Showing 294001 words to 297000 words out of 299981 words
kinga yadda yar agwai ta canza baki,
Abinda naita maki hasashe ke nan a lokacin amma sai kika ki ji giyar shedan ci yana rudin ki yanzu dubi wanan daulan Sadiya da kina cikin shi min huta da wanan bakin talaucin a rayuwan mu,
Ban aurar dake gareshi ba Saida nasa akai min duba akaga arzikin shi dake tafe ,
Yanzu dubi yadda yarinyar nan tabaje take cin arxikin ta kowa na kallo don yanzu ko yan uwan shi da uwar shi biye suke dasu,
Shi har yanzu rike yake damu don kiga bai sake fuska ba ai damu, ita ita ko kila ma ya bayar da kudi masu yawa a bamu ta boye ne taba mu kadan,
Sadiya tace ,a a mama nasan halin yar Agwai wallahi bata boye wa asalima fa da fushi tafito dakin, nasan ya gasa mata bakar magana ne kila,
Ni nasan halin hamza zai iya fiye da haka idon ranshi ya baci da abu aiko yanzu mungode da wanan da muka samu,
A gida kuma nan aka zauna a na tuna irin rayuwan da mukayi a zamanin Sadiya Biba tace yanzu shi akan wanan mumunan matar yai ta gasa mutane haka hat may yagani a gurin ta yayi daidai da yana fitowa a lokacin sai ji mukayi yace abinda nagani a gurin ki mana kaddara ,
Shiru tayi don tasan tund yafadi haka idan takara tankawa zasu kaule da fitina sosai, na kawar da zance da sauri da cewa wai kuwa ka samu zuwa gurin Anty hindatu ka dubota ,
Don in baka je ba nasan tana jirace da kai duk sanda kuka hadu sai kaji ta,
Yace cikin murmushi wani rufa min asiri Humaira kar ta hada dani tace aidani aka kulla mata yin kishiya,
Nace haba dai ai tadan kokarin da kayi akan zancen yace haka kike gani ke amma ai ita, cewa tayi nina koya mashi yin mata biyu,
Murmushi nayi nace antyna ke nan bata wasa da kishi kamar maman jafar bata san cewa komai mukaddari bane ga bawa duk abinda ke a littafin mutun sai yayi shi a rayuwan shi,
Ita dai maman jafar ai arziki tayi don Allah baiyi mijin ta da bakin aure aure ba amma ai mace bata cika baki akan namiji komai tsoron ta in Allah ya kaddara sai anyi,
Mutum dai ya zauna da kowa da zuciya daya sai Allah ya kawo mashi agaji ta inda bai zata ba,
Biba tace niko ina mamakin wasu mata da wai suce don sun shiga gida su basu yarda wasu su shigo gidan su,
Nace ai matsalan kishiyoyin ne na yanzu sai andace don haka kinga tana da gaskiyanta don bakasan wace kala za,a kawo maka mutum kawai ya dage da addua kawai shine mafita ga bawa,a
****** ********* ******
Wata sabu inji yan caca Hamza ne zaune a gaban Umma bayan ta gama sauraren maganan shi tace cikin yake baki,
Ashe kace mu shirya tafiya yazo ke nan don ba zan yarda ka barni nan ba gaskiya kafarka kafa na da kayana,
Ce haba Umma ina zan tafi dake in mun kwasa mun tafi wa zai zauna da sauran yaran a gida dole sai da babba a kusa dasu ai,
Umma tace Allah ko akwai wanda zai basu tsaron da Allah ke basu ne a duniya,
Balle ai ga hafsi nan ta zauna dasu mana ai ba komai dani da ita ai duk daya ne gare su,
Yace Umma ai ita mama hafsi dama yanzu a gurin mu take don haka kin ga da ita zamu tafi kece dai zaki tsaya dasu balle tafiya na aiba yana nufin na barku ke nan ba anan dole na rika zuwa don ita ma Biba ba ita zan tafi ba a nan zan barta ta zauna kada abar gida ba kowa,
Umma tai farat tace Allah baka isa ba hamza don ba,wanda zakaiwa dadin baki kafar ka kafa na don tare zamu,
Yace gaskiya Umma ba hakane tsarina ba tsarina ke nan natafi da Humaira can ta zauna da yara don ina son yara na suyi karatu sosai na boko da islamiya, shi yasa na zabi zuwa kaduna na zauna dasu,
Kaji na fada maka iya zance na sai dai in fasa yafiyan za,a yi a fasa muddin kace bazakaje dani ba, ehe,
