumiya na zan kaiki gurin mamaki anjima kadan, kinji,
Nan mama tana rike da hannun Jidd take cewa tau Hamza gamu munzo gare ka da yaya don yaya tace wallahi magana maka mancin wanan bai taba hadata da wanan yarinyar ba, ita,
Murmushi yayi yace mama ni mai zance yanzu Umma fa uwatace banda wanda yafi a zuciyana a duniyan nan kuma banga ma wanda zaifita ba a gareni,
Amma tunda haka ta zabar ma rayuwa ko yaushe tagani a cikin garari da tashin hankali a tare dani ai shike nan,
Yanzun dai Aisha tabar muna gidan sai a auro min wance hankalin ta ya kwanta da ita na zauna da ita,
Din iyayyen Aisha hakkurin su ya kare kinga ba abinda ya saura kuma,
Sai lokacin Umma tai magana tace zaman ta bai kare ba a gidan nan kuma ba zai kare ba sai ranan da babu dayan ku,
In ta tafi ina zata bar yaran ta da gidan ta dole ta dawo dakin ta don yanzu anzama daya,
Ita kuma wanan yarinyar na barta ga Allah don shine shedun tsakani na da ita idan na taba mata maka mancin wanan magana a,rayuwana,
A hankali Hamza yace ai tunda ta tafi yara zaman su dole ya dawo garesu tunda wa zan kai masu inbaku ba ,
Biban da kike so ko yarta bata iya rikewa balle na wani don haka bazan bar yarana a gurin ta ba,
Mama tace ni yanzu ba wanan ba don Allah a bar zancen muyi magana akan dawowan Aisha kawai don uwarta ta hau fiye da tsanmanin ku don jiya ma dakin ta bar min,
Nan sukai ta magana akan irin hakkurina dakuma kyautatawan da nake masu amna duk Umma baki gani gashi yau har su da kan su iyayyen ta sunzo sun dauki yar su wai a kanki haba Umma yaya kike son muyi da rayuwan mu ne wai,
Umma dai shiru tayi don zafin da take ji a ran ta Ibrahim yaci gaba dacewa yanzu kai yaya muje mu samu Baba mudi sai mu bashi hakkuri tadawo dakin ta,
Yace cikin murmyshin dole Ibrahim da wani ido zan iya kallon wanan bawan Allah,
Tun fa muna yara ba mutumin da ya damu da damuwar mu kamar wanan bawan Allah,
Umma ke kin sani don halarci ne fa aka bani Aisha ba wai don nakai na aureta ba alokacin amma suka rufa muna asiri suka bani ita don halarci kuma uwarta bata ja da hukuncin shi,
Yaya zan iya fuskantashi yau ace wai na kasa rike amanan da ya bani wai ma mahaifiyata ce da matsalar gaskiya ina jin nauyi da kunya wallahi,
Ibrahim yace in haka yanzu dole naje na samu su Baba Madu da magana don aje bikon ta tadawo,
Umma tace ku dai je ku gwada ku gani ai zai yarda shi mudin ba,sai maganan nan tafita waje ba,
Kallon Umma sukayi gaba dayan su da mamaki don sun gane bata son zancen yafita ke nan waje saboda baba Madu zasuyi mata rashin mutunci sosai kan zancen,
Tace kai hamza hakkuri zakayi kaje ku gan shi don a sasanta a gida,
Baida yadda zaiyi don yana son su rabu lafiya da ita yace tau shike nan zanyi wanka sai mu tafi,
Mimi tafito daga daki da gigin barci tana fadin mama mama ta nufi kofan dakina tana bugawa don in bude mata,
Mama ce ta jasu zuwa dayan dakin don tai masu wanka nan taga kayan yaran da na aje a saman gado,
Tai masu wanka ta shirya su tafito tana cewa, nasan ko abin kari babu ke nan yace Ibrahim yazo ya samo masu abinda zasuci kawai,
Mama tace barin shiga na hada don kowa ma,ai bai karya ba nake gani kitchen tafada tafa hada masu breakfast,
