Showing 291001 words to 294000 words out of 299981 words

Chapter 98 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17650

uban da zaibar yar shi a cikin wanan halin batare da,daukan mataki ba,
Yakamata wanan abinda yafaru ya zama maki ishara ki gyara halinki ki taimaki zurian ki daga shaguben yan gari, hakana,
Yanzu mutanen da Ibrahim ke neman dutar su daga nan nefa aka kwashi gulma aka kai masu har can kano,
Ni yanzu ai sunana ya riga da yayi kauri an azamin sheri da banji ba bangani ba a cikin gari,
Sunyi wa Hamza bayani duk yadda sukayi da iyayyena shima rokon Umma yayi da ta yafe mai kuma yana rokon ta da tazama mai kama kan ta ga yaran zamani don abinda Biba tai mata baiji dadin shi ba gaskiya,
Ya dai mata dan nasiha yadda ya kamata tsakanin da da mahaifi yai masu sallama yatafi abinshi yana maijin dadi a ran shi,
Ya koma gurin su Baba sukai mashi nasiha akan hakin iyayye dana iyalin shi yai masu godiya sukace ranan jumma yazo ya dauke mu mukoma gida tunda komai yawuce sai dai a faki gaba kawai,
Yai masi godiya akan kokarin da sukai mai kuma yakara ba Baba Mudi hakkuri kan sakacin da yayi na,rashin rike amanan daya bashi na Aisha dakyau ta sanadiyar mahaifiyar shi,
Baba yace mai aikomai ya wuce don haka afaki gaba kawai Allah ya tsare,
Mota ya dauka shata hargida tare da,alheri akai su Baba na har garin mu,
Mama hafsi ce taje gidan ranan alhamis tagyara ko ina nagidan don rashin mace a gidan yasa gidan yai kura sosai,

****** ********* ******
Washegari jumma,a kamar yadda,akai alkawari su mama na Rahana da mama saude da Atika suka rakani gida inda muka samu angyara ko ina dakunan mu dake rufe ne kawai ba,a gyara ba a gidan, don haka Madina ta shiga gyaran dakin ina falo dasu mama suna kara bani magana da zasu tafi ne Hamza yaba Ibrahim alheri ya basu,
Bai shigo gidan ba,sai wajajen tara nagida muna daki dayarana sai faman surutu mimi ke min cikin jin dadi ganin na a gida,
Tsaye yake daga kofan shigowa dakin hannayen shi zube cikin aljihun rigar shi yana mai kallon mu cikin murmushi sai dai har lokacin da,akwai alaman damuwa a tare dashi,
Sannu da zuwa nai mashi cikin yar siririyar murya da bata da karfin sauti ya amsa yana karasowa gare mu,
Zama yayi a bakin gadon hakan yasa madina dake dauke da Hassan mikewa tana cewa su Jidda suzo suje falo tare,
Bayan yaran sun fitane nani yai ajiyan zuciya yana cewa Humaira idon ki ke ga,
Nadago kai a hankali inace mashi may kuma nayi yai murmurshi yace a,a baki komaiba,
May yasa kika azabantar dani haka a,rayuwana Humaira na dauka ko da nine nai maki laifi bazaki iya min wanan horon ba haka ,
Ashe ban sani ba yadda na daukeki ke baki daukeni haka ba gaba daya kika haramta min koda jin muryan ki ne balle ganin ki why Humaira why zaki min wanan irin hukuncin haka Humaira na,
Kin san cewa kinzama pary din rayuwana yanzu sosai fiye da duk wani mahuluki na duniyan nan,
Amma sai kika biyewa su Baba aka barni maraya ina gararanba a cikin gari ba mai taimakona sai Allah dana dogara dashi,
Murmushi nayi nace kenan yanzu laifina ne zakagani banaka ba ko yace dane maki may Humaira ?