Shuru yayi zuciyar shi na tafasa sai dai bai da halin magana don da,wani ne yau da yaji shi ,
Mikewa yayi yai mata sallama yana tunane a ranshi may yasa Umma tafaye son kan ta haka da yawa ne, wai,
Yanzu duk da yafada mata cewa saboda yaran shi zai yi tafiyan amma bata yarda sai ta kanta kawai take yi,
Ranan haka ya wuni da bakin ciki da bacin rai a zuciyar baida wallawa don har zazabi yaji yana son kama shi don ya riga yagama shirin tafiyan tsaf komai na bukata ansa agidan a gyara ko ina har kitchen din gidan gaba daya har abincin amfani da drinks ya saya ko,
Yana fita Sa,ade tace ba kowa ya shirya haka ba sai wanan makiran matar tashi yar agwai wai ita tana ganin uban ta nada kudi bata son zama da mutane bari taja shi su tafi nisa da kowa,
Kuma wallahi Umma duk da mama hafsi aka,shirya wanan makircin sam mama bata kaunarki,
Umma tace barta kawai makiran banza da wofi ai nasan duk kule kulen da takeyi akan yaton nan,
In haihuwan mai arziki abin yine itama aida ta haifa, yanzu da taga ya zama abin kwarai ai tashige masu itace uwar kwarai,
To bazata ba ko ina anan zata zauna dani za,a muga tsiya kuma kema bazan barki a nan ba tunda zancen aurennki ya lalace,
Bai fadawa kowa yadda sukayi da Umma ba sai washe gari bayan yakai Biba gidan su vurin suna yar uwarta da,ta haihu ne yadawo yasamay mu a,falo zaune,
Ya zauna fuskan shi babu walwala mama ce tafara magana ganin yadda ya zauna a kasalance tace yaya dai dana,
Ya wani irin huci tare da shafa fuskan shi yace matsalan Umma daine mama,
Mama tace tau anyi wani abin ne kuma ko ka may yafaru haka kuma yace wallahi mama ni ban san may ke damuwan Umma ba,
Tasani cewa zan nisantane don yawan matsalata amma wai shine takafe wai dole da ita zamu tafi idan kuma ban yarda sai dai a fasa tafiyan a baki daya,
Wani irin son kaine ga Umma sam bata son farin cikin rayuwanane wai, komai fa na riga na shirya mama acan tafiyan mu ne kawai bansa rana ba,
Amma gashi yanzu ta bijiro min da fitina kuma zata tayar muna da hankali,
Mama tace wanan ma fadi ne bari zan tafi anjima nagane ta muyi shi yace mama dakin barta kawai tunda kikaji tafadi haka gaskiyar ta ke nan tafadi,
Don ko kinje ba fasawa zatayi ba tunda kikaji ta fadi haka haka dinne har cikin ran ta,
Bari dai naje muji matsalan ta don haka kawai baxai yi ta fito da zance haka ba babu dadin ji tabiku taje tayi may acan,
Yace na fada mata itama wanan ba da ita zan tafi anan zata zauna sai dai na rika zuwa don ai sa,ana kusan a nan take gaba daya,
Mama tace wa habiba kake nufi bazakada ita ba yace ita din mama don ban zuwa da ita anan zata tsaya ta tsaya a gidan nan kada mubar gida ba kowa acikin sa,
Ai kuwa ashe akwai wata fitinan tafe nace masu sai a lokacin nasa masu baki a zancen su nace kaima kasan Biba bazata yarda ba wallahi,
Yace idan bazata yarda ba sai tasan yadda zatayi amma ban zuwa da ita gaskiya don ban ma taba shirya hakan ba a raina,
Hmm kawai nace tare da ci gaba da abinda nake a,wayana ina sauraren hiran su,
Mama kamar yadda tace haka din ta,shirya ita da Jidda suka tafi gurin Umma don su gana da ita,
Umma taji zancen mama da tace mata, haba yaya yanzu da girmanki kice sai kinbi yaron nan kaduna may zakije yi,
Umma tace, ke mai zai sa ki bisu abinda yasa zaki bisu shi zai sa nabisu nima kafana kafan su na gaya mashi ai, ke ki zauna a gida da yaran,
Mama tace aini dama badani za,ai tafiyan ba don bance zanbisu ba ina nan ni,
Munafuka kin zaci bai fada min cewa dake zasu yi tafiyan bane shine ni don bakin cikin ni baki son ayi dani ko,