Sallama akayi daga waje Ibrahim ne yaje don yaga ko wanene mahaifin Biba ne da kan shi yazo gidan,
Fita Hamza yayi suka gaisa sai yake cewa jiya nadawo na samu habiba a gida take cewa wai kace tazo gida ,haka kawai ba,wani fitina,
Yace hakane Baba ni nace ta tafi don yar uwarta ma tana gidan su kowa yaje gida ya huta, don gaskiya zan iyacewa tun shigowan ta gidan nan ban taba samun kwanciyan hakali a gurin taba,
Sai hakkuri nake saboda darajan ku kawai yanzu Baba har yakai Biba ta daga hannu ta mari mahaifiya don rashin tarbiya,
Subbahanallahi dattijon yace ita habiban ta mari mahaifiyan ka yace kwari kuwa baba kuma duk ta bata mata jiki da kwalaben da ta rotsa mata a jiki,
Nan dai ya fada mashi duk irin abinda takeyi da tashigo gidan yakare da cewa gaskiya bazan iya ba ta kaini karshe wallahi,
Dattijon yace lalai kana da gaskiyan ka wallahi aima ka raga mata da shegiya kai mata dukan tsiya don nasan rashin kunyan habiba zata iya fiye da haka wallahi,
Amma kayi hakkuri don Allah tunda kace don mu kake hakkuri da ita ni hakkuri zan baka kati hakkuri za,a tsawata mata insha Allahu zata bari,
Hamza yai murmushi yace Baba ku barta kawai ai anzo karshe bazan iya daga ido na kalli Biba har na zauna da ita ba kuma a matsayin matana, irin abin da tai min,,
Nan dai dattijon ya ci gaba da bashi hakkuri ya tausan zuciyar shi sukai sallama yatafi da bacin rai,
Suna shiga gida wanka ya fada, yafito inda ya samu mama ta hada masu abin karyawa ko,
Umma sai kamay kamay take tana jan yaran da hira amma sunki sake jiki da ita, sai cewa suke Daddy ka kaimu gurin maman mu please,
Umma nacewa kuzo maman ku ta tafi uguwa anjima zata dawo kunji suke sai makewa suke basu yarda da ita,
Ibrahim yace Umma ki barsu kawai don basu sba dake ba indai Aliyun zarah ne su kan sun san ko sosai don sune jikokin ki,
Kai Ibrahim wallahi ka shiga hankalinka kada na bata maka rai don naga kana son raina min hankali,
Kabari in ka haifi naka ka hana su mamayni din tunda naga kana daniyan haka kaji min dan neman yaro mara hankali kawai,
Hamza yana gamawa ya mike yana cewa Ibrahim su tafi, din gidan Baba mudi su gan shi,
Sun yi sa a sin samay shi a kofan gidan shi zaifita sai dai ganin su ya sa shi tsayawa suka gaisa yace su shigo daga cikin zauren shi,
A saman tabarma suka zauna gaba dayan su inda suka kara gaishe shi a cikin ladabi,
Sai dan shiru ne ya biyo baya kadan shi Hamza din ne ya kawar da shirun yana cewa Baba dama mun zo ne akan zancen Aisha ayi hakkuri ta koma dakin ta tunda ba fada mu kayi da ita ba,
Baba yai dan murmushi yake yace ni Hamza a rayuwana ba kai min komai ba wallahi sai ma ince nagode kwarai da rikon da kaiwa Aisha,
Amma matsalar tana ga mahaifiyar ka don bazan yarda ya ta takoma gidan ka ba mahaifiyarta tana gwada mata sanan bakar tsana haka,
Yau har abin ya tashi a kan ta ita kadai ya koma ga zurian ta da kai,
Don haka don Allah ka koma kaje kayi hakkuri kayi biyayya ga mahaifiyar ka ka zauna da wace uwarka ke son gani a gidan ka,
Saboda haka kuyi hakkuri ku koma don yanzun ba abinda zan iyayi don ko uwar yarinyar naga ya hau sosai itma wanan karon don haka ayi hakkuri kawai da wanan zancen in Allah yaraya yaran sun isa yayye sai acire su a nono adawo maka dasu duk ku rike tunda badasu nabaka ita ba,
