Showing 288001 words to 291000 words out of 299981 words
su bane matsalarki ce kawai tafitar da ita daga gidan ga,
Yanzun kuma shine zaki tafi hada wani ki kara lalata zancen gaba daya kowa ya huta ko,
Jikin Umma yai sanyi ran ta yai matukar baci take cewa kai wallahi ni dai na shiga uku wallahi,
Mama tace ba uku ba yaya har tara ma wallahi kin shiga don kin bada waka an amsa maki,
Tun farko sai dana hore ki da hakan don gudu irin haka yanzu gashi an barki a cikin tsaka mai wuya ai don ko gulbi goma kika shiga baki fita sai ace kin yi din ne,
Dole ba don taso ba ta kyale zancen fan ta abace don ko magana ta kasa,
Mama tace irin ku ne iyayyen mazan da yaran zamani basu son shigowa su samu a gida, inda Aisha yar zamani ne wallahi da yanzu kun raba gari da ita ko duniya taji ku,
Ibrahim ya,shigo da murna yana fada masu wai mahaifina ya sayo min motar shiga kawai da mamaki suka ce mota fa yace wallahi har ma motar ta iso ko don jiya yaya yake fada min,
Nan su mama suka shiga murna da nuna farin cikin su Umma ko sai dariyan yake takeyi kawai,
Sun tafi gidan da Ibrahim ke neman mata,amma abinda sukaji ne ya tayar masu da hankali don iyayyen yarinyar sunce sun fasa,
Saboda sunji labarin halin mahaifiyar shi duk macen da dan ta ya,aura sai ta mayar da ita karamar bazawa tafito, don ta,
Saboda haka suje suyi hakkuri abar zancen bazasu ba da yar su ba kwana biyu a sako masu ita,
Sun dawo da wanan mumunan labarin Umma ta shiga dan koke koke wai mutane suna bin ta dasheri don kawai anki jinin ta,
Irahim yana samun labarin haka ya shiga tashin hankali sosai tsaye yai mata ranan yace wallahi shikan bazai yarda ba,
Da ya zauna bakin ciki ya kashe shi garin ma zai bari gaba daya ya shiga yawon duniya,
Tirkashi ranan Umm taga tashin hankali tai nadama sosai don Jibrin ma yace haka baban yarinyarcda yake bida yai mashi kashedi yabar zuwa gurin diyar shi kada uwar shi ta illanta mashi diyan shi,
Lokaci guda ta ramay ta zabge kamar ba ita ba ko abinci bata iyaci sai da ta sha dan hwaro hwaro a cikin ta na kunu,
Su Baba Madu da Liman sun zo gurin Baba Mudi amma yace suyi hakkuri abar zance don Aisha ta gama auren gidan Hamza,
Sunyi mamakin yadda Baba mudi ya cije akan bakarshi na,rashin yarda na koma haka duk da sunzo da kansu bashi hakkuri,
Sun dawo sun fada masu yadda sukayi da Baba mudi da kuma irin cin fuskan da na fuskan ta agidan gurin Umma da yaran ta mata tun shigowa na,
Don haka Baba Madu yace wallahi Rabi kin cuci rayuwan yaran nan yaran ga gaba dayan su basu rage ki da komai ba a duniyan nan amma kika jefa rayuwan su cikin wanan garari haka saboda ke,
Hamza ko saboda bacin rai baiko tsaya angama maganan ba ya mike yabar gidan rai a bace gashi ko wayana baya samu,
Da dare yazo gurin Baba hamza ya kara bashi hakkuri da kan shi sai dai magana guda ne a bakin Baba shine ya kawo min takardana kawai ba zan koma ba,
Dukar da kai yayi yana sauraren zancen baba da yake ji kamar ana zuba mashi garwashin wutane a zuciyar shi,
Hawaye ne masu dumi suka zubo daga fuskan shi ya bude baki da kyat yai magana yace Baba kodai nima Aishan tace nai mata wani abin ne da za,a yanke min wanan hukunci mai tsauri haka Baba,
Baba yace ko daya Hamza in bamu gode maka ba baza mu zage kaba kuma laifin uwar ka dai ne ya,shafe ka don haka aje ayi hakkuri Aisha amana take a gurina idan na yarda ta koma Rabi ba fasa halinta zatayi ba don haka duk abinda ya samu Aisha ni na ja mata shi,
Don sabodani ta aure ka don haka yanzu kuma nine zan raba,wanan auren wahala da bautar da yarinyar nan keyi ba a gani ya isa haka a hakkura kawai kowa ua samu nashi rabon,
Kuka sosai Hamza yake a gaban Baba yana rokon shi don Allah yayi hakkuri kada ya rabashi da Aisha don itace farin cikin shi baba yace na,sani hamza duk nasan da haka amma ayi hakkuri kawai shi yafi,
Yai mashi sallama yace shi zai shiga gida ya tashi ya koma kada dare yai mashi shi yagama yanke hukunci,
Har baba ya mike sai ya dan tsaya yana cewa, kayi kokari ka mayar da dayan matar ka,a dakin ta don zaman ka haka ba,alheri bane
Mutane kuma zasu iya cewa saboda Ausha ne yasa itama ka sallamay ta kaga zaka,shafa mata bakin jini bataci ba bata sha ba,
Nan ya,shige ciki yabar Hamza zaune a guri har tsawon wani lokaci ya tashi,
Yana fita yaji bai iya jan mota Ibrahim yakira ya kaishi gida,.