Subbahanallahi yaya may yakawo zancen bakin ciki a tsakanin mu kuma akan danki zanyi maki bakin ciki ke da kika haifi abinki da cikin ki aiko danakai annaminiya,
Tau ni dai yanzu ai duk ba wanan ba ina fatan kunji shakuwana dai ko dani fa za,a tafi duk inda za,a,
Mama tace yaya kardai har kin manta da sharudan da mutanen nan sukayi akan yarsu har kike son ki kawo wani sabon fitina kuma,
Wai don sun fadi sharadin su shine har da na, rabani da dana ko suyi min iko dashi komay wai,
To tsaya kiji ni dai ni haifi shi da cikina ba wani ya haifa min shi ba balle a juya shi a juyani yadda rai ke so wanan bazai yuyu ba ni iyakar magana ta ke nan ban hana shiba tafiya amma,yasan da sanin kafata kafar shi,
Mama tace to shi ke nan idan mutim baiyi sharan massalaci ba ai zaiyi ta kasuwa,
Sai mama,takawar da zancen duk da ranta ya baci da kalaman Umma amma take cewa zancen zuwa gurin gaisawa gidan su Asmau fa da sukace zasuyi,
Tace a hasale bazaniba kina iya zuwa idan kin tashi ni in na tashi zan tafi ,
Haka mama tabargidan cikin bacin rai taje gidan sarakan Asmau tai masu gaisuwan tsohon gidan da ya rasu,
Tadawo gida tana fada min yadda suka kwashe da Umma nai murmushi nace mama Umma sai hakkuri fa don haka Allah yayi ta ita,
Wasa wasa zancen tafiya yana son ya birkice don Umma ta kafe akan bakarta da ita zai tafi, shikuma yace ba haka ya tsara ba,
Da abin yakai tura dole yaje yadamu su baban shi yafada masu matsalar da ake ciki sukazo gidan suka samay ta,
Nan sukai mata tas suka ce wanan karon har in taki yarda da bukatan su to wallahi zasu cire hannun su ga al,amarin diyan ta baki daya,
Ganin da gaske sukeyi zasu iya mata abinda sukace shine tayarda da tafiyan badon taso ba a ranta,
Su zarah sun samay ta sun nuna mata bacin ran su yadda take ja masu abin gori a cikin yan uwan su ko yaushe,
Tace su suka damu dasu aiko bada su ba,zasu iya rayuwa zarah tace wallahi Umma dole mu damu dasu don kowa da dangin shi yake kuri a duniyan nan ai,,
Angama rikicin Umma sai kuma aka shiga na Biba a tsakanin su don tara mu yayi baki daya har mama a falo da dare yake cewa ,
Ina son kowan ku ta,saurari abinda zan fadi kuma ta fahince ni bawai nai haka,bane da wani manufa nayine kawai don kwanciyan hakalina da wasu dalilai na dani nasan dalilun yain haka,
Muna shiru muna sauraren shi yace na samu gida a kaduna don acan nake son nakai wasun ku da zama, don yanzu kun san business dina ba anan kawai ya tsaya ba,
Don haka ke Humaira sai ki shirya ke da yara ku koma can da zama ke kuma Biba ki zauna anan har mu ga abinda za a yi gaba,
Kafin ma ya kara wani kalma sai cewa tayi tunda gani Biban mahaukata ko,
Don ina shatalalagan ka sai na zauna gadin gida ita ka dauke ta ku tafi van kuji dadin ku kubarni nan gadin gida ko,
Yace naki tunanen ke nan yanzu kunji magana na don nagama magana ke nan ke Humaira sai ku fara shiri zuwa karshen wata in Allah ya kaimu zamu tafi hardake mama zamu tafi don haka ashirya kafin lokaci,
Wallahi ban yarda wa za,a cuta don ka maushini ban son ciwon kaina ba kun gama shirin ku yanzu zaka zo kace wai ni na zaunacmaka gadin gida,
Yace to inbaki yarda sai ki san yadda zakiyi ai don baki isa ki sani dole ba,
Tace ai in gaskiyane da dani da nake karama zaka tafi ita dake da yara ta zauna gida
Yace oho tunda ke ne yar son kai ko toni ba haka nake ba don tare kika ganmu kuma bazaki raba mu,ba
Tace to wallahi nima ban zama yace in baki zama,sai ki san yadda zaki yi ai ko don dai ni na tsayar dake inda na tsayar dake,
Haka taron ya,watse a hargitse Biba tana ta zage zage wai ita bazata yarda ba dole da ita za a tafi,