Baba don Allah ayi hakuri hakan ba zai kara faruwa ba insha Allahu inji Hamza wanda ke ji kamar ya fada a wuta don bakin ciki da tashin hankali,
Baba yace hamza na fada maka,wallahi kai bakai muna komai ba halin mahaifiyar kane dai bai muna ba gaskiya ayi hakkuri,
Shiru zauren yayi kaman babu kowa a cikin zauren saboda kowa da abinda zuciyar shi ke saka mai,
Babane ya kawar da shirun da cewa aiko mahaufita yazo ya samay ta a cikin wanan hakin zai ga ban wa yar shi adalci ba na bayar da ita inda ake gallaza mashi ya ne kawai,
Nan dai yabasu hakkuri tare da basu magana suka tafi gwiwa ba karci rai a bace,
Bai koma gida ba yace Ibrahim ya wuce dashi wani guri don yaga wani abokin shi,
Nan yabar shi yadawo gurin su Umma ya fada masu duk yadda sukayi da Baba Mudi din,
Wasa wasa karamar magana ta zama babba don Ummi ta kekashe kasa tace bani komawa gidan hamza,
Hankalin shi yai matukar tashi sosai don bai zaci abin zai kai haka ba sai ga wankin hula na son kaishi dare,
Ana wanan rikici shi kuma yana kokarin samun gida a Kaduna don yace can zai mayar da iyalin shi gaba daya, yafi mai hankali kwance,
Ga matsin da yake samu daga gurin iyayyen biba sun sashi gaba da bada hakkuri,
Shi kuma ya tsaya a bakan ba zai mayar da ita gidan shi ba yagaji tafita daga ran shi yace masu,
Nikan tun zancen yarana yana damuna arai har Ummi tagane wani dare tai min tas don haka na fitar da zancen su a raina na sake jikina,
Dafarko sai suka tsiri kawo su wai sunzo ganina amma sai Ummi tai masu kashedin kada,akara kawo su abarsu su saba da Umma,
Wanan abin ya taba ran hamza sosai don ranan da yaji har da kuka saida yayi da hawayen shi yabar gidan Umma,

****** ********* ******
Tunda Hamza yai tafiya bai dawo ba yau kusan sati uku baya garin ina gidan mu abina na kwantar da hankalina na fitar da komai a raina,
Ranan wata laraba mukaji ance wai ana wa baba sallama Atika tace baba bai nan sai ga yaron yadawo yace wai ance Fatima tana nan,
Aka ce yaron yaje yace waye ina jin haka kwance nake ina ba hassan nono, na mike zaune ina mamakin wanda zai ce a sallamo mashi Ummi,
Sai muryan yaron naji yana cewa wai ance Bello ne daga Burkusu ma,
Zubur na mike, tsaye na zari hijjab dina na zuwa waje da sauri na, wani High lender nagani bak wul a waje gidan mu sai dai ba,a ganin wanda ke cikin motar sai dai na ciki ya gan ka,
A hankali akafara bude kofar motar nacikin motar ya sako kafan shi takalman shi kawai mutum zai gani ya fahinci wanda ke cikin motan ba karamin mutum bane,
Ina tsaye na zurawa motar ido na kagara na ga ko waye a cikin motar,,,,, ,,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,


Fari ne sol ya bude motar a hankali yafito ga ba daya mutanen dake uguwar hankalin su, ya dawo ga motar da mutanen cikin motan,
Ina tsaye, kinkyam.na zurawa mai fitowa daga motar ido ina mashi kallon kurullah,
Kallo daya zakai mai shi kasan cewa naira ta zaunu daram a gurin daga motar har shi kan shi zuwa suturorin shi baki daya,
Daga inda nake a tsaye mutanen shiya sun tsuro min idanuwan su, suna muna kallon mamaki da kyat na iya bude bakina nace Abbana,
Cikin murmushi ya ware hannayen shi tare da nuna ni ya cewa Aisha ko ?