A hanya sai kuka yake cikin mota Ibrahim din ya kasa bashi hakkuri shima dai ran shi a bace yake daurewa kawai yayi yake jan motan ,
Ranan gidan Ibrahinm ya kwana yana ba Hamza magana da kuma yadda zasu bullowa baba mudi,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,
Ya samu gida kamar yadda yake bukatan samu a garin kaduna a wani sabon uguwar da matasa sukafi yawa acikin shi,
Sai dai,matsala daya yanzu shine akan zancen dawowana gidan shi don abin yafara wuce tunanen shi sosai don iyayyena sun kafe akan sai dai ya bani takarda kawai a rabu don Umma Rabi,
Ya,shiga cikin tashin hankali sosai ga mahaifin Biba yana ta faman bin shi akan yayi hakkuri ya mayar da ita dakin ta amma yaki sauraren shi,
Dare daya ya yanke shawara ya tafi can kauye gurin iyayyena na,asali ya fada masu abin da ke wakana a tsakanin mu,
Sunyi tafiyan shi da mansur da wani abokin su tun asuban farko suka bar garin zuwa kauyen mu,
Sun isa garin musalin karfe dayan rana da wani abu don nisa da ke tsakanin mu da garin Jega,
An masu taro yadda ya kamata sosai don yanzu ua zama dan gida sai da aka dama masu fura suka sha,suka koshi ban da hamza da hankalin shi ba a kwance yake ba,
Sai Baba Liman yasa ai masu iso da su shigo daga cikin zauren shi don su gana saboda ya fahinci magana ce ke tafe dasu,
Hamza bai boyewa su Baba na komai duk abinda yafaru sai da ya fada masu kaf,
Baba sahabi dayake shi dan zafin zuciya ne nan take yace shi Mudi ina ruwan shi da,zai kashe wa yarinya aure may nene hujjan shi na yanke wanan hukuncin bada sanin mu ba,
Ganin inda yake shiga ba nan yake fita ba yasa Baba Liman yadakatar da shi da cewa haba Sahabi shi fa Mudi bamu da mairaina akan shi kan zancen Aisha,
Don duk yadda akeyi yai muna saboda haka wanan zancen sai a tsaya ayi bincike akan shi, don idan baida hujja ba zai yanke danyen hukunci haka ba,
Don haka yanzu yadda za,ayi shine kai sahabi da Musa sai ku shirya ku tafi can Jega din ayi ta takare muji maganan dake nan idan kun ga za,a iya sasanta maganan sai ku sasanta ku dawo idan kuma maganan ba mai sasan tuwa bane sai abi shawaran da ya yanke ayi hakkuri,
Hamza baiso haka ba amma duk da haka yaji dadin da akace da Baba Sahabi za ai tafiyan,
Don yasan in ba wani ikon Allah zai iya yin galaba akan Baba Mudi da Ummi na,
Sai cikin dare suka shigo gatin Jega ana sallah magriba, don haka basu tsaya wani magana don gajiyan dake tare da su masaukin BLB guests,in ya sauke su tare da samo masu abinci mai kyau suka ci,
Sai washegari suka samu zuwa gidan Baba Mudi wanda yai matukar mamakin ganin su da,safe haka,
Su gaisa dashi a mutunce ya rasa inda zai sasu sai farin ciki da ganin su yakeyi,
Yace bari ya kawo masu abin karya dakatar dashi sukayi suna cewa a koshe suke sai da suka karya suka fito,
Nan Baba Musa ya isar masu da zancen Baba Liman din murmushi Baba Mudi yayi yace haka nake so dama,
