Showing 297001 words to 299981 words out of 299981 words

Chapter 100 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17678

zuciya har ana iya jina a fili,
Mama dake dauke da hassan a hannun ta tace cikin murmushi Aisha wanan ba komai bane kadan ne daga cikin riban hakkuri ,
Duk abinda bawa yai hakkuri a kan shi wata rana sai ya girbi alherin shi daga gurin Ubangin mu, ta hanyan da mutum bai tsanmani ba,
Yanzu da ace kin biyewa son zuciyar ki akan yawan auren da yayi tayi yana kawo mata kowace da halinta amma kika daure kika sawa ranki hakkuri yau ga riban hakkurinki kin girba ,
Yara hudu inji Allah a lokaci daya harda kyautan tagwaye akai
Hakane koba komai mijin ki ba mai wadata bane, Allah yasan hanyar da zai saka maki da alherin sa, saboda Allah yana alfahari da bayin sa masu hakkuri ga duk yanayin da suka tsunci kan su a ciki,
Sai kiga Allah ya,dube su da idon rahama yai masu sakaiyan da,alherorin shi don Allah Aisha ki kara kaimi gurin hakkuri da mijinki ku taru ku rufawa junan ku asiri da diyan ku,
Kada zancen auren shi ya taba ruda ki kawai ki dagd da addu,a da hakkurin da kika,saba yi Allah ya,tsaya muna na amsa da amin mama a hankali tare da,fadin nagode mama,
Kowan mu ya shiga gyaran guri yadda ya dace don adana yan kayan da mukazo dasu kaduna a,tare damu don ya hana mu kwaso kaya da yawa,
Sai dare ya dawo gidan da kaya,niki niki tufafin yara ne da su takalmomi masu kyau kowa kamar debosu yayi, nasan yayi hakane don mun shigo birni yanzu yasa ya sauya masu kaya kalar ta yan birni,

Sannu sannu mukafara fara sabawa da garin da rashin yan uwan mu da muka baro a gida,
Yasa yaran makaranta mai tsada sosai ta kudi, har da madina dan lokaci kadan sai gashi mun fara sajewa da yan gari saboda yana matukar kashe muna kudi sosai,
Tun zuwan mu ban fita ko kofar gida ba amma sai ga yaya ranan yasani gaba wai muje mukai yara makaranta inga hanya don nice zan dinga kwaso su kulun kuma inkai shi don nasan shi ba mai zama bane a gari,
Tsoro yakamani yadda zan gane hanya haka a lokaci guda gashi ba tukin mota na iya a birni haka ba iyakata garin Birnin kebbi kawai, nake dan shiga ko shi a,tsorace nake tuki ciki,
Da zamu dawo yabani mota wai naja muna tafe yana nuna min hanya har muka kawo gida da za,a dauko yaran ma tare muka tafi ni naja motar har makaranta ina bin kwantancen da yake min sai da mukai kwana uku a haka muna fita tare yana gwada min hanya har ya fahinci na gane don ina amfani da signbod din gurare da muke wucewa,
Haka da kwana biyar yai tafiyan shi ya barmu a gatin mutane dole na zage nice mai hidima komai kamar yadda ya koya min yi,
Ban samu wani matsala ba don ina amfani da kwakwalwa na gurin fahintar komai wasa wasa sai na fara sabawa, da garin,
Batare da naji tsoron komai ba haka yasa watara na,dawo daga kwaso yara mun jero da wata jar mota mai tsada a bayan mu ,
Sai da nazo na wuce matar dake jan motar naga ta bini da kallo, kusan gidajen mu a jere suke da juna,
Nai hon maigadi ya bude muna kofa saida nai parking muna fitowa sai ga wanan matar ta na hon daga kofan get din mu,
Dole na tsaya da mamaki nake kallon ta don dai ni ban san kowa ba,a,garin,
Ta fito daga motar ta takaraso gare ni fuskan ta da murmushi a makale nima dan murmushin nayi ina karba mata sallaman ta,
Tace ashe kece makwabciya ta ina jin yarana suna fada min masu gidan nan sun tare da yaran su farare sosai sai na dauka ku ba hausawa bane kila,
Nace cikin murmushi mu ko hausawa ne daga jahar kebbi muke,
Tace masha Allahu ni ga gidan mu nan na kusa da ku dinnan sunana Fatima ina da yara biyar, maza uku mata biyu,