Haba da sauri na nufe shi cikin wani murya nace Abbana Innalillahi wa,inna alaihim rajjiun wallahi kamar mu daya da Abbana don fari ne sol ga bakin suma a kan shi wululk, kamar bunzun kasar Niger,
Kamshin turaren shi duk ya kamsashe uguwa a lokaci guda wata irin shadda ce milk a jikin sai maiko takeyi don buguwa,
Rugumay ni Abba yayi tsab a jikin shi yana sauke numfashi a hankali cikin nuna jin dasin shi,
Yadan dago ni ya kalle sai kuma ya kara rikeni tsam a jikin shi na dan wani lokaci,
Jama,a dake gurin a lokacin sukayo kanmu suna min kallon mamaki don wasun su da yawa basu ma san ina uguwar ba a lokacin,
Nan suka fara dan rade radi kodai mahaifinta ne don kaman yai yawa sosai da mahaifina,
Kuka nake sosai don na rasa irin farin cikin da zan gwada ina ji a lokacin,
Shimmer Abbba kuka yakeyi yadan cire farin madubin idon dake makale a fuskan shi a hankali, ya dan share hawayen shi
Jaye jikina nayi daga jijin shi na juya zuwa cikin gida inda na,fito masu, da tabarma,
Nai masu iso da su shigo daga cikin zauren Baba Mudi nakawo masu ruwan leda sai bin gidan da kallo yake a tsanake,
Waya aka bugawa Baba dake kasuwa sai gashi gida ba bata lokaci,
Sun gaisa yake masu sannu da zuwa nan suka shiga hiran rayuwa da shi cikin mutinci ba nuna komai a tsakanin su,
Baba ya shiga gida yaiwa Ummi izzini da tafito su gaisa, yaba da kudi a sayo abinda za,a masu girki dashi da abokin tafiyan shi wanda ban tsanmani ya iya hausa ba,
Wani yare naji sunayi da French a bakin su hidima sosai aka shiga yi da su bayan sun gaisa da Ummi yake cewa sunyi waya da Hamza yace yana hanyan dawowa ranan,
Abbana yake tambayan ina yaran nawa suke akace mai suna gidan su gurin kakan nin su,
Duk inda nabi sai ido yake bina dashi yana kallo na don ban kara bi takan shi ba,
Sai da su kaci abinci sosai sai Baba yakawo wa Abbana zancen matsalan da nake ciki a gidan mijina,
Murmushi Abba din yayi yace hukunci yana a hannun Baba don shi ba zai sa bakin shi ba,,
Godiya sosai yaiwa Baba da ya rike mashi ni amana batare da wani matsala ba,
Yake cewa Baba ya tayashi rokona nayi hakkuri don yaga kamar ina fushi dashi saboda naki dawowa gurin shi tun dazun,
Baba yace ai ko ba halin Aisha bane fushi amma bari na kira maka ita ,
Nashigo zauren cikin hijjab dina sky color nasamu guri na tsugun nan daga gefen su sai Baba yake cewa, Aisha yau ga mahaifinki Allah ya dawo muna dashi gare mu ,
Amma kuma sai naga kamar baki wa Allah godiya ba da hakan don naga kamar kina nisanta kanki dashi kuma,
Maimakon nai magana sai wasu hawaye na sake masu zafi suka dinga silalin min nan nafara kuka mai tsuma zuciya,
Dakyat na bude bakina nace mashi, Baba may

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login