Nace yanzun dai ai zancen ya wuce Allah ya,tsare gaba yace amin tare da mikewa tsaye daga zaunen da yake yana cewa ina rokon alfarma azo a hada min ruwan zafi please nai wanka ko zandawo normal Hamza na,
Nace da ba normal kake ba kenan yace aikema kin sani don rabin raina bata tare da ni ,
Yafara tafiya yana cewa zan shiga don duk a gajiye nake wallahi nace gani nan tafe ai,
Nasamay shi yana rage kayan jikin shi ina shiga dakin zan shige bathroom ya jawoni zuwa jikin shi ya manne ni sosai da jikin shi a kunne na yake min magana kamar rada yana cewa,
I miss you my Humaira miss you alot my dear lovely wife why kika haranta min kaki haka da yawa please,
Kokarin kara shige min a jiki yakeyi yana min wasu maganganu a kunuwa na wanda kunne na bazai jure sauraren su ba,
Kiss yafara kaimin yana cewa a hauka ce humaira ki taimakeni kada ki kara guje min please humaira ki yarda da ni don Allah humaira,
Yaso yaci galabata a lokacin amma sai nai dabara da kyat na zille mashi nabarshi sabale da hannayen shi gurin a tsaye,
Sai da muka ci abincin da mama hafsi nasamu ta girka mu na muka koshi yaran suka fara barci daya bayan daya,
Sai a lokacin na samu na shige dasu daki nai masu addua nadawo gare shi,
Ranan kamar zai lashe ni gaba daya zakace a ranan yafara sani na diya mace a,rayuwan shi don ni kaina saida nai mamakin wanan kaunar da yake min haka,
Sai da komai ya lafa a tsakanin mune kowan mu yana mayar da numfashi sai naji yace min Humaira cikin wani murya mai sauya yani na amsa mashi da na,am yayana,
Yace don girman Allah daga yau ki rike ni amana a,rayuwan ki kamar yadda zan rike ki kema amana a,rayuwana,
Aisha Humaira ki yarda dani don Allah ki amince dani don bazan barki ba komai dadi komai wahala,
Nace ni yaya bakai min komai ba halin Umma daine ya bani tsoro har na dauki wanan matakin haka shiru naji yayi maimakon yayi magana sai naji sheshekan kukan shi kawai yana tashi,
Rudewa nayi hankalina duk ya tashi don irin kukan da yaya yakeyi bana wasa bane,
Nace cijin rudewa don Allah yaya ka daina kukan nan haka please yace cikin kuka Aisha dole ne nai kuka don nasan in har Umma bata daina halinta ba akanki zan iya raski wata rana don irin sharuddan da su Baba suka sa a tsakanin mu,
Nace yaya indai nice zan fada masu insha Allahu bazan kara bari su sani ba zan yi kokari na zauna da duk halin Umma nayi hakkuri don kai,
Ya jawo ni jikin shi ya manne yana sauke nufashin kukan shi yana cewa tare da matseni a jikin shi nagode Humaira nagode da kika fahinci matsalata har kika amince min da bukatana a gare ki,
Don haka na yanke shawaran barin garin nan da ku baki daya don kara gujewa fitinan umma nan gaba,
Da sauri nace zamu koma ina kuma yaya yace kaduna nake son komawa mu zauna a can don komai nawa zan mayar dashi can don haka zaifi muna sauki,
Nace amma kana ganin Umma zata yarda kayi nisa da ita haka a cikin sauki,
Yace cikin dan murmusawa tare shafa min kaina da yaji kitso kanana yace, yarda ya zama dole a gareta tunda haka shine mafita gare mu,
Nace to Allah ya kyauta yasa hakan shi yafi zama alheri a gare mu baki daya yace amin tare da sa hannayen shi duka biyu ya rugumoni dasu cikin jikin shi haka barci ya dauke mu sai can cikin dare naji madina tana buga kofa wai Hussaini yana kuka ,
Zare jikina nayi cikin nashi sai naji yariko ni zuwa jikin shi yana cewa bari na karbo shi kawai,
Shi ya tashi yakarbo yaron na fara bashi nono dama shi acicine muna cewa yabiyo baban shi Jibrin,
Washe gari na kara tsabtace gidan tako ina muna zaune na kalli kofan Biba sai ta fado min a rai nace ko yaya matsayin auren su yake da ita yanzu oho,
Na tuna da fitan nan ta na kadavkaina kawai nace a raina kai Biba Biba problem ce wallahi tazo kawai ta yamutsa muna gida gaba daya don son kai irin nata,
Da zata zauna mu fahinci juna muyi zaman lafiyan mu da duk haka bsi taso ba amma ina ita gurin ta kawai ahine ta zauna ita kadai a gidan batare da wata mace ba,