Masha Allahu na bata amsa nace Aisha nake ina da yara hudu maza biyu mata biyu tace wake da shimkafa ke nan sai nai murmushi,
Tace Allah ya bamu hakkurin zaman da junan mu a matsayin mu na makwabta nace amin cikin murmushi,
Take ce min ita yar jahar bauchine zamane ya kawo su kaduna su ba yan jahan bane, nace ashe duk mune nima zama ya kawo,
Tace ok bari na barki ki shiga don naga daga gurin kwaso yara kike daga makaranta,
Sai na shigo taronki don ni yakamata na fara shigo nace nagode tajuya tana mu na sallama tafita,
Muna shiga daga ciki mama tana masu oyoyo har ta,fara cire masu kayan makarantar dake jikin su,
A,gaskiya ina matukar jin dadin zama da mama don duk wani nauyi tana dauke mana sam bata gajiya da aiki ita,
Kasancewa weekend zamu shiga yasa nasa na gyara kayan abinci masu yawa,don nasan yaran zasu wuni damuwar mu agidan,
Da,dare unexpected sai ga yaya ya,dawo garin ddaga tafiya yazo muna da kayayakin marmari iri iri na kasar wajen Nigeria,
Yara suka hau murna da jin dadin ganin shi bayan kwana goman da yayi baya tare damu a kasan,
Bai samu matsalar taro ba don komai a shirye yake yai wanka yafito falo don yaci abinci, sai yaran suka rufe shi,
Ina fitowa daga dakin naga yaran suna damuwan shi da,surutu na karasa gurin ina cewa oya kubar gurin kubar daddy ya huta haka baku ga yana cin abinci bane,
Sai ya dakatar dani da hannuwan shi yana cewa, bar su kawai Humaira let them enjoy there time with me for a moment please,
Tsaye nayi ina kallon yadda suke hira shi da yaran cikin so da kainan junan su freely,
Zuwa can ya,dago kai yana ce min sako nan Anty cost, ta bayar nakawo maki wai let's desegn ne na,shaddan mata,
Na lumshe idanuwa nace Allah sarki Anty aiko ta kyauta min sai cewa yayi amma Abba yace nace ki bar kudin su shi zai biya kudin,
Wani dadi naji har kasan raina nace Allah sarki Abbana na gode Allah yabar kauna da dalili,
Da murna nake fadawa mama abinda Abbana yai min sako dasu ta tayani murna,sai kuma tace to amma ai naga garin nan baki san kowa ba,cikin sa nace nima tunanen da nake kenan wallahi, amma dai Allah zai kawo muna mafita,
Kirana yayi na kwashe kayan da suka ci abinci still yana gurin da yara yana tambayan su labarin makarantar su,
Tambayan su yake a cikin hikima akan makarantar su din,
Nan ya,fahinci cewa Jidda tana fuskantar matsala daga wasu daga cikin yan ajin nasu na challenges,
Suna ce mata wai bata iya hausa ba kuma suna mata wayo gurin karbe mata abinci breakfast din su, inda taje dashi,
Ina jin su sai naji kunya da nauyi abinda ya kamata nayi a matsayina na uwa na fahinci damuwar yara na da kuma wa yanda suke hurda dasu amma ban yi azancin yin hakan ba,
Inda nake tsaye ya dan kalle ni cikin lumshe idanuwan shi alaman kin gani ko,
Yace wa yarinyar ta bari gobe shi zai kaisu school da kan shi zai yi complain wa malaman su, din,,,
Kwance na samay shi a,dakin yai rigingine ya sa hannayen shi daya ya tare goshin shi dashi, jin motsina yasa shi sauke hannun shi ya dan kalli inda nake tsaye ina aje mai dan flask din ruwan zafin shi a gefe,
Ina,saye da kayan barci riga da,wando masu shara sharan hannu sai dai babu abin da kayan ya boye daga jikina kamshi kuwa ba,a magana a jikina,
Ya saukar da idon shi gaba daya a kaina tare da,sauke numfashi a hankali,
Kallo na yayi tare da murmusawa yana jin wani irin sanyi da begena a ran shi yace,
Hummaira kayan nan sun maki matukar kyau sosai sai dai mama ta shige ne da kika fito haka,
Fuskana dauke da murmushi nace tashige da yara tun shigowan ka ya mika min hannu alaman nazo gare shi,