Ni bata ma san tafiyan ya zama min dole bane bandai son na musa mashine kawai don ban son iyi nisa da Ummina da yan uwa na,
Muna shirin mu su ko sai faman fitina suke da Biba kullun cikin jidali suke a tsakanin su kan tafiyan,
Da naga fitinan yai yawa nace ni zan zauna ita su tafi yayo cikina da masifa yace ni har na isa yace ga abinda yake so kan wata can nace ban yi,
Naje har gidan Hindatu na fada mata abindake faruwa tace, min wai ke Aisha yaushe ne zakiyi wayo mijin ki yana kokarin nema maki sauki kina son jefa kanki ga fitina
Wallahi maza ki shirya kibi mijinki bakin ki alaikum in baso kike kijawa kan ki fitina ba kidawo kina dakin sani daga baya,
In zuwan ba,sun hango alheri bane aida baki ga harda Umma tsohuwa tana fadan da ita za,a tafi ba,
Nan dai ta kara sani a hanya nadawo gida na sa hinma ga shirina itako Biba sai faman masifa suke kwasa dashi tana wallahi bata zama,
Komai da muke bukata mun tanada a,tare da mu inda motar kayan mu ce tafara wucewa bayan kwana uku muma muka,shirya mu kaiwa yan uwa da,abokan arziki sallama
Umma ma da zamu tafi mun tafi har gidan sallaman ta sai cewa aje lafiya kawai gadai amanan dana nan nabarshi a hannun ki
Nace cikin murmushi ni Umma gawa nawa amanan yake da ni zan rike nashi tace wanan kuma ke kika,sani da mama ma basuyi sallaman dadi da ita ba, haka muka kama hanya sai kaduna garin gwauna dani da mama da yarana gaba dayan su har madina nan mukabar biba tana ta kumfar baki da zage zage wai gidan su zata tafi bata zaman yi mashi gadin gida don ita ba sakariya bace ai,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,,
Mun isa garin kaduna misalin karfe hudu da yan mintina na rana gaba dayan mu a gajiye muke sai bin garin muke da kallon mamaki har muka isa masaukin mu watau gidan mu,
Wani gida ne mai babban get aka,bude muna motan mu da dayan motan da yake bin mu a baya suka shigo daga bayan mu su ma,
Bayan mun fifito ne hankalin mu ya dauke ga kallon gidan cikin mamaki gaba dayan mu,
Yafito shima a gajiye yana cewa Bissimillah ku mana ku shigo daga cikin ko,
Jidda this is your new home, so feel free, is your home here, enjoy your self,,
Gaba daya a falo muka zube saman dima diman kujerun dake mamaye a falon sai raraba idanuwan mu muke yi,
Photo na mu ne a ka man na ko wani kusurwan falon cikin dauki yaran ke murna da nuna min photo su a bango tare dani da baban su photo da muka dauka da sallah ke nan, tare da su, shine yasa aka wanke mai manyan glasses din su ya manna a nan,.
Sallah na Umurci kowa da su mike muje mu fara sauke farali tukun,
Shi da kan shi ya nuna muna yadda gidan yake ko ina kowa ga inda ya kamata ya zauna,
Sai muka shiga da kayan mu dakunan da ya gabatar muna din kowa sai da yai mamakin kyau dakin da haduwan shi komai morden one classic,
Abinci aka fara gabatar muna wanda aka kawo daga gidan Nasir abokin shi, dake nan garin kaduna din,
Abinci ne lafiyayye sai kamshi ke tashi irin girkin zamani na yan birni komai yaji zam,,
Sosai muka kwashi girkin mu sai kuma muka,fara hiran mutanen gida,
Hamza ne ya shigo falon ya sauya tufafin jikin shi zuwa kananan kaya,
Ina matukar son nagan shi a cikin irin kayan nan don yakan fitar mai da kurciyar shi a fili duk da nasan hakan zai iya jawo hankalin wasu mata a kan shi amma ban faye damuwa ba da hakan don wani dare ne jemage bai gani ba,
Bayan fitan shi da yan mintina sai namike nafara shiga dakunan gidan daya bayan daya, ni da mama da sauran yaran,
Dakina yadda naga an kashe mai kudi sai da abin ya bamu mamaki sosai a hankali na sauke ajiyan