Niko nasan haka ba zai samu ba agare ta don na riga na ga yiwa zuciyar hamza barna ko ba yadda zai rabu da ni don ita don hakkuri da kawaici baibar komai ba a duniya,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,,,,,,



Iyayen Biba har gida suka tasa keyan ta gurin Umma ta roke ta garafa amma sai shi gogan yakafe ba zai mayar da ita ba duk ta jemay ta shiga tashin hankali lokaci guda ta sauya baki daya,
Da kyat da sudin goshi ya yarda ya mayar da ita bayan su Baba Madu sun sa mashi baki dole ya hakkuri ya mayar da ita amma da sharidin bata kara tayar mai da fitina a gidan shi,
Haka ta dawo tsamo tsamo da ita daga ita har yar ta suka dawo kamar sunyi jinya,
Tunda tadawo ba wani daga kan da takeyi a baya irin na farko sai zaman lafiya da mukeyi da ita yaran mu kuma mun hada su guri guda komai tare ake masu,
Mun shirya tafiya gurin mahaifina tare dasu Baba na Sahabi da baba liman da,sauran yan uwa a bisa jagorancin Hamza zai kaimu,
Tafiyan kwana da yini muka isa garin da yake don zuwan bazata mukai mashi yai matukar mamaminganin mu,
Nan mutanen garin duk da basu jin hausa haka sukai ta zuwa ganin mu natafi duk da yarana hudu harda Madina da mama hafsi, don ta taimaka min da daukan yara,
Bani ba har su baba sai da suka tsinke don ganin irin daulan da Abbana yake ciki,
Shiko don murna ya rasa inda zai samu fon dafin dayake ji saboda dama mutanen garin suna mashi gori wai baida,asali amma yazo kasan su yafisu kudi,
Matar shi fara ce amma ba sol ba doguwa siririya da ita da yaran ta biyu mace da na miji kamar yadda Abba yace muna,
Da farko bataso zuwan mu ba amma sai na lura tana tsoron Abba sosai inajin fada yai mata sai ta dan fara sake jikin ta damu kadan,
Kwana biyu su Baba sukayi suka barni a can don zan kwana biyu gurin Abba kamar yadda ya roko yai masu goma ta arziki suka dawo,
Zaman mu gurin Abba bazan iya cewa ga irin dadin da mukaji ba don ya nuna min so da kauna sosai a fili har matar ta,shiga nuna kishina a fili,
Sai dai wani ikon Allah yaranta sun shaku dani sosai ko yaushe suna gurina ba hausa suke jiba amma haka muke zama muna gwalanci da junan mu tunda ba turanci ake a kasan ba,
Sannu sannu matar ko may tagani ta dan fara sake jiki dani har muna zama mudan yi hira da ita takaini har gurin yan uwanta suka ganni amma ban yarda naci komai nasu ba don duniya abin tsorone yanzu,
Satin mu uku Hamza yazo yadauke mu yai min shatara na,arxiki bani ba harda mama da ta rakani ta samu rabon ta sosai,
Dinkunan mutanen kasar da shaddan su sai da Abba yai min akwati biyu na dinkakkakun kayan su na can,
Kudi masu yawa yabani idan na dawo nayi sana,a dasu tun acan nasaro zannuwa mutanen kasar na shigo dasu Nigeria, da sauran abubuwan bukata yai muna rakiya har iyakar kasar dashi da mutanen shi,
Mun dawo gida lafiya da gajiya a jikin mu mama a gidan mu ta sauka don yanzu na gane dadin ta sosai saboda tsakani da Allah take kula min da yara hakan yasa na roke ta tazauna damu don nadan samu saukin lalurar yarana, agurin ta,
Biba bataso zaman mama da mu ba amma ba yadda zatayi dole ta hakkura aka zauna ba mai tsagwaman wani na ciki na ciki,

****** ********* ******
Ya gama duk wani shirin barin garin da yai niya duk da baso ba don ni a gani na ai komai ya wuce ko ga kowa,
Ina zaune nadawo daga Birnin kebbi duban wani shago da aka bude min a can na kayan kitchen equipment, na mata sauran abubuwan gida na matan zamani,
Yara sun rufe ni suna son nabasu tsaraban da nazo masu dashi daga can,
Sallama akayi wasu matane su biyu suka shigo sai da suka zauna na sheda mama Sa,ace kawar Umma dayar na kalla da kyau nagane Sadiya ce da goyon ta,
Gaisawa mukayi dasu na katbi goyon nata ina cewa sannun ku da zuwa nace madina takawo masu abinsha,
Drinks da ruwa mai sanyi takawo masu Sadiya sai bin gidan da kallo takeyi tana sauke ajiyan zuciya,