Ina zama yake cewa cikin sauke ajiyar zuciya nai saurin dagowa na kalle shi don yadda naji ya sauke ajiyan zuciya da,alamar damuwa a ranshi,
Yace don Allah ina son ki saka idanuwanki sosai akan yaran nan musanman ma matan don yanzu muna a cikin lokaci ne sosai,
Yanzu kinga suna cikin damuwa amma baki maida hankali ba balle ki fahince su,
Idan da kina bibiyan komai nasu dake dake zama dasu ya kamata ki gano wani abu daga gare,su,
Amma dai koma maynene Monday insha Allahu zanga malamin ajin nasu a kan Jidda din,
Sai kuma ya dan matseni a jikin shi yake cewa dake dasu duk amana kuke a gareni kinga nan birni ne kai koma kauye ne yanzu dole mutum yada ido akan duk wani movement na yaran shi ko a gida ko a,waje saboda lalacewan zamani,
A hankali nace insha Allahi yaya zan mayar da hankaki akan komai nasu baki dayan su,
Fara bin jikuna yayi a hankali yana mai fara aiwatar da sunna a kaina ban tsaya wani jikiri ba nashiga mayar mashi da martani yadda ya,dace dashi,
Washegari da safe kafin mu tashi har mama ta shirya muna abin karyawa ko yadda ya,dace don koda na,fito nasamu tana wa yaran shirin zuwa islamiya
Naji dafin ganin hakan don nasan ko fiye da haka zan samu a gurin mama din, don komai ita da zuciya daya take abinta,
Wani lokaci nakan ce a raina dama ace itace mahaifiyar su Hamza da nafi kowa sa,ar uwar miji mai mutunci amma dai ko yanzu ma ba laifi don ta cancanci yabo sosai gaskiya, ko a haka ma din na godewa Allah na,
Bayan fitar yaran zuwa islamiya yafito fallon saye da wando tree quarter, sai yar farar tshirt da yake saye dashi,
Yana gama breakfast ya koma saman doguwar kujeran falon ya kwata da,waya achannun shi yana yi,
Na fito daga daki cikin wasu kananan kaya, wandone da riga sun matseni sun shafe min jikina tsaba, surana yafito tsab a cikin shigar,
Tunane naga yanayi ko may yaks tunand oho, na isa gurin shi ina cewa cikin dan durkusowa gare shi, laiya dai maigida,
Yai murmushi tare da kamo min hannu na yana cewa Humaira naga fa shigowa kaduna yafara saki bushe fitilar ki ta kunya,
Yar dariya nayi nace ai akai kawai nake bushewa ba ga kowa ba yake ce min mama fa dake gidan,
Nace ai itama tafi bukatar taga na gyara maka,abinda kake so da kauna a,rayuwan ka,
Yai wani galala yana kallona tankar wani wawa can yace eyyeh har fada bagana yanzun kin koya ashe, ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa Allah ya barmin matata uwar yayana kuma uwargidana rangidana,
Yinin ranan yaya bai fita ko ina ba yana gida a tare damu ya hutawan shi,
Tun ina jin nauyin yadda yake min har na bushe fitilar nawa nima nashiga mayar mai da martani ba tare da kunyan idon mama dake cikin mu,
Da yamma ni da kaina nashiga kitchen na,shirya muna abincin dare inda na hada muna ferfesun kayan cikin rago dayaji kayan yaji na,gargajiya sai fankasau da miyan naman kaji,
Duk wanda yaci sai da ya,yaba da girki sai faman santi sukeyi suna ci da kari,
Sai washe gari kayan shi ya iso inda yabani sakona na dibarwa makwaciyana tsaraba mama ta karba da kanta tashiga gidan takai mata don tace tana son fita ta mike kafan ta,
Da yamma Fatima tashigo gidan mu tai min godiya sosai ta zauna muka dan taba hira har nake nuna mata kayan da aka kawo min,
Tabani shawaran akwai bukin da zata na yar uwar ta da ta haihu a kabala sai muje tare na dan fara nuna,wa mutane take ce min nafara online business ina turawa ana gani mai so zai min magana ta nan ma,
Bayan na,raka nadawo na,samu yaya a,falo yake tambayana inda nasan fatima na fada mai yadda muka hadu da ita yake ce min nadai bi sannu don nan birni ne fa,
Nace zan kula insha Allahu, nan muka zauna dashi ata hira da dariya yana jin dadi a ran shi,