Kamar yadda Hamza ya fada masu shima haka ya,mayar masu harda ma abinda Hamza ya boye a lamarin mahaifiyar shi bai fada masu ba duk Baba Mudi sai da ya fada masu kaf,
Yace bazan taba kashewa Aisha aure da hannuna ba sai dai idan abin yafi karfina to zan iya don ya zama dole amma gaskita shi mijin Aisha sam baida maraina a gare mu,
Don yaron kirkine a,gabana aka haifeshi kuma ya taso agabana nasan halin shi fiye da tsanmanin ku don haka ni banga wani aibi a kan yaron
Matsala dai itace mahaifiyar shi da tasa yar mutane a gaba har da zancen kissa don kissa mana idan ta halaka yaran wa yai hasara ba Aisha,ba don ita mace ce shiko dan ta namijine zai iya auren wasu mata su kara haifa mai wasu,
Ni bukatana da na yanke wanan humuncin mai tsauri haka shine sai sun san daranjan ta da muhin mancin ta a gare su in ba haka,ba da na mayar da ita haka kai tsaye abin ba,za,a samu saukin shi ba,
Su baba sukace wanan gaskiya don tunda ba mutunci ke gareta ba zata kara bullowa ta wani hanya ne kuma,
So nake sai dan sun kai ruwa rana da ita tazo har gidan nan da kafan ta ta roki Aisha gafara kan abubuwan da take mata, shine kawai zai kawo saukin al,amari amma ai har yanzu indai Rabi ce bata saduda ba gaskiya,
Baba Musa yace gaskiya malam Mudi kayi hikima sosai a nan don gaskiya irin wa yan nan Uwayen wuyar sha,ani ne dasu,
Yanzu abinda za,ayi shine zamu kira shi yaron nan mu bashi hakkuri yaje su sasanta da,uwar shi, idan har ta yarda ta bari to tazo nan gidan ka da kan ta,taba da hakkuri kaga haka,zai sa mu fahinci ko tayi taushi ga,al,amarin,
A haka suka tsayar da zancen suka kira shi ta,waya yazo sun mashi bayani akan duk yadda sukayi da shi,
Shiru yayi kan shi a duke can ya dago kan shi da kyat ya iya bude bakin shi yace Baba kuna ganin idan anyi haka ba wani matsala kuma,
Sukace haka din shine daidai don su zauna da Umma a fahinci juna ya sauke ajiyan zuciya yace ba matsala Baba zan je nagan ta,
Yai masu sallama yafita suka bishi da kallon tausayi kawai a ran su suna cewa baida matsala komai uwarshi ce kawai matsala ga al,amarin,
****** ********* ******
Ya shigo gidan da sallama ya samay a zaune gaba dayan su guri guda, ya gaishe su ya samu guri ya zauna,
Kallon shi suke a cikin tausaya don duk ya ramay yai baki ga kasunba a fuskan shi saboda rashin sheven da bai samun yi,
Kako ci abinci dana mama take tambayan shi yayin da mimi ta shige mai jiki tana tambayan shi maman ta,
Yai murmushi yace mimi maman ki tana na dawowa kinji, kara tambayan shi Umma tayi tace kako ci abinci ana tambayan ka,
Yace Umma na karya ai yanzun ma daga gidan Baba Mudi nake don iyayyen Aisha sunzo,
Mama tace da kyau sunzo dai ne akan zance ko yace eh shiya kawo su sai kuma yai shiru Umma tace to yaya kukayi dasune wai,?
Yai dan ajiyan zuciya yace gaskiya akwai matsala don sunce badani zasuyi magana da Umma suke son yin magana,
Shiru ne ya dan biyo baya kowa yai shiru sai mama tace to ai ba matsala sai mu tafi muji shakuwar su ko,?