Mama Sa,a ce tafara magana da cewa Hajiya Aisha gurinki mukazo nace tau mama gani ai ina wasa da hannun yaron da ke kukan kiyyau ,
Mama Sa,a tace hajiya da farko muna baki hakkuri kan abinda yafaru a baya don Allah kiyi hakuri ki yafe muna,
Nace kai haba mama ai rayuwan zamane haka abin yake ni ban rike komai a raina ba tace gaskiya don gashi ai naga kin tare mu da mutunci don bamuyi zaton samun haka ba agurin ki,
Ta gyara zama tana cewa dama hajiya munzo don Allah ki taimake mu yadda Allah ya taimake ki ki taimaka muna yau satin Sadiya uku ke nan da zuwa amma mun kasa samun kufin motan da zata koma don wallahi abin duk ya kakare muna baki daya,
Nace a ina Sadiyan take ne yanzu tace tana aure ne acan cikin kauyen niger a wani garin nufawa fategi,
Gashi kwanakin da mijinta yaba ta shanyesu harda dori shine muka ce bari dai muzo gurinki ko zaki taimaka muna don Allah kiyi hakkuri ki taimake mu na samu takoma dakin ta hakana,
Kafin in yi magana sai ga Hamza ya shigo gidan a lokacin Biba da,ta tashi da barci take ce min ashe har kin dawo ne nace mata eh ai na tambayi yara sukace min kin dan kwanta,
Sannu da zuw muke mashi inda yake ce min yanzu nake tunanen ko kin dawo sai da nazo naga motar ki a,waje nasan kin dawo, cikin nuna so da kauna yake min magana,
Nace ai na samu an hada komai dubawa nayi da dan masu gyara kawai sai na juyo don nabar wa yan nan gida kada su dami mama da kuka nono,
Yace ai da gangan kika barsu a gida don kin san halin su da kiuya sosai, yace ai gobe insha Allahu zan shiga naga yadda akayi nima

Zai shige nace mashi affa yaya gasu mama fa da Sadiya sai lokacin ya waigo yana cewa wata Sadiya ke nan fa,
Cikin mamaki nace mashi Sadiyan mama Sa,a sunzo ne su gaishe mu don Sadiyan zata koma garinsu inda take aure yace mungode,
Ya juya inda suke suna gaishe shi ya amsa cikin daure fuskan shi tamau dashi kamar bai dariya a baya,
Ya shige dakin shi nan nake nunawa Biba Sadiya nai mata bayani cewa kishiyata dasuka rabu da yaya a baya,
Wani kallon raini tai masu tace Umm,wummm, kawai taci gaba da harkokin ta tashi nayi nabi bayanshi dakin shi yana tsaye yana rage kayan jikin shi nashigo dakin nace,mai,
Idan kana da wani abu kakawo a basu sai na kara masu wani tsawa yadaka min tun ban karasa zance naba yace wai may yasa Aisha baki san ciwon kanki bane har yanzu,
Matar da taita kulla muna sheri da makirci iri iri shine yau zata wanko kafanta tashigo min gida,
Wai yaya ma kika bari suka shigo min gidane wai harda zama sukayi fa don sunga ido a gurin ki,
Nace haba yaya ai ko don albarkan haihuwan da kukayi tare taci na basu fuska ko,
Wani kallo ya,watso min na shekeke yace haihu haihuwa dawa ke kika,san wanan ni hada min ruwa na watsa kinji ban iya ramay ramay ki kinji,.
Nace haba yaya taimako ne fa zamuyi amma kace wani abu yace ai ban hanaki ba je ki taimake su ke amma bani hamza ba dan matsiyata,
Duk yadda naso ya fahince ni yaki yada shigewa ma yayi bathroom din yabar ni tsaye gurin,
Nafito dakin rai a bace sai dai nadan kirkiro dan murmushi a fuskana don kada su gane bacin raina,
Idon mama Sa,a a hannu na taga ban fito da komai sai tai murmushi yake nace ina zuwa mama daki na shiga na dauko masu turmi biyu cikin na,sayarwa na da kudi dubu goma nakawo masu nace mama ga
wanan kuyi hakkuri kun samu banda kudi a gida yau weekend ne,
Su ka karba suna ta min godiya nace babu komai ai nan su kai muna sallama suka mike zasu tafi sai ga mama tafito da hussaini a hannun ta tace a,a yau Sa,a kune agidan dan nawa kuma,
Tana murmushin yake suka gaisa ta juya tana cewa zasu tafi don tasan mama zata iya sake mata layi yanzu,
Nai masu rakiya har kofan gida ina ma Sadiya Allah ya tsare hanya idon ta ya canza kalla da kyat take amsa min suka,tafi,
Suna batin gidan tace cikin muryan kuka mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login