Sai godiya yake ga Allah daya,bashi mata mai kyau hali da iya tattali irin Humaira,
Yace a ran shi gaskiya zai ce yafi kowa sa,an mata mai kyau da kyaun hali da kuma hakkuri a duniya don macen da ta tara haka rahama ce ga mijinta ga kuma yara masu kyau da tarbiya da nake haifa mashi,

****** ********* ******
Kamar yadda yai alkawari ya tafi makarantar su Jidda yaga classmaster su yai mashi bayanin komai tare da dan bashi dan ihi sanin wani abu, don yanzu duniya sai da hakan,
Munje gidan bukin mata sun rude da gani kayan da naje dasu sai dai ban yarda naba da bashi ba kamar yadda fatima ta gargadeni dayi haka yasa nai ciniki sosai a gurin ban dade ba nadawo gida abina,
Wanan fitan ne yai silar fara hurda na da mata da yawa suka fara sanina muna hurdan arziki dasu na,saye da,sayarwa a gida,
Alhamdullahi don, gaskiya yanzu, komai ya bude muna arziki sosai Hamza yayi don yanzu fita yake kasa shen duniya yana harkokin sana,ar shi,
Duk da yana da arxikin shi hakan bai hanani neman nawa ba ni don business nake sosai ban zauna jiran nashi ba nima da taimakon Allah dana Abban na mike yanzu sosai,inji Allah,
Sai dai sam hakan bai hana hamza ya dauke min nauyi duk wani hakkin shi dake akan mu ba,
Komai da ya kamata na miji yaiwa iyakin shi muna samu daga gare shi sosai fiye da tsamanin mu,
Matsala daya shine kullun fitana suke da Biba idan yaje ko kuma ta waya zagi da tonon asiri yana zuwa yana dawowa ko yaushe sai kira mashi azzalumi macuci takeyi wani zuwan da yayi yasamu ta shirya wai zata biyo shi ita bazata zauna ba,
Yakai katanta gurin iyayyen ta suka zo aka zauna suke tambayan ta ko akwai abinda ya rage ta dashi nadaga hakkin aure ne tace da su babu ko daya ita dai kawai bazata zauna ba a jega mu muna can kaduna,
Sai da kyat akasamu tayi hakkuri ta zauna sai dai ashe ba har cikin ranta ba, bayan tafiyan shi da kwanaki ta shirya tai shatan mota sai kaduna,
Baya gari ni mun dawo daga uguwa ke nan da Fatima naga mota ana masu nune da gidan mu,
Mun kurawa motar ido sai ganin Biba mukayi na tare su da murna tare da karban yarta tayi wayo sai dai da,alaman akwai alolayi a tare da ita muka shiga cikin gida sai wani fuskewa take tana shan magani,
Bingidan da kallo take tana mamakin irin kyau gidan da muke cikin shi na bata ruwa da abinci amma sai ce min tayi ki barshi kawai nuna min part dina nakai kayana aciki,
Nace tau Biba problem anzo ke nan wata sabuwar fitina takawo kai kuma ke nan a gidan,
Nace cikin dakewa amma dai ni maigidan bai nuna min part din dake dasu nan ki a gidan nan ba gida dai yace na Aisha ne da yaranta tace wanan kuma fadi ne wallahi kada ki manta cewa gida namune ni dake don gidan mijin mune ba na Ubanki ba,
Nace tau harda zagi kuma haka Habiba tace koma may ye dai bakinki ya saba da cewa mijin mu,
Ban bi ta kantaba na bata wani daki tagyara shi tsab ta shiga da yar ta,
Bayan kwana biyu ina jin kamar na bar gidan yadda Biba ta azazzaleni nida yaran don ma mama tana sa mata waigi ga wani abin,
Da dare muna falo ya bugo waya a lokacin yaran sun dauko yarinyar sai kuka take don bata saba dasu ba,
Yake tambayan wake kuka haka hussaini ne ko hassan nace a,a mama kara mace ke kukan kiuyya,
Yace wacece kuma mama karama din nace a,a mama dai mana mai sunan mama hafsi, yace what ,
Nace ai suna nan yau kwana biyu ke nan sai naji ya kashe wayan dip ba shiri,
Koda na kirashi akece min wai bussy yake bani samun shi don haka na kayale shi sai dai ina mamakin ke nan yana nugin bai san da zuwan su bane ko may wai,

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login