Shiru Umma tayi aran ta tana cewa a gaskiya tana jin nauyi da kunya don bata san da,wani ido zata kalle su ba ma kuma may ma zasu fada mata ne wai da zasu ce sai da ita zasuyi magana,
Muryan mamane ya katse mata tunanen ta tana cewa yaya ai sai mu shirya muje muji shakuwar su ko don asamu matar shi ta dawo dakin ta abu kusan fa wata daya da kwanaki ke nan har tayi arbain a gidan su,
Ba don Umma taso dole ta tashi suka shirya zuwa gidan Baba mudi din ita da yar uwarta,
Sun samay su zaune a zaure suna hiran su da dariya irin ta maza ganin shigowan su mama yasa suka tsagaita dariyan su,
An gaisa inda su mama suka samu guri daga gefe suka zauna suna masu sannu da,zuwa da tambayan mutanen gida,
Mikewa baba mudi yayi yashiga gida ya kira Ummi da mama saude suka fito,
Su ma sun samu guri sun zauna daga gefe suka gaisa da su mama da tambayan su su yan biyu,
Sai dan shiru da gyaran muryan da Baba mudi yayi yasa gurin natsuwa kamar yadda ya dace,
Baba ya fara da addu,a bayan sun shafa yake cewa, da farko dai ina son muyi magana ta natsuwa da fahintar junan mu,
Kowan su yace Allah yasa hakan sai yaci gaba dacewa ba,wani matsala bane don kowa ya san abinda ke faruwa ga a tsakanin "ya"yan mu da Allah ya hada aure har da zuri,a,
To ba komaine yasa muka gaiyato kuba ku uwanshi sai don matsalan daga gare ku ne shiyasa yau muke son ayita takare don kowa yasan matsayan shi hakana,
Ke Rabi kin dai samu a cikin uguwar nan kamar yadda muma muka sanki don haka mu abin yana daure muna kai don bamu san abinda Aisha take maki wanda yake kawo tsana mai tsanani wanda har yanzu ya shafi zurian da ta samu da dan ki,
Shine mukace ya kamata mu gaiyato ki don muji abinda ke kawo matsala a tsakanin ku har ta zama kiyayya irin haka,
Shiru Umma tayi sai wani irin zufa da taji yana kokarin karyo mata daga duk sasan jikin ta,
Shiru ba wanda yai magana har wani dan lokaci sai Baba Sahabi ne yake cewa ki muna bayani don mu tsawata wa ita Aisha indan da bukatan haka,
Da kyat Umma ta iya bude bakin ta tace masu yanzu ni hakkuri kawai zan baku insha Allahu irin abubuwan da suka faru ba zasu sake faruwa ba insha Allahu,
Don Allah kuyi hakkuri ku mayar mashi da matar shi dakin ta don samun kwanciyan hankalin su,
A,a boyar Allah mu muna son akawo karshen al,amarin ne don baza mu yarda mu mayar maki da yarinyar mu ba dakinta batare da munji hujjanki ba don mu tsawata mata inda bukatan haka,
Shiru Umma tayi sai kara dukar da kan ta tayi mamace tace don Allah kuyi hakkuri abar wanan zancen don yawuce babu abinda zai sake faruwa maka mancin haka,
Ita ma Umma din sai cewa tayi adaiyi hakkuri don Allah tasan tayi kuskure a baya amma yanzu insha Allahu komai ya,wuce don Allah su mayar da Aisha dakin ta,
Baba Sahabi yace munji maganan ki amma gaskiya in hakane sai dai kowa yayi hakkuri don bazamu mayar da ita,ba a dinga cusguna mata ana ganin kamar bata,da gata da,galihu ne,
Hawayen nadama yazo ma Umma take cewa cikin kuka gwanin ban tausayi don Allah kuyi hakkuri ku yafe min nasan nayi kuskure sosai a,rayuwana don idan nace maku ga laifi daya da Aisha tai min tun ranan da,ta,shigo gidan da a matsyin sarakuwana,
Tausayi sosai Umma ta basu yadda take kuka da kaskantar da kanta a gare su,
Baba Sahabi yace to Alhamdullahi tunda munji daga,bakin ki mudai dan ki bai yi muna komai ba arayuwan mu sai sambarka,
Matsala dama daga gareki ne don haka ga,sharadin mu kafin muce mun yarda takoma dakin ta da farko dai duk muka kara jin tsana ko tsangwama yafito daga gareki ku dake nan ku sheda ni da kaina wallahi zanzo na fitar da ita a gidan dan ki,
Idan kuma wani magana yakara tasowa akan zancen na,sihiri ko wani abu haka shima dai bazamu kyale ba don mu gidan mu gidan malaimaine bamu gaji aiki da sihiri ba ko wani abu na daban,
Yara de jikokin kine halal malam don haka ko yankasu zakiyi mu bamu ruwan mu yar mu kawai muka,sani don ba kyale ki zamuyi ba ,
Hakan ma bazai faru ba insha Allahu inji mama data ari bakin yayan nata nan dai suka kara,bada hakkuri aka sahirtawa juna a tsakanin su,
Har zasu tafi mama take cewa yaushene sarakuwar nawa zata dawo dakin ta sai baba yace zata dawo amma sai mun gama magana za,a sa lokaci zakuji a gurin hamza din, in komai ya daidaita,
Sukai sallama ana rokon juna gafara a tsakani da yar raha irin ta manya,
Sun koma gida suka zauna a,tsakanin su mama take cewa Umma tau yaya kin daiji zancen mutanen nan kuma gaskiya suka fada don babu